Showing 6001 words to 9000 words out of 72718 words

Chapter 3 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt

16 Dec 2024

2284

found him my lord, amma mum naso ta kawo min matsala, chummy tayi dariya mai karfi tace ur mum ko kuma gvn mum,
kin manta u sacrifice her sannan kika samu alhj basheer yasan inda kike,
cikin faduwar gaba oyiza tayi kasa da kanta tace I love my mum my lord,
chummy tace I knws dat amma in har kinason jin dadi dole ki katse numfashin mahaifiyarki, kuma bari in fada miki kina shiga gidanshi zaki samu ciki so u will be d apple of d house saboda u bring air to d family, ,
mum dinki ta fara tsufa so let her go ke kuma ki fara rayuwarki mai daďi,
haka tayita convincn dinta har ta gamsu ta fitar da uwarta a ranta tayi alkawarin yau da dare zata bada uwarta saboda komai ya tafi mata daidai,
sun kusa awa suna tattaunawa kafin Chummy ta bace, oyiza ta mayar da komai na tsafinta ta fito ta shiga kitchen dan tayi ma innocent mum dinta girki, tsayawa tayi a kitchen ta kasa komai tana tunano rayuwar da tayi da mahaifiyarta da irin wahalar da mahaifiyarta tasha akanta da karatunta, tayi tsaki a zuciyarta tace kuďi yafi min komai ciki harda ke mum,
am so srry mum u have to go,
ina son sunana ya shiga jerin mata masu arzikin duniya,
girki ta farayi duk da jikinta a mace yake amma ta dake saboda zuciyarta ta daďe da kangarewa da shan jinin bil adama,


Oyiza ta shiga cikin kungiyar asiri ne tun shekararta ta farko a jamiar lagos,
wata kawarta esther Babajo ita tasata lokacin tana shan wahalar rashin kuďi da abinci saboda mahaifiyarta bata da kuđi, sannan kuma sun shiga ne dan su dinga samun first class result a set dinsu,
haka kuwa yake faruwa dasu dan su biyun nan saida ya zamana babu wanda yake iya bugesu, kuma kuďi ma babu macen da zata nuna musu shanawa a cikin skull, duk irin gulmarsu da akeyi babu wanda ko wacce ta isa tazo gabansu tayi saboda tsabar tsoronsu da ake ji,
jini kuwa su kansu basu san adadin na mutanen da suka sha ba,
oyiza ta hadu da alhj basheer ne a airport lokacin sun dawo daga Italy ita da esther, tunda ta daura idonta akanshi da suka sakko daga jirgi taji sonshi mai tsanani ya kamata,
tun a airport suke bin bayan motar da ta daukeshi har zuwa hotel din da zai kwana kafin safiya ya wuce kano,
Saida suka bari ya shiga ciki sannan suka samu drivern da ya daukoshi suka tambayeshi sunanshi, da kyar da kuma kuďi da suka bashi ya sanar dasu sunanshi da kuma garin da yake, godiya sukayi mishi sannan suka wuce,
tun daga ranar Chummy ta fara mata aiki akanshi, nan ta gano irin kudin da yake dashi da kuma wanda zaiyi nan gaba, ta kuma gano matsalar da yake ciki na rashin haihuwa ,
jin yunwarshi da tsayuwa a restaurant dinsu 4d first tym duk aikinsu ne..
dariya oyiza tayi bayan ta gama tunano wadannan abubuwan sannan ta sauke abincin da ta daura ta kwashe ta haďa juice ta jere su akan dining ta zauna zaman jiran mamanta dan suyi hirar karshe....


Allahu akbar,,,
tabbas mun tsinci kanmu a zamanin da kuďi suka fi wadanda suka kawo mu duniya daraja,
kuďi sunfi ďan da ka tsuguna ka haifa saboda a cikin 100% 85% zasu iya bada komai nasu dan su samu kuďi dattin duniya,,,
tabbas a wannan zamanin da muke ciki masu karancin imani da tawakkali zasu iya aikata komai saboda kudi,
Ya Allah ka tsarkake mana zuciyarmu da ta yan uwa musulmi baki ďaya,
Allah ka azurta mu da baye bayenka kayi mana rowar talaucin da zai kaimu ya baro mu,, ameen thumma ameen....


Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 7⃣
By Aysha Ya'u Kurah


Daren ranar bayan sun gama hirah da mamanta ta nuna mata ta hakura da maganar alhj basheer, mum ta yi murna sosai dajin hakan daga bakin oyiza,
sai gurin sha ďaya taga mum na hamma ta dafata tace mum bacci kike ji, mum tace eh bacci sosai nakeji bari inje in kwanta, oyiza ta mike tace bari in kara gyara miki ďaki saboda kiji dadin bacci da kyau,
mum tayi murmushin jin dadin ganin yadda yarta ke tarairayarta, dakinta oyiza ta wuce ta yaye shimfiďar zanin gadon tasanya mata wani fari kall a kasa sannan ta ďaura nata akai,
idonta yayi ja lokacin da ta dauko wata kwalbar farin magani zata yayyafa a gadon, sai da ta ďan zubar da hawaye sannan ta yayyafa maganin ta fita taje ta taso mum da ta fara bacci,
har ďaki ta rakata ta rufo kofar ta koma ďakinta tayi tagumi tana jiran dare ya raba ta tafi gurin meeting, ,,


2:45am


Tsugune suke gaban "CHUMMY LORD" cikin jajayen kaya su kusan goma sha biyar maza da mata masu neman arziki da mulki,
jini ne a kwarya wani bakin mutum ya ďauko ya mika ma wacce take gaba ta sha ta mika ma sauran duk suka sha sannan suka ajiye kwaryar, wani irin kirari haďe da ihu "chummy" tayi akan wani farin kyalle sai ga wasu yara yanmata basu wuce shekara 14 ba sun bayyana a gabanta cikin night gown, yara ne farare kyawawa masu kama da juna da ganinsu yan biyu ne,
a firgice yaran suka fara waige2 suna kankame junansu, chummy tayi dariya sosai tace Alhaji Sambo aikinka yayi kyau lallai ka tabbatar kana son cin wannan kujerar,
da sauri yaran suka fara kallon mutanen gurin ko zasu ga wanda aka kira da sunan mahaifinsu, jikinsu ya kara rawa lokacin da idonsu ya sauka akan babansu mai kaunarsu dare da rana wanda a wannan daren kafin su kwanta bacci saida yayi yawo dasu cikin garin abuja da kewayenta ya kashe musu makudan kudi na ban mamaki, cikin rawar murya suka ce PA--PA,
alhj sambo ya sunkuyar da kanshi kasa,
daya daga cikinsu tayi karfin halin zuwa gabanshi ta dafashi dan gani takeyi kamar mafarki takeyi,
jin da gaske shi ďinne yasa ta rusa ihu ta kalli yar uwarta tace "Fanne" ba mafarki nakeyi ba wallhy papa ne, meyasa zaka mana haka, yanzu ashe neman duniya zai iya saka ka bayar da ya'yanka na cikinka,
papa sanda zaka bada damu bakayi tunanin bazaka kara ganin mu ba,
cikin fushi dayar tace "Fanna" meye a ciki dan ya bada mu an kashe,
kika san iya adadin mutanen da ya kashe saboda neman duniyarshi,
kukan me kikeyi? Saboda bazaki kara shakar iskar duniya ba kome?
Inda zamu tafi nan zai zo yau ko gobe ko jibi in kwananshi ya kare shima,
gara ma su kashemu da zama karkashin zalunci da cin kudin haram da na kawunan mutane,
wani mugun mari aka dauketa dashi ta waiga ta kalli bakin mutumin zuciyarta ta kara zafi tace ba mari nake bukata ba kashemu zakayi mu huta,
"chummy" tayi dariyar kusan minti uku sannan tace ai dama kun mutu ruhinku ne anan,
in naso zan iya barin ruhinku yayita yawo shi kadai a duniya gangar jikinku kuma tana rami,
Fanna tace ki so din,
fanne tayi saurin cewa dan Allah dan annabi ku maida mu gurin mammi ta waiga ta kalli mahaifinta tace papa kaji tsoron Allah,
Oyiza cikin Fushi tace chummy lord yaran nan na bata mana lokaci gashi har asuba ta gabato ga kuma mum can daure gara ayi mata abinda za'ayi in wuce gida,
Fanne ta waigo ta kalleta a hankali tace mum? U mean mum dinki kika bayar saboda--- wannan karan chummy ce da kanta ta kai mata duka a baki,
chummy tace bazan kashe yaranka yanzu ba alhj sambo dey wl be under my control, zan watsasu duniya saboda naga za'a dama dasu,
fanne tace karya kikeyi jininmu ne yafi karfin ki,,,
chummy tayi murmushi tana girgiza kai,,
Alhj sambo cikin tsoro yace my lord ina tsoron kar suyi min illa, chummy tace babu kai babu su saboda zaku binne gangar jikinsu a grave so ka kwantar da hankalinka, yayi ajiyar zuciya yana kallon hararar da fanne take musu shi da oyiza,,,
dafa kansu chummy tayi da wata sanda mai kyalli nan da nan suka bace,,


