Showing 3001 words to 6000 words out of 72718 words
Chapter 2 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt
fara jarabawa ne,
yace au too to Allah ya bada sa'a, tace Ameen ta wuce ciki idonta kan motar jabeer tasan tabbas yana ciki,
kai tsaye ta wuce dakin Ummi ta murda ta shiga hade da sallama,
amsa sallamar yayi haďe da ďago kanshi suka haďa ido,
kallonshi ta tsaya yi idonta cike da kwalla shi kuwa murmushi yake mata yana mai jin dadin ganinta,
girgiza kanta tayi ta wuce kitchen inda taji buruntun ummi,
ummi na ganinta ta fadada fara'arta tace Afee yan matana,
Afiya ta tsuguna ta gaisheta, ummi ta amsa haďe da ďagota tace kin gujeni kwana biyu ko ďan girki kin daina zuwa tayani, afee ta sunne kanta tace wallhy ummi jarabawa zamu fara yanzu bana fita amma ay nazo ran Saturday bakya nan,
ummi tace eh kwarai naje daura, ya hajja, afiya tace tana gida ita ta aikoni wai gashi a kaima anty Asiyah,
ummi ta karbi maganin tace Allah sarki kice mata an gode sosai kinji,
afiya ta gyaďa kanta sannan tace bari in tayaki wanke wanken, ummi tace aiko nagode kamar kinsan na gaji, ga dayyaba har yanzu bata dawo ba, Afee ta fara wanke2 tace ummi Amirah fa, ummi ta wanke hannunta tace tana can kaduna gidan Asiyah har yanzu bata dawo ba,
Afeeyah tace Allah ya dawo da ita lafiya, ummi tace Ameen yar albarka ta fita ta tarar da jabeer zaune yana latsa waya tace au ashe baka fita ba,
yace walhy ummi nagaji ne sosai,
tace ay da gajiya ni bari in ďan kwanta kafin la'asar,
yace to ummi Allah huta gajiya tace Ameen ta wuce ciki,,
saida ya tabbatar ummi ta kwanta sannan ya mike ya shiga kitchen ďin,
tana tsaye tana goge kwanukan da ta wanke tana mita tana girgiza kai,
dariya ta bashi a zuciyarshi yace yau ya shiga uku da masifarta,
karasawa kusa da ita yayi ya dauki plates din da ta goge zai jera tayi saurin rikesu tace malam ka ajiye ni ban sa ka ba, yace ay nasan baki sani ba tayaki kawai zanyi, tace to banaso ko dole ne,
yayi murmushi yace dole ne mana in ban tayaki aiki ba wa zan taya,
tayi tsaki tace wacce ka samu a cikin sati biyu nidai ka fita kawai, da nasan ma zan sameka a gida da ban shigo ba,
yayi dariya haďe da rike kafadunta yace makaryaciya dan ki ganni ne ma kika yarda aka aiko ki,
tace God forbid, in ganka inyi maka me, yace kiji daďi mana in kuma bakiji dadin ganina ba kalli cikin idona ki faďa min,
ta ďago a tsiwace zatayi masifa suka haďa ido tayi saurin sauke kanta saboda wani abu da ta gani a cikin kwayar idonshi, yayi murmushi yace nasan kinyi missing ďina,
cikin muryar shagwaba tace ni banyi missn dinka ba, yace um um fa karki sani in tafi gurin da bazaki kara ganina ba, muryarta ta fara rawa tace me ya rage kuma tunda har ka iya yin sati biyu baka neme ni ba, ya dago kanta ya kalli idonta da hawaye ya fara zuba a cikinsu yace bake kikace in tafi ba,
ta dunkule hannunta ta buga a kirjinshi da karfi tace to ba wasa nakeyi ba, shine ka daina bari in ganka baka ma damu da halin da zan shiga ba kasan ko kwana ďaya ne in ban ganka ba banajin daďi ni nasan yanzu ka daina sona tunda har ka iya yin sati biyu baka ganni ba kuma ka zauna la-fiya ta karasa fadi cikin kuka mai tsanani,
kwantar da kanta yayi kan kirjinshi dake bugawa da sauri yace am so sorry Afee nah kece bakya ji in na miki magana,
tace wallhy na daina kaje ma ka tambayi hajja Allah ko sun tsokaneni bana tanka musu,
