Showing 69001 words to 72000 words out of 72718 words

Chapter 24 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt

16 Dec 2024

2302

shirinta na zuwa gidan alhj basheer ta gama da Afeeyah ta huta, takardun da ta ajiye can kasan katifarta ta daga cikin izza zata dauka taga wayam,
hankali tashe ta bankade katifar tanata dubawa ko idonta ne amma sam bata gansu ba,
cikin tashin hankali ta karaďe arear da take zaune ko zata ganshi nan ma babu labari,
a gigice ta sa takalminta ta nufi cikin gari rike da kwalbar acid da ta tsaya ta siya jiya da daddare kafin ta dawo makwancinta,
bacewa tayi kamar yadda ta saba ta shiga gidan, dakin alhj basheer ta shiga yana kwance yana bacci hankali kwance gidan sai kamshin girki yakeyi,
tana kallon side drawer dinshi ta hango takardun da ta tabbatar ta kwana dasu a dakinta,
a rude ta daukesu tace ya akayi suka dawo nan,
rungumesu tayi tace koma wani tsinannan ne ya dawo dasu to sun dawo hannuna kuma bazasu kuma fita ba,
saurin bacewa tayi saboda jin motsin kofa tayi dakin su Afeeyah,


Kwance ta sameta tana bacci cikin bargo shi kuma Affan yana zaune a gefenta yana duba wasu takaddu, murmushi tayi ta makale jikin bango ta buďe kwalbar hannunta ta ďaga zata zirara a kyakykyawar fuskar Afeeyah,
juyi Afeeyah tayi hade da mika tana faďin
"la'ila ha illallahu muhammad rasoolullah sallalahu alaihi wasallam"
Alhamdu lillaahil-lathee 'ahyaanaa ba'da maa 'amaatanaa wa'ilayhin-nushoor.,,
nan kwalbar hannun oyizah ta fara girgiďi nan take tayi taka juye a fuska da jikinta,
a gigice ta saki takardun hannunta tasa razanannan ihun da saida ya girgiza gidan saboda kararshi,
a firgice Affan yaja Afeeyah yana kallon oyizah da ta sauya kamanni,
mikewa yayi da sauri yana fadin "Allaahumma 'innaa naj'aluka fee nuhoorihim wa na'oothu bika min shuroorihim."
Da gudu su alhj basheer suka shigo dakin suna fadin lafiya, ganin oyizah sukayi a kwance tana birgima ta yage duka kayan jikinta tana ciccisge gashin gabanta dan tsananin azaba,
da kafarta alhj basheer ya ganeta yace safiya!!! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
ya waiga ya kalli zeenatu yace kin gani ko na fada miki safiya bazata kyalemu ba,
"Tabbas bata kyaleku ba dan tana bibbiyarku kullum a cikin gidannan, tare kuke yini da ita,"
sukaji wata murya ta ratso kunnensu mutumin ya bayyana a gabansu,
gaba dayansu suka ja baya a tsorace,
da sauri tsohon yace kar kuji tsorona, ni ba mugu bane, asalima na zama kariya a gareku tun lokacin da take bibiyarku,
a jiya ne ta samu damarta da take ganin ta gama samun komai saboda kwashe wadancan takardun da tayi,
a daren na maido da takardun shine yau ta dawo ta kwashesu kuma tazo da niyyar kashe Afeeyah ta hanyar zuba mata ruwan batir,
cikin ikon Allah sai ta farka da addu'a nan take mai kowa mai komai ya tsareta ya mayar mata da kaidinta,


