Showing 57001 words to 60000 words out of 72718 words
Chapter 20 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt
nayi mafarkinsu bana iya bacci da daddare,
alhj basheer yace subhanallahi to gaskiya gara a fitar dasu daga gidannan dan kar su shafi lafiyar dan cikin ki,
oyizah da ta shigo dakin dan taci uban Afeeyah akan abinda tayi ma farida tace baka isa ba wallhy, babu wanda zai fitar min da kifi,
ance dole sai kinje gurin ne bare ki gansu,
Afeeyah ta kara narkewa tace amma mummy ay a gidan suke, dan Allah kiyi hakuri a fitar dasu wallahy suna firgitani cikin dare,
oyizah tace to zanga uban da ya isa ya fitar min da kifaye daga cikin gidan nan,
alhj basheer yace haba safiya, ni bansan amfanin kifayen nan ba, ace shekara uku ana kiwon kifaye basa girma saidai su dinga cin abinci kullum, gaskiya yanzu za'a fitar dasu daga gidan nan kije can fili na na Na'ibawa ki cigaba da kiwata su,
oyizah tace haba alhj yanzu saboda yarinyar nan tace bata son abu shin--- yayi saurin katseta yace saboda kar mu shiga hakkinta ita da abin da ke cikinta karki fassara maganar dan Allah yasa kai ya fita..,
oyizah ta kalli Afeeyah ranta a bace ji takeyi kamar ta shaketa ta huta,
mikewa Afeeyah tayi tana gyara jikinta tana murmushi tace mummy bakiji daddy na kiranki bane,
oyizah ta harareta sama da kasa tayi kwafa tace billahil lazi sai kin gane ba'a shiga gonata, tasa kai ta fita,
Afeeyah tace gonarki na nawa kuma,
ta karshen ta rage in shiga in saki nometa da hannunki..
Karashe 54
Ba karamin tataburza akasha da oyizah ba gurin fitar da kifayen nan,
saida alhj basheer ya nuna mata matukar bacin ranshi sannan ta yarda aka kwashesu ruwan ciki na yauki da kyar aka gama kwashewa,
ana sakin ruwan wani irin wari ya gauraye gurin kowa a gurin saida ya toshe hancinshi,
da gudu mati ya ruga ciki ya samu oyizah zaune tayi tagumi yace hajiya an gama kwashewa,
wani irin harara ta sakar mishi cikin tsawa tace dazu saboda ka rik'a shine ka hake flowers din dana hanaku tabawa ko,
mati ya marairaice fuska yace alqur'an hajiya sani akayi,
tace ka fada min abinda ka hako a gurin, yace na rantse da---- babu abinda ya hako mummy, Afeeyah ta katseta, tace a gabana ya gama gyarawa akwai abin da kika binne a gurin ne,
oyizah ta dafe kanta ta dago tace kan ubanki na binne,
Afeeyah tayi gaba tana dariya tace kan ubana tauri gareshi,
oyizah ta kalli mati tace bace min da gani banza shashasha,
da sauri ya mike ya fita yana bata hakuri,
wani irin juyawa taji kanta nayi saboda abin da ke shirin faruwa da ita yau,
farin cikinta daya da mati yace bai hako komai ba,
to ya zatayi da wadanan kifayen tsafin nata da alhj yasa a fitar dasu daga cikin gidan,
duuffffffff taji saukar mutane akanta suna maida numfashi,
da sauri ta hankade farida da Afeeyah ta kalli su tanimu tace lafiya kuka shigo min parlour,
a ruďe farida tace mummy kifayen nan sun bace a cikin kwanon da aka sasu.......
Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Zaro ido oyizah tayi tace kamar yaya sun bace,
Afeeyah ta kalli alhj basheer da ya fito yana gyara hula tayi saurin cewa wallahi bacewa sukayi mummy,
haba shiyasa suke tsorata ni cikin dare ashe ba kifaye bane,
alhj basheer ya karaso da sauri yace kifayen ne suka bace,
oyizah ta galla ma su Tanimu harara sum sum suka fice ta juyo ta kalli alhj basheer tace iskancin su ne ni nace ma wanda ya kwashe kifin ya dauka na bashi shine dan basu gansu ba suke tunanin sun bace, to ina zasu,
Fareeeda tace wallhy tall--- oyizah tayi saurin katseta tace dalla rufe mana baki, shekarun su nawa a gidannan kin taba ganin sun bace, dallah ku wuce ku ba mutane guri,
Afeeyah ta ja hannun Affan da jikinshi ke kyarma suka wuce daki a zuciyarta tace 99days 4 the thief muje zuwa, Allah dai ya kara bani sa'a...
Tun karfe hudu na yamma oyizah ke gurin chummy cikin matsananciyar damuwa tana faďa mata anyi destroying fishpond dinta na tsafi,
dariya chummy tayi sannan ta buga kasa nan take ya tsage ruwa haďe da kifaye suka fara fitowa daga ciki, saida suka gama fitowa tsaff sannan suka haďe kansu guri ďaya,
oyizah tayi murmushin jin dadi tace ashe suna nan,
har hankali na ya kwanta, bacewarsu ba karamin daga hankali na yayi ba dan ba karamin taimako na sukeyi ba,
chummy tayi dariya mai karfi tace fitarsu a gidanki tonan asirinki ne saboda haka kisan duk yadda zakiyi ki mayar dasu gidan nan Affan ya dinga ganinsu kullum,
oyizah tayi tagumi tace ta yaya zan mayar dasu bayan alhj da kanshi yace a fitar dasu,
yanzu ina komawa dasu zai fara zargin wani abu,
chummy tace karki damu, akwai abun da zan baki kisa mishi a abinci daga yaci shikenan ko yagansu hankalinshi bazai kawo su bane,
oyizah tayi dariyar jin daďi tana faďin thank u my lord,,
mikewa oyizah tayi ta shigo da wani yaron da zasu sha jininshi a gurin meeting,
da ganin yaron kasan mugun takadiri ne dan ko gezau baiyi ba idonshi a soye babu alamar hawaye,
dakyar ya tsuguna a gabansu,
chummy ta harareshi sannan ta umurceshi da ya miko mata kafafuwanshi,
tirjewa yayi yaki mikowa, babu yadda batayi ba akan ya miko kafafuwanshi tayi wani aikin dasu yaron nan yaki,
kwala kiran BULADUNA tayi nan suka shigo shida abokin aikinshi,
cikin isa ta umurcesu da su kamo yaron su kawoshi gabanta,
da karfinsu suka fara kokarin kama shi yana tirje musu yana tokarinsu da hannu, sai sun daukeshi sunyi sama dashi sai yasa iya karfinshi ya zille ya fado kasa,
daukar da sukayi mishi na karshe ne yasashi wani irin kukan kura ya hankaďe buladuna yayi baya,
tartsasssssss sukaji dukansu suka duba gurin da sauri,
glass din da fanne da fanna ke ciki ne yayi tarwatse ya bullo tun daga bayan buladuna har cikinshi, nan take ya fadi kasa matacce, da sauri su chummy suka yo kanshi suna kiran sunanshi,
su kuwa su fanne cikin azama suka fito cikin glass suka nufi gurin yaron da aka kamo da niyyar taimaka mishi ya gudu,
cikin tausayawa yace ku meyasa bazaku zo mu tafi tare ba,
fanne cikin sauri tace mu matattune gawar mu ta dade a rami kai kuwa ba'a riga an birne gangar jikinka ba kayi saurin komawa gida,
da sauri yace waye ya kawo ku nan,
fanna tace mahaifin mu ne Alhj sambo ministern Abuja na yanzu,
kafin yaron yayi magana ya hango su chummy sun doso su suna kokarin kama su fanne,
da sauri kurwar yaron tabi ta inda su fanne suka nuna mai ya bace daga gurin,
cikin kunan rai chummy ta ciro sandar tsafinta ta fara nuna su fanne dashi,
zagayen dakin suka farayi har suka kai inda kwalbar gunkin zeenatu take,
da sauri fanne tasa hannu ta dauki kwalbar,
wani irin ihu oyizah tasa tace karki fasa, karki fasa,
zan taimakeku in maida ku gidan ku, fanna tace fanne fasa da sauri saboda mu dama a mace muke gurin wa zata maida mu,
kafin chummy ta cimma fanne har ta fasa wannan kwalbar ta karya gunkin ciki,
zama oyizah tayi a gurin tana girgiza kanta tana fadin shikenan, shikenan my lord,
sai da nace miki mu gama da yaran nan saboda nasan zasu iya zame mana matsala, yanzu nasan duk inda zeenatu take ta farfado,
chummy bata ba oyizah amsa ba saida ta tabbatar ta kwantar da fanne da fanna sannan tace yau dinnan zan gama dasu, ki kwantar da hankakinki dan sun fasa kwalbar a banza dan babu wanda yake tunata bare har yayi mata adduar da zaisa ta gama dawowa hayyacinta,,
yanzun nan zan kara yin aikin da yafi wancan akanta,
oyizah ta saki ajiyar zuciya tace nagode my lord..
