Showing 9001 words to 12000 words out of 72718 words

Chapter 4 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt

16 Dec 2024

2292

duka sosai, parking yayi suka fito duka su ukun suna mika gasu ďirka2, sannu alhj basheer yace musu sannan ya fara tafiya suna binshi a baya,
yana buďe kofar main parlon yayi arba da zeenatu cikin kyakykyawar shigar material dinkin stone work fatar nan tata sai kyalli takeyi ga wani kamshi da sanyin dadi ko'ina a cikin parlon, da sauri ta karaso tana mishi sannu da zuwa,, gabanta ya faďi sosai da ta hango su oyiza amma sai ta kara fadada fara'arta tana musu sannu da zuwa, karasawa sukayi cikin parlon suna yabawa da kyau da tsarin parlon ga kuma kula da yake samu ta musamman,
zeenatu ta nuna musu guri suka zauna ta wuce kitchen cike da tambayoyi a zuciyarta, kayan shaye2 ta kawo musu da snacks tanata yake,
ta kalli alhj basheer da ya dafe kanshi tace yallabai gajiyar ne, tashi muje ciki kayi wanka,
oyiza cikin kishi ta watso ma zeenatu harara,
alhj basheer yace zauna zeena akwai maganar da nakeso muyi dake,
ta nemi guri kusa dashi ta zauna,
a hankali ya fara magana yace sai kuma kika ganni da baki,
tayi murmushi tace eh,,
yace dafatan zaki fahimceni zeenah, kinsan komai nufi ne na Allah kuma matar mutum duk inda take sai ya aureta,
ya nuna oyiza yace wannan matata ce jiya aka ďaura min aure da ita bawai dan inci mutuncinki ko kuma dan bana sonki ba, "a'a" wannan auren ki ďaukeshi kaddararre ne daga Allah kuma babu mamaki safiyya na tafe da alkhairai masu yawa cikin gidan nan,
zeenatu da tayi mutuwar zaune tayi maza ta saita kanta ta kirkiri murmushi tace kaii barka Allah ya sanya alkhairi nayi maka murnar samun karuwa,
ay aure cigaba ne yallabai Allah ubangiji ya bayyana alkhairan dake cikin wannan auren kuma alkhairan ya wanzu a tsakaninmu,
yace ameen yar albarka zeenatu nagode sosai da kika fahimceni,
tace ba komai yallabai bana jayayya da abin da Allah ya kaddara Allah ya bamu zaman lafiya,
yace ameen, nan yayi introducn zeenah a gurin oyiza da irin muhimmacin da take dashi a gurinshi,
oyiza ranta ya baci da irin praisn zeenah da yakeyi a gabanta da kawayenta,
bayan ya gama maganganun da zaiyi yace ma oyiza su tashi ya nuna mata part dinta, suka mike kamar samudawa suka rataya jakunkunansu suka wuce,
zeenah da kiris ya rage ta fashi da kuka ta danne kishinta ta shiga kitchen ta hado musu abinci ta kai musu dakinsu ta fito tayi nata dakin ta rufeshi da key ta faďa gado tanata rusa kuka,


Can dakin oyiza kuwa bin ko'ina sukeyi ita da kawayenta suna tsalle suna murna ganin irin dukiyar da alhj basheer ya zuba a ciki, zama sukayi a kan gado esther tace oyee baby sai kinyi da gaske da wannan matar dan da ganinta ta iya munafurci, evelyn tace green snake kenan, gata very pretty, gaskiya akan matar nan na kara yarda black is beauty kuma suna kama da bash,
oyiza tayi tsaki tace trust mee mana ai matar nan sai mai aikina ta fita daraja bari dai in haihu, kunsan bata haihuwa kuma na riga na gano abinda alhj yafi so a rayuwarshi kenan haihuwa,
ta shafa cikinta tace baby boy zan haifa maka alhj a lokacin ne zan nuna karfin ikona a gidanka,,
duk suka kwashe da dariya evelyn tace shegiya a ina kika san baby boy zaki haifa, oyiza tace bansani ba amma dat's wat I want kuma zan samu kinsan ni duk abinda nake so sai na samu, suka kara kwashewa da dariya suka cigaba da hira har dare ya raba sannan sukayi bacci oyiza batai maganar sallar magrib da isha ba,
wa ma yasani ko tayi na safe da rana ohooo......