mamaki suka dinga yi suna Allah wadai da oyizah dake ta faman ihu tana fisge fisgen gashin gabanta,
godiya suka dinga yi ma tsohon har ya bace ma ganinsu sannan suka dawo akayi waje da oyizah dake zabura babu komai a jikinta,
gudu ta dingayi tana ihu kamar mahaukaciya ta fada gidan Malam Atiku,
suwaiba na zaune tana cin kosai tana hararar hajja taji an fado kanta ana ihu,
da sauri suwaiba ta mike tana ihu ta fada daki ta datso tana leke tana haki,
cikin kuka oyizah tace suwaiba nice, nice safiya, suwaiba tace safiya, safiyar alhj basheer,
oyizah tace eh ita, ki bude min kofa,
suwaiba tace Allah ya kyauta in bude ma matsafiya kofa,
safiya ta kara sa ihu tace suwaiba na daina, wallhy na daina, nayi dana sani, ki yafe min, ni na kashe abulbait, ni na bashi sweet yasha ya mutu muka sha jininshi,
suwaiba ta saki salati tayi saurin bude kofar tace ke kika kashe abulbait,
oyizah tace nice ki yafe m--- ay bata karasa ba taji saukar tabarya a bakinta,
wani ihun ta saki ga azabar konewar fuska gata jibgar tabarya,
bugunta suwaiba takeyi baji ba gani tana kuka tana fadin kin cuceni,
dakyar hajja ta hankada oyizah waje ta dawo bawa suwaiba hakuri,
cikin kuka tace hajja ki yafemin na cuci kaina, dan ALLAH ki yafemin,
hajja tace babu komai ai dama duk wanda ya hau motar kwadayi to babu a inda zata saukeshi sai tashar wulakanci,
wannan ya zama darasi ga masu hali irin naki,
daki suwaiba ta shige cikin nadama tana kukan mutuwar danta....


Kwanan oyizah huďu tana yawo akan titi babu wanda yake kulata bare yayi yunkurin taimaka mata,
gaba daya ta gama cisge gashin gabanta da hannunta,
ga ciwon jikinta da fuskarta yana mata radadi kamar zai tarwatsa kwakwalwarta,
gurin wata kwata take zama ta dinga ďiban ruwan gefe tana watsawa a jikinta ko zata samu sassaucin azaba,


a ranar kwana na biyar din ne tana zaune tana ihu tana fadin irin mugayen abubuwan da tayi taji an tsuguna a gefenta,
da ido ďaya ta kalli gurin taga Afeeyah ce ta daga kanta taga fareeda tsaye tana kuka,
mikewa tayi tana kokarin rungume farida tayi saurin ja baya tace karki tabani mummy,
zuwa kawai nayi in ganki saboda an fada min hakkinki a kaina,
Afeeyah tace a'a fareeda uwa uwa ce, kome tayi mahaifiyarki ce,
oyizah tayi tsaki cikin azaba tace kece ma kike fada mata abinda zata min,
ta kalli farida tace wannan ce take saki a hanya,
zata kara magana ciwon jikinta ya mintsileta ta zaburah ta fara tsalle tana kokarin sosa jikinta, Afeeyah ta kalli farida tace kije ki kamota farida mu suturc--- bata karasa magana ba sukaji karar bugun abu,
da sauri suka kalli gurin wata katuwar trailr ce tayi ciki da oyizah ta murje kanta,
da gudu suka isa gurin mutane har sun taru ana kallon oyizah amma babu wanda yayi yunkurin taba ta, wasu daga sun kalleta suke barin gurin,
sunfi karfin awa daya a gurin babu wanda ya taimakesu dakyar drivernsu ya dauketa aka nadeta cikin boot suka tafi da ita gida,


saida zeenatu tasa baki sannan alhj basheer ya kira akayi mata wanka aka suturce ta,
daga alhj bara'u sai alhj basheer sai malam atiku da masu aikin gidan kadai suka tafi kai oyizah gidan ta na gaskiya,
gidan da kafa bata fitowa,
gidan da ibadarka sune abokan hirarka,
gidan da kudi ko mulki bazasu hanaka kwanciya kan kasa ba,
gidan da babu fanka bare a.c babu iskar shaka sai in kayi aikin alkhairi,


Allah kasa mu cika da kyau da imani......
Ameen


Tunatarwa--
Ya yan uwana mata masu son mallakar namiji ta kowane hanya,
shin in mun mallakeshi muna tunanin in mun mutu wannan mallakar bazata hana namiji ya manta damu yaje ya nemi wata ya aura ba,
mallakar namiji itace biyayyarki in kikayi ma namiji biyayya tsakani da Allah wallahy kin gama mallakeshi duniya da lahira dan bazai taba mantawa dake ba,
akwai matan da suke wanke najasar gabansu su sawa namiji a abin ci ko sha,
wallhy,
wallhy,
duk macen da take wannan aikin in tazo mutuwa sai ta cisge gashin gabanta gaba daya da hannunta, shan najasa haramun ne,
cutarwa ne ga dan uwa musulmi,
in mallaka muke so to muyi koyi da matan manzon Allah s.a.w, akwai ayoyin saka soyayya a zuciya ko ita muka rike mun gama mallakar mazajenmu ba cuta ba cutarwa,
saboda saida soyayya mallaka ke tafiya,
Allah ya ganar da dukkan yan uwa musulmi baki daya, su kuma mazajenmu masu sa mu kauce hanya ta hanyar wulakanta mu Allah ka ganar dasu ka basu ikon kulawa da hakkokinmu Ameen thumma Ameen...


