Showing 12001 words to 15000 words out of 72718 words
Chapter 5 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt
ta cire rigarta tana kallon kanta a mudubi, kirjinta ne kadai ya ciko amma mararta a shafe take, maida rigarta tayi tana adduar Allah ya tabbatar da wannan abun,,
Washe gari tun asuba ta gama shiri dama bata rintsa ba tana ta addua,
karfe takwass dai2 ta fito suka wuce dan mai gidan baya gari sunyi tafiya shi da oyiza mai laulayi wai batasan warin gidan da nigeriar gaba ďaya, (samun guri),
AKTH suka nufa, basu wani sha wahala ba saboda akwai kawar Abida a asibitin,
test din jini akayi mata aka tabbatar da tana da ciki,
scanning ppr aka bata suka je tayi scanning inda ya nuna makalallen ciki na wata hudu, '"HAMDAN KASIRAN DAYYIBAN MUBARAKAN FIHI,"" abinda zeenatu ke fadi kenan hade da kuka, saida suka gama komai a asibitin Abida ta maidata gida cike da murna ta tsaya tayi wa su Ma'u albishir sannan ta wuce aiki,
Hajja da ma'u a lokacin suka shigo taya ta murna,
har ta ďaga waya zata kira alhj basheer ta fada mishi sai wata zuciyar ta haneta, haka gida ma so takeyi ta musu surprise,
Kula sosai take bawa cikinta da ya kai wata biyar har ta fara zuwa awo alhj basheer da oyiza basu dawo ba, gidan Abida take zama suyi hirarsu lokacin ta haifi ďanta namiji mai suna JABEER,
Cikin zeenatu na wata bakwai su oyiza suka dawo itama da nata cikin watanshi bakwai, fitowa tayi cikin hijab tana musu sannu da zuwa,
alhj basheer ne kadai ya amsa babu yabo babu fallasa, ta kalli salma tace ummu ya hanya,
salma tayi banza da ita suka wuce daki ita da mamanta, saida alhj basheer yayi wanka ya huta sannan ya fito cin abinci, zeenatu ce tayi serving dinshi tana mishi hira yana amsawa jefi2, bayan ya gama cin abincin ne ta fara mishi magana cikin hikima,
tace ranka ya dade kudi nakeso,
ya yatsuna fuska yace me zakiyi da kudi, ta sunkuyar da kanta kasa tace siyayya nakeso inyi ma kyautar da Allah ya bani,
cikin rashin fahimta yace ban gane ba, ta daga hijab din jikinta ta dauko hannunshi ta ďaura kan cikinta tace Allah ya azurtani da ciki har na tsawon wata bakwai,
"karaf a kunnen oyiza da ta fito cin abinci,"
fuskar alhj basheer ta kasa boye farin cikin da yake ciki a wannan lokacin, janyota yayi ya zaunar da ita kan jikinshi sam bai kula da oyiza ba, ya kalleta yana shafa cikin da ya dan taso yace da gaske zeenah,
ta gyada mishi kai, yayi murmushin jindadi ji yakeyi kamar wannan ce haihuwar da zaiyi ta fari, yace Allah ya fito min da abinda ke cikin nan kuma yasa namiji--- ta maza ta toshe mishi baki tace namiji da mace duk Allah ke hallitarsu,
muyi fatan samun masu albarka shine kawai yallabai,
yaji wani nutsuwa ta ratsashi yace hakane Allah ya bamu masu albarka, "mtswwwwwww" sukaji an ja tsaki mai karfi suka waiga suka ga oyiza tayi gaba tana huci kamar zakanya,
kau da kanshi yayi ya cigaba da kallon cikin zeenatu yace gobe ta shirya suje siyayya da asibiti a kara duba lafiyarta,
sun dade suna hira cikin jin dadi ya ma manta da wata oyiza a rayuwarshi...
