Showing 45001 words to 48000 words out of 72718 words

Chapter 16 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt

16 Dec 2024

2300

ya mutu shiyasa shegen bakinta ya mutu,
oyizah tace ai ko shugaban kasa ne ya tsaya mata bata isa ta min ba bare wannan tsinannan yaron mai shegen girman kan tsiya..


Afeeyah ta yar da mop din hannunta ta runtse idonta zuciyarta na tafarfasa,
muryar salma taji a bayanta cikin isa da gadara tace
kee..
je kiyi min pepper soup mai yaji sosai yanzu nan ki kawo min,
Afeeyah bata juyo ta kalleta ba ta tsalleke ruwan da take mopping dashi ta kama hanyar side dinta,
da sauri salma ta bita tana huci taja rigarta ta baya har saida wuyan ya yage tace ke dan uban--- Afeeyah ta juyo cikin azama ta dauketa da gigitaccen marin da ya hanata karasawa yasata sakin Afeeyah bata shirya ba....


Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah


A firgice oyizah da suwaiba suka yo kan salma dake rike da kunci idonta yayi jajur,
fuskarta oyizah ta ďago tana shafawa ta kalli Afeeyah murya a sarke tace m-ari,
suwaibah ta jinjina kai a munafurce tace tabdijam, lallai yarinyar da tsaurin ido kike, ki kalli girman salma ki dauketa da irin wannan marin,
Afeeyah taja tsaki ta juya zata wuce oyizah ta saki salma ta janyota da karfi tana huci,
ihun da Afeeyah ta saki yayi daidai da shigowar alhj basheer parlon,
da sauri ya karaso yace subhanallahi lafiya safiya, me tayi miki,
oyizah ta saki Afeeyah da sauri ta juyo ta fara hawaye tace alhj ace kamar yarinyar nan ta dubi salma ta tsinka mata mari,
Afeeyah ta durkushe ta fashe da kuka tace dan Allah daddy ka kaini gurin hajja, wallhy kasheni zasuyi, dukana sukeyi kullum, yanzu ma dukana suka gama yi har suka yaga min riga,
dan Allah ka kaini gurin hajja,
kafin alhj basheer yayi magana mahmud dan suwaiba ya shigo rike da kular abinci a hannunshi,
ta gefen ido Afeeyah ta hangoshi cikin muryar kuka tace mamu kai min daki ka dauko kular jiya,


alhj basheer cikin mamaki yace meye a cikin kular nan, Afeeyah tace abincin rana na ne,
alhj basheer cikin tashin hankali yace duk abincin dake gidan nan sai an kawo miki abinci daga gida,
oyizah da ta gama tsurewa tace umm al--- Afeeyah ta katseta da sauri tace sunce abincin gidan nan ba na talakawa bane wai ban saba cin irin shi ba saboda haka kar in taba musu,
oyizah ta sankare cikin mamakin sharrin da Afeeyah ta lafto musu,
alhj basheer ya juya ya kalleta cikin tuhuma tayi saurin cewa wallhy karya take min alhj, ya za'ayi in hanata abinci,
alhj basheer ya kalli mahmud yace kai tun yaushe kake kawo ma Afeeyah abinci, mahmud yace kullum nake kawo mata da safe da rana da daddare,
alhj basheer ya saki salati yace kin kasheni safiya,
kin tozarta ni a unguwar nan, yanzu kowa ya gama sanin sirikata daga gidansu ake kawo mata abinci,
oyizah tace wallhy alhj kar---rufe min baki ya fadi cikin daga murya,
ya dago Afeeyah ya kalli wuyan rigarta yace yi shuru ki share hawayenki karki kara cewa zaki je gida sannan yau ďinnan zan siyo miki komai na abinci ki dinga girkawa kina ci a dakinki,
salma cikin kuka tace daddy marin da yarinyar nan tamin taci bulus kenan,
alhj basheer ya juyo yakai mata wani marin a baki yace in mafaďin magana wawa ne ai majiyinta ba wawa bane,
yaya za'ayi Afeeyah ta iya daga hannu ta mare ki,
salma cikin kuka sosai tace na rantse da Allah daddy ta mareni,
ta kalli Afeeyah suka hada ido ta sakar mata gwaloo hade da murmushi salma ta kara tunzura tayo kanta zata duketa alhj basheer yace wallhy tallahi kika taba yarinyar nan sai na lahira ya fiki jin dadi,
oyizah dai tana tsaye kamar gunki mamakin Afeeyah ya hanata cewa komai, haka suwaiba,
Affan ne ya fito da gudu jin muryar mahaifinshi, rungumeshi yayi iya karfinshi yace daddy ka dawo,
alhj basheer yace na dawo Affan kana nan lafiya ko,
Affan ya noke wuyanshi ya haďe rai yace daddy nayi fushi da Afeeyah bazan kara mata magana,
alhj basheer yayi murmushi yace me tayi maka,
Affan yace batason wasa dani kullum sai su anty salma suyita sata aiki ta goge can, ta goge nan, tayi girki da yawa kuma ita bata ci, kuma sai ta rufe kofa ta hanani shiga inyita bugawa taki buďewa,
alhj basheer ya harari salma da oyizah sannan ya kalli Afeeyah yace meyasa bakya bude mishi kofa,
oyizah tayi saurin cewa dan Allah alhj kabar maganar nan muje ka huta anjima sai ayita,
alhj basheer bai kalleta ba yace Afeeyah dake nake magana,
Afeeyah ta dago kanta ta kalli oyizah da zufa ya jikata tace daddy saboda shan maganinshi ne na dare, kafin lokacin yayi nayi bacci bana sanin yana bugawa,
oyizah ta saki ajiyar zuciya a hankali..