In shaa Allah gobe zan gama muku gaba daya,
kuyi mini afuwa na rashin posting da wuri


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣6⃣ By Aysha Ya'u kurah


Rayuwa mai cike da so, kauna, nishaďi, farin ciki, da annashuwa shi akeyi a gidan alhj basheer, rayuwar mai cike da koyarwar addinin islama,
Ni'imtacciyar rayuwa sukeyi wacce duk a da suka cire rai da samunta,
Alhj basheer yana matukar kula da kowa a cikin gidan, duk wasu hidimdimu nasu yana kokari wajen daukeshi ba tare da sun kai ga bukata ba,,
haka zeenatu kulawa sosai takeyi ma kowa har masu aikinta, bata bari kowa ya koka saboda matukar sanin darajar biladama,
Fareedah ma rayuwa takeyi me dadi wacce take ganin ashe da can baya ba rayuwa takeyi ba saboda tana zaune cikin duhun kai ga rashin samun nutsuwar zuci saboda rashin ibada da batayi, yanzu kuwa wani nishaďi take ciki musamman in ta idar da sallah sai ta dinga jin kamar iskar wannan lokacin daban take saboda yadda take ratsa ko ina na jikinta...


( tabbas iskar wannan lokacin kam daban take ga wanda ya hankalta,
duk wani musulmi da zaran ya idar da sallah to nasan a wannan lokacin zaiji kamar an sauke mishi wani nauyi akanshi kuma zai dinga jin yalwatacciyar iska mai dadin gaske,
kaii musulnci yayi, Allah ka sa duk ibadun mu karbabbu ne, Alhamdulillah ala ni'imatul islam)....


Soyayya da shakuwa su suka shiga tsakanin ma'auratan biyu, soyayya sosai suke gwadawa junansu haďe da mutuntawa, basa taba yarda su bata ran juna,
komai nasu suna yinshi cikin so da kulawa gwanin ban sha'awa,
Affan sam baya kaunar ganinta ita kaďai tana damuwa dan yasan damuwar akan jabeer ne,
wani lokacin ma in ya sameta tana kuka in ya bata hakuri sam bata yin shuru har sai ya dangana da zeenatu sannan dakyar zasu hadu su rarrasheta tayi shuru,
shima kuma duk ranar jumma'a sai ya kai ziyara kabarin amininshi bayan yasa an sauke qur'ani yayi sadaka sannan ya zauna a gurin ya dade yana mishi addu'a,
haka cikin dare in sun idar da sallah addu'a ta musamman suke mishi da sauran yanuwa musulmai wadanda suka rigamu gidan gaskiya...


Cikin ikon Allah cikin Afeeyah ya isa haihuwa yayi girma sosai dan ko mikewa bata iya yi in kuwa ta mike to sai tafi minti ďaya kafin ta iya daga kafarta,
rubutu da magunguna sosai take shansu dan kaka liman musamman yake mata jarkar rubutu tun cikinta na wata,
a wannan lokacin ne wani dare ta farka da nakuda mai zafin gaske,
cikin gaggawa suka kaita asibiti, likitoci sun fi karfin awa biyu akanta ana abu ďaya,
Affan kuka ya fita waje yakeyi saboda jin irin kukan azabar da takeyi,
ganin har lokacin ba improvement doctor ya yanke shawarar yi mata c.s saboda service dinta bai buďe ba,,
alhj basheer da kanshi yasa hannu saboda yadda yaga ta galabaita,
a gaggauce suka shiga da ita dakin theater suka fara aikinsu cikin kwarewa,


cikin farin ciki doctr ya fito musu da jarirai mata manya manya guda biyu,
da sauri zeenatu ta mike ta karbi ďaya alhj basheer ya karbi daya sunata ma doctor godiya,
Affan kuwa bai bi takansu ba dakin da aka kai Afeeyah ya shiga ya zauna gefenta yana shafa kanta yana mata addu'a yana jin sonta na kara ratsa ko ina jikinshi...


