Showing 60001 words to 63000 words out of 72718 words

Chapter 21 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt

16 Dec 2024

2297

me akeyi a ciki,
da bismillah ta yaye zanin gadon sannan ta daga katifar,
dakyar ta iya cire katakon dake kasan gadon saboda nauyinsu,
a razane ta ja baya saboda hango wani makeken rami a karkashin gadon,
hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai take fada saboda ta matukar tsorata da ramin, zuciyarta sai bugawa takeyi saboda tuna ita fa xata sa hannunta cikin ramin,
girgiza kanta tayi ta fara ja baya tana fadin wallhy bazan iya ba,
ji tayi kamar ta daki mutum a bayanta ta juyo a razane taga babu kowa sai muryar kaka liman dake mata yawo cikin kunnuwanta,
"na rokeki karki tsorata ke kadai ce garkuwar bayin Allahn nan,
in kika tsorata babu wanda zai iya,
"in kika gansu Ruwanki ne ki barsu ko ki ciresu ki taimaki mahaifi da kakar abinda ke cikinki""
A hankali ta karaso gurin ramin idonta cike da kwalla tasa hannu ta fara ciro kulle kullen dake ciki,
gumakan dake cikin ramin uku ne, daya an soke kanshi da mashi, biyu kuma an haďe su guri daya an kulle,
saida ta tabbatar ta fitar da komai daga cikin ramin sannan ta maida kayan gadon tana yi tana share zufa,
gaba daya a lokacin ta nemi tsoro ta rasa, kwashesu tayi cikin hijab din da ta rufama Affan ta buďe kofar dakin tayi saurin wucewa dakinta,
kitchen ta wuce cikin dakewar zuciya ta fara warware duk wani kullin garin magani tana zubarwa a cikin zinc tana kwarara mishi ruwa, haka layunma duk tayi musu,
gunkin lakan da aka hade su guri daya ta fara warwarewa ta sa tabarya ta dakeshi ya zama gari sannan ta kwararar dashi cikin zinc,
dauko dayan gunkin tayi wanda akayi shi da roba,
da bismillah ta zare mashin ciki,
tana dauko wuka zata fara yankashi taji wata guguwa mai karfi ta bude windown kitchen din,
hannaye taga an ziro ta cikin windown tayi saurin yar da wukar hannunta ta cilla wannan mashin bayan cabinet,
a hankali taga gangar jikin mutum na shigowa,
da gudu tayi hanyar waje tana addu'a,
tana zuwa kofar taji an datseta da karfi,
ja da baya ta fara yi tana salati tana kiran sunan hajja,
oyizah ta gani muraran ta bullo ta cikin kofar,
zaro ido tayi murya na rawa tace m-u-mm-y,
oyizah ta buga mata wata sanda a bakinta,
rike bakin tayi tana ta nemo addu'a a bakinta ta rasa,
cikin kunan rai oyizah ta fara matsowa fuskar nan babu rahama tace yau sai na kasheki, daga yau kin daina numfashi a doron kasa bare har kiyi yunkurin shiga rayuwata,
da hannuna zan kasheki tunda duk wani abu da nayi akanki bana samun nasara,
ban taba haduwa da abin da ya dameni ba sai a kanki dake da matsyacin saurayinki jabeer,
kamar yadda na kawar da jabeer da mahaifiyar Affan kema haka zan kawar dake kije can ki samesu dan babu wanda ya isa ya shiga gonata ya fita ba tare da yayi noma ba,
tayi wani huci hade da daga wannan sandar zata buga ma Afeeyah, da sauri ta goce ta rike sandar sosai,
nan suka fara dambe sosai har oyizah tayi nasarar kwace sandar,
da karfi ta shiga laftar Afeeyah da ita,
ihu Afeeyah takeyi tana ja da baya saboda azaba,
wani jug ta rarumo a gefenta ta kwaďa ma oyizah akanta,
nan jini ya fara zuba sosai,
da sauri Afeeyah ta bangajeta ta kama kofar kitchen din tana jijjigawa tana ihu sosai kamar zata tsaga gidan,
ganin kofar taki buduwa yasata daukar wuka ta nuna ma oyizah dake tahowa kusa da ita tace wallhy kina matsowa zan kashe ki,
oyizah ta goge jinin gefen idonta tayi wata irin dariya tace wai gawa ce ke maganar kashe me rai,
cikin kuka Afeeyah ta juya tana faďin ya Allah ka taimakeni,
tana jan kofar taji ta buďu tayi saurin fita ta datso oyizah a ciki,
da mamakinta tana bude kofar parlonta ta tarar da oyizah da wata mata mai gebararran halitta,
runtse idonta tayi ta fara fadin hasbunallahu wa ni'imal wakil, la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin,
wukar nan dake hannunta ta ďaga da niyyar buga ma oyizah, nan tayi saurin dukawa ta kamo kafar Afeeyah ta daga ta sama tayi wurgi da ita ta bugu da bango da tiles din dakin,
kara mai karfi ta saki wacce ba alhj basheer kaďai ba har masu gadin gidan saida suka girgiza da jinta,
tun daga wannan karar Afeeyah bata kara sanin inda kanta yake ba,
jin Alhj basheer ya bude kofar dakinshi yasa chummy ta bace,,
da sauri oyizah ta yar da sandar hannunta ta tsuguna tana ihu a gaban Afeeyah,
da gudu Alhj basheer da farida suka karaso gurin, cikin rudewa alhj basheer ya shiga jijjiga ta yana kiran sunanta,
kallon oyizah yayi tana kuka sosai yace safiya me ya sameta, cikin makirci oyizah tace nima fitowa nayi na tarar da ita anan tana dambe da iska, ina matsowa kusa da ita sai naji saukar wannan wukar a goshina,
anya alhj yarinyar nan ba matsafiya bace kuwa,?
alhj basheer ya daka mata tsawa yace kamata mu kaita asibiti muji abin da ke damunta,
oyizah ta share hawayen karya ta kamata a zuciyarta tana murna dan suna zuwa asibiti zata karasa ta acan,