alhj basheer yace wannan ba hujja bace daga yau ma duk magungunshi ke zaki dinga bashi,
Affan ya kalli oyizah yace mummy wai ita zata dinga bani magani?
Oyizah ta haďiye miyau tayi murmushi tace eh hakan ma yafi, Affan ya kalli Afeeyah yace zaki dinga bani magani dakyau yadda mummy take bani,
Afeeyah tayi murmushi ta saci kallon oyizah tace sosai ma, kasani ma ko in fita iya baka da kyau,
yayi tsalle ya rungumeta yace to muje mu dauko magungunnan mukai dakin mu ko,
alhj basheer yayi dariya yace banason shirme ka bari mummynka zata kawo maka har ďaki,
ya kamo hannun Afeeyah yace zo muje muyi wasa irin na rannan,
Afeeyah tayi saurin fisge hannunta ta wuce daki cikin jin kunya, ya bita a baya da gudu,


alhj basheer ma daki ya wuce ba tare da ya kalli oyizah ba,,
suwaiba tace kinga abinda nake faďa miki game da yarinyar nan ko,
oyizah tace uhummm kawai ta wuce daki salma ta bita har lokacin kuka takeyi,,, suwaibah taja gyalenta itama tayi waje...


Karfe huďu na yamma alhj basheer ya dawo gida motarshi cike da kayan abinci,
masu aikin gidan maza su suka shiga da kayan lokacin Oyizah na zaune a parlor tana ta tufka da warwara, ko kallonsu batayi ba har suka gama shigewa da kayan suka fita,
shigowar alhj basheer ne yasata mikewa da sauri tana mishi sannu da zuwa, bai amsa mata ba yace kin kai wa Afeeyah magungunan,
oyizah tace yanzu zan kai mata alhj, dan Allah ka fahimceni wallhy--yayi saurin dakatar da ita da hannu yace babu abinda zaki fada min in yarda,
tsakani da Allah safiya a bani amanar yarinya ku hadu ke da yayanki ku dinga kuntata mata,
oyizah ta fashe da kuka tace wallhy alhj sharri tayi mana, kaima kasan abinda zanyi da wanda bazanyi ba,
yace in ke baki mata ay yayanki na mata kuma bakya tsawatar musu,
Oyiza ta kara tsananta kukanta tace dan Allah kayi hakuri wallhy zan dauki kwakwaran mataki akan su,
dakyar alhj basheer ya hakura kuma yasa ta kira su salma yayi musu concrt warning akan Afeeyah...
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Cikin fushi tace dalla ni sakeni in gaida ubangijin da ya halicceni kuma ya raine ni da ni'imominsa,
Affan ya kwantar da kanshi a kafadarta yace ni kike ma ihu ko?
Tayi tsaki tace ay kai duka ne ma ya kamace ka ba ihu ba,
ya dawo gabanta yayi narai2 da ido yace zaki iya duka na,
tace sosai ma in dai bazaka dinga yin sallah ba,
ta tallabi fuskarshi da hannunta ta rage murya tace kasan falalar dake cikin yin sallah?,
Affan ya girgiza kanshi,
tace ko na fada maka bazaka gane ba,
ka faďa min duk abinda kakeso wanda yake ranka yanzu,
ya rufe idonshi cikin murna yace ammmm inason ganin abokina, ya bata rai kamar zaiyi kuka yace abokina ya gudu ya barni ya daina zuwa guri na nayi fushi dashi,,
idon Afeeyah ya ciko da kwallah tace kar ka damu zaizo ya ganka, amma fa sai ka yarda kayi sallah, yace in nayi zaizo tace sosai ma,
Affan yace to sai kuma ina son kullum ki dinga tayani wasa,
mu buga game tare, mu buga kwallo tare, Afeeyah tayi saurin cewa har abinci ma tare zamu dinga ci mu dinga bacci tare amma fa sai ka yarda kayi sallah,
ya daka tsalle yace yeeee zanyi,
Afeeyah tace sai me kuma,
ya bata rai yace sai kuma su anty salma, banason suna min ihu suna zagina wata rana harda duka na akai, in nayi sallah zasu daina, tace sosai ma, ai in ka yarda kayi sallah ko sun maka ihu zan rama maka,
yayi dariya yace yauwa barbie na to muje muyi sallah,
ta dauko dadduma ta shimfiďa mishi duk da tasan ba daidai zaiyi sallar ba amma gara yayi wit tym zai fara yinta daidai,