Kwananta hudu a asibiti aka sallameta suka koma gida aka cigaba da kula da ita da yaran dan jikinta har lokacin baiyi kwari ba,,
Ranar suna yara suka Amsa sunan Asma'u (Nuwairah) da Zeenatu (Nawwarah),
anyi shagalin suna cikin kwanciyar hankali dangi kowa ya halarci sunan harda su suwaiba da akayi nadamar gaske...


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah


★ 7yrs ltr ★


Tsaye take a kofar islamiyya tana jiran fitowar yara su tafi gida,
tana tsaye jikin motarta da ďan cikinta na wata hudu tana siyan tsamiyar biri,
ihun fitowar yara ne yasa tayi saurin mika ma mutumin kuďi ta bare daya tasa a bakinta ta fara hangen yara,
can ta hango rabon faďa cikin taron yara malaman na rabawa yaron na kara tusa kanshi yana kuka yana fadin shi sai ya rama,
da sauri Afeeyah ta jefa ledar hannunta cikin mota tayi gurin yaron tana faďin Oh my Word JABEER again,
ta kamo hannunshi da karfi tace wuce mu tafi, ya tsala ihu yana magana cikin kuka ta make bakin tace rufe min baki masifaffe kawai,
ta kalli Nawwara dake kwaso mishi takalmi tace kuna tsaye ku bazaku iya kamo hannunshi ku fito ba kun tsaya kuna kallonshi yana fada,
Nuwaira tace wallhy mummy mun hanashi yaki har haurin Nawwara yayi,
tsaki tayi ta bude motar ta wurgashi baya su Nuwaira suka shiga ta ja motar ta wuce tana masifa shi ko sai tsala ihu yakeyi,
shop rite ta wuce dasu tayi siyayyarta ta sai musu ice cream suka fito suka wuce gurin mota,
tana buďe motarta taji ihun wani yaro cikin motar kusa dasu,
da sauri ta rufe kofar ta nufi gurin taga jabeer tsaye yana huci, cikin bacin rai tace me yayi maka ka dukeshi, jabeer ya turo baki cikin maganarshi ta yara yace tun da muka shigo yake kallona,
Afeeyah ta dauke keyarshi da mari tace uban me zai kalla a jikinka,
dan kaga bana dukanka shiyasa kake iskanci san ranka ko,
ta ja hannunshi yana ihu ta turashi cikin mota ta koma ta rarrashi yaron taja mota suka wuce gida,
a bakin gate suka tarar da Affan,
tun kafin a bude gate din jabeer ya balle motar ya fito ya ruga gurin shi yana kuka ice cream din hannunshi duk ya zube a kasa,
kwace robar yayi ya wurgar ya dagashi sama yace waye ya taba min kai,
jabeer yace ba mummy bace tun a islamiyya take dukana har mukaje chopurite tana dukana tana zagina suna ta min dariya,
Affan ya hade rai kamar gaske yace tun a islamiyya take dukanka har a chopurite,
jabeer ya gyada kanshi,
Affan yayi kwafa yace muje gidan yau sai ran kowa ya baci,
suna shiga ya tarar da ita a kitchen tare da Amirah ya kalleta yace me babyna yayi miki kika dukeshi,
Afeeyah tayi tsaki tace nidai dan Allah gobe ka siyo min rago wallhy canjin suna za'ayi wannan ba jabeer bane,
jarabar tayi yawa, kullum sai yaro yayi dambe a islamiyya,
sai shegen tsaurin ido ko kallonshi akayi sai ya daki yaro in yafi karfinshi,
Amirah tayi dariya ta dungure kanshi tace gaskiya yaya Affan ka siyo mana ragon suna wannan bai amsa sunanshi ba,
jabeer ya kai ma Amirah duka yana kuka Affan yace har da ke ko Amirah,
to zanga mai canza mishi suna,
ya kalli Afeeyah yace ke meye bakiyi ba, tace naji nayi amma bankai wannan mai katon kan ba,
kuma canza suna ya zama dole in na haifi salihi sai insa mishi jabeer amma wannan JAZULI zan sa mishi,
Amirah dasu Nawwara suka fita suna dariya sosai,
Affan ya share ma jabeer hawaye yace rabu dasu yanzun nan zamu fita yawo ko mutum daya bazai bimu ba,
jabeer ya shanye kukanshi yana ma Afeeyah gwalo, tsaki tayi ta cigaba da abinda takeyi tana mita....


