Showing 30001 words to 33000 words out of 72718 words
Chapter 11 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt
bullo ta kanshi,
kuka mutanen gurin sukeyi suna salati saboda sun tabbatar da wanda suka ciro a cikin motar nan bashi da sauran rai,
da sauri suka soma bincika aljihunshi dan motar babu abin dauka a cikinta, driving licences suka gani sai kudin da ya baci da jini ko ta ina,
farar shaddar jikinshi ma babu wanda zaice fara ce dan duk ta koma ja, basu samu adress dinshi jikin d.l din ba sai dai sunanshi,
daukarshi sukayi cikin mota suka shigo cikin garin kano suka zarce police station dashi,, (innalillahi wa inna ilahir rajiun)
A kuma dai2 wannan lokacin Affan na zaune kusa da daddynshi suna dan taba hira duk da rabin hirar tasu shirme ce,
a hankali ya karkatar da kanshi yana kallon daddy idonshi ya ciko da kwalla yace daddy yau ma kaga har dare yayi abokina baizo ba, ya kalli inda ya tara wasu fararen duwatsu guda 8 na kirga yace daddy kagani yau kwana 8 kenan,
alhj basheer ya shafa kanshi yace kayi hakuri Affan kasan yanata shirye shiryen biki dole ka rage ganinshi,
Affan ya marairaice fuska yace to daddy ni yaushe zaka min aure, alhj basheer yayi dariya yace duk ranar da ka shirya Affan,
Affan yayi dariya shima yace daddy ay na shirya, daddy yace to wacece matar,
Affan ya rufe idonshi yana girgiza kai fuskar Afeeyah nata mishi yawo a cikin kwayar idonshi da kwakwalwarshi,
yayi saurin bude ido yace Barbie din jabeer, daddy ya kara sautin dariyarshi yace wacece kuma barbie, Affan yace AFEEYAH, daddy yayi dariya yace Afeeyar da jabeer zai aura,
Affan ya gyada kanshi yana dariya yace eh daddy ay yace zai bani ita ta dawo nan gidan da zama,
daddy yayi dariya yace to naji tashi kaje ka kwanta kaga ruwa na neman tsugewa,
Affan ya mike yana murna yana fadin daddy zai aura min barbie..
dariya alhj basheer yayi ya mike ya wuce dakinshi dan oyizah tayi tafiya tun da safe..
Affan na shiga ďaki ya haye kan gado yanata wakar abu ďaya, tsawar da akayi mai karfi tayi daidai da faďuwar gabanshi, mikewa yayi daga kan gadon ya leka window yana kallon ruwan da ya tsuge kamar da bakin kwarya,
Affan cikin tsoro ya rike kirjinshi dake tsananin bugu ya fita da gudu yayi dakin daddy,
da kyar daddy ya lallabashi suka kwanta tare amma fa bacci ya kaurace a idonshi dan daga ya runtse idonshi to fuskar jabeer zai gani yana kuka mai tsanani..