jabeer yace to yi shuru na yadda ki daina kuka kinji,
ta gyada kanta tace promise me bazaka kara yin bacci baka ganni ba,
yace I promise baby in dai da rai da lafiya bazan kara ba kinji, tayi murmushi tace Allah ya kara maka tsawon rai da kuma lafiya in dinga ganinka har karshen rayuwata,
ya ja kumatunta yana murmushi yace Ameen my queen,
tayi dariyar jindadi suka cigaba da kife kwanukan suna hira har suka gama,
a parlor suka zauna yake tambayarta karatun jarabawa, tace tanayi sosai saidai maths ke dan bata wahala, yace baki da matsala zamu dinga yi kullum kafin ku fara exams tashi ki rakani gidansu Affan,
ta turo baki tace nidai bazan shiga ba,
ya harareta yace yau sai kinzo munje kin gaisheshi rabonki da shiga gidan tun kafin ya fara ciwo saboda haka yau sai kin shiga, ta marairaice tace ni fa ba ruwana in wadannan masu kama da iyamuran sukayi min wllhy ramawa zanyi saidai kace bani da hakuri,
ya murďe bakinta har saida tayi kara yace suwaye masu kama da inyamurai,
tace oho ni nasan sunansu ne,
yayi dariya yace bazaki taba canzawa ba afee sai dai addu'a, tace wallhy zan canza amma fa baza a dakeni a hanani kuka ba,
yace to naji tashi muje bazamu daďe ba, tace too ta mike suka fita suka shiga gidan Alhj Basheer,,
Cigaban na 4..
Yana zaune as usual a gurin kifaye yayi kasake yana kallonsu kamar me nazarin wani abu,
jabeer ya dafashi ya juyo a firgice ganin jabeer yasa shi washe hakori sosai yana kaďa kanshi cikin murna,
jabeer yace Affan abokin jabeer kuma abokin kifi,
Affan yayi dariya cikin maganar dolaye yace jiya baka zo ba inata kallon can kofar mota har dare baka zo ba, jabeer yace kayi hakuri na danyi wata tafiya ne,
Afiya dake tsaye fuskarta dauke da tausayin halin da affan ke ciki tace ina wuni, ya ďago kanshi dake rawa yana washe hakori yana kallonta baya ko kiftawa, duk maganar da jabeer ke mishi bai kalleshi ba idonshi na kan Afeeya kanshi yaki tsayawa guri daya,
jabeer ya kalli afeeya da ta rabe tana jin tsoron kallon da Affan ke mata yayi murmushi yace affan baka gane Afeeyah ba, affan ya girgiza kanshi ya runtse idonshi kamar yana son tuno wani abu can ya bude idonshi yace na ganeta amma na manta a wani cartoon na taba ganinta,
jabeer ya kwashe da dariya haka shima affan suka dinga dariya tare saida jabeer yayi shuru sannan affan ma yayi,
jabeer ya kalli afeeya da ta cika tayi fam ya maza ya mike yace Affan ka jamin bala'i,
affan ya mike shima ya matso kusa da afiya sosai kamar zai shige jikinta yasa hannu ya shafi fuskarta wani irin laushi yaji haďe da sanyi mai fisgar zuciya ya maza ya cire hannunshi yana tsalle yace bari inje in fada ma mummy yau na taba fuskar cartoon, jabeer ya janyoshi yace karka kara ce mata cartoon,
Affan ya bata fuska yace to mecece in ba cartoon ba kalli fa idonta kato irin nasu, kuma ka taba fuskarta kaji,
jabeer yace idonka ne ya ga cartoon wannan Afeeya ta ce,
ka tuna ta, Afeeya mai kyuiya mai kukan banza ya faďi yana mata kallon tsokana,,,
affan ya kara rufe idonshi ya bude yace mai kuka irin na mage, Afiya tayi tsaki cikin fushi ta fara tafiya, affan yace jabeer kace ma cartoon ta dawo dama bani da barbie din wasa,
jabeer yabi bayan afeeya yana cema affan jeka kace ma mummy ta siyo maka wannan barbie din tawa ce,
Affan ya bata rai yace sai na fadama daddy in ya dawo ince kaki bani barbie,