Oyiza kuwa tana shiga ďaki ta maida salma ďakinta, ta hau kan buzun tsafinta sai gata ta bayyana gaban "chummy" idonta jawur take fada ma chummy halin da take ciki, chummy tayi iya yinta da duk wasu siddabarun da zatayi tace oyee wannan cikin bazai zube ba, cikin jikinta na tare da kariyar adduoi sosai sai dai ki bari in ta haifeshi sai kisan abun yi,
cikin tashin hankali tace "my lord" to idan ta haifi namiji fa, chummy tace sai kinso ya rayu in ya fito duniya,
oyiza hankalinta ya ďan kwanta tayi sallama da chummy ta bace ta nufi gida....
Ciwo takeji sosai amma hakan bai hanata ci gaba da aikinta da tasbihi a bakinta ba,
wani irin Murďawa mararta tayi ta tsuguna da sauri tana faďin "YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKHA ASTAGITHU ASLIHLI SHA'ANI KULLAHU WALA TAKILNI ILA NAFSEE ĎARFATU AYNUN" da dai taga abun kamar gaba yakeyi ta mike tayi hanyar parlo tana maimaita adduoi a bakinta,
oyiza na zaune tana cin abinci zeenatu ta shigo da kyar, tace dan Allah safiya ki taimak--- ta kasa karasawa saboda wani irin nishi mai karfi da yazo mata,
oyiza tayi tsaki ta juya tana adduar Allah yasa ki mutu ke da ďan cikinki,
zeenatu kuka sosai takeyi ga wani ruwa dake bin kafarta, sallamar Abida taji nan taji kamar an sauke mata zafin wani bangaran, da sauri Abida ta karaso ta ajiye jabeer tace haba zeenatu ay da sai ki kirani a waya, zeenatu ta runtse bakinta ta rike hannun Abida dake kiran Ma'u a waya,
da sauri ma'u ta shigo suka kamata,
Abida ta kalli oyiza tace dadin abin nakuda Allah bai ďauke wa uban kowa ba, kowacce yar iska zata dandani nata in lokaci yazo,
oyiza ta harzuka matuka ta mike tana bala'i suka fita sukayi banza da ita, drivrn gidan ya karaso da sauri suka wuce asibiti,
Suna shiga Allah ya taimaketa batayi wata doguwar nakuda ba ta haifo ďanta namiji kyakykyawa mai kama da iyayenshi,
likitoci suka shirya baby suka kimtsa mamanshi suka kwashe mata jini suka turota dakin hutu, murna a gurin su ma'u ba'a cewa komai, Abida ta kira Alhj basheer tayi mishi albishir,
murnar da yayi a lokacin ba mai faďuwa bace, saida yaje gida ya shirya sannan ya fito zai tafi asibitin, oyiza ta fito rike da kugu tace ina zaka je, ya fadada fara'arshi yace hospital zeenatu ta haihu,
oyiza ta kauda kanta tace Allah ya raya, yace ameen, har yayi gaba, ta tuna ta kwala mishi kira ya tsaya tace me ta haifa, yace baby boy,
wani irin murdawa mararta tayi cikin ruďewa tace namiji kenan ta haifa,, yace eh mana,
ya shiga mota cikin farin ciki ya wuce ya barta tsaye kamar an dasata hawaye masu zafi suna kwaranya a idonta....
ayshakurah.mywapblog.com
Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Ciki ta juya tana tafiya da kyar, ga bakin ciki ga kullewar mara,
a gado ta kwanta tana kuka sosai kamar wacce akayi ma mutuwa,
sai da tayi kuka ma'ishi sannan tayi shuru da tunanin itama fa cikin gareta kuma chummy ta bata assurance din namiji zata haifa,
yanzu kawai abinda ya rage mata shine tasan yadda zatayi ta kashe jaririn nan tun kafin ya girma yasan kanshi, da wannan tunanin zuciyarta tayi wasai ta mike ta shiga wanka..
