Showing 15001 words to 18000 words out of 72718 words

Chapter 6 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt

16 Dec 2024

2290

tunda ba mata bane ku,
suka rufe kwanon danwaken suka mike sukayi sallama da hajja da ma'u,, sun kusa da kofar fita kausar yar suwaiba tana rarrafe a tsakar gida tsirara ta mike ta rike wani abu tana dabo ta fetso kashi saura kaďan ya taba wandon Affan,
da gudu suka fita jabeer na mishi dariya harda rike ciki yana tayashi dubawa ko ya taba wandonshi, dakyar ya karasa gida yana masifa ya wuce bayi saida yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito ya shiga ďakin mahaifiyarshi,
zaune ya sameta tana waya ya zauna kusa da ita, sai da ta gama wayar ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace daga ina haka,
yace gidan maman jabeer, tace ya jarabawar kun gama ko, yace mun gama umma sai dai ayi mana adduar samun nasara,
tace addua kullum yinta akeyi Affan, saidai a ďaura, ni dai ina kara jaddada maka ka rike ibada da karatun qur'ani da tsoron Allah wadannan abubuwan in ka rikesu sun isheka duniya da lahira,
yace in shaa Allah umma, Allah ya kara mana karfin imani, tace ameen,
ya mike zai fita kenan Asiya ta shigo da sauri,
tace ina wuni umma, zeenatu tace lfy lau dan asy, ya na ganki haka,
tace ummi ce tace in zo in fada miki anty ma'u ta haihu yanzun nan tana can gidan ma,
da sauri zeenatu ta mike cike da murna tace me muka samu, asiya tace nima ban sani ba,
ta dauko hijab ďinta suka fita da sauri a ranta tana adduar Allah yasa zaunanne ne abin da ta haifa,
tun kafin su shiga ciki kukan yarinyar ke musu kuwwa cikin kunne,
kuka takeyi irin na jarirai da iya karfinta wata nurse a unguwar tana gyarata,
Affan a kofar gida ya tsaya dan yana tsoron ya shiga ya kara arba da kausar dan bai sani ba ko wannan karan a jikinshi zatayi kashin,

A cikin gida kuwa murna sukeyi lokacin an gama kimtsasu anyi ma mai jego allura tana kwance tana hutawa,
duk makota anata shigowa tayata murna banda suwaiba da tace meye na barka a gurin gawa, mudai je zuwa nan da anjima itama zata bi layin yan uwanta su cike su bakwai,
karaf wannan furucin na suwaiba ya shiga kunnen jabeer, hararta yayi ya mikama mamanshi babyn suka fita shida Asiya, a kofar gida suka hadu da affan suka wuce gidansu..


Anyi suna dai2 na masu rufin asiri,
mai jego ta samu kaya da kudi masu yawan gaske haka mahaifinta ya samu kudi sosai haihuwar tazo mishi da goshi, jaririya taci sunan Hajja "Hajara" Abida tace a dinga kiranta da "AFEEYAH", suwaiba kuwa bakin ciki kamar zai kasheta da taga har kwana bakwai jinjira na raye ga kaya da kudi da uwarta ta samu kamar za'a bude shago dasu, sam ta kasa boye bakin cikinta har saida sukayi fada da Abida ta gaggaya mata bakaken maganganun da yasata shigewa ďaki ba shiri dan Abida ba kanwar lasa bace itama...