Hakan ta kasance da Afeeyah, wannan tsawar da akayi ita ta farkar da ita daga baccin da bata san tayi ba mai cike da mafarkai,
agogon wayarta ta duba taga 9:56 ta zauna tana sauraron zubar ruwan sama tana kara duba agogo kirjinta na harbawa da sauri,
10:20 ta kira wayar jabeer taji ta akashe, a hankali ta koma bayan hajja ta kwanta tana duba wayarta ko zata ji kiranshi shuru taji har 11 ta gota,
a hankali ta fara rero kuka tana kiran sunanshi,
kamar a mafarki hajja taji kukan ta farka da sauri tace yanzu ke Afeeya har yanzu baki bar kukan nan ba,
wani irin iskanci ne wannan,
Afeeyah tace hajja sha ďaya fa ta wuce kuma shi ya cemin goma da wani abu zai dawo,
hajja cikin masifa tace shikenan kuma ana wannan ruwan in ya dawo sai yaki zuwa ya huta yazo gurinki saboda gaki yar gwal ko,
Afeeyah ta shige jikin hajja tana kuka sosai tace hajja fa ya kashe wayar shi ne, kuma tun jiya fa ban ganshi ba, dan Allah ki taimaka min wallhy bazan iya bacci ba in ban ganshi ba,
hajja taji tausayinta sosai tace to yi shuru ya isa haka,
kinga yanzu dare yayi babu mamaki wayarshi ta mutu babu charge kuma bayason yazo ya sameki kina bacci kinga kuma ruwa akeyi kina son ya fito cikin ruwan nan ne, Afeeyah ta girgiza kanta,
hajja tace to ki mishi uzuri gobe nasan tun kafin ki tashi daga bacci zaizo kinji, Afeeyah ta gyada kanta tana share hawaye haďe da ajiyar zuciya,
hajja ta kwantar da ita tace yi addu'a kiyi bacci,
Afeeyah ta fara karanto adduoi hawaye na zubo mata ta gefen idonta a zuciyarta tana jin haushin jabeer na kin cika alkawarin da yayi mata, yanzu haka zanyi bacci banganka ba yaya jabeer, atlst ko waya ya kunna naji muryarshi zan dan rage wani zafin abinda ta dinga fadi a zuciyarta kenan, baccin ranar a gurin Afeeya rabi da rabi ne, saboda duk farkawa saita duba wayarta taga ko ya kirata,
( Allah sarki Afee zanso ace kinsan gani da muryar jabeer ma bazaki kara ji ba bare har kiga missd call dinshi,)
Abida ma juyi take tayi idonta na kan agogo, babu irin kiran da batayi ma wayar jabeer ba amma taki shiga,
Alhj bara'u yace Abida ya kamata ki cire duk wasu tunani a ranki kiyi addu'a ki kwanta kiyi bacci in shaa Allahu babu abinda ya sameshi babu mamaki mota ce ta bashi matsala,
Abida tace matsalar mota sai tasa ya kashe wayarshi yasan dole hankalin mu zai tashi alhj,
alhj bara'u da shi kanshi daurewa yakeyi yace kinsan sharrin netwk mu zuba ido zuwa da safe mu gani, Abida dai uhum kawai tace saboda yadda takejin nauyi a kirjinta, rungumeta yayi ta baya yana faďa mata kalamai masu kwantar da hankali dan in ya bari tasan shima hankalinshi a tashe yake to fa zata kara daga hankalinta fiye dashi ma,
Kaka liman ma ya kira har sau uku yaji ko ya iso,
shima hankalinshi a tashe yake saboda jin har lokacin jabeer bai isa gida ba...
Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Washe gari tunda alhj Bara'u ya idar da sallah yake zaune kan dadduma,
hankali tashe ya kalli Abida da ta zuba tagumi tana jan carbi yace Abida har yanzu wayar yaron nan bata shiga ba ko,
Abida ta gyada kanta kawai tana kallonshi,
yace innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah dai yasa jabeer lfy yake dan bai taba irin wannan abun ba, ko wayarshi nada matsalar charge ay duk inda yake bazai rasa wayar da zai kiramu ya sanar damu halin da yake ciki ba,
Abida tace uhummm zuciyata tana faďamin duk inda jabeer yake ba lafiya yake ba,
alhj bara'u yace ki daina faďin haka, haka kawai zuciyarki ta dinga kitsa miki mugayen tunani, ya mike tsaye yana duba lokaci yaga 7 har ta wuce ya fita daga dakin yayi hanyar waje,
