Showing 42001 words to 45000 words out of 72718 words
Chapter 15 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt
alhj na daura ruwan zafin tea a gas na manta ban kashe ba, sakkowa yayi jiki na rawa yace innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
bari inje in duba, tace koma ka kwanta alhj ka riga kasha magani, hanyar kofa yayi yace wani irin magani ay gara inje in duba kar kije wani abun ya sameki,
dafe kanta tayi lokacin daya fita tana sake tunanin hanyar da zata bi,
waya ta dauko da sauri ta shiga kiran salma, numbr busy aka dinga sa mata tayi tsaki ta kira farida taji a kashe,
wurgi tayi da wayar tace wadannan tambadaddun kuma wayarsu taki shiga,
yanzu ni ya zanyi, muryar alhj basheer taji akanta yace safiya kin tsoratani wallhy, gas a kashe yake,
ta dafe kanta tace lallai tsufa ya fara zuwa min sai naga kamar ban kashe ba, yayi murmushi ya zauna haďe da rungumeta yace baki ma kunna ba a flask kika dibi ruwan,
tace hakane shaff na manta ne wallhy,
nan alhj basheer ya shiga faranta ranshi a jikin oyizah sakin jikinta tayi suka faranta ran juna duk da bataso hakan ba...
Asubar fari oyizah ta farka a gigice sakamakon mafarkin da tayi,
ko wanka batayi ba ta fita tayi dakin Affan,
buga kofar takeyi kamar zata ballata tana kiran sunanshi, cikin bacci Afeeyah taji bugun kofar ta mike a hankali ta fara ture Affan da ya cikwikwiyeta hawaye kwance a gefen idonshi, kara matse jikinshi yayi da nata yana sheshekar kuka haďe da ajiyar zuciya, ba karamin tausayi ya bata ba duk da itama abar tausayin ce saboda irin azabar da tasha,
bugun da mummy kema kofar ya karu muryarta ta cika cikin gidan tana masifa tana fadin in Affan bazai bude ba dan uwarki da ubanki ke bazaki bude ba,
Afeeyah ta fara kokarin yi mishi dabara ta cire hannunshi ta dan turashi tasa pillow a gurin ta daura hannun kan pillown taja bargo ta rufa mishi,
hijab dinta taja tana tafiya dakyar ta karasa kofar dakin da oyizah ke jijjigawa kamar zata ballata,
murda kofar tayi taja ta tsaya,
da karfi oyizah ta hankado kofar har saida ta sameta,
kallon Afeeyah ta tsaya yi daga sama har kasa tana hararrta, ta janyo hijab dinta da karfi tayi wurgi dashi tabi duk jikinta da kallo,
cikin fushi tace a ina kika kwana,
Afeeyah baki na rawa tace a-a-a- -- sambatun Affan ya katseta yana kiran sunanta yana fadin wasu kalmomi na shauki haďe da matse pillow a jikinshi,
oyizah tayi saurin kallon inda yake ta karasa ta cire bargon da Afeeyah ta rufa mishi,
wani irin ihu ta saki hade da mayar da bargon tace na shiga uku, me kikayi mishi naga babu kaya a jikinshi,
Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na tsere cikin idonta,
oyizah cikin hassala ta shakota tace yau sai kin fada min abinda kikayi mishi, yaudarar mahaukacin nan kikayi kika mishi fyade ko me,
Afeeyah ta kara sautin kukanta tace wallhi babu abinda na mishi, oyizah ta tsinka mata mari tace karya kikeyi dan uwarki,
ga shi nan babu wando a jikinshi kema kuma kalli yadda kike kin kasa tsayuwa da kyau,
Afeeyah ta kasa magana sai kuka kawai takeyi,
nan mummy ta cigaba da magana cikin ficewar hayyaci tana dukan Afeeyah,
ihun Afeeyah ne ya tada Affan daga bacci ya mike da sauri ganin oyizah tana dukanta, baibi takan daukar wando ba ya diro daga kan gadon yasa duk iya karfinshi ya turata ta faďi kasa ya dago Afeeyah yace yi hakuri barbie me kikayi mata,