Alhj basheer na tada mota yaji kamar muryar Affan a gefen glass din motar, kallonshi yayi yace Affan ka tashi ne,
Affan ya gyaďa kanshi idonshi jajur yace daddy ina zaku kaita,
alhj basheer yace asibiti zamu kaita yanzu zamu dawo je ka kwanta kaji,
bude motar yayi ya zauna a inda aka kwantar da ita yace muje daddy,
alhj basheer yace kayi hakuri Affan ka je ka kwanta kafin mu dawo, Affan kamar zaiyi kuka yace daddy bazan iya bacci ba,
oyizah cikin fushi tace ka sauka akace ko bakaji abin da aka ce maka bane,
kallonta yayi cikin ido hawaye na sauka cikin nashi yace saidai idan tare da Afeeyah zaku saukemu,
oyizah zata kuma magana alhj basheer ya tada motar yace muje kyaleshi,
oyizah tayi kwafa dan wannan mayen ya rusa mata plan dinta,
har suka kai asibitin idon Affan bai bar zubar da hawaye ba,
janyoshi daddy yayi yana rarrashinshi akan ya daina kuka babu abinda zai sameta,
sun dan dade a tsaye kafin doctor yazo, direct ya wuce dakin da aka kaita,
ya dade yana treatn dinta yiyi dressn ciwukan dake jikinta,,
oyizah ma ta je wata nurse tayi mata dressn sannan ta wuce dakin da Afeeyah take,
zaune ta samu Affan ya kwantar da kanshi akan hannun Afeeyah yana kuka alhj basheer na tsaye a kansu yana rarrashinshi,
tsaki tayi a hankali ta karaso gurin tace alhj ya kamata kuje gida ni sai in kwana anan,
Affan yayi saurin dago kanshi ya noke wuyanshi yace um um nima zan kwana,
oyizah tayi dariya tace ya za'ayi mai jinya yayi jinya, kai da ba wani isashshen lafiya gareka ba ina kai ina jinya,
Affan ya kara fashewa da kuka yace ni babu inda zani,
alhj basheer yace to duk babu inda zamu a nan zamu kwana, oyizah ta ja baya cikin bacin rai ta watsa ma Affan harara a zuciyarta tace shege mayatacce ka kusa daina ganinta kwata2.....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah


A tsaye suka kwana a kanta babu wanda ya runtsa,
oyizah taki runtsawa ne saboda tana jiran su alhj basheer su rufe idonsu ta ida mugun nufinta akan Afeeyah,
alhj basheer kuwa yaki runtsawa ne saboda ganin Affan bai runtsa ba kuka kawai yakeyi wanda babu wanda a cikin su yasan dalilin yinshi har ni da nake dauko muku rahoto,


karfe 6 doctor ya iso, dakin Afeeyah ya shiga suka gaisa da alhj basheer yace bata farfado ba har yanxu,
alhj basheer yace ko motsi bata yi ba doctor da fatan dai ba wata gagarumar matsala bace,
doctor musah ya bude idonta a hankali yace buguwa ce kawai tayi sai wadannan ciwukan,
ya akayi ta samu wadannan raunin haka alhj,
alhj basheer cikin damuwa yace ina ganin gamo tayi cikin dare dan ni ihunta kawai naji na fito na sameta a sume ina fatan dai bai taba lafiyar cikinta ba ko doctor,
doctor musah yace dakyar ne alhj dan buguwar a kai tayi amma anjima zanyi scanning dan tabbatar da lafiyar shi,
alhj basheer yace Allah yasa muji alkhairi, doctor musa yace Ameen alhj sannan ya fita,
oyizah tace alhj ya kamata ku tafi gida kuje kuyi wanka sai ku kawo mana abin kari ko,
alhj basheer ya dafa kan Affan yace tashi muje gida ka dan yi bacci ka huta anjima sai mu dawo,
Affan ya ďago idonshi da ya kumbura ya girgiza kanshi yace kaje daddy,
alhj basheer yace haba Affan baka ganin yadda idonka yayi nasan ka gaji kuma bacci kakeji, kayi hakuri kazo muje kaji,
Affan ya mike yana murza idonshi ya fita ba tare da ya kalle su ba,
saida alhj ya dan dade a ciki sannan ya fito ya samu Affan a mota ya daura kanshi kan murfin kofar,
shiga yayi ya tada motar suka wuce...


Suna fita oyizah rufo kofar ta dawo gurin Afeeyah tana dariyar murna,
pillown kan Afeeyah ta cire tana fadin yau taki ta kare,
yau zan karar da duk wata matsalata in huta da bakin ciki, tana daura pillown kan Afeeyah taji an murďa kofar,
da sauri ta zauna ta zame pillown tana dariya tace doctor ka dawo,
doctor musah ya kalleta sosai yace eh na dawo,
nazo daukarta muje ayi mata scanning daga nan zata wuce resting room,
zaifi kyau ki tafi gida hajiya saboda bama yarda kowa ya shiga dakin hutu in ba likita ko nurse ba,
oyizah tayi mishi wani irin kallo tace kana nufin ita kadai xamu bari a asibitin babu wanda zaiyi jinyarta sai kace marar gata,
doctor musah yace haka ka'idar take hajiya baki ga conditn din da take ciki ba, oyizah ta fara masifah tace wallhy baka isa ba, babu inda zaka kaita haka kawai zaka wani zo kayi min iyayi anan,
to anan zaka barta tunda ko ina ka kaita Allah ne zai bata lafiya ba kai ba,
yayi mata wani irin kallo sannan yasa aka shigo da wani gado yace hajiya aiki na nakeyi tunda ba ke kike biyana ba dan Allah ki barni inyi aiki na,
ya kalli nurses din yace ku daura ta muje, suka kinkimeta suka daurata akan gadon,
rike gadon oyizah tayi tana ta bala'i tana wallhy baza'a tafi da ita ko ina ba,
mutane suka taru a gurin anata bata hakuri amma tace ita sam babu inda za'a tafi da ita,
doctor musah da kanshi ya amshi gadon yasa iya karfinshi ya fara turawa oyizah na binsu tana bala'i kamar zararriya,
dr musa bai tsaya a ko ina ba sai office dinshi, da karfi ya bude kofar ya tura gadon haďe da bangajeta ta fadi kasa yayi saurin shigewa ya datso kofar,,
wani sabon bala'i oyizah ta dasa ta dinga masifa cikin daga murya,
babu wanda ya kalleta a asibitin kowa harkar gabanshi yakeyi saboda su a ganinsu mahaukaciya ce in ba mahaukaci ba waye zaiyi wannan daga cewa za'a kai patient resting room,
ita kuwa oyizah musabbabin tashin hankalinta shine yanzu Afeeyah tasan ita wacece in har tabar Afeeyah ta kara kwana a doron kasa to tabbas asirinta zai tonu dan zata iya farkawa a ko da yaushe,
(oyizah bata san ba tun yau Afeeyah tasan ko wacece ita ba, kuma bata san bayan Afeeyah akwai mutanen da suka san ko wacece ita kuma suna nan tunkarota cikin kankanin lokaci )
sai da ta gaji da masifar dan kanta sannan ta wuce gida cikin kunan rai...