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:33] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Tun daga ranar suwaiba ta samu gurin zuwa su zauna suyita hira suna shewa suna kulle kullensu dan ta kuntatawa zeenatu, anan suwaiba ke yini In ba ranar girkinta bane,
ko kallon zeenatu ta daina yi, saboda ita a ganinta tayi kawa wacce zata ci arziki da ita kamar yadda ma'u ke ci da zeenatu,
(bata san bomb ta samu a madadin kawa ba)..


Watansu uku da aure oyiza bata fara nuna komai na halin tsafinta ba,
sai dai abinda ke bawa alhj basheer mamaki game da ita shine rashin sallarta, ko ya matsa mata tayi sallah to fa zata san yadda tayi ta zille dan baza tayi ba,
gurin zeenatu kuwa mugun kyankyamin cin abincin oyiza takeyi saboda sam bata yarda da musuluncinta ba, ko sun haďu a dinning ana cin abinci sai tace ita yanxu abinci mai nauyi bata mata cikinta yakeyi,,


a cikin wannan lokacin ne oyiza ta fara laulayi mai zafin gaske,
komai bata iya ci, haka ta tsani kamshin gidan gaba ďaya, tunda alhj basheer yasan ciki ne makale jikin oyiza shikenan duk wani kula da soyayya ta duniya ya ďauka ya daura mata,
babu dama zeenatu tayi abu in oyiza tace bata son kamshin shi to fa shikenan zai hauta da faďa sosai kamar tababbe,
suwaiba ce ke shigowa ta kula da ita suyita yada habaici dan zeenatu taji haushi, duk da zeenatu na jin haushin abin amma sai ta danne ta dinga tambayar oyiza ko akwai abin da takeso, ko kallonta oyiza batayi bare ta bata amsa,
abubuwa suka hadu sukayi ma zeenatu yawa, gashi sam mijinta ya juya akalarshi gurin kula da oyiza a cewarshi,
gurin Ma'u da amaryar da Alhj bara'u yayi kadai zeenatu ke samun sauki,


Kayan baby babu wanda alhj basheer bai siyo ba a nan nigeria da waje, kuma duk kayan maza ya siya dan a scaninng an tabbatar mishi namiji ne, itama chummy ta tabbatar mata namiji zata haifa, gaba daya oyiza ta gama wasa wukarta dan ta gama hada plan din yadda zata mallake gidan da duk wasu kadarori na alhj basheer,


Cikin oyiza ya kusa wata tara alhj basheer ya ďauketa suka tafi india acewarshi zasu fi samun kula ita da babynshi,
tafiyarsu ita tasa zeenatu tasamu sauki take bacci da adduointa cikin kwanciyar hankali, da rana su ma'u da Abida amaryar Alhj bara'u su shigo su ďebe mata kewa da bata shawarwari duk da Abida itama ba isashshen lafiya gareta ba saboda cikin dake makale jikinta na wata hudu,


A daren ranar talata ta idar da sallar tana shirin kwanciya taji ringing din waya, daukar wayar tayi taga alhj basheer ta dauka cikin mamaki dan rabonshi da ya kirata har ta manta,
sallama ta mishi ya amsa murya babu walwala tace ya mai jiki, yace da sauki ta sauka lafiya,
zeenatu ta washe baki tace Allah ya raya ya kuma bata lafiya, me muka samu,
kukan da oyiza ke yi ya hana shi bata amsa, kuka takeyi sosai tana fadin ya za'ayi ace ya' mace ta haifa,
tsawa ya daka mata yace to ubanwa kike tunanin ya canza miki, ko wannan din ke kika bawa kanki,
ki rufe min baki kar ranki ya baci,
zeenatu ta kashe wayar da sauri ta hau gado ta dukunkune (nidai bansan me ke ranta ba a wannan lokacin, farin ciki ne ko kuma tausayin oyiza,, masu kishiya su bamu amsa plss..)..


