Showing 51001 words to 54000 words out of 72718 words
Chapter 18 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt
bazan iya yinshi ba saboda wani lokacin kwakwalwar yaro tafi ta babba kaifin rike abu,
Afeeyah ta gyada kanta tace to Allah ya bani juriyar iyawa yace ameen abinda ya kamata ki fadi kenan,
wadannan layun a karkashin pillown ki zaki sasu,
in zaki kwanta kiyi alwala kiyi sallah kiyi addu'a sosai akan Allah ya bayyana miki guraren da akayi wadannan binne binne, sannan ki shafa wannan turaren a jikinki ki kwanta kina mai kyautata niyya, in shaa Allah cikin kwana bakwai Allah zai nuna gurin da suke,
duk wani abun tsoron da zaki gani na rokeki ki daure kar wannan tsoron ya sare gwiwarki,
ke kadaice garkuwar bayin Allahn nan, in har kika sare to ki sani babu wani wanda zai iya daurewa yayi wannan aikin,
Afeeyah ta gyaďa kanta tace in shaa Allahu kaka zan daure, nasan ina tare da Allah da kuma kai,
yace masha Allah, sannan wannan maganin ki dinga ba Affan yana sha, kafin kwana bakwan nan zai dinga yin wasu abubuwa wadanda zasu dinga dawo dashi cikin hayyacinshi ya dinga tunanin abubuwan mamakin da suka faru dashi a shuďaďdun lokuta, kin gane bayanin ko,
Afeeyah ta gyada kanta tace eh na gane, to amma kaka yaya zanyi in na gansu,
kaka liman ya mike yace wannan kuma shawararki ce,
in kiga zaki iya ciresu ki taimaki uba da kakar abin dake cikinki to in kuma zaki barsu su dawwama a haka nidai na gama nawa yanzu naki kadai ya rage sai mu barma Allah sauran,
Afeeyah tace to kaka nagode sosai, ya miko mata wayarshi yace samin numberki kiyi flashing in wani abu ya shige miki duhu kya nemeni,
Afeeyah ta amsa tasa mishi numbrta sukayi sallama ta bishi da kallo har ya bace ma ganinta
, ganinshi kadai yana kwantar da hankalinta, badan tsufan shi ba da babu abinda zai hana a kirashi da jabeer dinta....
Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Karfe 9 na safe aka sallameta suka ďunguma zuwa gida a motar alhj basheer,
oyizah na zaune a parlonta tana gyara farce hankalinta sam ba'a kwance yake ba dan
tun jiya take jiran jin mummunan labari game da Afeeyah amma shuru gashi har gari waye,
Shigowar motar alhj basheer ne yasa ta mike ta kwashe kayan gyaran kumban dan taje ta tarboshi ko zataji wani labari a gurinshi,
tana buďe kofar parlon tayi tozali da mai taurin kashi wato Afeeyah,
kallon mamaki ta tsaya yi mata a zuciyarta tace to ko karya hajja take mata yarinyar nan bata ci abincin ba,
Afeeyah ta katse mata zancen zucin da takeyi tace ina kwana,
oyizah ta sauke ajiyar zuciya tace lafiya lau ta juya ciki bata ko bi takan hajja dake rike da kaya ba,
Side dinsu ta wuce tana kallon hanya ko zata ga Affan,
da bismillah ta murďa kofar dakin suka shiga ita da hajja,
bayi ta wuce ta cire kayan jikinta tayi wanka ta dauro alwalar walha, ta windon bayin ta hangoshi
zaune gurin fishpond idonshi kyar a cikin ruwan baya ko kiftawa, murmushi tayi ta fito daga bayin,
sai da tayi sallah ta shirya cikin bakar jallabiya sannan ta fita gurinshi,
A hankali ta karasa gurin tayi saurin rufe mishi ido da hannunta, shafa hannun yayi cikin firgici yasa ihu yana ďaga kafarshi dan kar ya faďa cikin ramin kifin,
da sauri ta toshe mishi baki tana dariya tace nice matsoraci, juyowa yayi ya kalleta nan take ya saki dariyar farin ciki ya rungumeta yace ina kika tafi ki barni,
ta dago fuskarshi tace ina daddy yace maka ya kaini,
ya shagwabe fuska yace mummy tace min bazan kara ganin ki ba, jiya suka dinga min ihu anty salma har da duka na,
Afeeyah tace am sorry gani na dawo daga yanzu babu wanda zai kara maka kallon banza ma bare har ya dukeka tashi muje kaci abinci,
ya mike da sauri yana dariya suka wuce daki...