Mum din oyiza kuwa kuka ta dingayi ganin ďiyarta ce ta bada ita, gaba daya magana ma kasa fita tayi a bakinta sai girgiza kai kawai takeyi tana tunano rayuwar da tayi da yarta,
cikin minti goma aka gama da maman oyiza suka gama shaye shayensu sannan kowa ya bace, ,,


Kuka oyiza takeyi a bakin gadon da mum ke kwance tana ihu makotan da ta aika mai gadinsu ya faďa musu suna kanta suna bata hakuri,
ta kira can kauyensu ta fada musu suma suka dinga ihu suka shirya suka kamo hanyar abuja,
Guraren karfe biyu akayi mata sutura da kyar dan yan uwanta sunce saidai su kaita can okene a binneta ita kuma oyiza ta kafe saidai a binneta anan saboda tsoron kar asirinta ya tonu dan tasan kakarta na ganinta zata san abin da ya kasheta dan itama mayyar kanta ce,
saida malamai sukayi ma yanuwanta nasiha sannan suka yarda akayi mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya...


Washe gari ta kira john a waya tace yaje ya buďe shago in alhj basheer yazo ya kawoshi gidansu,
haka kuwa akayi yaje ya bude shago amma har dare babu alhj basheer, washe gari ma haka,
oyiza hankalinta in yayi dubu ya tashi tana ta kai kawo saboda rashin zuwan alhj basheer gashi har an kusa sati daya,
a daren ranar ta bayyana gaban chummy da matsalolinta, chummy ta gama incantation dinta tana girgiza kai tace yana karkashin kulawar matarshi,
ta nuna mata wata kwarya,
bakar mace ta gani a ciki sanye da hijab tsaye gefen gadon mijinta dake bacci tana sallar dare in ta idar sai tayi adduoi ta tofeshi dashi sannan ta mike ta kara tada kabbara,
chummy tace kin gani da idonki ko? Oyiza ta haďe rai tace na gani amma ay ni babu ruwana da wannan, mum na bayar saboda haka so kisan duk yadda zakiyi,
chummy tayi dariya tace dadina dake wutar ciki, trust me Oyee cikin satin nan za'a daura miki aure da alhj basheer,
cikin farin ciki oyiza tace yanzu naji magana.....


Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 8⃣
By Aysha Ya'u Kurah


Alhaji basheer tsugune yana gyara canvas din kafarshi cikin shigar blue nd white track suit,
mikewa yayi bayan ya gama ya kalli matarshi zeenatu dake gyaran gadon da ya tashi yace to ni na fita training, tace to a dawo lafiya yallabai,
yace Allah yasa sannan yasa kai ya fita,
Zagaye ya dinga yi yana jogging cikin farin ciki saboda yadda sanyin safiyya ke kaďashi,
yayi zagaye na tara yana yi yana hutawa, a zagaye na goma ne ya hango wani shima jogging din yakeyi dai2 gurin wata katuwar kwata kafarshi ta gurďe ya tafi zai faďa alhj basheer yayi saurin rikoshi yana fadin subhanallah sannu,
mutumin ya ďago yana gyara kafarshi yace yauwa nagode sosai gaskiya ka taimake ni, alhj basheer yayi murmushi yace mu gode ma Allah, mutumin ya mika ma alhj basheer hannu yace sunana Bara'u ina nan zoo road, "BB close" opp gidan alhj Basheer Balarabe,
Alhj basheer yayi dariya yace ni kuma sunana Basheer Balarabe (BB) nima ina zaune a zoo rd BB close cikin gidan Alhj Basheer balarabe,
Alhj Bara'u yayi dariya sosai yace ikon Allah alhj basheer, kaga yadda Allah ke abunshi ko, .
alhj basheer yayi dariya yace kai gaskiya bamu fitar da hakkin makobtaka in ba haka ba ga gida ga gida ace bamu san juna ba,,
Alhj bara'u yace ko 1week banyi da tarewa ba kuma nasa ayi min magana da duk makota na kai kaďai ne Allah baiyi zamu hadu ba saboda ance min baka gari,
alhj basheer yace kwarai kuwa ban daďe da dawowa ba, to ya unguwar tamu da fatan dai baka samun matsala,
Alhj bara'u yace walhy babu matsala unguwar cike take da mutanen kwarai naji dadin kasancewata cikin ku, Alhj basheer yayi murmushi suka fara tafiya yace to ya iyalin fa, Alhj bara'u yace tukunna dai har ansa rana jiranta nakeyi ta karasa skull zuwa nan da 3monts sai ayi in shaa Allah,
Alhj basheer yace Allah ya nuna mana kai kadai ne a cikin gidan kenan, alhj bara'u yace eh ni kadai ne amma weekends a daura nakeyi saboda rashin iyali, alhj basheer yace hakan yayi Allah ya taimaka yace ameen har suka karaso gida suna hira cikin kankanin lokaci suka saba da juna, a dai2 kofar gida sukayi sallama kowa ya shiga gida,
kanshi tsaye yake tafiya cikin gidanshi yana amsa gaisuwar masu musu hidima, yazo gab da shiga parlo yaji wata muguwar faďuwar gaba,
juyawa kanshi ya fara yi sosai ya dafeshi ya karasa parlon dakyar ya zauna kan kujera, zeenatu na can kitchen bata san halin da mijinta yake ciki ba,
runtse idonshi yayi siffar Oyiza ta dinga mishi yawo a cikin kwakwalwar kanshi, buďe idonshi yayi da sauri da ya tuno da oyiza gaba daya yaji wani abu ya tokare mishi kahon zuciyarshi, ga wutar son ganinta da ta ruru a zuciyarshi kamar wacce aka iza da petur,
mikewa yayi da sauri ya shiga bayi yayi wanka sharp2 ya fito ya shirya da gaggawa ya feshe jikinshi da turare ya debi kudi a sv dinshi na gida masu yawan gaske sannan ya wuce kitchen ya sami zeenatu,
Cikin rashin fahimta tace tafiya weekend kaiko ina zaka, yace abuja zeena alheri ne yake kirana,
tayi murmushi tace to Allah ya kawo mana alkhairin tare,
yace ameen yar matata sai na dawo, tace to Allah ya tsare ya kuma kiyaye hanya, yace ameen ya fita da sauri,
biyoshi tayi da gudu tace na manta ban fada maka ba, dan Allah zan shiga gidan Malam atiku gurin Ma'u tayi min kitso, yace to adawo lafiya tayi miki mai kyau fa, tace karka ji komai in dai kitson ma'u ne, yayi murmushi ya fita ya tafi...