Tana isa gida ta faďa ma alhj karya da gaskiya akan abun da doctor musah yayi mata,
alhj basheer yace safiya mutumin nan fa aikin shi ne ya fiki sanin abinda ya dace, oyizah tace babu abinda ya sani alhj kawai mu canza mata asibiti,
alhj basheer ya girgiza kanshi yace babu inda zan kaita a can zata zauna har Allah ya bata lafiya,
in ma yace kar wanda ya kara zuwa gurinta to na yarda dan nasan zai kula da ita sosai, oyizah ta tsaya tana kallon alhj basheer tana huci kamar bakar zakanya,
mikewa yayi ya fita daga gidan gaba ďaya ya barta tsaye kamar zata kurma ihu...


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Kwanan Afeeyah uku a asibiti bata farfaďo ba, a cewar doctors buguwa tayi sosai kuma suna iyakacin kokarinsu gurin ganin ta farfaďo nan da yan kwanaki,
babu wanda ke zuwa dubata daga gida sai alhj basheer da Affan da har wannan ranar bai bar zubar da hawaye ba,
ba karamin damuwa alhj basheer yakeyi ba akan yawan kukan Affan,
gani yakeyi kamar yin kukan yanada nasaba da ciwonshi,
saida doctor musah ya kwantar mishi da hankali yace babu abinda ke damunshi may be ciwon matarshi ne ke sashi yawan kuka,
alhj yayi dariya da dr musa ya fada mishi haka, yace yanzu wannan da kwakwalwrshi bata da amfani har yake iya yin kuka dan wani nashi baida lafiya, kenan yasan zafin ciwo kuma yasan meye damuwa,,
doctor musah yace me zai hanashi yin kuka, alhj ni fa har yanzu kana bani mamaki akan wasu abubuwa da ka kasa fahimt-- wani irin kallo Affan yayi ma doctor musah nan da nan yayi saurin canza magana yace kamar ciwon Affan ka kasa fahimtar kullum yana samun cigaba dan wani lokacin yakanyi abubuwa irin na masu hankali,
alhj basheer yayi murmushi yace hakane doctor, Allah dai ya kara bashi lafiya,
dr musah yace ameen alhj, mikewa alhj basheer yayi yace to mu zamu wuce dan inada inda zani,
dr musah yace to sai anjima alhj, nan suka fita dr musah ya bi Affan da kallon mamaki...


Affan ne zaune a kan kujera a palour ya haďa kai da gwiwa yana kuka sosai harda sheshsheka,
mamakin al'amarin nayi a zuciyata nace shi kuwa wannan tababben ko kukan me yake yawan yi tun ranar da aka kai Afeeyah asibiti oho,,
a hankali naji yana faďin sai na dauki fansar kisarku, bazan kyale duk wanda yakeda hannu a cikin kisan ku ba, wannan yakin ni zan karasa shi cikin kankanin lokaci in shaa Allahu,
sosai yake kuka yana faďin wadannan kalaman,
cikin kidima na kureshi da ido a zuciyata nace anya wannan bai samu sauki ba,
anya ba basaja yakeyi ba kuwa?,