Tun daga lokacin kullum sai suwaiba ta kasa kunne ko zataji kururwar mutuwar jinjinra amma shuru takeji ga jinjira har ta wuce wata bakwai kullum cikin koshin lafiya,
Afeeya ta taso cikin kulawar mahaifiyarta da kakarta hajja, yarinyar duk wanda ya ganta sai yayi sha'awarta saboda kullum a tsaftace take kan nan nata baya rabo da kitso da ribbons saboda tana da yalwar gashi, gata yar lutuya goyonta gunin ban sha'awa, saidai fa akwai azabar kuka da masifaffen kwuiya, banda mamarta da hajja babu wanda take yarda ya ďauketa a duniya sai jabeer, shima dan tana ganinshi kullum a dakinsu kuma yana fita da ita yawo,
sam bata yarda da affan dan ko ya miko hannu zai ďauketa in ta soma tsala ihu bata taba yin shuru har sai taga baya gurin, wannan dalilin yasa kullum ya shiga gidan sai yasan yadda akayi yasa ta kuka ta hanyar daukanta ta karfin tsiya,,
Afeeya na da shekara biyu jabeer yasa babanshi yasata a makarantar da suke zuwa lokacin suna js2, dakyar ma'u ta yarda dan gani takeyi kamar wata hidimar ta ďaura musu,
tare suke zuwa makaranta in sun dawo ya wuce gidansu da ita sai can yamma yake mayar da ita gida, duk wani kuďin break da ake bawa jabeer akan afeeya yake karewa,
gata sosai takesha gurin yan samarin biyu duk da har lokacin bata cika yarda da affan ba,
salma da farida ba karamin tsanarta sukayi ba, in suna cikin mota ta kallesu sai su sakar mata harara,
turo baki takeyi a tsiwace irin na yara itama ta rama sai tayi lamoo a jikin jabeer ta runtse idonta dan kar su daketa,
haka a skul ko takata yaro yayi bai sani ba ko yafi karfinta sai ta bishi ta rama in ya daketa taje ta faďa ma jabeer, in kuma tafi karfinshi to ta samu nama dan sam bazata raga mishi ba....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah


★ bayan shekara 6★


Jabeer ne ya fito daga makarantar (buk) cikin motarshi "vibe pontiac" da L a jikinta saboda har lokacin bai kware sosai ba,
waya sukeyi da Affan da ya tafi karatu egypt wata uku da suka wuce, hira sukeyi sosai cikin jin dadi da kewar juna,
saida yayi parking dai2 skool din su Afeeyah sannan sukayi sallama,
can ya hangota cikin yara suna dambe ita da wata yarinya yara na ihu suna musu waka,
da sauri ya karasa gurin ya raba fadan ya riketa tana kuka saboda yarinyar tafi karfinta karfin hali ne kawai irin nata,
fisge2 ta shiga yi ita dole sai an barta ta buga ma yarinyar dutse,
tsawa jabeer ya daka mata ya rike hannunta da karfi yace wuce mu tafi ko in zaneki a gurin nan,
ta kalleshi cikin mamaki dan bai taba mata magana mai karfi ba bare tsawa, yace baki ji abinda nace bane,
ta saki wani razanannen ihu tana buga kafa tana kuka sosai kamar wacce ake yanka ta,
tsaki yayi ya ďauketa tana tirjewa ya turata cikin mota, Safna kawarta ta miko mishi school bag da L.B dinta yasa aciki ya zagaya ya shiga,
dago kanta tayi tana kuka ta hango wasu yara suna mata gwaloo,
haba nan ta fara kicin kicin bude kofar tana bugawa tana ihu kamar zata tsaga motar,
kashe motar yayi ya janyota jikinshi yana rarrashinta tana zillewa,.
dakyar ya rarrasheta yace ta faďa mishi abin da ya haďa su, kumburo baki tayi tace dukana tayi wai dan ban sani ba na yaga mata littafi shine har da cire min beets din da mama tasa min, kuma taja min gashi da karfi,
murmushi jabeer yayi dan yasan tana sane ta yaga littafin yace banason karya fadamin gaskiya tsokanarki tayi kika yaga mata ko? ta turo baki ta gyaďa kanta, yace nasani ay,
kuma shine dan rashin gaskiya kika fito kuna dambe ko, bana hanaki faďa ba? idonta ya fito waje tace to ay sune suke fara neman fada na,
ya zaunar da ita kan kujera ya tada mota yace munyi faďa yau babu ruwana dake, dama na siyo miki cake kuma na fasa baki,
ta rike mishi hannu tana kuka tace zan daina,
yace bazaki daina ba kullum haka kike faďa, ta kwantar da kanta kan hannunshi tace Allah zan daina gobe, yayi dariya yace to naji in kika kara me zan miki, ta boye fuskarta tana dariya tace hakuri zakayi mana,
ya kwashe da dariya yace yarinyar nan kin raina ni da yawa, yaja motar suka wuce..
Tsayawa yayi ya siyo ma Ma'u dake fama da ciwon 'koda' tun wata biyar da suka "fruits da rake" dan shi take yawan sha ance yana wanke infection din 'koda', sannan suka wuce gida,
Tun kafin ya kai kofar gidan ya hango cikowar mutane, karasowa yayi jikinshi a mace yayi parking a gefe can ya hango maza sunata alwala ana jimami,
bai bi takan fruits din da ya siyo ba ya dauko schl bag da lunch box din Afeeyah ya kama hannunta zasu shiga ciki, ta dinga waige2 tana cewa yaya jabeer baka dakko ma mama raken ba,.
bai kulata ba ya jata suka shiga ciki, a tsakar gida ya tarar da taron mata cikin hijab kowacce tayi tagumi, dakin Ma'u ya shiga nan ya tarar da tashin hankali,
kallon mutanen dakin yakeyi ya karasa kusa da mamanshi yace ummi me ya faru, ina mama,?
Abida ta share hawayenta ta nuna mishi ma'u kwance cikin likkafani, matsawa kusa da ita yayi da sauri ya bude fuskarta ya fashe da kuka sosai yana kiran sunanta,
Afeeya ta matso kusa dashi jikinta a sanyaye ta rikeshi itama tana kuka, rungumeta yayi sunata kukan da ya kara sa mutanen gurin kuka, Abida cikin kuka tace ya tashi ya wuce gida,
kin tafiya yayi ya haďa Asiya da Afeeya suka wuce gidansu shi kuma ya zauna akayi mata sallah tare dashi aka kaita gidanta na gaskiya,,
mutuwar ma'u ta girgiza jabeer sosai saboda ba karamin shakuwa sukayi ba, ita taci kashin shi tun yana karaminshi har yasan kanshi saboda mahaifiyarshi ba mazauniya bace..