Abida ta share kwallar data ďan fito daga idonta tace ya Allah ka sassauta min zafin da nake ji a zuciyata ka bani ikon jure duk wani abu da zanji game da jabeer,
Malam Atiku na kwance idonshi a lumshe da radio a gefenshi yanajin labaran karfe 7 kamar yadda ya saba kullum, bayan an gama labarai akan halin da kasarmu take ciki da kuma na kasashen ketare, sai aka sako labaran kwallon kafa, cikin kosawa ya mika hannu zai kashe radion saboda sam labaran kwallon kafa basa gabanshi,
tsayar da hannunshi yayi sakamakon jin sanarwar hatsari da akayi anan hanyar shigowa gari wanda akace an tsinci gawar saurayi mai suna Jabeer Bara'u, wadanda suka cinci gawar sunyi saurin mikashi ga hukumar yansanda, yanzu haka yana can asibitin Aminu kano, ga duk wanda yaji kuma yasan inda yan'uwan baw----- ay malam Atiku bai karasa sauraro ba ya diro daga kan gado yana faďin innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
ko takalmi baisa a kafarshi ba ya fita waje da sauri jikinshi na rawa,
a kofar gida ya samu alhj bara'u zaune kan dakali, da sauri alhj bara'u ya mike yace malam Atiku lafiya na ganka haka ko takalmi babu,
Malam Atiku ya saki ajiyar zuciya yace tunda na ganka zaune lfy lau ay alhamdullh, wallhy wata sanarwa naji yanzu a radio akan wani hatsari da ya faru a daren jiya kuma sai naji an kira sunan jabeer shiyasa hankalina ya tashi,
Alhj Bara'u ya mike yana salati kamar zararre, malam atiku yace alhj lafy,
Alhj bara'u baki na rawa yace jabeer dina ne,
jabeer dina ne wallhy, tun jiya muke neman layinshi bamu samu ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
malam atiku yace lahaulu wala kuwwat illa billah, alhj bara'u ya rike hannun malam atiku ya rasa ta inda zai fara sai janshi yakeyi yana fadin muje asibitin da suka ce, malam Atiku zaiyi magana parking din motar alhj basheer ya dakatar dashi,
da sauri ya fito yace lafy alhj bara'u ,
alhj bara'u ido zuru2 yace jabeer ya tafi,
alhj basheer cikin rudewa yace ina ya tafi,
malam atiku yace karka yanke hukunci alhj muje asibitin tukunna, in shaa Allahu ma bashi bane, alhj basheer yace wani asibiti,
malam atiku ya fada mishi abinda yaji a radio, alhj basheer da sauri yace kuzo mu tafi asibitin,
alhj bara'u da bakinshi bai daina salati ba ya shiga motar jikinshi a sanyaye suka wuce Aminu kano T.H,
Tunda suka shiga gaban alhj bara'u ke faduwa har suka karasa cikin mortuary, suna shiga aka nuna musu D.L din jabeer sannan aka karasa dasu inda yake,
Juyawa alhj bara'u yayi da ya kalli gawar sau ďaya ya fara addua cikin sambatu kamar tababbe,
D.L din kawai yake kallo yana jujjuyashi yanaso ya gasgata shin wannan gawar ďanshi ne da gaske ko mafarki yakeyi,
dafashi alhj basheer yayi yana zubar da hawaye yace alhj muje kayi signn mu amshi gawarshi muje ayi mishi sutura,
alhj bara'u bai kalleshi ba yace kaima mahaifinshi kaje kayi signn din, Allah ya amshi bakuncinshi yana gama faďin haka ya fita,
nurse din dake tsaye a gurin ta fashe da kuka tace alhj kuje kawai no need, Allah ya jikanshi da rahama,
nan aka gunguro gawar jabeer aka sata a ambulance suka wuce gida cikin jimami suna kallon alhj bara'u da ya kurawa d.l din jabeer ido,
kallon motar aka dinga yi a layin wasu suka bita dan ganin inda zata tsaya, motar na tsayawa a kofar gidan, alhj bara'u ya fito da sauri ya shiga ciki,
a parlor ya tarar da Abida Amirah na tsaye a kanta da ruwan tea da magani a hannunta, kallon Amirah yayi kamar babu abinda ya faru yace har yanzu baki shirya kin wuce makaranta ba,
Amirah tace nayi wanka baba yanzu zan gama in---, sallamar su malam Atiku da wadanda suka shigo da gawar jabeer ita ta hana amirah karasawa,