Kwanan zeenatu huďu da haihuwa kullum da daddare alhj basheer na makale a ďakinsu, duk wanda ya ganshi a kwanakin yasan farin ciki ne cike da zuciyarshi, haka mai jego na samun kulawa daga gurin makotanta da kanwar kakarsu Yadikko da tazo daga cameroon,
a ranar da suka cika kwana shida da yamma sunyi wanka ita da baby yadikko ta debo rushi tasa garin "habbatis sauda" a ciki tana sa hannunta a hayakin in ya dau zafi saita daura a kan cibiya da marar jaririn tana karanto adduoi tana tofa mishi, juyawa oyiza tayi da sauri da ta tunkaro dakin da wasu magungunan tsafinta wanda chummy tace in har ta shafi babyn da maganin a hannunta to tabbas jininshi zai kafe ya mutu,
jin hayakin tayi kamar zai tafi da ranta, ta shiga daki da sauri ta datso kofa tana haki haďe da kakarin amai, ta dade sosai a haka kafin wani irin murdaddan ciwon mara ya dawo da ita daga duniyar azabar shakar hayakin habbatis sauda,
ciwon da oyiza taji ne yasata sakin ihu tana karawa kamar zararriya, babu wanda yajita dan su yadikko suna can suna hira dasu hajja da suka shigo a lokacin sunata preparation din suna washe gari,
sai da ta galabaita sosai tana ihu tana faďin "ohh my lord" "chummy wr are u,"
Ma'u ce ta fara jin ihun saboda zagayawa baya da tayi dan kwaso shanyar baby, da sauri ta zagayo ta faďa musu suka mike sukayi dakinta suka murďa sunata bugawa yaki buduwa saboda tasa key,
kiran alhj basheer zeenatu tayi lokacin har oyiza ta suma saboda azaba,
cikin yan dakiku ya baro inda yake ya dawo gida ya dauko spare key ya bude dakinta,
kwance cikin jini suka sameta, da sauri suka karasa suka kamata suka sata a mota sai asibiti,
dakin theater aka wuce da oyiza, cikin gaggawa likitoci suka shiga ceton ransu ita da babyn,
cikin nasara suka samu fitowa da baby mai kyan gaske gata katuwa dan da sukayi wghn dinta ta kai 6.2kg, doctor yayi ma oyiza "PS" nurses suka shirya baby suka fito ma alhj basheer da ita, cikin murna ya karbeta yana kallonta yana mata addua,
ita kuwa oyiza sai can cikin dare ta farfado tana ihun kuka dakyar,,,,
wata nurse ce a gefenta da yadikko suka matso suka riketa suna fadin sannu,
ta kwanta lamoo tana shafa cikinta dakyar tace na haihu ne, yadikko ta daga mata kai tace eh kin haihu, tayi murmushin da bata san ya fito ba saboda azabar ciwo tace ina yaron yake, yadikko ta fito da babyn cikin gadon jarirai tace gata nan, oyiza cikin rashin fahimta ta gwalo dasassun idanuwanta tace gashi nan ko gata nan,
yadikko tace gata nan dai inaga bakiji da kyau bane,
oyiza ta waigo a hankali ta kalli babyn ta juyar da kanta tana kuka sosai tace "why chummy" why? Meyasa zan haifi mace, kin manta alkawarin da kikayi min,
meyasa zeenatu zata haifi namiji ni mace,
meyasa zanyita haihuwar mata, magana oyiza takeyi cikin zaucewa tama manta da wata yadikko a kusa da ita, saida tayi kuka sosai nurse tazo tayi mata allura sannan ta samu bacci,
Yadikko komawa tayi ta zauna tana kallon oyiza tana mamakin furucinta, tabbas sai sun mike tsaye akan zeenatu da ďanta saboda wannan furucin na oyiza ba karamin ďaga hankalin yadikko yayi ba, '"CHUMMY" kalmar da ta dinga maimaitawa kenan a ranta, wacece kuma chummy? tambayar da yadikko tayi ta ma kanta kenan ta kasa samo amsa daga karshe ta mike ta shiga tayi alwala ta fara nafilar nemawa jikokinta tsari daga sharrin makiya...