Ta runste idonta da sauri ta dakko wando ta mika mishi ya karba ya fara sawa,
oyizah na huci ta mike ta karaso gurinshi ta daukeshi da mari har sau biyu tace dan ubanka ni zaka ture saboda wannan kodadiyyar matar, Affan ya rike kuncinshi ya kumburo baki yana hawaye yace mummy ni kika mara,
tace zan maka abinda yafi mari indai har kace zaka fara bijire min,
ta kalli Afeeyah tace Affan bai taba min musu ba, bai taba bata min rai ba kullum yana kaffa2 dani amma gashi daga zuwanki Affan har tureni yayi na fađi kasa,
yau sai na miki dukan tashin hankali inga uban da ya tsaya miki,
da sauri Affan ya shiga tsakiya yana kuka yace mummy ni ki dukeni dan Allah ki kyaleta jiya fa naji mata ciwo,
wayyyyyo oyizah ta faďi ta hankaďashi gefe tayi kan Afeeyah dake ja da baya da kyar,
tana cimmata ta daga hannu zata fara dukanta alhj basheer ya shigo da sauri yace lafiya me yake faruwa anan,
Da gudu Affan yayi gurin daddy yana kuka yace mummy ce zata duki barbie na daddy dan Allah ka hana ta bata da lafiya jiya muna wasa naji mata ciwo a---- alhj basheer yayi saurin toshe bakinshi yace ya isa haka,
oyizah ta kirkiri dariya ta sauke hannunta kan Afeeyah tana shafawa tace wa yace maka dukanta zanyi,
alhj yarinyar nan taji ciwo sosai shine nake son in kaita bayi in mata wanka shine fa take kuka shi kuma ya dauka dukanta nakeyi, alhj basheer cikin mamaki yace sannu Afeeyah,
tashi kije bayi dan Allah kiyi hakuri kinga yanayinshi komai baya yinshi a hankali,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka tace dan Allah ka kaini gurin hajja,
alhj basheer yace kiyi hakuri zan je in kira miki ita in gari ya waye kinji,
yanzu tashi kije mummynku ta miki wanka,
Afeeyah tayi saurin girgiza kanta tace wallhy zan iya,
alhj basheer yace to safiya zo muje ki hado mata abinci,
ya tura keyar Affan dake kallon Afeeyah shima yana kukan..
Toilet Afeeyah ta shige da sauri tasa key ta sirka ruwan zafi ta shiga ta zauna tana kuka sosai tana kiran hajja da jabeer,
saida tafi minti talatin a bayi sannan ta fito a zuciyarta tana tunanin to yanzu waye zaisa Affan yayi wankan tsarki,
Ďaga kafadarta tayi tasa ma dakin key tayi sallah tayi adduo'i sannan ta hau gado ta kwanta tana tunano alamuran da suka kasance tsakaninta da tababben mijinta..
Alhj basheer kuwa bayan ya je ya dauko hajja ya kaita har dakin Afeeyah da kanshi, ya fito waje yana mamakin alamarin da ya kasance tsakanin mahaukacin danshi da matarshi,,
shin dama mahaukaci wanda ke da matsala a kwakwalwarshi yana iya saduwa da mace ko dai ita Afeeyar ce ta sadu dashi,
tambayoyi marasa amsa ya dinga yi wa kanshi sai daga karshe ya samo mafitar yaje gurin doctr musa ya tambayeshi yadda abin yake,,
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI◆◆ 42 By Aysha Ya'u Kurah
A can gida kuwa Afeeyah na kwance kan cinyar hajja tana kuka sosai tana fada mata abinda ya faru tsakaninta da Affan da su oyizah,
a hankali ta ďago kanta tace hajja ni tsoro Affan dinnan yake bani wallhy, sai yayi magana kamar me hankali kuma sai ya juye mahaukaci,
sannan hajja mahaukaci ma na iya yin abinda yayi min, hajja ta share hawayenta tace zai iya Afeeyah tunda yanada duk wata halittar da muke dashi kwakwalwa ce kadai ta samu matsala,