Da sauri oyizah ta bar gurin dan kar Afeeyah ta ganta,
wani irin bakin ciki ne yake taso mata a cikin zuciyarta,
shin me zata ma wannan yarinyar ta daina ganinta kwata2 a rayuwarta,
a cikin yan kwanakin nan ganin yarinyar nan shine abinda yafi komai bakanta ranta, aiki biyu kenan tayi akanta kuma duk masu karfi amma basu kama ta ba,
tabbas wannan gara inyi mata me kankat, tabbas yau ne numfashinta na karshe a duniya dan barin Afeeyah a duniya barazana ce a gareta dan yarinyar na neman fin karfinta,
a tarihin rayuwar oyizah tun tana karama babu abinda ke tsaya mata a gaba bata kau dashi ba dan haka wannan karan Afeeyah bata isa ta rusa sa'arta ba,
da wadannan tunanin ta karasa ďaki ta zauna neman mafita, wani sashi na zuciyarta ya bata amsar cewar ta bada Afeeyah kawai su "chummy" suyi bandaro da jinin tsinaniyya, in ba hakan tayi ba to kuwa tana zaune kwado zai mata kafa,,
dariya tayi cikin gamsuwar shawarar da zuciyarta ta bata, nan ta mike ta fara shirye2 kafin dare yayi ta sadaukar da jinin ďiyar ma'u da malam Atiku,
To oyizah muje zuwa muga zaki iya da Afeeyah...
Cikin jindadi suka kammala cin abincinsu na dare wanda hajja ta aiko musu,
bayan sun gama ta jiko maganin da kaka ya bata ta bashi yasha dakyar yana sha yana furzarwa,
saida ta nuna mishi bacin ranta sannan ya sha da yawa,
yana gama sha ta gyare gurin ta dawo ta zauna suka fara yar hira,
murďa kofar suka ji anyi suka waiga suna kallonta,
da fara'a ta karaso gurinsu tace amarya da ango, sannunku da hutawa,
Afeeyah ta kau da kanta tace yauwa, oyizah ta zauna gefensu tace Afeeyah ya kamata ki ďan leka gida ki gaishesu dan gani nayi tunda kikazo gidan nan baki shiga ba, daga nan sai ki dan zaga da Affan yaga gari ko ya kikace,
Afeeyah tace hakane mummy amma ay naga affan baya fita ko,
oyizah tace shiyasa nake so ki ďan fara fitar dashi yayi refreshing,
Afeeyah tace to duk yadda kika ce, ta mike ta dauko hijab dinta tace tashi muje,
ya tashi yana kallon oyizah alamun yana so ya tambayeta yaje ko a'a,
gyaďa mishi kai tayi alamar yaje, dariya yayi ya bi bayan Afeeyah suka fita,
dariyar jin dadi oyizah tayi ta rakasu har gate sannan ta juyo da sauri tayi dakinta ta kwaso kayan tsafinta ta nufi side din su Afeeyah,
Tafiya takeyi da sauri saboda manta Turaren da tasa a ranta duk ranar da xata gida zata kaima mahifinta,
tun a parlor ta gane akwai mutum a bed room dinta,
labewa tayi ta leka a hankali,
ba karamin firgici ta shiga ba ganin oyizah tsaye a gefen gadonsu tana shimfiďa farin kyalle a kasan katifarsu,
da sauri ta fita daga dakin lokacin da taga ta dauko zanin gadon su ta mayar ta shimfidashi yadda yake,
a guje ta fita ta samu affan a inda ta barshi murya na rawa tace muje,
ya kalleta yace ina turaren, dakyar ta saita kanta tace muje dai gobe zan kai mishi..