Satinsu biyu a india suka dawo gida cikin koshin lafiya,,
tun acan ya raďa mata sunan mahaifiyar oyiza wato Salamatu (ummu Salma) tunda suka dawo makota ke shigowa yi mata barka, suwaiba sai tausarta takeyi akan gara ita tana haihuwa ba juya bace,
wannan kalaman na suwaiba suna matukar sosa ran zeenatu su ke sata kuka a kullum dare da rana tana rokon Allah akan ya bata farin cikin rayuwa itama,
dan haihuwa farin cikin rayuwa ne, in ka haihu ka wuce bakin cikin duniya da lahira,
ya Allah ka azurta wadanda basu haihu ba da ya'ya masu albarka cikin gaggawarka bata shaidan ba,
wadanda suke dashi kuma Allah ka shiryar mana kuma ka tayamu raino ameen thumma ameen.....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣2⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Shekarar ummu salma uku, in ka ganta sak uwarta gata katuwa kamar renon agric, tana matukar samun kulawa gurin mahaifinta dan ba kananan kudi yake kashe mata ba,
a wadannan shekarun banda karfin imani da salatin annabi da tuni zuciyar zeenatu ta buga saboda ko kallo kwakwkwara tayi ma ummu salma to fah zata fashe da kuka ta dinga nunata, shi kuwa alhaji basheer babu bincike babu komai zai hauta masifa wani lokaci harda gorin haihuwa,
zeenatu sam ta kasa gane kan mijinta saboda kullum alamuranshi kara tabarbarewa sukeyi sam babu sauki a tare dashi game da ita dan ko hanyar dakinta baya bi, ta ma manta rabon da su kebe tare a matsayin mata da miji,


Oyiza kuwa yanzu burinta ta samu ciki amma kafin ta samu sai ta shirya tsaff saboda wannan karan bazata taba yin sakacin haihuwar ya mace ba, sai kace ita zata bawa kanta haihuwar,,
( kaii Rashin ilimin addini shine babbar cuta a rayuwar dan adam)


A cikin kwanakin kullum dare suna gurin meeting duk dan saboda ta samu haihuwar ďa namiji, chummy ce ta kalleta bayan ta gama duk abinda zatayi na tsafi, tace oyee zaki haifi ďa namiji amma sai kin bamu jinin yaro karami namiji kar ya wuce 2yrs,
oyiza ta dafe kanta tana tunanin inda zata samu ďa namiji, chummy tace ki kokarta oyee wannan bazai miki wahala ba in kikayi la'akari da yanzu iyaye na sakin yan 1 nd half year a titi da sunan wasa,, sweet kadai zaki bawa yaro shikenan,,,
kije ki kawo zuwa jibi sai muyi aiki mu gama cikin satin nan..


Munafurci dodo ne tabbas mai shi ya kan ci,,
Oyiza ce zaune a tsakar gida tana kallon salma na wasa cikin motarta da a kiyasi zata kai 350k dan har petur ana zuba mata ta fita yawo da ita cikin unguwa,
suwaiba ce ta shigo rike da Abulbait tana ma ummu wasa,
zama tayi a kasa kusa da kafar oyiza ta fara mata kirari, nan da nan oyiza ta saki fuska suna hira tana bin Abulbait da kallo,
oyiza ta kalli suwaiba tace wai ni ko yanzu abul ya kai shekara uku, suwaiba tayi dariya tace wane uku, shekararshi 1 da wata takwas,
oyiza ta haďiye miyau ta shafa kanshi tace naga yayi saurin girma ne, suwaiba cike da murnar an yabi ďanta tace a hakan, ay ko ni ganinshi nakeyi a motse kamar fara, oyiza tace aiko ya girma wallhy bari in bashi sweet kema akwai wata yar kyautar da zan miki, suwaiba cikin murna ta mike tana godiya ta bi bayan oyiza jiki na rawa,
dubu ashirin oyiza ta bata tace ta kara jari sannan ta bare sweet ta bawa Abulbait tace shanye kar ka bawa kowa kaji,
bakin suwaiba ya kasa rufuwa tanata godiya kamar wacce akayi ma kyautar aljanna,
oyiza tace haba ba komai ay zaman tare ya wuce komai nima kin min abinda ya fi wannan,
har gate ta raka suwaiba tana kallon Abulbait saida ya shanye tass sannan ta juya gida,


