Showing 18001 words to 21000 words out of 72718 words
Chapter 7 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt
yayi ta mudubi yayi dariya yace amirah shigo muje,
suna isa kofar gida ta buďe motar ta shige ba tare da tabi takan kayan da ya siyo musu ba,
Amirah ta kwashi nata kayan ta shige gida itama, jabeer ya gyara parking ya kwaso kayan ya fito dasu ya shiga gidansu,
kwance ya sameta can karshen gadon hajja tayi ruf da ciki hajja na mata magana tayi banza da ita,
jabeer ya zauna bakin gadon ya gaida hajja ta amsa tace yau kuma me kayi ma mutuniyar taka,
jabeer yayi dariya yace wallhy babu abinda nayi mata rigima ce kawai, Afeeya ta ďago idonta a kankance tace har kana wallhy,
ya kalleta yace to me akayi,
tace nima bansani ba, ta mayar da kanta kan katifar ita kanta bata san me zata ce ya mata ba ita dai tasan taji masifaffan zafin ganinshi da tayi da wata,
juyin duniya yayi ta faďa mishi abinda yayi mata amma sam taki ďago kai ma bare ta bashi amsa,
hajja taja tsaki tace tashi ka tafi ka rabu da ja'ira da kanta zata nemeka, in ba iskanci ba babu abin da aka ma mutum ya hau fushi, to in kin ga dama ki fashe,,
jabeer zaiyi magana ya ji wayarshi na ringing, ya mike da sauri yace hajja dan Allah ki rarrasheta kafin na dawo tun dazu Affan ke jira na, hajja tayi tsaki tace ni ban iya wacce ka iya ba, ya fita yana dariya. ..
Sai bayan isha suka rabu Affan ya wuce gida,
ya na sa kafarshi cikin gidansu yaji muguwar faduwar gaba,
wucewa ciki yayi a hankali jikinshi a mace ya shiga dakin mahaifiyarshi,
zama yayi ya dafe kanshi yana jiranta dan a tunaninshi tana bayi ne,,
wani irin ihu yaji mai firgitarwa ya mike da sauri yana kasa kunne yaji daga inda ihun ya fito,
kafa kunnenshi yayi a jikin toilet yaji ba alamar mutum a ciki, umma... umma.. ya kira sunanta sau biyu yaji shuru ya tura bayin,
juyawa yayi da sauri da yaga bata yana kwala kiranta,
muryoyin mutane ya dinga ji a can saman gidansu gurin shan iska,
a hankali ya karasa gurin yana leke a tsorace saboda muryoyin da yaji harda ta maza a ciki,
wani razanannan ihu ya saki haďe da faduwa kasa sumamme sakamakon abinda idanuwanshi suka gani.....
Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah
A gigice oyiza da wasu maza suka saki zeenatu da babu alamar numfashi a tare da ita ta faďi timm a kasa,
kan Affan sukayi da gudu oyizah ta ďago shi cikin tashin hankali tana faďin shikenan asirina ya tonu, na shiga uku na lalace, wani bakin kato ya yarda wuka da farin kyallen hannunshi yace yanzu ya zamuyi kenan, dayan cikin dakewa yace mu gama da mamanshi sai mu dawo kanshi,
oyiza ta girgiza kanta tace Nooo mu fara dashi tukunna saboda kar ya farfaďo ya tona min asiri,
bakin katon da naji sun kira da "BULADUNA" yace yanzu me kike so mu mishi, oyizah ta runtse idonta a zuciyarta tace "help me my lord", cikin mintina uku dabara tazo mata ta mike da sauri tace ku kama min shi,
cikin rashin fahimta sukace ina zaki kaishi, ta nuna kasa da hannunta tace anan zai karasa, kunga babu wanda zai zargeni za'a ayi tunanin faďowa yayi by mistk,,