Sai goma saura suka dawo gida,
babu wanda Afeeyah ta faďa ma abin da tagani dan ta riga ta gama kudira abinda zatayi tana komawa gida,
suna shiga ta zaunar da Affan a parlor ta kunna mishi tv tace kar ya tashi bari ta gyara cikin dakin,
tana shiga daki ta yaye zanin gadon da bismillah ta ciro farin kyallen ta naďe zanin gadon ta ajiyeshi gefe sannan ta fito ta kalli affan tace ina zuwa bari in mayar ma da mummy zaninta,
yace to ya cigaba da kallon cartoon dinshi,
tana fita tayi hanyar ďakin mummyn cikin sanďa dan tasan yanzu tana gurin daddy,
a hankali ta murďa kofar ďakin ta shiga da addua a bakinta,
da sauri ta yaye zanin gadon tasa farin kyallen kamar yadda taga oyizah tayi sannan ta maida zanin gadon ta shimfidashi yadda yake tasa kai ta fita daga ďakin da sauri.....
Mrs Tijjani shattima
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Tana komawa daki ta tarar da Affan na gyangyaďi a kan kujera,
da sauri ta shiga ďaki ta canza zanin gado ta tofe ko'ina da addu'a ta sa layun karkashin pillownta sannan ta shiga bayi ta ďauro alwala ta fito ta wuce parlor ta tarar har ya bingire a gurin yana bacci,
tashin shi tayi a hankali ta kaishi ďaki ta tofeshi da addu'a ta rufeshi da bargo sannan ta shimfiďa dadduma tayi raka'a biyu,
a gurin ta zaune har pss 2 tana addu'a tana tunanin abinda oyizah tasa mata a karkashin gurin kwanciyarta,
a zuciyarta tace koma meye ya kare miki can Allah ya kara tsaremu daga sharrinki,
mikewa tayi tana hamma ta hau gado ta kara shafa addu'a sannan ta kwanta tana kara rokon Allah ya nuna mata guraren da akayi binne binnen nan dan alfarmar annabi da hasken al qur'ani....
Ke dai kinji kunya wallahi,
mutum yayi ta tusa sai kace bodari gaba ďaya kinyi polluting iskar ďaki,,, salma ke magana da karfi hancinta a toshe ta doshi parlor,
fareeda ta biyota tana dariya tace ashe ba dadi kullum kike kumbura min ciki cikin dare,
salma tayi tsaki ta zauna tace wallhy bana irin wannan haba wannan irin tusa haka sai kace ana kwasar kashi,
fareedah ta kwashe da dariya ta koma daki tana faďin oho dai in kinga dama ki dawo ďaki ki kwanta dan 12 ta wuce,
salma tace wallhy bazan kwana a dakin nan ba dan bansan wace iri zaki kuma saki cikin dare ba,
fareeda ta shige ďaki tana dariya,
mikewa salma tayi ta leka dakin da affan yake kwana taganshi kaca2 tayi tsaki ta wuce dakin oyizah,
da murnarta ta shige ďakin ganin mummy bata ciki,
kwanciya tayi akan gadon ta cigaba da chattn din da takeyi, sai gurin biyu na dare bacci yayi gaba da ita...