Guri ďaya suka tsaya ya maida hankali yana yin duk abinda tayi yana waige,
isha'i sukayi da shafa'i kadai banda wutiri,
saida ta gama lazimi sannan tace mishi ya ďaga hannunshi sama kamar yadda tayi, yayi yadda tace,
tace yauwa to duk abinda nace kace "Ameen" ya sauke hannunshi yace nace "Ameen" tace a'a kar ka sauke hannun ka ďaga hannun, yace "Ameen"
tayi dariya ta kama hannunshi tace haka zaka barshi, ya kuma cewa ameen,
cikin dariya ta fara karanto adduo'i yana cewa Ameen,
inuwar mutane ta gani a kansu ta ďago da sauri ta kallesu,
bata tsayar da addua'r ba saima sake mata salo da tayi ta hanyar faďin
"Auzubillahi minash shaidann rajim"
Affan yace ameen da karfi yana kallon oyizah dake huci fuskar nan babu annuri,
salma ta daka mishi tsawa tace tashi ka fita a dakin nan,
jikin Affan ya fara rawa yana kokarin mikewa Afeeyah ta matse hannunshi ta shafa addua'r da ta idar tace ina zaka je,
Fareeda tace gidan uwarki zaije, tashi ka fita ko in tattaka ka,
Afeeyah tace ikon Allah, to dai nasan Affan baida wani dakin da ya wuce na matarshi,
saboda haka babu inda zashi,
oyizah cikin fushi tace kika ce me?
Afeeya ta kalli salma tace maimata mata inaga kamar tana da matsalar ji,
salma cikin fushi ta kai mata naushi da sauri Afeeyah ta kauce tace toh fah!!, ashe dai rashin aure ba masifa kadai yasa ku harda harkar dabanci, fisabillihi ku ko kunya bakwa ji, ni bansan meyasa kuke bakin ciki dani ba dan nayi aure at dis age of mine, dan Allah ku barmu muci soyayyarmu ni da mijina zan muku addua' kuma Allah ya kawo mashinshini nan bada dadewa ba dan rik'ar da kukayi a gida ta isa haka, abun ma ni har tausayi yake bani,
babu wanda ya iya cewa komai sai kallon mamaki da suka bita dashi,
cikin karfin hali salma tace ina mijin yake anan da zamuyi bakin ciki,
ke nan har wani miji ne, wannan tababben da baisan kanshi ba ma bare mace,
Afeeyah tayi saurin cewa tabdijam,, ke kike ganin tababbe,
ta rungumoshi tace ni nan namiji nake gani wanda a cikin maza ma sai an tona kafin asamu irinshi,
dan Allah ku fitar mana a ďaki dan naga alamar baku san wannan lokacin na hutawar ma'aurata bane,
fareedah ta harzuka matuka ta ajiye maganin hannunta tayi kan Afeeyah zata duketa oyizah tayi saurin dakatar da ita da hannu, tace barta fareedah wallhy sai tasan ta faďa muku wadannan maganganun,
kuzo mu tafi,