da sauri Abida ta mike tabisu da ido har aka shimfiďe gawar jabeer a kasa,
cikin firgici ta karasa kan gawar zuciyarta na dukan uku uku ta tsuguna ta buďe fuskar da tayi faca2 da jini, runtse idonta tayi da sauri tana fitar da wani irin numfashi tace nasani jabeer, zuciyata ta sanar dani, Alhamdullilah da Allah yasa aka tsinci gawarka akan lokaci, Allah ya rahamceka jabeer, yadda ka faranta mana kayi mana biyayya Allah ya faranta maka a cikin kabarinka dan nan ne gidanka na gaskiya, Allah ya sanya aljanna firdausi ta zama makoma a gareka,
ta shafa fuskarshi a hankali tace na yafe maka,
na yafe maka jabeer,
ta mike da sauri ta wuce daki alhj bara'u ya bita,
Amirah kasa gasgata gawar tayi dan gaba daya ta kasa fahimtar abinda ake nufi, ta kalli su alhj basheer da suke sharar hawaye tace daddy, Abba, me ya samu yaya jabeer, alhj basheer yace Amirah addua zakuyi mishi dan wanda ya fimu sanshi ya karbi abinshi,
Amirah ta saki kofin hannunta ta tsuguna a gabanshi tana kuka mai tsanani tana kiran sunanshi,
da kyar alhj basheer ya rarrasheta yasa Dayyaba dake tsaye tana kuka ta shiga da ita ciki,
Mahmud kanin Afeeyah ya shiga gida da gudu ya ajiye biredin da ya siyo a tsakar gida ya karasa ďakin hajja,
hajja na zaune tana gyaran wake, Afeeya kuma tana kwance jikinta ya ďau zafi sosai saboda zazzabi, fadowa dakin mahmud yayi, hajja tace haba mahmu irin wannan shigowar ba sallama ay sai ka tsoratani, yace hajja motar gawa ta asibiti na gani kofar gidan alhj bara'u kuma naji mutane suna cewa yaya jab-- Afeeya ta diro daga kan gado tayi ma mahmud wani irin riko tace me ya sameshi, mahmud cikin jin zafin rikon yace ban sani ba mutane sunce sunga an fito dashi cikin jini...
Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣2⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Wurgi Afeeyah tayi da mahmud ta fita da gudu,
duk irin kiran da hajja take mata baisa ta tsaya ba,
da gudu ta shiga gidan ta tarar dasu baba ado zaune da wasu mutane sunyi tagumi a bakin gate, da sauri ta karasa kusa dashi tace baba ado me ya samu yayana?,
baba ado ya kauda kanshi da sauri yana share hawayen dake zuba a idonshi, Afeeyah ta bar gurin da gudu ta shige cikin gidan,
murďa kofar parlon tayi da karfi kamar zata balleta,
tana shiga ta dinga bin mutanen dake parlon da kallo,
ganin mutum kwance cikin jini a kasa yasa zuciyarta bugawa da karfi,
a hankali ta fara motsa kafarta tana tafiya har ta isa gabanshi,
tsugunawa tayi ta yaye abin da aka rufe mishi fuskarshi da shi, gaba ďaya hanyoyin sadarwa na jikin Afeeyah suka daina aiki sakamakon ganin fuskar jabeer,
kallonshi ta tsaya yi bata ko kiftawa,
alhj basheer ya taso ya karaso gurinta ya ďagota dakyar dan jikinta a sake yake kamar wacce bata da rai,
zaunar da ita yayi akan kujera ya fara mata nasiha, ko kaďan bataji abinda yake cewa ba idonta na kan jabeer da alhj bara'u da mahaifinta ke kokarin ďaukarshi suyi mishi wanka,
alhj basheer ya girgizata yace Afeeyah kina jina,
lumshe idonta tayi lokacin da aka fita da gawar,
alhj basheer zaiyi magana hajja ta shigo da gudu tana faďin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me yasamu jabeer alhj, na shiga uku na lalace, alhj basheer yace dan Allah hajja kiyi shuru kar gidan ya rikice adduarmu jabeer yake bukata ba kuka,
hajja ta zauna tana kuka tana fadin kukan ne babu mai iya hana shi fita alhj,
ta kalli Afeeyah da idonta ke lumshe har lokacin ta riketa sosai ta kira sunanta har sau uku taji shuru,
ta girgizata da karfi tace ki bude idonki Afeeyah, nasan abinda kikeji dan Allah kiyi tawakkali, kar wata cutar ta kama ki,