Tun asuba esther ke kiran wayar oyizah bata ďaga ba saboda wani nannauyan bacci da yayi gaba da ita,
sai gurin bakwai da rabi ta tashi babu sallah bare salati, agogon gefenta tayi saurin kallo taga 7:34 da sauri ta diro daga gado tana mamakin baccin da ya dauketa har ya hanata zuwa shan jinin matsiyaciyar yarinyar nan,
karar shigowar kira wayarta ne yasata saurin dagawa tace morning esther, jiya bacci ya hanani zuwa meeting,
esther tace haba ay ni tunda naga ban ganki nasan kina can kina shegen baccinki, amma oyeee meyasa kikayi haka,
meyasa kika bada jinin yari---- oyizah tayi saurin katseta tana dariya tace badai an gama komai kuma kun riga kun koshi da jinin ba, to ay shikenan,
esther cikin damuwa tace oyizah me tayi miki haka da zafi har kikayi sacrificn dinta 4 no reason,
oyizah tace meye ma bata min ba yarinyar nan,
kedai zamuyi magana bari inje mu fara shirye shiryen jana'izah, esther tace to sai munyi waya,
oyizah ta kashe wayar ta shiga bayi ta wanke fuskarta cikin farin cikin ta yar da kwallon mangwaro ta huta da kuda,
a zuciyarta tace yanzu ne zan kara daure alhj da Affan ta yadda su da dukiyarsu zata dawo karkashin iko na gaba ďaya, bazan kara yarda a auro ma affan mace ba bare ma har ta zame min damuwa,
Tana fitowa ta wuce parlor inda alhj basheer ke kallon news,
saida ta gaisheshi sannan tace bari inje in dubo lafiyar Su Affan sai in kawo maka break ko,
yayi murmushin jin dadi yace ya kamata kam saboda mai larurar ciki,
ta shafi fuskarshi tana dariya tace su alhj ana ji da wannan jikan, yace sosai ma,
Allah dai ya fito min da ita ko shi lafiya,
oyizah ta kaurara dariyarta tace ya Hajjjj kenan sannan ta wuce side din su Affan..
Da izzarta ta buďe kofar tana murmushi, bata samu kowa a parlon ba dan haka ta tura kanta bedroom ďin,
zaro ido tayi cikin firgici saboda ganin Affan kishingiďe da towel a jikinshi Afeeyah na zaune da night gown a gefenshi tana mishi gyaran fuska suna kallon juna suna murmushi,
A-f-e-e-yah oyizah ta faďi bakinta na rawa, Afeeyah ta mike tana gyara gashin kanta tace naaaam ina kwana mummy,
oyizah bata iya amsawa ba sai ma fita da tayi dasauri kamar zararriya,
tana gab da shiga dakin alhj basheer dan daukar wayarta ta kira esther taji ihun farida a ďakinta,
da sauri ta juyo ta karaso ďakin dan ganin abin da take ma ihuu.....
Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Cikin ruďewa ta isa gaban gadon tana fadin ke lafiya, ihun me kikeyi,
Fareedah ta kasa magana sai nuna salma takeyi da hannu tana kuka sosai,
a firgice oyizah ta fara girgiza salma tana kiran sunanta,
wani irin ihu ta saki haďe da zama a kasa tana faďin wayyyo salma,
da gudu alhj basheer ya shigo ďakin yana faďin me ya faru, oyixah cikin ihu tace salma, salma--- yace salma me, tace salma ta mutu alhj,
karasawa gaban gadon yayi kirjinshi na bugawa da karfi ya ďagota yana dubata,
sakinta yayi da ya tabbatar bata rai ya shiga fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
oyizah ta mike kamar zararriya tace alhj ka tasheta wallhy karka bari ta mutu,
wayyyo na shiga uku na lalace,
alhj basheer ya daka mata tsawa yace wani irin hauka ne wannan, waye ya isa da dawo da matacce,
oyizah ta kara rusa ihu tana faďin wallhy sai ta dawo salma bazata mutu yanxu ba,
tsaki alhj basheer yaja ya tashi ya fita daga ďakin hankali tashe,
ihun suka cigaba dayi ita da farida suna kuka suna jijjiga salma suna faďin ta tashi,
Ihun da sukeyi ne ya janyo hankalin Afeeyah dake zaune suna karyawa ita da Affan,
da sauri ta mike tace ya karasa bari ta duba taga ihun me akeyi,
tana fita tayi hanyar dakin mummy dan nan takejin ihun,
sankarewa tayi da ta shigo dakin ta hango salma kwance inda ta shimfida wannan farin kyallen,