Afeeya ta koma ta kwanta tace hajja to ya zaiyi yayi wanka yayi sallah,
hajja tace wannan ne kuma bansani ba,
tashi muyi magana kuma ki share wannan hawayen ki saurareni sosai,
Afeeyah ta mike zaune tana share hawayenta tace ina jinki hajja, hajja ta kalleta sosai tace Afeeyah kuka yanzu ba naki bane, daga yadda kika bani labarin abinda safiya tayi muku ke da Affan na ďago wasu abubuwan da ke yarinta ya hanaki dagowa,
tabbas rayuwar yaron nan na cikin haďarin da bashi da mataimaki sai Allah sai kuma ke da Allahn ya bashi a matsayin garkuwa,
"Hajara"
yau na kiraki da ainihin sunanki saboda inason in karfafa miki gwiwa dan naga kin shagwaba kanki da sunan da jabeer ya shagwaba ki dashi, dole ki jajirce kiyi amfani da damar
da Allah ya baki gurin kwatowa wannan yaran yancinshi,
dole kisa shi a hanya ki dinga nuna mishi hanyoyin bi masu kyau da marasa kyau,
dole ko yaya ne ki fara koyawa kanki sonshi dan sonshi bashi zaisa ki manta da jabeer ba,
dole duk inda yasa kafarshi kema kisata saboda kuyi shakuwar da duk abinda kika ce mishi yayi zaiyi ba musu,
sannan Addu'a, dole ki jajirce ki yawaita addu'a domin itace makaminki a yanzu, dole kuma kiyi hakuri da duk abinda za'ayi miki saboda mai hakuri shi keda nasara a ko da yaushe,
kina jina ko,
Afeeya ta gyada kanta tace ina jinki hajja,
kafin hajja ta buďe baki ta sake wata magana sukaji an tokari kofar dakin da kafa,
da sauri Afeeya ta ďago tana gyara dankwallin kanta,
hajja ta kalli oyizah dake musu kallon raini tace ina kwana safiya,
oyizah ta kirne fuska tace bamu haďu dashi a hanya ba,
hajja ta kauda kanta, salma ta karaso tace ma Afeeyah kee, kinsan karfe nawa yanzu,
Afeeyah tace a'a, salma tace dan ubanki jiya me mummy tace miki,
oyizah tace ai ta manta da abinda nace mata tunda ta kauda budurcinta a gurin tababbe,
salma tace hmm lallai, naga alama mummy,
ta kalli Afeeya tace wallhy kafin 11 ki tabbatar kin kammala komai na gidan nan in ba haka ba na rantse da Allah sai jikinki yayi tsami,
oyizah tace ay ni bani da bakin magana ki ji da ita dan in har nace zan sauke fushi na akanta to wallhy dakyar zan barta da rai,
salma tace ay dama mummy bai kamata ki dinga kulata ba mun isheta dan tasan babu sa'anta a gidannan, ko shi garan mijin nata bai isa ya hanamu yin komai akanta ba,
Afeeyah ta mike dakyar tace ma hajja tana zuwa,
hajja tace muje in tayaki,
Afeeyah tace haba hajja zauna yanzu zan gama,
hajja ta maida kwallar idonta tace to Afeeya,
hijab ta ďauka tabi ta gefensu ta wuce ta barsu tsaye sunata habaici suna zaginta,
kitchen ta shiga ta tarar dashi kaca2, nan ta shiga gyarashi ta haďe kayan wanke2 tayi ta gyara ko'ina tayi mopping,
tana gamawa taji muryar farida a bayanta, da sauri ta waiga ta kalleta tace na'am me kikace,
farida ta harareta tace ance ki daura rice nd stew 4 lunch akwai komai na amfani ki duba zaki gani sannan ki haďa min corslw,,
salma kuma tace ki soya mata plantain ki kawo mata yanzu,
Afeeyah ta gyada kanta ta wuce store din da ta hango kayan abinci,
saida ta daura white rice sannan ta bare plantain, ta daura shi a wuta ta soya,
ba karamin wulakanci sukayi mata ba da ta kai ma salma plantain din,