Da kyar ya gane restaurant din, yana isa ya fito cikin farin ciki,,
tsayawa yayi turus saboda ganin gurin da yayi a rufe, jingina jikin motarshi yayi ya rasa me ke mishi daďi yanzu wa zai fara tambaya inda take anan gurin, ya kusa 30mins kafin ya shiga motarshi da niyyar tafiya,
kamar daga sama ya hango john yana bude gurin,
fitowa yayi da sauri kamar wanda akayi ma albishir da gidan aljanna, karasawa yayi yana kiran yaron, john ya juyo rai a bace saboda yadda yaji ana kiranshi ganin alhj basheer yasa john jindadi ya fito da gudu ya tsuguna a gabanshi ya gaishe shi,
alhj basheer ya amsa suka shiga ciki,
ya kalli john yace ina madam dinku, john ya raunana fuska yace madam is no more alhj tun ranar da kazo washe gari ta mutu, alhj basheer ya girgiza kanshi cikin tausayin oyiza yace Allah ya jikanta to ina yarta oyiza,
john yace tana gida dama tace idan kazo in kaika can gida, alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi dan a tunaninshi kafin mahaifiyarta ta rasu tayi mata bayanin komai, tashi yayi suka fito shi da john suka shiga mota suka wuce gidansu oyiza...


Bayan ya gama yi mata gaisuwa yana rarrashinta saboda kukan munafurcin da take yi ita a dole tayi rashin uwa,
tausayinta sosai ne ya ratsashi ya tambayeta ko mahaifiyarta tayi mata bayaninshi,
tayi kasa da murya tace eh a daren ranar ta fada min komai kuma tace in ka dawo zata yarda ka aureni, ta fashe da kuka tace ashe bazata ga auren ba,
alhj basheer zuciyarshi ta kara narkewa yace kin yarda to zaki aureni, tayi kasa da kanta tace ko banaso zan yarda tunda shine last will din mahaifiyata, alhj basheer yace haka ne naji dadi sosai da kuka amince dani, yanzu ina son cikin satin nan a gama magnar komai muyi aure in tafi dake,
wani daďi ya ratsata tace to ba matsala bari in turo maka kanin babana kuyi magana, mikewa tayi ta shiga ciki ta turo mishi kanin babanta da wan mamanta,


Kudin da alhj basheer ya wankesu dashi da kuma nuna yanason ya auri oyiza saboda yana tausayinta shi kadai yasa suka yarda da auren suka sa rana ya biya sadaki da komai, sannan ya tafi cikin farin ciki,
A daren ranar ya fita da oyiza yawo ya siyo mata duk wani abu da mace zata bukata na aure,, sun daďe tare har suka saba sosai kafin su rabu,
Tana shiga gida ta dinga tsalle tana murna nan ta shirya ta wuce gurin chummy yin godiya....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 9⃣
By Aysha Ya'u Kurah


Cikin satin aka ďaura auren alhj basheer da Safiya oyiza a okene, shiri na musamman chummy tayi ma oyiza ta haďata da special kayan tsafi a cewarta su zasu taimaketa ta zauna lafiya saboda wannan matar tashi mai yawan addu'a,

Washe garin daurin auren ne ya dauki matarshi da kawayenta biyu suka kamo hanyar kano, tunaninshi ďaya shine yadda zai fara tinkarar zeenatu da maganar ya auri oyiza saboda sam duk wainar da ake toyawa bata sani ba, ita dai taga ana ta aikin gyaran part din gefenta sama da kasa amma sam bata kawo aure yayi a ranta ba, sai gurin bakwai suka shigo garin kano, kallon garin oyiza da esther keyi har suka kawo kofar dankareran gidan alhj basheer dake zoo road,
a kofar gidan alhj bara'u ya hango su tsaye shi da malam atiku suna hira, ganin motarshi yasa suka mike suka karaso gurinshi da saurinsu, ya leko ta cikin glass cikin fara'a suka gaisa, yace ga amarya fa ku gaisa,
alhj bara'u yayi dariya yace wace amaryar kuma, alhj basheer yace amaryata da aka ďaura min aure da ita jiya,
malam atiku yace shine ko labari ranka ya daďe to Allah ya sanya alkhairi sannu amarya,
oyiza ta gyara gyalenta tace yauwa, alhj bara'u ma yayi mishi addu'a suka ja suka tsaya shi kuma ya danna kai cikin gida kirjinshi na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login