Washe gari da safe suna zaune suna shan tea,
kowanne jikinshi da skool uniform gwanin ban sha'awa,
jabeer na zaune yana shan tean shi yana daukar bread baya ko kallon su Nuwaira,
kallonshi sukeyi suna dariya dan yaci slize bread fin shida kuma ya cinye kwan gabanshi,
yana jin dariyar da sukeyi kasa2 bai tanka musu ba,
yana gamawa ya mike yana mika ya zagayo gefen da suke ya ďauki kofin tean Nawwara ya kwara musu a jiki ya dauke kwan plate dinta ya ruga cikin daki da gudu yana dariya,
mikewa sukayi baki bude ga zafin tea ga haushin yasa sai sun canza kaya,
Nuwaira da idonta ya ciko da kwalla tace wallhy sai na ma yaron nan dukan tsiya, Nawwara tace ki kyaleshi sai munje skool,
Nuwaira tace wallhy a gida zai daku ji yadda ya bata min jiki,
cikin fushi tayi hanyar dakin ta murďa kofar, wayar av din jikin game ta cire ta fara tsuga mishi,
nan ya dinga ihu yana shigewa jikinta Nawwara ta fincikoshi tana dukanshi da hannu yana ihu yana ramawa,
a gigice Afeeyah ta diro a gado ta fito tana kiran me aikinta taji ko lafiya,
kafin ta kai ga shiga dakin Affan dake parlor yana jiransu har ya shige yana ta ma su Nuwaira masifa,
cikin fushi Afeeyah ta kwace wayar hannunta tace dukanshi kukayi har da waya,
Nuwaira ta fara kuka tace mummy ruwan zafin tea fa ya watsa mana a jikinmu kalli kayanmu,
Affan yace me kuka mishi ya watsa muku nasan haka kawai bazai watsa muku ba, Nawwara tace wallhy babu abinda muka mishi,
jabeer yayi saurin cewa karya takeyi dariya suke ta min,
Afeeyah ta kalleshi a hassale tasa hannu zata janyoshi ya sa ihu ya shige bayan Affan yana fadin wayyo mummy kiyi hakuri, Afeeyah ta rike kanta tace wallahy yaron nan zai iya haukatar da mutum,
na kusa daukar ka in mayar dakai bolar da na tsinto ka kaje can cikin yanuwanka spiders, coacroach da sauransu,
jabeer ya leko yace wai haka daddy,
Affan ya daukeshi suka fita yace eh mana tunda baka jin magana,
Afeeyah ta kalli su Nuwaira tace tsayuwar me kuma kukeyi,
ko inzo in shiryaku ne, sukayi saurin fita daga dakin suka je suka canza kaya suka wuce skool...


Bayan yan kwanaki, Afeeyah na zaune ta mike kafarta tana tsinkar ayayo, yara kuma na gefenta suna wasa,
jabeer kuwa yana zaune yana shan cornflakes yana kallon cartoon,
Amirah ce ta shigo gidan tana ma jabeer wakar tsokana, hararrta yayi ya cigaba da kallonshi,
kanshi ta taba tace su jazuli ba tayi,
ya buge hannunta ya turo baki yace kece jazuli,
Amirah tayi dariya ta zauna kusa da Afeeyah ta dauki sandar ayayo daya tace har yanzu su umma basu dawo ba,
Afeeyah tace kedai bari ina missing dinsu wallhy ko dan wancan dargozon,
Amirah tayi dariya tace ummi ce ta aikoni tace ki tambayi yaya Affan gobe zanje kaduna wai su Nawwara su shirya mu tafi tare,
Afeeyah tace to ba matsala amma banda jabeer ko,
Amirah tace wake gaba in ba shi ba, kin san anty asiya in bamuje dashi ba sai munsha query, Afeeyah tace wallhy masifarshi ce bana so, gashi in sun hadu da irfan dinta suyi ta fada kamar jakai,
Amirah tace ay duk daya suke mugun rashin jin tsiya,
Afeeyah tace ay inaga ke zamu hadawa kuje can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login