Suwaiba da rawa ta shiga gida tanata ďaga kuďin sama tana nunawa ma'u dake ma Asiya yar Abida kitso, rawa takeyi tana habaici wai wata saidai bauta amma bata samun kudi, kullum aikinta renon yayan da ba nata ba daga a bata ragowar abinci sai a bata na batarwa,
Ma'u ko kallonta batayi ba ta karasa ma asiya kitso tayi mata wanka ta bata abinci ta goyata kafin mamanta ta dawo daga gurin aiki,,,


Tun bayan isha'i Abulbait ke kakarin amai kamar zai amayar da yayan hanjinshi,
jike jike suwaiba ke tayi mishi tana bashi amma ina amai yaki tsayawa,
kudin da oyiza ta bata ta kalla a zuciyarta tace nasan yanzu in nace zan kaishi asibiti zan kashe fin dubu biyu, ta maxa ta mayar dasu tace inaa a gida zaka zauna bari in jiķa maka tazargade dan da gani aman hakori ne,
tashi tayi tana bincika tazargade bata gani ba, ta duba ko ina na dakin amma bata ganshi ba kuma tasan tana dashi ko dazu ta ganshi,
mikewa tayi ta fita da gudu ta shiga gurin hajja dan bata rabo dashi, hajja ta dubo ta mika mata tace Allah ya bashi lafiya, tace ameen ta fita da gudu,
tana shiga ďaki ta tarar da gawarshi bakinshi duk ya baci da jini,
wani irin ihu ta saki tana jijjigashi tana kiran sunanshi, da gudu hajja da ma'u suka shigo cikin dakin, ganin Abulbait ya daga musu hankali hajja ta daukeshi tana dubashi ko da sauran numfashi, girgiza kanta tayi tace saidai kiyi hakuri suwaiba Allah ya karbi abinshi, ta kara sa ihu tana kuka tana birgima kamar tababbiya, dakyar aka lallasheta tayi shuru akayi mishi wanka aka suturceshi malam atiku ya daukeshi ya kaishi dakinshi yayi kwanan keso acan...


Aiki sosai chummy takeyi ma oyiza akan ta samu cikin ďa namiji,
tace mata ta nesanci alhj basheer har tsawon kwana uku, a ranar na hudun ne zata bata magani sai tasa ya kusance ta,
haka kuwa akayi oyiza ta kauracewa shimfidar alhj basheer gashi mabukaci gashi kuma ta hanashi kusantar zeenatu, abin na damunshi amma haka ya daure dan kar ya bata mata rai..