Ko kallansu batayi ba ta juya ta koma kitchen ta cigaba da aikinta,
sai sha biyu saura ta gama komai ta gyare ko'ina sannan ta wuce parlor da niyyar gyarawa,
Zaune ta sameshi a parlon yana buga game yana ihu shi kaďai,
bata kalleshi ba ta fara gyara cikin parlon, buruntu yaji ya waigo ya kura mata ido yana dariya,
sam bata lura ya ganta ba tana can tana kakkabe kujeru,
rungumeta taji yayi ta baya yana faďin yeeeee na ganta,
Afeeyah tace dan Allah sakeni aiki nakeyi,
ya saketa ya zagayo yana kallonta yace har yanzu fushi kikeyi dani,
ta dauki remote ta kaishi mazauninshi ba tare da ta kalleshi ba,
binta yayi a baya yace ki yi hakuri ni bansan zaki ji ciw-- dan son annabi ka kyaleni kaje ka cigaba da game dinka haba ta fadi da karfi rai a bace,
hanyar waje yayi kanshi a kasa kamar zaiyi kuka,
Kallo ta bishi dashi har ya fita sannan taja tsaki a hankali ta cigaba da aikinta cikin kwanciyar hankali dan har ta gama bai dawo ba,
ďaki ta koma tana haki saboda yunwar da takeji ta samu hajja a kan dadduma ta idar da sallah,
zubewa tayi a jikinta tana maida numfashi tace hajja yunwa nakeji, dan Allah ki samo min wani abu inci a gida,
hajja ta shafa addua tace ke kuwa duk girkin nan da kikayi bakici ko kadan ba,
Afeeyah tace umm banason abinda za'a kira uwata da ubana a zaga,
hajja tayi murmushi a zuciyarta tace lallai mutuwar jabeer ta kashe zuciyar yarinyar nan,
ta kalleta tace kinyi dai2 kici gaba da hakuri wata rana sai labari,
bari inje in kawo miki abinci a gida,
Afeeyah tace to hajja bari inyi sallah kafin ki dawo,
Ta windon bayi ta hangoshi zaune yayi tagumi yana kallon ramin kifi, da ganinshi kasan baya cikin walwala,
tsaki tayi ta cigaba da alwalarta ta fito tayi sallah,
tunanin maganganun da hajja tayi mata ta dinga yi sannan ta tuno da abinda tayi mishi dazun da kuma bacin ran da ta karanta a fuskarshi,
mikewa tayi ta naďe daddumar ta fito tana neman hanyar da zata sada ta da gurin kiwon kifin,
da kyar ta gano hanyar ta karasa gurin ta zauna, sam baisan tazo gurin ba ta waiga gurin da taga abincinsu ta ďiba ta watsa musu,
da sauri Affan ya waigo suka haďa ido ya kauda kanshi ya juya mata baya, murmushi ta kirkiro tace kayi hakuri,
dazu banaso ka hanani yin aiki ne shiyasa,
ya noke wuyanshi yace naki yin hakurin,
ta kamo hannunshi a hankali tace Niko?
yayi murmushi haďi da fari da ido kamar yana kallonta sannan ya kara haďe rai yace eh ďin,
tace to juyo kaga wani abu,
ya juyo yana turo baki yace meye?
tayi murmushi tace fushin fuskarka zan nuna maka,
ta nuna bakinshi da hannu tace kaga yadda bakinka yayi babba, sannan fuskarka tayi katuwa saboda fushi,
ya kara turo bakin yayi kasa da idonshi yace to bake bace kike min ihu,
tace to ai zan daina nace maka,
yayi murmushi kadan yace yaushe zaki daina, tace yanzun nan, ya wangale baki ya rungumeta yana dariya sosai yace yauwa barbie na, to tashi muje can ki tayani buga kwallo,
tace a'a yanzu dai inaso insan ko kayi wankan tsarki,
yace eh nayi wanka sosai jikina yanata kumfa,
yanata kumfa,
yanata kumfa na koma fari sosai,
tayi dariya tace to sallah fa,
nan ya kirne fuska yace ai ni bana sallah, Afeeyah ta kwalalo ido waje tace la haulu, baka sallah,
saboda me,?
Kafin yayi magana sukaji muryar oyizah a bayansu tana cewa saboda ubanki bai koya mishi ba.....
Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Afeeyah ta sunkuyar da kanta da sauri kirjinta na dukan uku2,
Affan ya kalli oyizah yace mummy dama saboda babanta bai koyamin ba shiyasa bana yi,
oyizah ta mika mishi cup din hannunta tace amshi maganinka kasha rabu da wannan kinibabbiyar,
Affan ya karbi ruwan asirin da ya saba sha kullum ya fara sha ya miko ma Afeeyah yace kema zaki sha, Afeeyah ta girgiza kanta ta mike zata wuce oyizah ta janyo hijabinta tace dawo nan ban gama dake ba, ta kalli Affan tace tashi ka kai cup din kitchen sai kaje kayi wasanka, Affan ya mike yana yafito Afeeyah da hannu yana cewa zo muje ki tayani buga game,
oyizah tace a'a jeka kayi wasanka zata zo ta sameka,
ya wuce da gudu yana dago ma Afeeyah hannu,
Wani irin kallo oyizah tayi ma Afeeyah sannan tace jiya me nace miki game da Affan,,
Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa tace dan Allah kiyi hakuri,
oyizah taja kunnenta da karfi tace hakurin uban me kike bani, bance miki kar ki shishshige ma Affan ba? bance miki karki shiga rayuwarshi ba, ohhh wato kema zaki fara tursasashi akan sallah kamar yadda ďan iskan saurayinki yayi ko?
Afeeyah ta runtse idonta zuciyarta na zafi saboda kiran jabeer dan iska da oyizah tayi,
Rankwashi mai karfi ta sakar mata akai tace zan miki kashedin karshe,
kashedin da idan kika ďauka kin tseratar da kanki daga fushi na,
anyi na farko anyi na karshe tsakaninki da Affan, kin fahimci abinda nake nufi ko sai na warware miki?
, Afeeyah tayi shuru kirjinta na tsananta bugawa,
oyizah tace to ina nufin kwana ďaki daya ke da shi, anyi ta yanke ta gille tsakaninku,
wallhy kinji na rantse duk ranar da kika kara yarda Affan ya shigo dakinki har kika barshi ya kwana, hmmm faďin hukuncin da zan miki ma bata baki ne kina jina ko?
Afeeyah ta gyaďa kanta tace eh inaji, oyizah ta saki hijab dinta ta kara kai mata duka a kai tace bace min a gaba ko in illata ki, da sauri Afeeyah ta wuce daki tana kuka******
Bayan hajja ta gama rarrashinta ta zuba mata abinci ta karba ta fara turawa da sauri saboda azabar yunwar da takeji,
cikin tausayawa hajja ta fara bata baki cikin hikima da kalamai masu taushi,
sai da ta tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan ta tashi tafi gida cike da tausayin yar jikarta da ta fara dandana rayuwar duniya, dan da sam Afeeyah bata san bacin rai ba kullum cikin farin ciki take in ka ganta tana kuka to na shagwaba ne, babu wanda zai taka ta ta barshi bare har ya daura mata bacin rai duk wanda yayi mata take zata mayar mishi ta wuce hankalinta kwance..
Haka rayuwar Afeeyah ta kasance cikin kunci da bauta,
wulakanci kala2 babu wanda bata gani,
sam bata bari Affan ya ganta ko yazo yana bubbuga kofarta bata budewa,
ba karamin tausayi yake bata ba in ya fara buga kofar dan baya bugun hankali yana bugata yana ihu wani lokacin ma harda kukanshi,
abinci kuwa saidai hajja ta kawo mata dan bata nasu,
duk wannan wainar da ake toyawa alhj basheer bai sani ba saboda baya gari,
A ranar da ta cika sati uku a gidan tana tsaye tana mopping dining room,
oyizah da suwaiba suna zaune cikin parlon suna gulmarta,
suwaiba tace lallai yarinyar nan ashe duk iskancin da take mana guri ta samu,
ji yadda take muku bauta kuma duk zagin da kuke mata ta kasa tabuka komai,
oyizah tayi dariya tace ay wargi ma guri ya samu,
ni yaushe kamar wannan yarinyar zata tsaya min a gaba, ai wallhi kema suwaiba harda laifinki,
suwaiba tace ai da dinma daurin gindi ta samu to yanzu mai shagwabatan