Ranar suna jariri yaci suna AFFAN, anyi taron suna na gani na fada mutane sunzo sosai tayasu murna, faďin farin cikin da duka su biyun suke ciki bata lokaci ne domin bazai taba misaltuwa ba, oyiza kuwa tana can cikin bakin ciki dan tunda ta farka anyi anyi ta bawa baby nono taki, kuka kawai takeyi tana tufka da warwara, maimakon isharar da Allah ya nuna mata yasa ta saduda tasan babu wani mai yi sai shi taki ta gane, sam batayi gv up ba sai ma wani karin mugunta da zuciyarta ta naďo, babu abinda yafi daga mata hankali sai cewa da doctor yayi mahaifarta bazata kara rike kwai ba saboda ta samu gagarumar matsala,
a wannan lokcin likitoci sunga bori saboda tsine musu kawai takeyi tana zaginsu, dakyar alhj basheer ya lallabata da kalamai masu kwantar da hankali,,,
Kwananta hudu a asibiti aka sallameta ta dawo gida da muggan kudirai a cikin ranta, a zuciyarta tace wannan karan ita zata zama shaidaniyar kanta dan taga yanzu aikin chummy baya tafiya mata yadda ya kamata,
haka ta cigaba da jinyar jikinta da kula da yarta wacce taci suna FAREEDAH,
oyiza kullum idonta na kan side din zeenatu taga ko sun bar Affan shi kaďai amma bata samun wannan damar saboda yadda yadikko ke manne dashi a ko dayaushe,
sai da yadikko tayi wata biyu a gidan tana kula da zeenatu,
tun ana saura sati ďaya ta tafi kullum dare bata aikin da ya wuce yi ma zeenatu faďa akan ta kula da kanta da ďanta da kuma adduoi,
zeenatu saidai tayi dariya dan abin na yadikko ya zame mata kamar waka tunda kullum sai anyi maimaicinshi..
Cont 14
Salma ta kalli mahaifiyarta tace mummy kika ce wannan nawa wannan na affan ko,
oyiza tace a'a wannan ne naki, ki kula fa sosai, ta gyaďa kanta ta fita da gudu fareeda na binta a baya,
Affan zaune suna bin karatun lptp din yara na "alifun ba'un" shi da jabeer lokacin shekararsu biyu da rabi shi da fareeda ita kuma salma ta kusa 6, dafashi salma tayi yayi saurin ďago kanshi, a razane ya matsa dan mugun tsoronta yake ji saboda dukkan da take mishi,
zama tayi kusa dashi ta kara duba ice cream din dan ta tabbatar da wanda mummy tace na affan din ne, mika mishi tayi tana murmushi tace gashi inji mummy,
farida cikin gwaranci tace "wanshan ne naci," salma ta harareta tace wannan ne, farida ta dage akan dayan ne saboda tafi salma wayau, kuka ta fashe dashi da taga alamar salma bazata bashi wanda mummyn tace ta bashi ba,
da sauri zeenatu ta fito tace lafiya me aka miki farida,
salma tace ice cream mummy ta bani in kawo ma affan kuma wannan ne nashi wai ita dole sai dai in bashi Nawa, farida cikin kuka tace "wanshan ne mummy ta kaya mici sugar" kuma "cha kiji" ,
gaban zeenatu ya faďi sosai tace to duk bari in raba muku gardama ke salma je ki kara tambayota wanne ne na affan din,
da gudu suka fita suka bar zeenatu cikin jimamin maganar farida,
innalillahi kadai take fada tana kara rokon Allah ya tsare mata ďanta da a kullum sai an kawo mishi harin kisa tun yana karaminshi,
shafa kansu tayi shi da jabeer tace ma jabeer tashi kuje gidan Antie Ma'u kafin umminka ta dawo kaji,
ya gyada mata kai ya kama hannun affan dan yafi affan wayau, har sun fita ta tuna da kar su hadu da su salma ta bashi ice cream din yasha,
binsu tayi da sauri tace ku dawo bari Gaje ta dawo daga kasuwa sai ta kaiku kunji, ta kamo hannunsu suka shigo ciki dai2 lokacin su salma suka dawo da ice cream daya suka ce gashi wannan ne nashi,
zeenatu ta amsa tace to kuce ya gode sosai, salma tace mummy tace yasha a gaban mu sai mu tafi, zeenatu tace to an gama yaran kirki bari in raba musu shi da jabeer,