Da sauri na maida computer cikin kwakwalwrta baya zuwa ranar da Afeeyah ta aiwatar da ayukanta na karshe wanda yayi sanadiyyar zuwanta asibiti,
da sauri na ciro yar makallaliyar camerar da ke makale a dakin oyizah na kunna,
cikin mamaki na fara dauko muku rahoton abin da ke ciki,
da naso in boye muku kamar yadda Affan ya boye ma su daddy sai naji wayar "Badiyya Aliyu" tana gargadina akan in rubuta muku komai har coma, da fullstop. kamar yadda "bingel" takeyi,


Da sauri na dauki wayata na shiga typo muku abin da na gani mai ban mamaki,


cikin bacci naga Affan ya rike kanshi yana juyi anan inda yake kwance a kasa,
a hankali bakinshi ke motsi yana faďin umma,
Jabeer,
daddy,
can kuma naga ya matse kanshi da karfi yana faďin wayyo ummana,
sun kasheta,
sun kasheta,
sun kashetaaaaaaaa....
ya faďi da karfi hade da mikewa zaune zufa duk ta jika mishi jikin shi,
waige2 ya fara yi a rude yana fadin ina ne nan, waya kawoni nan,, ya maza ya mike ya buďe kofar dakin a firgice ya farayin hanyar dakin zeenatu,
ihu ya jiyo a side dinshi yayi saurin daukar hanyar gurin, yana zuwa kofar dakin yaji oyizah na faďin "kamar yadda na kawar da zeenatu da jabeer" kema haka zan kawar dake,
lekawa yayi dan ganin ko dawa take,
a gigice ya ja baya saboda ganin Afeeyah da yayi bakinta duk jini,
a ruďe yace yaushe jabeer ya mutu, me Afeeyah takeyi a nan gidan, yanzu ummanshi ta mutu kenan,
tambayoyin da ya dinga ma kanshi kenan idonshi na ambaliyar hawaye,
da sauri yaja baya ya boye ya shiga dawo da abubuwan da suka faru dashi shekaru uku da suka wuce,
babu abinda idonshi ke hangowa sai lokacin da ya tarar da kartin maza su biyu sun bankare mahaifiyarshi suna shirin shaketa da farin kyalle gabansu cike da kayayyakin tsafi mummy kuma tazo da wuka tana kokarin dab'a mata a wuya,, ,
shi dai yasan tun daga lokacin bai kara sanin inda hankalinshi yake ba sai yau da ya farka ya kuma tarar da wani tashin hankalin,
me jabeer yayi mata ta kasheshi,
wani irin kuka ya kufce mishi mai ban tausayi ya mike da niyyar komawa dakinshi ya ceci Afeeyah daga kaidin oyizah,
har yakai kofar ďakin ya hango oyizah da wata a bakin kofar,
da sauri ya juya yayi hanyar dakin da ya farka ya ganshi a ciki ko zai samu makamin da zai iya yakar ta dashi,
yana shiga dakin yaji karar waya, da kamar bazai dauka ba, sai kuma yayi saurin dauka,
ba"a bari yayi magana ba daga daya bangaren, murya yaji ta tsofaffi cikin rudewa tana cewa ina fatan kina nan lafiya Afeeyah,
nayi wani mummunan mafarki akanki,
ki tabbatar kin mike kinyi sallah dan komai na iya faruwa cikin daren nan,
a hankali Affan yace waye ke magana, daga daya bangaren kaka liman yace kai din waye,
Affan yace nine Affan, kai fa,
cikin mamaki kaka liman yace Affan nine, kaka liman ne na daura,
Affan ya fashe da kuka yace kaka kana ina aka kashe min jabeer, me jabeer yayi kuka bari aka kasheshi,
kaka liman yayi kabbara da karfi yace Affan ka dawo cikin hayyacinka,
Allah mai iko,
ka daina kuka wannan maganar ba ta waya bace yanzu ina matarka,
a gigice Affan yace wacece matata kaka,
kaka liman yace Afeeyah itace matarka wacce take dauke da cikinka,!
wacce ta yarda ta aureka cikin larura domin ta kubutar dakai daga cikin masifar da kake ciki,!
wacce ta fara zame ma matsalarka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login