dan Allah Afeey--- Afeeyah tace hajja me kika gani yanzu, kuka nakeyi ko me, ba tawakkalin nayi ba,
me kukeso inyi, ku faďa min me zanyi yanzu hajja,, kome kukace inyi zanyi walhy,
alhj basheer ya fita da sauri saboda kukan da yaci karfinshi yasan sam Afeeyah bata cikin hayyacinta,
hajja cikin kuka tace addu'a zakiyi Afeeyah, addu'a jabeer yake bukata,
Afeeyah ta bude idonta sosai tace hajja a ina zanyi adduar,
hajja ta rungumeta tana sheshshekar kuka tace a bakinki zakiyi ta,
Afeeyah tayi yake tace hajja kunce kar inyi kuka, kuma ku gashi kuna yi dan Allah kiyi shuru bari in shiga gurin ummi,
hajja ta rike hannunta suka shiga gurin Abida inda makota suka kewayeta,
tana ganin Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa sai a lokacin wasu hawaye masu zafi suka fito daga idonta,
Afeeyah tace ummi kuka kikeyi, daddy yace kar muyi kuka,
ta kalli Amirah tace Amirah dan Allah ki faďa min yadda zanyi hawaye su fito a idona, Amirah ta fada jikinta tana kuka sosai, Afeeyah tace dan Allah ku fadamin yadda zanyi, zuciyata zata buga ku taimakeni inyi kuka ko zan samu saukin nauyin da zuciyata tayi,
Alhj bara'u ne ya shigo ďakin shima idonshi jajur yace Abida kuzo kuyi mishi addu'a an gama shiryashi,
Abida kanta a kasa tace kuje kawai rahamar ubangiji ita kadai nake mishi fatan samu a kabarinshi, Afeeya ta mike ta fita da gudu a tsakar gida taga gawar an shiryata cikin likkafani,
da gudu ta karasa bata lura da mutanen da sukayi dafifi a gurin ba ta faďa kan gawar tana shafawa,
a hankali tace yaya jabeer alkawarin da kayi min kenan, meyasa zaka tafi ka barni, saida nace maka mu tafi tare kaki yarda ka tafi kai kadai yanzu ka faďamin yadda za'ayi in cigaba da rayuwa babu kai, meyasa bakayi tunanin abin da mutuwarka zata haifar a cikin zuciyata ba, dan girman Allah yaya jabeer ka tashi karka tafi ka barni, kai kaďai gareni,
malam atiku ya matso kusa da ita ya dafata yace Afeeyah Allah baya barin wani dan wani yaji daďi, Allah ba ruwanshi da duba shakuwarku,
Allah ya kaddara--- ta katseshi ta hanyar bige hannunshi tace wace irin kaddarace wannan, meyasa bata daukeshi tun kafin inzo duniya ba, sai yanzu zata zo ta dauke min shi a lokacin da nake bukatarshi,
ta mike tsaye tace abba dan Allah ka fadamin yadda zan iya cigaba da rayuwa, kasan dai bazai yiwu ba,
malam atiku ya rungume yarshi yana kuka sosai, yace Afeeyah nasan yadda kikeji,
ta sakeshi tana girgiza kai tace wallhy abba babu wanda yasan yadda nakeji sai yaya jabeer,
ta kankameshi tace kai kadai kasan yadda nakeji, dan Allah ka tashi,
duk rashin imaninka sai ka zubar ma da Afeeyah hawaye, babu yadda ba'ayi a banbareta jikin gawar ba amma abin ya faskara tana kwance kanshi tana sambatu babu ko ďigon hawaye a idonta,
dago kanta tayi saboda ganin mutum yayi kneel down a gefenta yana shafa tun daga kafar jabeer har kanshi,
kallonta yayi yana kaďa kanshi hawaye na fitowa a idonshi yace barbie yau kwana 9 banga abokina ba, yanzu kuma naga sun rufeshi da fararen kaya ina zasu kaishi,
kice mishi ya buďe idonshi inason muyi magana, I missd him so much,
sai a lokacin Afeeyah ta kara maida kanta kan jabeer ta fara kuka mai tsanani tana fadin maganganun da ita kanta bata san suna fitowa daga bakinta ba,
Affan ma duk da baya cikin hankalinshi yaji a jikinshi wani mummunan abu ya samu abokinshi,
da kyar aka iya banbare Afeeyah jikin gawar jabeer,
ana sashi cikin makara ta kara fashewa da kuka tana faďin dan Allah ku dawo min dashi wallahi zai dawo gareni, dan Allah karku fita dashi, ta dinga fisge2 jikin