Showing 72001 words to 72718 words out of 72718 words
Chapter 25 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt
ku karata ke da angon ki,
Amirah ta rike baki tace akai singa market, ta ina zan fara dasu,
Afeeyah tayi dariya tace hanyoyi da dama, Amirah ta mike takai ayayo kitchen tace bada ni ba sa lallen hen,
Afeeyah tayi dariya ta mike ta bita kitchen...
Karfe 12 na rana driver ya kwashesu suka tafi kaduna,
dawowa ciki Afeeyah tayi tace yau zan huta da fitina,
dakinta ta wuce ta kwanta tayi bacci,
karfe biyu da kwata ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta fara gyare gyaren gidan kafin mai gidan ya dawo,
Karfe 6 suka gama komai ita da mai aikinta,
ta wuce tayi wanka tayi sallah ta shirya cikin free gown mai shegen kyau,
parlor ta dawo ta zauna ta canza tashar zee world ana sacred ties, nan tayi paying attention saboda tana matukar son film din,
a hankali ya shigo gidan bata san ya shigo ba,
ta baya ya tsaya ya ziro macijin roba ta saitin kafarta yana mata waiwayi,
a gigice ta kalli kasa, wani irin tsalle ta daka hade da ihu tana fadin na shiga uku na lallace wayyo hajja, wayyo kuzo ku taimakeni, rungumeta yayi ta baya yana dariya sosai yace matsoraciya kawai,
ďanewa tayi kan jikinshi ta kankameshi tana faďin maciji, wallhy maciji na gani,
dariya sosai yakeyi ya sa macijin a saitin kunnenta,
wani ihun ta kara sawa tayi saurin turashi baya cikin masifa tace wannan ay mugunta ne,
kasan inada larura kuma kake tsorata ni, yanzu fisabillilahi da karamin ciki ne na haka zakayi min,
wurgo mata macijin yayi ta goce ta dauko shi ta fara buga mishi tana masifa,
chakk ya ďauketa yana dariya yace am sorry sweety,
tasa baki a kunnenshi ta cijeshi da karfi yayi saurin direta yana ihu,
daki ta gudu tana dariya sosai tace gobe ma ka kara,
bin ta yayi yana dariya yace wallhy sai na rama yau sai jikinki ya faďa mishi,
zaki san kin cijeni,
da sauri tasa ma kofar key tana dariya tana faďin sai dai ka rame a nan,
yayi dariya yace zaki ga rama zaki fito ki sameni ya wuce ďakinshi...
Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin farin ciki,
Afeeyah ta kara haihuwar ďa namiji wanda yaci sunan Basheer, abba suke ce mishi,
yanxu haka tana final year ďinta a "international relationship" dan tana matukar kaunar course ďin..
To ALHAMDULILLAH, Nan zan tsaya da wannan kagaggen labarin nawa,
Godiya ta musamman ga Allah s.w.t da ya bani ikon farawa kuma na gamashi ba tare da na gaza ba,
alkhairin da muka fada ciki Allah ka bamu ladanshi, sharrin dake ciki ya Allah ka yafe mana..
Allah ya kara muku tsawon kwana mahaifana waďanda sukayi sanadiyyar zuwana duniya, Allah yayi muku sakamako da gidan aljanna firdausi,,,
Allah ya barmu tare mijina, ya kauda duk wata fitinar dake cikin auren mu, Allah ya raya mana zuri'armu kan tafarkin Addinin musulunci,,,
Jinjina ga kungiya mai albarka.
HANNU DA YAWA WRITERS,
Allah ya kara haďa kanmu ya kauda fitina a tsakaninmu...
Godiyah ta musamman gareku yan fcbk nagode sosai da soyayyarku gareni, ...
Aysha kurah novels...
Khaleesat haydar novels...
deeja abdul novels....
Mu sha karatu....
Dama sauransu....
Banda kamarku... kawata ta da da yanzu 😀 Badiyya Aliyu umar,
Namcy Dangusau, $
Aneesah Abdulsalam....
Godiya ta musamman gareku yan uwana masoyana yan "world of Hausa novels 1 nd 2," bansan wanda zan tsame in kira sunanshi a ciki ba MAXXY, NI'MA NAKOWA, NABAYI, BIEBEE, SADEE, NAMSY MISAU, HASKE, ASMEE YA'U, SOFTIE, DEEBOX ku fito ku tayani lissafo sunansu,,, thanks for ur support dearies Allah ya barmu tare...
jinjina gareku yan uwana yan group ďin Ruffy na classic ladies novels nd ROF novels, Allah ya barmu tare ameen,
Godiya gareku..
Yan group din kawalli ummu abdool, Taskiraa.. ku ma Allah ya barmu tare,
Hausa novel group na sheedat..
Hausa novel group na Raff...
Zauren karatu...
Feenat jaafar novels...
Excellent writers...
Wisdom writers...
Perfect writers...
M jabo novels...
Only hausa novels....
Fasahar marubuta....
Matan kwarai....
Hausa novels na Pherty....
Hausa Novels na chuchu Ammani....
Zarah bb novels....
Meesha love novels....
Fillin takarddun hausa....
Khadija candy novels.....
Taskar ya'ya mata....
Sahaf's novel ...
Best hausa writers....
Kamshi novels.....
Haima fans....
Autar hajiya novels....
Da duk sauran groups ďin da ban anbata ba kuna raina Allah ya bar mu tare cikin Aminci da kaunar juna..
Ga masu bukatar littafai na, kuyi searching blog ďina ayshakurah.mywapblog.com ko kuma facbuk group dina Aysha kurah novels
Mrs tijjani shattima kema dukkan masoyanta fatan alkhairi Allah ka hada fuskokinmu a cikin aljanna firdausi...