Afeeyah na zaune tana lazumi, tunda ta idar da sallar la'asar bata tashi daga kan daddumar ba sai gurin biyar,
shafa addu'ar tayi ta mike ta nade daddumar sannan ta zauna a kasa a gefen gadonta ta tura hannunta karkashin gadon ta zaro zanin da ta kunshe damon nan a ciki,
a hankali ta warwareshi ta nade hannunta da leda cikin dakewar zuciya ta fara kakkabe kasar tana kokarin bude bakin damon,
cikin sa'a ta budeshi sai wari yakeyi ta karkatar da bakin ta girgizah shi, nan wata katuwar laya ta faďo kasa,
da sauri ta ajiye wannan damon ta naďeshi cikin zanin ta dauki layar ta warwareta,
babu abinda ta gane a cikin rubutun sai sunan zeenatu,
nade layar tayi ta mike ta fita da wannan damon ta kulleshi a leda takai main bolar gidan sannan ta dawo ta kona layar ta tattara tokar ta zubata a magudanar ruwa...
★ Magaryah Nijar★
Indo!!! tankaďen ne har yanzu baki gama ba, baki gudun malam ya dawo ya tarar ba'a gama abinci ba,
wane irin shashanci ne wannan,
nda tashi ki ban guri sai shegen Nawar tsiya,
indo ta turo baki ta mike tayi hanyar waje,
Sallamar da akayi ne ya tsayar da ita,
da sauri ta rungumeta tana faďin "Tanti Gaje" sannu da zuwa,
Gaje tayi dariya tace sakan ni yar Magaryah ya na same ku,
indo tace kalau muke sai dai har lau Tanti Ayyu na nan da masifarta,
Gaje tayi dariya ta karasa cikin gidan tanti ayyu ta mike tace maraba da gaje mutan jigawa,
gaje tace ina wuni Ayyu,
ayyu ta amsa tana shimfiďa mata tabarma tace ya jigawar,
ay tun shekaran jiya muke zuba ido shuru,
Gaje tayi murmushi tace mun yi sabga ne a kazaure dan haka baki ganni ba,
ya kokari ya kuma mai jikin an samu cigaba kuwa--- kafin Ayyu tayi magana wani razananen ihu ya fito daga ďakin majinyaciyar ya ziyarci kunnuwansu,
kallon kallo suka fara yi sannan suka mike da gudu suka shiga dakin har suna bige juna,
zama sukayi a gefenta gaje ta fara shafa kanta tana faďin sannu hajiya,
wani ihun ta kara saki tana faďin zasu kasheni, zasu kashe Affan, Gaje kije ki dauko min shi, gashi can zasu kashe shi, wayyo Allah nah zasu kashe min ďana,
cikin sauri Ayyu tace indo maza je ki kirah malam kice mishi ya taho maza ta farfado.....
Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Cikin sarkewar murya malam maina yace dagaske kike indo,
jiki na rawa indo tace walllhy kawu da gaske nake,
mikewa yayi ya gyara takalman kafarshi yayi sallama da abokanshi suka wuce gida,
Yana shiga ya tarar har lokacin zeenatu na ihu sosai,
da sauri ya karaso ya zauna ya umurci indo da ta kawo mishi ruwa, nan da nan ta fita ta kawo mishi ruwa ya jika wani ganye ya daďe yana tofa addu'a a cikin ruwan sannan ya mika ma Ayyu da take rike da ita yace ta ta bata tasha,
dakyar suka iya ďagata suka bata tana ihu tana zubarwa, a haka har Allah yasa ya shiga cikinta,
kwantar da ita sukayi suna shafa mata ruwan tayi wani irin kakari haďe da amai mai yauki, tana gama aman suka gyare mata jikinta suka kwantar da ita har lokacin idonta a rufe yake, saida suka tabbatar ta samu nutsuwa sannan suka tashi suka fita a dakin suna tattauna yadda zasu billowa al'amarin....
Tun a hanya kan alhj basheer ke sarawa a zuciyarshi yana tunanin wani abu da yayi ma rayuwarshi gibi kuma yakeson tuno shi,
yana isa gida ya wuce ciki yana kallon ko ina na gidan, a hankali ya fara bin dakin zeenatu da kallo komai na rayuwar da sukayi a baya ya shiga dawo mishi har lokacin da aka nemeta aka rasa, tambayar zuciyarshi ya shiga yi akan ko an ganta, ko ta mutu ne, meyasa kwata2 ta bace a cikin kwakwalwarshi,
da sauri ya karasa kofar ďakin ya murďa yaji ta a rufe,
kitchen ya wuce shi kanshi ya rasa me zaiyi a kitchen din, yana shiga ya tarar da oyizah tsaye tana tsiyaya fresh milk a kofi,
wani irin kallo yayi mata wanda shi kanshi baisan yayi shi ba,
a hankali yace safiya ina zeenatu? har yanzu ba'a ganta ba? ko ta mutu ne,?
saboda tsananin ruďewa saida oyizah ta kusa ajalin glass cup din hannunta tace alhj wace zeenatun,
alhj basheer yace zeenatu nawa kika sani a rayuwarki,
cikin in ina tace to ni ina zan san in--- kafin ta karasa magana wayar alhj basheer ta katseta,
da sauri ya dauka yace ina wuni baffa, daga ďaya bangaren ya amsa yace bashiru shin ina labarin zeenatu, dazun nan tunaninta ya fado min bayan dogon lokaci har yanzu babu wani labari game da ita,
alhj basheer cikin damuwa yace tunanin da na gama yi kenan baffa, gaba daya na rasa yadda akayi har tunaninta ya bace min,
Baffa yace na cire rai da ita bashiru, addu'a kawai zanyi mata akan Allah ya kai rahama kabarinta,
shekara uku babu amo babu labari,
alhj basheer yace baffa baza'a cire rai da ita ba in har tana da rai, yanzu addu'a kawai zamuyi akan Allah ya bayyana ta in kuma bata raye Allah ya jikanta,
sun dade suna jimamawa a waya sannan suka kashe alhj basheer ya fita daga gidan da sauri ba tare da ya kalli oyizah ba...
Ajiye kofin tayi da sauri ta wuce daki cikin tashin hankali,
kai kawo ta dinga yi idonta yayi jajur tace tabbas mati ya hake wannan damon,
cikin sauri ta bazama gurin tsafinsu domin neman mafita...
Gidan alhj bara'u ya shiga shi kanshi yayi mamakin tsawon shekarun da suka dauka ba tare da an nemi zeenatu ba, Abida harda kukanta dan kamar yadda ake shafe rubutu a allo haka aka shafe babin zeenatu cikin kwakwalwar mutane,,
a ranar saida suka je gurin malamai hudu duk inda suka je sai anyi bincike ace tana raye amma bata cikin hayyaci da nutsuwarta, , addu'a sosai suka baza makarantar almajirai da gurin malamai,
alhj basheer bai koma gida ba sai can dare gurin 11..