A tare suka haďa baki sukace Good idea, gaskiya oyee u are very sharp shiyasa kungiya take ji dake, tayi murmushi tace "Lts make it snppy", kar wani yazo ya cim mana thou nasan ba kowa a gida,
cikin rashin imani da rashin ganin tsawon ginin bene hawa huďu suka wurgo Affan ta kai,,
su kansu saida suka runtse idonsu saboda ganin tsayin gurin amma dayake zuciyarsu a kangare take nan da nan suka sake suka juyo gurin farin kyallen da zeenatu take,
a firgice suka haďa baki suka ce ina ta shiga,
oyizah ta kwalalo ido tana duba ko ina a gurin amma basuga koda sawun kafar zeenatu ba bare ita,, hankalinsu yayi masifar tashi suka shiga duba ko'ina na cikin gidan amma basuga zeenatu ba, oyizah ta buga tagumi tace to ina ta shiga, bana tunanin da kafarta ta tashi saboda ko sanda Affan ya ganmu Kurwarta na gurin chummy,
to waye zai dauke gangar jikinta? Buladuna yace oyee kin tabbatar babu kowa a gidannan,
tace babu kowa,
su farida sun fita sannan na aiki mai aikinta guri mai nisa I don't think ta dawo kuma ko ta dawo ay baza ta hawo nan ba, dayan cikin kosawa yace mu tafi kawai tunda mun samu abinda mukeso me zamuyi da gangar jiki, buladuna yace hakane, lets go oyee,
cikin rashin kuzari ta bisu kan buzun tsafinsu suka bace daga gidan..
Ba karamin tashin hankali suka shiga ba da chummy tace kurwar zeenatu ko 5mints baiyi ba ta nemeshi ta rasa, oyizah idonta yayi jawur tace to ina yaje,? kodai ya koma jikinta ne, shikenan asiri na ya tonu,,,
Chummy tace calm down oyee, duk inda take yanzu hankalinta baya jikinta, saidai tana tare da wacce take mata addua yanxu haka, wannan dalilin ne kadai ya hanani dawo da ita, amma zansa suyi nesa sosai kuma zanyi mata abin da har ta mutu bazata taba motsi ba bare ta tashi ta dawo ta tona mana asiri,
oyizah ta dafe kanta tace my lord wacece wacce suke tare yanzu ďin,
chummy tace na kasa gane ko wacece, but koma wacece tanada kusanci da gidan,
oyizah ta shiga kogin tunani, a zuciyarta tace to wacece wannan za ta dauke zeenatu, ita dai tasan babu wacce keda kusanci da zeenatu sai Abida to ko Abida ce ta dauke ta, wata zuciyar tace to ta ina abida ta shigo gidan da daddare, ta dinga tunanin da baida amsa ta kara kallon chummy cikin tsananin damuwa tace my lord ya akayi har ta samu damar guduwa,,
Chummy bata iya bata amsa ba ta kalli wani katon glass din da ta tura Fanne da Fanna tayi kwafa cikin takaicin abinda sukayi mata,
dariya fanne tayi tace munci dubu sai ceto, sai dai ki rufemu anan dan wallhy indai muna bude babu wani rai da zai kara salwanta a gurinku,
oyizah taji kamar zata shakesu sabo takaici amma babu hali,
ta kalli chummy tace my lord ya kamata a gama da yarannan if not zasu dinga bata mana aiki,
chummy tayi murmushin mugunta tace very soon oyee,,,
saida suka gama tsaface tsafacensu sannan kowa ya bace itama '"chummy" ta tafi gurin jigajigan matsafa na gaba da ita dan samo sababin lakanin tsafi...
Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Tsaye take cikin zauren gidansu tana leken kofar gidansu jabeer ko zata hango shi,
tun bayan magriba take tsaye a gurin amma har bayan isha'i bata hango inuwarshi ba,
juyawa tayi zata koma ciki kamar zatayi kuka taji an rike hannunta ta baya, tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba hawayen da ya gama taruwa a idonta ya fara zubowa,
a hankali ya juyota ya ciro wayarshi yana haska fuskarta,
murmushi yayi da yaga hawaye akan kumatunta yasa hannu ya fara share mata a hankali yace shikenan ke kuka bashi da wuya a gurinki,
da abun kuka da wanda ba na kuka ba duk sai kin musu kuka, yanzu faďa min abinda aka miki,
ta kara fashewa da kukan da daga ji na shagwaba ne tace ba kai bane--- sai kuma tayi shuru,
yayi dariya yace ba ni bane mee? Ta kauda kanta tace ban sani ba, ya juyo da kanta yana kallon cikin idonta yace fadamin laifin da nayi in hukunta kaina yanzun nan,
ta turo baki tace tun ďazu nake jiranka anan kuma kasan zan jiraka shine ka tafi gurin wannan kawar taka mai kama da nunar rana,
jabeer ya kwashe da dariya yace wacece me kama da nunar rana?
Afeeya ta kara turo baki tace ohoo ka fini saninta,
jabeer ya kasa tsayar da dariyarshi ya kamo hannuwanta ya hadesu guri ďaya ya sa bakinshi ya sumbace su a hankali haďe da lumshe idonshi, magana ya fara yi ba tare da ya bude idanuwanshi ba yace gurin Affan naje Afee, kinsan babu abinda da zai hanani zuwa gurinki da wuri sai ganin Affan,
ta zare hannunta daya ta kai saman idonshi ta fara jan zara zaran gashin idonshi tace ni dai ban yadda ba ka fada min gaskiya ko in tura hannuna cikin idonka,
ya buďe manyan idanuwanshi da sauri yace ki makantar dani kenan,
tace eh mana sai inga da idon da zaka dinga zuwa yawo,
yace haba Afee nah yanzu in kika makantar dani wacece zata aureni,
ko bakya so ki samu anty wacce zata dinga kula dake,
Afeeya tayi narai narai mayatattun idanuwanta tace yaya jabeer in kayi aure shikenan zan daina ganinka, zaka daina zuwa gurina,? zaka daina kulawa dani ko?,
ya janyota jikinshi yace babu abinda zai hana jabeer kula da Afeeyah in dai yana raye,
bana fatan abinda zaisa rana ta faďi har inyi bacci batare da nasaki a idona ba,
ta kara narkewa a jikinshi kamar karamar yarinya tace to ay in kayi aure zan daina ganinka haka hajja ta ke cemin kullum, da karfi yace inji hajjan, afeeyah ta gyaďa kanta tace eh mana kullum sai ta faďa min da daddare wai in rage sabon da nayi da kai saboda zan sha wahala in kayi aure, ay nasan bazaka bari in sha wahala ba ko?
ya gyaďa mata kanshi zuciyarshi na kara zurfi a cikin soyayyar afee,
da afeeya tafi haka da babu abinda zai hanashi faďa mata abinda yakeji game da ita,
girgizashi tayi yayi firgigit, tace to karkayi aure ko kuma ka aureni sai mu zauna gida ďaya ka dinga goyani muyi bacci tare ko,
ya kalleta sosai yace kina sona?
ta rufe fuskarta tace sosai ma,
yayi dariya ya buďe fuskarta yace da gaske kikeyi, tace dagaske yayana, to in ban soka ba wa zan so, kaima ay kana sona ko?,
yace fiye da yadda nake son kaina wifey na,
ta daka tsalle tace bari inje In faďa ma hajja ta daina min gori, yace muje dai mu faďa mata tare ko,
tace eh hakane ta kamo hannunshi cike da murna suka shiga ciki...
Sai goma saura ya fito daga gidansu afeeyah, zama yayi kan dakalin gidansu yana kiran wayar Affan dan ya fito su ďan rage dare,
sau huďu yana kirah ba'a ďauka ba,
mikewa yayi a ranshi yace may be yayi bacci ko kuma yana can suna hira da umma,
dakinshi ya wuce ya kwanta yana tunanin Afeeyah,
Allah ya sani yana matukar kaunar afeeya, hakuri kawai zaiyi ya jirata ta gama sec skool ya aureta ya maida ita mallakinshi ya bata duk wasu nau'in kulawa da gata marasa yankewa,
da wannan tunanin bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba dashi....
Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Karfe 6 na asuba Alhaji basheer ya iso gida a gajiye,
bacci sosai yakeji dan haka ya wuce ďakinshi don ya kwanta ya samu isashshen bacci, ya yi matukar mamakin rashin ganin zeenatu ta fito tarbarshi kamar yadda ta saba, amma sai ya share da tunanin ko itama bacci ne yayi gaba da ita ko kuma dai wani abun daban amma haka nan zeenatu bazata taba kin fitowa tarbarshi ba ko da kuwa bazaii kulata ba, da wannan tunanin bacci ya ďaukeshi...
Ihu ya dinga ji kamar a cikin mafarki,
a hankali ya buďe idonshi yaji bugun kofar da ake ma ďakinshi yaki tsagaitawa, da sauri ya diro daga kan gado jikinshi na rawa ya bude kofar,
Salma da farida ya gani tsaye suna ihu suna kuka suka ce daddy Affan-- Da sauri ya katsesu yace me yasamu Affan din, kasa bashi amsa sukayi sunata nuna hannunsu saitin kofa, da gudu ya fita waje ya'yan hanjinshi sai kaďawa sukeyi,
turus ya tsaya ganin masu aikin gidan da oyizah tsaye kan affan suna kuka jini ko ta'ina a kasa da kanshi,
wani irin ihu alhj basheer yayi haďe da karasawa yana girgizashi yana kuka, da kyar yake iya hado sunan Affan ya kira saboda tashin hankali, daukarshi yayi bai kula da jini da fashewar da tsakiyar kanshi yayi ba ya turashi cikin mota, binshi oyizah tayi tana kuka tace alhj ina zaka kaishi, ya riga fa ya mutu,
alhj basheer ya watso mata ashariyar da baisan yadda akayi ya fadeta ba ya shiga mota yayi asibiti da affan,
likitoci kansu sun tsorata da ganin Affan, wani a cikinsu yace ranka ya dade wannan ay ya mutu,
alhj basheer yayi kanshi yace ubanka ne ya kasheshi? Doctorn yayi baya yace sorry alhj,
nan likitoci sukayi caa akan Affan duk da bawai sun sa ran yana raye ba saidai dan bala'in da alhj basheer ke musu,
Cikin ikon Allah karfe 2 na rana Affan ya fara motsa hannunshi, cikin mamaki doctor musa ya kura ma hannun ido ko gizau yake mishi, ganin ba gizau bane yasa shi fita kiran sauran likitocin cikin murna,
alhj basheer dai binsu yakeyi kamar zararre yana fadin bai mutu ba ko, dr musa ya gyada mishi kai kawai suka wuce dakin da Affan yake,
sai hudu suka fito kowa yayi hanyar office dinshi,
doctr musa ya kalli alhj basheer yace ka kwantar da hankalinka alhj muje office inyi maka bayani,,
alhj basheer ya bishi office din ba tare da ya ce uffan ba,,
Doctor musah ya kalli alhj basheer cikin damuwa yace alhj ka saurareni da kyau kuma duk abinda zan faďa maka kasani bani nayi ba kuma ba wani bane yayi Allah subhanahu wa ta'ala shine ya jarabceka kuma ya jarabci danka, saboda haka dan Allah alhj kayi tawakkali saboda cuta ba mutuwa bace,
alhj basheer ya share hawayen da ya zubo a idonshi yace faďamin komai doctor, fadamin abin da ya sami Affan,, doctor musah ya mika mishi takardun hotunan kwakwalwar da sukayi ma Affan,
ya karba hannunshi na rawa yace bazan gane komai a ciki ba doctor kayi min bayanin komai da baki,
doctor musah yayi ajiyar zuciya yace alhj, Affan ya samu "brain disorder" abin da yabamu mamakin anan shine duk girman ciwo da karfin buguwar nan bashi ya taba kwakwalwar shi ba har yasamu "mental illness" sai wani abun daban,,,,
ya mika mishi wata takarda yace wadannan sune ciwukan da kwakwalwar shi ta samu
"Psychological trauma":
wannan cutar may be triggered by P.T suffered as a child, kamar "severe emotional", physical, or sexual abuse;" abinda ke kawoshi kuma shine, "a significant early loss", kamar the loss of a parent; and neglect...