Tun daga lokacin rikon Afeeyah ya koma gurin hajja dama acan take rabin zamanta ko sanda mamanta ke da rai,
jabeer kuwa wata sabuwar kulawa yake bawa Afeeyah wacce take mantar da ita rashin uwa,
gaba ďaya ya daina mata faďa kuma ya hana kowa yi mata faďa,
ko an kawo kararta saidai ya basu hakuri yace ay yarinyace, sosai ya shagwabata, basu rabuwa ko da na kwana ďaya ne in kuwa tafiya ta kamashi in har ya tafi to ranar ba cin abinci babu bacci, wani lokaci ma har ciwo takeyi, shiyasa yake tsoron duk wani abu da zai sa yayi tafiya ya barta,
haka su zeenatu da Abida ba karamin kula sukeyi da ita ba dan sun ďauke mata komai duk da malam atiku shima yana iya kokarinshi yaga ya debe mata kewa, suwaiba kuwa mutuwar ranar ne ya taba ta amma anayin uku shikenan ta sake tama manta da wata ma'u a rayuwarta, ganin Afeeyah da kuma jarabar rashin hakurinta su kadai suke tuna mata da ta taba yin kishiya...


Mrs tijjani shattima..
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Yar Kyakyawar budurwa ce zaune cikin bakar doguwar riga mai adon jaa a parlon ummi,
duka shekarunta baza su wuce 14 ba amma in ka ganta zaka rantse ta kai 16 saboda kayataccen jikin da makerin yammata ya fara kerashi,
bazan iya fadin kyawun fatarta ba saboda ya zarce misali, ita dai ba fara bace kuma sam bata dauko hanyar bakake ba,
wani irin colour ne mai daukar hankali wanda yake shan gyara da mayuka masu tsada, manyan idanuwanta da ďan hancinta da bai cika tsawo ba su suka kara ma fuskarta kyau, bakinta dan dai2 mai cike da masifar tsiwa,
gefenta Amirah ce yar shekara 11 zaune sun maida hankali kan TV suna kallon series a mbc bollywood,