Afeeyah najin shigowarshi ta dauki hijab dinta dama ta shirya duk yadda zatayi yau tasa daddy ya barsu su kwana a dakin oyizah,
wani macijin roba ta dauko ta turashi karkakashin kujerar da Affan ke zaune hankalinshi na kan cartoon,
zama tayi kusa dashi tace manya kallon har yanzu bai isa ba,
yayi dariya yace yanzu za'a gama yau bana jin bacci ina zaki naga kinsa hijab,
tace sallah na idar shine ban cire ba,
a hankali ta daura kafarta kan tashi tana mishi waiwaiyi,
da sauri ya matsar da kafarshi ya kalli gurin dan ganin abunda ke mishi yawo a kafa,
wani irin tsalle ya daka hade da ihu mai karfi ya runtse idonshi yana tsalle yana faďin wayyo daddy maciji,
Afeeyah tayi saurin dauke macijin ta boyeshi taja hannushi a rude suka fito suna ihu tare,
da gudu daddy da oyizah suka fito suna fadin lafiya,
Afeeyah tace daddy maciji ne a dakinmu yana can ya shige karkashin gado,
a ruďe alhj basheer yace maciji,
Affan yace eh daddy har ya hau min kan kafata,
alhj basheer yayi hanyar dakin, Afeeyah tayi saurin cewa daddy karka je ya sare ka, ka bari zuwa gobe in Allah ya kaimu sai a nemo masu wasa da macizai su dubashi,
Alhj basheer yace hakane kuma amma a bar maciji ya kwana a daki, wai ni ta ina ma shigo,
Afeeyah tace nima tunanin da nakeyi kenan,
alhj basheer yace yanzu dai bazaku kwana a dakin ba zo muje bangaren safiya ku kwana daki daya, oyizah tayi saurin cewa alhj dakin da na bawa Affan cike yake da kaya a ina zasu kwana,
alhj basheer yace ba ga dakinki ba tunda ba a ciki kike kwana ba, yau kadai ne fa gobe zasu koma dakin su,
oyizah ta kumbura fuska tace sam baze yiwu ba alhj, akan me daki na privacy na in bar wata ta kwana a ciki,
alhj basheer cikin mamaki yace Afeeyan ce wata,
oyizah ta galla ma Afeeyah harara tace ba nufi na kenan ba alhj, alhj basheer yace na riga na gama magana suje can su kwana, Afeeyah ta kalli oyizah tayi murmushi tace to daddy ko za'a bude mana can dakin umma sai mu gyara mu kwana a ciki,
hankalin oyizah ya kara tashi dan tasan in Affan ya shiga wannan dakin to komai zai iya faruwa,
da sauri tace kuzo muje ku kwanta a nawa dakin,
Afeeyah tace a'a mummy kar mu takura miki da dai munje dakin umma,
oyizah tayi mata kallon zaki sani yau cikin dare, tace muje babu komai,
ciki suka shige alhj basheer ya wuce side dinshi oyizah ta kai su Afeeyah nata zuciyarta cike da mugayen kulle kullen data gama shiryawa akan Afeeyah....
Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Suna shiga dakin Afeeyah ta cire hijab dinta ta kalli Affan dake tsaye har lokacin a tsorace yake tace zo ka kwanta mana,
ya karaso gurin gadon zai hau tayi saurin tare shi tace karka kwanta kan gadon mummy kaga ita babba ce, muyi kwanciyarmu a kasa ko,
ya gyada mata kai yana murmushi ya kwanta a kasa yana kallo sama,
bayi ta shiga tayi alwala ta kare ma bayin kallo tana gyada kai cikin mamaki dan cike yake da magunguna da sabulan bleaching,
fitowa tayi ta dauki hijab dinta ta kwanto dankwalin kanta ta shimfiďa dan bata ga dadduma a dakin ba,
sallah ta hau yi in ta idar ta kara tayar da wata kabbarar,
tun Affan na kirga sallahr da takeyi har bacci daukeshi bata idar ba,
☆ 2:30am ☆
Lokacin ta idar da sallolin da takeyi ta fara adduo'i tana neman taimakon Allah akan abin da zata aiwatar yanzu,
saida tayi addu'a sosai sannan ta mike ta cire hijab dinta ta rufe Affan dashi ta tofe shi da addu'a,
Saida ta tabbatar ta rufe windows din dakin sosai ta yadda ko kuda bazai iya bi ba bare ido yaga