Suna zaune a kofar gidanshi shi da alhj bara'u suna hirar rayuwa, alhj bara'u ya tuno da wani tsumi a motarshi ya shiga ya dakko ya mikawa alhj basheer daya, alhj basheer yace na menene wannan, alhj bara'u yayi dariya yace goggo ta aikomin shi daga daura maganin basir ne,
alhj basheer ya fara sha yace lallai wannan irin bauri haka da basu sa zuma ba dakyar zai shawu,
sai gurin sha ďaya suka rabu kowa ya shiga gidanshi,
a parlor ya tarar da oyiza cikin wata matsiyaciyar shiga mai tada sha'awa, karasowa yayi kusa da ita ya zauna,
matsawa tayi sosai tace meye haka kuma, idonshi yayi ja yace ki taimakeni safiyya,
, tayi tsaki ta mike tace in taimakeka akan me, nifa banason jaraba na fada maka kayi min hakuri na tsawon 3dys jibi ne fa
, ni banason gajen hakuri walhy, ta wuce ciki ya bita da sauri tayi maza tasa keyy ta datse dakin,,
ya koma ya zauna cikin tashin hankali,
mararshi yaji tana murďa mishi sosai ya rasa yadda zaiyi sai juyi yakeyi,
kamar an mintsileshi ya mike rike da mararshi ya wuce dakin zeenatu, tana zaune tana addua tana kai kukanta gurin Allah ya murda kofar ya shigo,
waigowa tayi ta kalleshi ta mike da sauri saboda yadda taga idonshi yayi ja, karasawa tayi kusa dashi cikin damuwa ta rikeshi tace lafy me ya sameka,
kankameta yayi yana fitar da wani wahalallen numfashi yace ki taimakeni zeenatu, dan Allah ki taimakeni in sauke nauyin da rataya a wuyana akanki saboda ina cikin mawuyacin hali,
ta rikeshi sosai itama tace babu taimako tsakanin mata da miji, duk lokacin da kake bukatata a shirye nake in amsa kiranka,
ya sauke ajiyar zuciya yace Allah ya miki albarka zeenatu,
nan suka shiga faranta ran junansu,
tabbas zuciyarshi tayi missing zeenatu ta ko wane bangare amma ya rasa meye ya tokare wani shashi nata har baya iya kyautata mata,
Alhj basheer ya ji dadin wannan daren saboda yayi gamsuwar da ya dade baiyi ba,
ga zeenatu ma haka abin yake domin ganin daren tayi kamar duk yafi sauran darurruka amma ta dangantashi da missing din mijinta da tayi,
sai da yayi wanka a dakinta yana sa mata albarka sannan ya fita cikin tsananin ciwon kan da yarasa dalilinshi,
a daren ranar Alhj basheer da zazzabi mai zafi ya kwana saukinta ma ya sauke wani nauyin, sai kawai yaji da na zazzabin.....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Satin Alhj basheer daya yana zazzabi har saida yasha allurai, zeenatu ke kula dashi dan oyiza na fushi dashi tun da ta ganshi ya fito daga dakin zeenatu a ranar,
Ga kuma maganin da chummy ta bata ya wuce ka'idar amfaninshi saboda ciwon da yakeyi,
a ranar da taga alamun yaji sauki ne ta fara neman hanyar da zatayi amfani da maganin har ya kusanceta,
haka kuwa akayi sai da tasan duk yadda tayi da kissa da yaudara har ya kusanceta,,
oyiza ta kasance cikin farin ciki a wannan dare dan gani take ma har ta haifi ďan komai ya dawo under her...


4mnts ltr


Zeenatu ce zaune suna hirah da Abida dake da tsohon ciki,
Abida ta kalli zeenatu tace matar nan fa ni ban gane miki ba, tun wata biyu da suka wuce kika wani canza kikayi fresh, yanzu kuma gaba daya kin cika famm sai kace me ciki,
zeenatu ta shafa cikinta tace sai kace yin cikin wasan yara ne, ko sign fa ban taba ji ba,
Abida tace ji ki da wata magana, akwai cikin da haka yake ba'a taba ganeshi sai in ya fito da kanshi kuma wallhy alamu sun nuna cikin nan ya dan dade a jikinki, zeenatu tayi dariya sosai tace to doctr Abida naji bayaninki, dama ana jini in ana da ciki,
Abida tace nawa akayi kedai ina zuwa, gida ta shiga ta dauko ragowar "pt strip" din da tayi amfani dashi farkon cikinta sannan ta dawo ta bata kwalba tace taje tayi fitsari,
zeenatu ta mike tana dariya tace Abida kenan wahala kawai zaki bawa kanki,
Abida tace tunda ba ke zaki wahala ba meye na compln, ta yi dariya hade da shiga bayi tayi fitsari ta fito ta mika mata kwalbar,


Wani irin ihun murna Abida tayi da taga postive, ta kalli zeenatu tace wallhy nayi tunanin hakan, wayyo dadi kasheni, zeenatu a ruďe ta shafa cikinta tace kina nufin ciki gareni, u mean akwai halitta mai rai a cikina,
Abida tace sosai ma kuwa in baki yarda ki shirya gobe kafin na tafi karbar hutun haihuwa muje asibiti, zeenatu idonta ya ciko da kwallar farin ciki tace Abida bansan irin farin cikin da zanyi ba in har wannan maganar taki ta tabbata,
Allah ka tabbatar da wannan maganar kasa Abida ta faďi a bakin mala'iku,
Abida tace ameen zeenah,
tashi zeenah tayi ta shige ďaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login