Afeeya tace to sai da safenku Allah ya aurar daku ku huta da kunci, amma fa mummy baki nuna min yadda zan bashi maganin ba,
oyizah kamar ta rusa ihu tasa kai ta fita ba tare da ta bata amsa ba,
Afeeyah ta bisu da li'ilah fi quraish ta datso kofar ta dawo ta kalli Affan da ya gama tsurewa tace matsoraci to sai ka zauna tunda dodonka ta tafi,
Affan ya zauna murya a sarke yace mummy tayi fushi dani ko,
Afeeyah tace batayi fushi ba bari in kawo maka abinci kaci sai kasha magungunanka kayi bacci kaji,
Affan ya gyaďa kanshi,
Da kanta ta bashi abinci yana gama ci yasha ruwa da drink ta dauko magungunan da oyizah ta kawo,
saida ta karance su tsaf ta kalli wani ruwan jarka shi ba ja ba shi ba maroon ba, daga kafadarta tayi tace may be na gargajiya ne,
na asibitin ta fara bashi duk wanda ta kai bakinshi sai tace yayi bismillah sannan zata zuba mishi,
tana bude na jarkar taji wani karni karni, da kyar ta tsiyayya a cup tace wa'iyazubillah wannan irin karni haka, ta mika mishi tace kayi bismillah, yana yin bismillah ya kai bakinshi yaji hannunshi na rawa sosai, da kyar da taimakon Afeeyah ya shanye maganin,
boye magungunan tayi ta gyara gurin ta dawo ta zauna tana mishi hirah yana kyakyata dariyah harda buga kai a pillow,
sun shagala sosai cikin farin ciki Afeeyah taji ana buga musu kofa, mikewa tayi tana mita a zuciyarta,
tana budewa taga oyizah tsaye kamar gunki,
Afeeyah taja baya tace kin dawo ne mummy,
Oyizah ta kalleta tace tambayar da ya kamata kiyi min kenan ni da gidan mijina, Afeeyah tayi dariya tace to ai wannan tambayr tafi da inyi miki shuru in kyaleki, kuma nima nan turakar mijina ce,
oyiza tace wallhy zan babbalaki a gidan nan in bawa karnuka kasusuwanki su cinye,
Afeeyah tace waii ay ko da sunci kashi da wahala dan wallhy kashi na taurin tsiya gareshi,
oyizah tayi shuru dan taga abinda ke neman fin karfinta tace kin bashi magungunan,
Afeeyah tace wannan dole ne tunda inason mijina ya samu sauki, oyizah tace akwai wani a jarka ki tabbatar yasha dama dan in jaddada miki ne yasa na dawo,
Afeeya tace karki damu in ma akwai wani ki karo bazan gajiya ba,
oyizah tayi tsaki ta wuce ranta a bace,
ta riga ta gama kudirawa a ranta a daren nan zata lalata rayuwar yarinyar nan, wallhy yau sai tasan ta tabo ni, dan bazan barta ba abinda ta dinga fadi kenan,,,,,


To oyizah sarkin sa'a muna miki fatan nasara akan Afeeyah... ...


Mrs tijjani shattima....