sai kuma
"Environmental stressors":
"itama ana samunta ne a shock din mutuwa ko macen da aka saka, ko kuma dysfunctional family life,
sacking 4rm jobs or schools, and substance abuse -- it can trigger a disorder in a person who may be at risk for developing a mental illness."
Kaga kenan akwai abinda ya gani ko kuma ya sameshi cikin waďannan abubuwan amma sam ciwon kanshi bai da alaka da cutar,
Alhj basheer cikin tashin hankali yace yanzu doctor kana ganin Affan zai samu lafiya nan kusa,?
doctr musah cikin tausayawa yace sauki na gurin Allah alhj, in yazo yanzu baiyi gaggawa ba sannan in baizo yanzu ba baiyi jinkiri ba saboda Allah ne kadai yake iya bada sauki a lokacin da yaso,
sannan ina tsoron sanar dakai mostly mental illnesses irin wannan are caused by a combination of factors and cannot be prevented so easily, saidai a dage da addu'a saboda babu abin da ya gagari Allah kuma babu wanda yasan gaibu sai Shi..,
da sauri oyizah da tun shigewar su office din doctor ta iso ta juya cikin jin dadin ciwon da taji ya sami Affan da kuma firgicin jin affan nada rai kuma zai iya samun sauki a koda yaushe,
kuma tasan yanzu alhj na dawowa zai fara tambayarta ina zeenatu? Kuma me ya samu Affan me ya gani har ya haddasa mishi wannan cutar,
fita tayi daga asibitin da sauri cikin tsananin tsoron abinda zai je yazo, bata zame ko ina ba sai gurin tsafinsu.....
Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣2⃣ By Aysha Ya'u kurah
Alhj basheer ya fito daga office din doctor Musah idonshi jajur saboda kukan da yaci, dakin da aka kwantar da Affan ya shiga ya zauna gefenshi yana zubar da hawaye yana ta tunanin yadda akayi har Affan ya faďo daga wannan saman nisan gaske, to wai ma me Affan ya gani da har ya firgita shi haka,
da sauri ya mike da ya tuno da tun asuba baisa zeenatu a idonshi ba, kuma ace har Affan baida lafiya batazo inda yake ba, girgiza kanshi yayi a fili ko dai wani abu ne ya samu zeenatu, gabanshi ya faďi sosai da ya tuno da kalaman doctor,
jikinshi ya fara rawa ya murda kofar dakin da affan yake ya fita da sauri yana fadin innalillahi a zuciyarshi,
da taimakon Allah ya isa gida, a waje yayi parking motar saboda tashin hankali,
yana shiga ya wuce dakinta,
babu inda bai duba ba a ďakin bai ganta ba, cikin kiďima ya fito yana haďa sunayen mutanen gidan yana kirah da karfi,
da gudu suka firfito, oyizah da bata fi minti 5 da dawowa daga gurin tsafinsu ba ta matso kusa dashi tace lafiya alhj,
ya nuna dakin zeenatu yace ina zeenatu take, fareeda da salma suka ce daddy tun jiya bamu ganta ba,
oyizah tace ni rabona da zeenatu ma ay tun ranar da zaka tafi mukayi maka rakiya,
cikin karaji yace to ina ta shiga,
oyizah ta dafashi tace calm down my dear muje ka huta ka kira can gida kaji ko tana can,
cikin damuwa ya kalli fuskar oyizah, nan ya tsinci kanshi da kasa yi mata musu ya bi bayanta suka wuce gurin dinning,
saida ta bashi abincin da ta haďasu da sinadaran asiri sannan ta zauna gefenshi tana matsa mishi kafa, kallonta yayi har