innalillahi kawai take maimaitawa a zuciyarta,
sam ta kasa karasawa gurin saboda tsoro,
a zuciyarta tace yanzu da ni ce zan mutu, meyasa matar nan takeso ta kashe ni,
wani irin kuka ta fashe dashi ta ruga dakinta da gudu a zuciyarta tana dana sanin sa farin kyallen a gurin,
da tasan na mutuwa ne da ta daukeshi ta konashi bata shimfiďa wani ya hau ya mutu ba,
kuka sosai takeyi tana fadin shikenan nayi kisan kai,
da sauri Affan ya matso kusa da ita yana tambayarta abinda ya faru,
bata bashi amsa ba ta shige can cikin daki ta dauki wayarta ta kira kaka liman,
ringing biyu wayar tayi ya dauka,
cikin muryar kuka ta gaisheshi ya amsa yace lafiya me ya faru, ta kara fashewa da kuka tace kaka nayi kisan kai,
wallhy bansan abun mutuwa bane, na dauka wani tsafin tayi dan ta nakasa mu ashe na mutuwa ne, kaka liman yace nutsu ki fada min komai yadda yake dan bana fahimtar abin da kike fadi,
nan ta tsagaita kukanta ta faďa mishi duk abinda ya faru,
kaka liman yayi ajiyar zuciya yace kwantar da hankalinki Allah baya kama mutum da laifin da bai sani ba, lallai Allah na tare dake Afeeyah shiyasa har ya nuna miki wannan mummnan alamarin ya kuma baki basirar ki mayar mata da kaidinta,
wannan aya ce Allah ya saukar gareta in har tana da hankali,
har gurin Allah baki da laifi dan ba ke kika kasheta ba uwarta ce ta kasheta,
ki dage ki cigaba da addu'a saboda yanzu ne zata kara karfin tsafinta in har tasan kaikayi ne ya koma kan mashekiya,
Afeeyah ta share hawayenta tace to nagode kaka dan Allah ka cigaba da yi min addu'a dan wallhy abubuwan tsoro suke bani,
kaka liman yace babu komai jikata addu'a kullum munayi saidai akara bude wuta, Allah ya dauraki bisa kanta,
Afeeyah tace ameen sannan ta kashe wayar ta fita ta wuce gurin gawar salma....
Kafin karfe 10 angama shirya salma cikin suturarta za'a kaita gidanta na gaskiya,
har lokacin oyizah bata bar ihu ba sai sambatu takeyi tana fadin wallhy babu inda za'a kai mata ya, babu wanda ya isa yaje ya binne mata 'ya a rami,
sosai ta fita hayyacinta tun kukan na fitowa har ya daina fitowa,
dakyar aka fita da gawar salma daga gidan, sai da oyizah ta suma sai uku saboda tashin hankali,
tana farfadowa ta shiga tsine ma mutanen gurin tana fadin ita fa yarta bata mutu ba dan ko ciwon kai batayi ba,
Da mutane suka ga abin nata jahilci ne sai suka watse suka barta da kukan takaici,
Bayan azahar esther ta kara kiran oyizah,
cikin kuka oyizah ta ďauka tana faďin esther salma ta mutu, batayi ciwon komai ba, ko mura ba tayi ba lafiya lau muka rabu jiya da daddare,,
esther tayi dariya tace kin iya acting oyizah halan kina cikin taron mutane ne,
oyizah cikin ihu tace wane irin acting ina fada miki yau da safe mun tashi ba salma shine har kike dariya,
esther tace to ay abin naki ne,
ki bada yarinya da hannunki sannan kizo kina kuka,
oyizah ta zaro ido tace wace yarinya,
esther tace salma mana,
salma kika kawo jiya,
kinsan kuwa saboda hakan da kikayi har mukami aka kara miki saboda kin kawo yarki wacce kika fi so dalilin da yasa na kara kiranki kenan dan inyi miki albishir,
oyizah ta saki wata kara mai rikirtarwa ta mike ta shige ďaki tace esther jinin salma kuka sha,
esther tace wai ko kin haukace ne,
har kiranki fa nayi da safe kikace kina sane kika bayar,
oyizah tace wayyyo na shiga uku,
ni ba salma na bayar ba Afeeyah na bayar, ya za'ayi in bada salma,
esther tace ha'a to ya akayi muka ga salma,
oyizah tayi wurgi da wayar hannunta ta yaye zanin gadonta, nan tayi arba da farin kyalle,
cikin firgici ta fara shafa kyallen tana fadin ya akayi wannan kyallen yazo nan gurin, waye ya kawo wannan kyallen nan,?
waye ya kashe min salmata ta fadi cikin karaji,?
da sauri farida ta shigo dakin