[PM, 05/04/2016] Ummu Nan: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Tun sha biyun dare Afeeyah ke jin wasu irin sautittika masu ban tsoro ta windon ta,
kallon Affan tayi yana baccinshi hankali kwance,
cikin dabara ta cire hannunshi a jikinta ta gyara mishi kwanciya ta mike a tsorace saboda sautin karuwa yakeyi,
cikin karfin hali da dakewar zuciya ta ďaga labulen windon dakin,
sakin labulen tayi da sauri taja baya tana maimaita "HASBUNALLAHU WA 'NI'IMAL WAKIL" saboda ganin wasu halittu masu ban tsoro kewaye da windon,,,
wani kara taji an saki nan take taji ďakin da suke ciki yana girgiza ta ko'ina,
runtse idonta tayi tana karanto adduo'in neman tsari,
da dai taga kamar kara girgiza ďakin akeyi sai tayi karfin halin buďe kofarsu cikin sauri tayi hanyar da zata sadata da ďakin oyizah,


Tana zuwa kofar dakin ta kama murfin xata bude taji sautin magana da karfi wanda ya sata sakin kofar bata shirya ba,
sunanta taji sosai ana kira a ďakin ta kuma ji wannan sautin na windon su ya dawo nan inda take tsaye,
a gigice ta leka ta windo don jin mai ambaton sunanta cikin wannan sigar a kuma wannan talatainin daren,
tana lekawa ta hango oyizah cikin jajayen kaya tsugune gaban "chummy,"
sai wani bakin basamude a tsaye a gafensu rike da wani bakin kare,
Afeeyah bata kara firgita ba sai da taga oyizah ta dauki kwaryar jini ta shanye tass sannan ta kara daukan wani ungulu tana kiran sunanta dashi,


fitsari ta saki nan take saboda ganin duhu ta ko'ina bata iya hangen gabanta,
lalube ta fara yi tana addu'a da karfi tana kiran sunan hajja dan ta tsorata matuka da abin da idonta ya gane mata, ga wannan girgizar har lokacin bata bar jinta ba,
a cikin laluben taji hannunta ya taba mutum, nan take ta tsandara ihu haďe da faduwa kasa sumammiya,


A gigice alhj basheer da ya fito dan ganin abinda ya samu wutar gidan ya haskata da torch light,
cikin kidima ya fara kiran sunanta yana fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, safiya, safiya,
oyizah ta tsorata matuka da jin muryar alhj basheer dan tasan yayi bacci,
cikin azama ta tattara kayan tsafinta ta cire na jikinta ta mayar da night gown din jikinta ta fito tana mutsika ido,
alhj basheer yace safiya zo ki kama min yarinyar nan mu kaita asibiti ko numfashi bata iya yi na rasa me ya fito da ita cikin daren nan,
oyizah ta matso da sauri tace wace yarinya,
alhj basheer yace Afeeyah ce, kamata da sauri dan Allah,
oyizah cikin murna ta kama Afeeyah dan a tunaninta tsafinta ne ya kamata,
suna fitowa wutar gidan ta kawo alhj basheer ya bude motar suka tura Afeeyah ciki, oyizah ta koma ta dauko hijab dinta suka wuce asibiti,


Tunda aka kaita asibiti a wannan daren likitoci ke iya kokarinsu suga ta farfaďo amma abin yaci tura,
oyizah cike da murna ta nemi guri ta zauna a zuciyarta tace yarinya ai tunda kika shiga gona ta sai kinyi noma wallhy,
alhj basheer kuwa hankalinshi ba karamin tashi yayi ba dan baisan meye ya sami yar mutane ba, safa da marwa kadai yakeyi a cikin asibitin,
dakyar doctor musah ya lallabashi akan in shaa Allahu zuwa gobe zata farfado in kuma bata farfado ba sai musan abin yi,
alhj basheer akanta ya kwana ko runtsawa baiyi ba,
ana kiran sallar asuba yaje yayi sallah ya wuce gidan malam atiku,
hajja a firgice ta fito idonta ya ciko da kwallah tana tambayar wane asibiti,
alhj basheer yace ki kwantar da hankalinki hajja, safiya na can zaune da ita ba sai kin je ba,
hajja tace inaaa aiko sai naje wallhy, ai kowane aiki da wakilinshi bazamu daura mata nauyin jinya ba,
malam atiku yace Baba ay tunda yace kar--- tayi saurin katseshi tace walhi danbaba babu abinda zai hanani zuwa gurin hajara,
alhj basheer yace to shikenan hajja muje,
tayi saurin sa takalmi jiki na rawa ta bishi,

Suna isa asibitin suka tarar oyizah na bacci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login