ta mike ta shiga kitchen, Allah ya taimaketa akwai nashi na jiya a fridge, daukowa tayi ta raba musu shi da jabeer ta fito ta mika musu tace gashi maza ku sha ku tafi gidan anty ma'u wanda bai shanye ba a gida zai zauna, suka karba suka fara rige rigen sha,
salma da farida suka fita da gudu tun kafin su kai ďaki suke rige rigen faďin mummy yasha,
suna karasawa ta toshe bakinsu tace ku rufemin baki ku wuce ku bani guri, suka wuce ciki suka dau nasu suna sha,
zama oyiza tayi cikin farin ciki dan tasan yau babu makawa aikinta yaci tunda har sun tabbatar mata yasha,,
har bayan isha tana kasa kunne taji ihu, amma shuru takeji hankalinta ya fara tashi,,
karfe 9 lokacin taji dawowar alhj basheer ta mike ta fito ita da yaranta,
zaune ta taddashi affan na kan ruwan cikinshi suna hira suna kyalkyace dariya kamar da sa'anshi yakeyi,
wani abu ne ya tokare mata wuya wanda ta kasa controlling dinshi har ya kaita ga jan razanannan tsaki, taja hannun farida dake kokarin zuwa gurin babanta tace dalla wuce kuje ďaki, an faďa muku ta taku yakeyi, ai ku muna ya'ya ne a gidan nan amma ba ya'ya ba,
alhj basheer ya dago da sauri yace haba safiya,
me yasa kike faďin haka, da affan da su salma duk daya ne agurina,
da karfi tace biyu ne, karka kara cewa ďaya ne, ka riga ka nuna musu tun yanzu basu da wata daraja a idonka saboda sun zo a ya'ya mata,
nan ta shiga masifa kamar zata tsaga gidan, bakin ciki ne dankare a zuciyarta saboda yadda in tayi abu akan affan baya kamashi,
alhj basheer bai kalleta ba ya kara rungume affan da ya tsorata ya mike ya wuce ciki ya barta anan tana bala'i......
Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a gidan alhj basheer,
kullum da sabon makirci da muguntar da oyiza ke fitowa dashi na tsafi da kuma na magunguna amma dayake rayuwarmu da mutuwarmu tana gurin rabbil izzati babu abinda ya faru da zeenatu da affan duk da wani lokacin in tayi tana cin nasara saboda ance tsafi gaskiyar maishi sai dai duk tsafin mutum in har ka dogara da Allah to ko ya kamaka na ďan lokaci ne zai sake ka,
a yan shekarun da suka wuce oyiza ta kara karfi cikin kungiyar asiri dan yanzu haka tana cikin kungiyoyi masu karfin gaske guda hudu, zeenatu kuwa addua takeyi ba dare ba rana akan Allah ya kare su ita ďanta ya ďaurasu akan makiyansu...
Affan da jabeer zaune ďakin hajja suna cin danwake,
jabeer ya kalli affan yace kaii yau banga su anty salma a skool ba, affan ya juyar da kanshi yace ohoo musu wai dan daddy yace shi zai kaini zana C.E exams su su jira driver shine sukayi fushi mummynsu tace bazasu ba,
Hajja dake gefe tana saka suwaitar kulu tace ca nakeyi ajinku daya da farida kenan bata rubuta jarabawar ba,
jabeer yayi dariyar shakiyanci yace dondi kenan hajja, ay anyi mata repeating yanzu p4 take,
Affan yace p4 din ma da ya aka bari ta kai,
ni ay ban taba ganin wacce brain dinta baya ďaukar karatu irin farida ba cewar jabeer,
Affan yace tabb ay wallhy gara farida a haka, dan anty salma knws nottn banda mugunta,
ma'u ta ďeko dakin hajja da tsohon cikinta da kullum suke adduar Allah yasa zaunanne ne tace ashe baku wuce gida ba, na ďauka ma kun tsufa a gida,
jabeer yace eh "Mama" sunan da yake kiranta dashi kenan saboda a gurinta ya girma bacci kadai ke maidashi gida", yanzu zamu tafi muna nan muna cin ďanwaken tsohuwa,
Ma'u ta juya tace ai ya kamata kuje gida ku faďa musu kun gama jarabawar sai kuma a ďan fita yawo