kwala kiran Amirah ummi tayi zata aiketa gurin zeenatu (umma), Amirah ta fara kunkuni kamar zatayi kuka dan bata so film din ya wuceta,
gwalo Afeeya tayi mata ta cigaba da kallo,
Amirah taja tsaki tace wallhy zan kashe kowa ya huta kuma in gudu da remote din,
Afeeya tace yi hakuri meerah je ki dawo zan baki labari, ki gaisar min da masu suffar samudawa,
ummi na kitchen dariya ta kufce mata da karfi tace su waye kuma masu suffar samudawa,?
Afeeya ta toshe baki tace ummi Amirah ce ta faďa,
Amirah tace nagode Allah da ya banbanta muryata da taki da ba karamin bomb zaki dinga haďa min ba,
Afeeya tace ummi taki tafiya fa tana tsaye tana kallo,
ummi tace to ke amsa kikai kinji yar albarka, kice wai ina gaisheta,
Amirah ta fara rawa tana mata gwaloo, Afeeya tace dan Allah rakani muje,
Amirah tace wallhy ke kadai zaki tafi,
ummi tace bana fa son iskanci in bazaku ba ku bani in shiga da kaina,
Afeeya ta ďaďa ma Amirah duka taja gyalenta ta ďaura kan gashinta da yayi tutsu a tsakiya,


Da bisimillah ta shiga gidan dan Allah yasan ta tsani ganin su fareeda dan basa ga maciji ko kadan,
parlon ta wuce ta dinga sallama taji shuru ta wuce ciki ta murďa kofar dakin umma haďe da sallama, tana sa kai ciki sukayi karo sosai da Affan wayarshi ta faďi kasa,
baya taja da sauri rike da kanta tace washhh Allah kaina,
kai baka san mutum zai shigo bane,
ya tsuguna ya ďauki wayarshi yace saboda idon mudubi gareni da ke hasko min abinda ke waje ko,
ta turo baki tabi ta gefenshi zata wuce ya tare kofar yana kallon cikin idonta yace baki iya bada hakuri ba ko, ta sakar mishi harara tace kai zan tambaya wannan tunda ni ka bige ma kai kuma har yanzu zafi yakemin,
yayi murmushi yace lallai yarinya zaki kwana anan dan bazaki taba wucewa ba sai kin bani hakuri, tayi dan guntun tsaki ta juya ya maza ya janyo hannunta ya matseta sosai numfashinsu na gaurayuwa,
runtse idonta tayi tace ka sakeni in tafi, bin ko'ina na fuskarta yakeyi da kallo yace ina zaki,
a tsiwace tace ina ruwanka dalla ni ka sakeni ko inyi maka ihu,
yayi dariya yace bakinki a bude yake ay go ahead, ya ďauka wasa takeyi yaji ta saki ihu da karfi,
da sauri ya saketa ya koma baya a zuciyar shi yace wannan wace irin yarinyace,
da gudu zeenatu ta fito tana waige tace Afeeya me ya sameki, ta ruga bayanta tace wancan ne ya bige min kaina kuma wai sai na bashi hakuri,
zeenatu ta kalleshi tace zanci maka Affan ba gurin jabeer kace zaka ba,
yace wallhy umma karya takeyi sai yanzu ma na gane afeeyah ce, ya harareta yace jarababbiya kawai, yasa kai ya fita yana mamakin irin girman da afeeya tayi,
gurin aikin jabeer ya wuce dan ya kosa ya ganshi rabon da su ga juna tun da ya tafi egypt dan ummanshi ta hanashi dawowa hutu saboda lafiyarshi dan ita kanta a ďarare take a gidan saboda yadda oyiza ke hurda da wasu mutane a cikin gidan da kuma yawan mafarke mafarken da takeyi akan oyizar da ďanta, ga alhj basheer ma sai yadda tayi dashi,


Sunyi matukar farin cikin ganin junansu dan jabeer ma gurin aikin ya bari suka fita yawo sunata hirar yaushe gamo,
sai gurin karfe 5 na yamma suka dawo gida,
gidansu afeeya jabeer ya sauka dan tun safe bai ganta ba kuma yasan tana can ta damu......


Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah


A daren ranar da Affan ya dawo suna zaune a parlon dukkansu har su salma da suka ri'ka a gida ba aure,
zeenatu dai na ďakinta dan ko tazo ta zauna cikinsu to fa takaici zai sa ta tashi ta koma daki saboda alhj basheer ko kallonta bayayi,
hira sukeyi shi da Affan saboda farin cikin ganinshi, duk irin hararar da oyiza take mishi baisa ya daina hira da ďanshi da yakejin kamar shine ma ranshi gaba daya, mikewa yayi yace ina zuwa affan je ka ce ma ummanka tazo,
Affan ya tashi yaje ya kira zeenatu, dakyar ta yarda tazo dan bata san dalilin kiran ba, wasu takardu ya fito dasu masu yawa yana mikama affan daya baya,
yana gama mika mishi yace kasan takardun menene wannan,
Affan ya girgiza kanshi, alhj basheer yayi dariya ya kalli zeenatu da oyiza yace ku zama shaida na malakkawa Affan company na na lagos dana nan kano,
sai kuma estate dina na Abuja da gidana dake nan Nasarawa, wannan kyautar da nayi wa Affan ba wai dan yafi sauran ya'ya na bane, a'a sai dai dan shine namiji kuma nasan ko bayan raina zuri'ata bazata taba shiga cikin kunci ba in dai Allah ya tayashi riko da duba dukiyar, ya kalli salma da farida yace ku mata ne, kuma aure zakuyi, dan haka duk wata kyauta da zan muku bazata yi wani tasiri a gurinku ba saboda karkashin wani zaku tafi,
wata rana Affan shi zai zama uba a gareku,,
wayyo zan so ku hango min oyiza a wannan lokcin,
kiriss ya rage zuciyar ta buga saboda alhj basheer ya kyautar da duk wata muhimmiyar kadararshi ga affan, shuru kawai tayi jikinta na fitar da zufa, a zuciyarta tace hmmm maiyi baya faďa wannan karan ka kaini bango alhj,
mikewa tayi tace ma su salma ku tashi mu tafi, suka mike suka wuce fuuu cikin bacin rai,
zeenatu ta sauke ajiyar zuciya tace dan Allah ka rufa mana asiri, wallhy Allah kadai yasan abinda kyautar nan zata haifar,
yace ta haifar da komai zeenatu, Affan ďana ne ko bayan raina shi ne magaji na, dan haka ki bishi da adduoin neman tsari kawai,
tace to Allah ya tsaremu da tsarewarshi, ameen yace sannan suka cigaba da hira yace ma affan ya tashi yaje ya adana takardun, Affan ya mike yana jujjya takardun ya wuce ďaki ya bar iyayenshi na hirar da suka daďe basuyi ba...


Tun safe jabeer ya fita da Afeeyah da Ameerah yawo, duk guraren shakatawa da wasannin dake cikin garin kano saida suka je, a shop rite suka tsaya yayi musu siyayya suka fito a gajiye zasu shiga mota,
wata kyakyawar farar yarinya suka hango ta tunkaro su tana dariya,, rufe mota jabeer yayi yana dariya ya karasa kusa da ita yace "Nadiya Lameeďo" idonki kenan, tayi dariya tace kai zan ma wannan tambayar Jabeer, ya kake?, yace am cool walhy, ya skull ko aiki, tace duka, bani cntct dinka zamuyi magana a waya dan naga sauri kakeyi,, ya ciro card dinshi ya bata itama ta bashi nata sukayi sallama ta wuce,
mota ya shiga ya kalli Amirah dake gaba ya waiga ya kalli Afeeyah da ta cika tayi famm yace juyin mulki akayi kenan,
ke Amirah koma gurinki itama ta dawo gurinta,
Amirah ta buďe kofar zata fita Afeeya tace saidai fa mu zauna tare a baya, amirah tace kaji ko yaya, wallhy tun ďazu nake ce mata ta dawo nan taki,
kallonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login