jabeer bai kulashi ba shidai hakuri kawai yake bawa afeeya, suna kaiwa gate zasu fita shima affan yasa kafa zai bisu yaji wani irin tsawa mai firgitarwa sannan gabanshi yaga kamar namun daji suna so su biyoshi,
a sittin ya ruga ciki yana ihu yana kiran sunan mummy,
jabeer sam bai lura da yanayinshi ba ya ďauka shirmenshi ne dan baya taba wuce kofar mai gadi yauma yayi mamakin da ya biyosu har gate saboda barbie,,
Har cikin gida ya
rakata yana rarrashinta da kyar ta sauka da alwashin ta gama shiga gidan Alhj basheer har ta koma ga Allah dama sam jininta bai haďu da flowers din kofar gidan ba ma bare a kai ga mutanen cikinshi gara ma daddy da shi affan din suna gaisawa in jabeer ya kaita gidan, ta saki ajiyar zuciya tace yaya jabeer haka Yaya affan ya dawo rabona da ganinshi tun ina js3,
Amma wai wane irin ciwo ne wannan,
hajja dake gefensu tace au ke yau kin shiga kin ganshi,, ay a unguwar nan babu wanda ake bari yaje dubashi ko meye dalili oho,
jabeer yace hmm babu wani dalili hajja kawai dai matar gidan ce bata yarda a ganshi ni ma dan ta rasa yadda zatayi dani ne shiyasa ta barni,, ga daddy ba mazauni ba dan sai yafi wata bayanan,
hajja tace to Allah dai---- sai bakinta ya sar'ke kamar a datseshi da gum...
wannan itace babbar jarabawar da Allah ya daurawa AFFAN ta hanyar kishiyar uwa babu wani mahaluki a doron kasa da zai iya yi mishi addu'ar samun sauki,
jabeer shi ne kadai yake iya ganinshi har yayi yunkurin sanyashi a hanya amma saboda karfin iko da lokacin da Allah ya ara ma mummy, daga affan ya fara jin maganar jabeer kamar kiftawar walkiya sai ya mance abinda yace ya bijire mishi,
duk yadda taso rabasu ta kasa saboda amintar su mai karfi ce wacce zaiyi wuya kasamu labarinta a kasar hausa,
Bari in baku takaitaccen tarihin gidaje ukun...
Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣
By Aysha Ya'u Kurah
A unguwar "zoo road" dake cikin garin "kano" ta dabo tumbin giwa nan zan ďan tsakuro muku tarihin gidajen makota ukun,
Alhaji Basheer Balarabe dan asalin k'asar Cameroon ne, sana'ar Gwal ita ta shigo dashi kasar nigeria tun yana saro kaďan2 yana siyarwa har Allah ya sanya wa abin albarka ya koma sarinsu da yawa yana shigowa dasu yana siyarwa,
a duk cikar kasuwar gwal dake cikin garin kano babu wani wanda yakai Alhj Basheer kawo ingantattun gwalagwalan da babu mixed a cikinsu, wannan dalilin ne yasa duk wanda ya tashi siyan gwal to fa a gurinshi zai siya dan shagunanshi sun fi karfin goma a cikin kasuwar,
Alhj Basheer ya auri matarshi ta farko kuma yar uwarshi Zeenatu,
auran zumunci akayi musu wanda ganin girma da kuma karamcin rik'on da iyayen zeenatu sukayi mishi yasa ya yarda da auren amma badan yanaso ba,
shekararsu uku da aure suna zaman lafiya saboda irin biyayyar da take mishi, a cikin wannan shekarun ne ya dakko ta suka dawo Nigeria da zama kwata2 sai dai suje cameroon hutu,
a shekararsu ta biyar da aure ne hankalinsu yayi matukar tashi saboda rashin haihuwa,
babu ma kamar alhj basheer da yake ganin madarar kuďi babu maciyansu sai dai yan uwa da makota,
ya kosa matuka yaga yana da ya'ya barin ma ďa namiji dan wani lokaci har mafarkin gashi nan an haifa mishi ďa kuma namiji yakeyi,
a wannan yan lokutan ne ya fara tunanin k'aro aure duk da a lokacin ba mazauni bane saboda bai fi yayi sati a nigeria ba sauran kwanakin duk a kasar waje yake yinsu yana turo kaya,
Wata ranar asabar ya baro airport cikin tsananin jin yunwar da ta bashi mamaki, nan ya tsinci kanshi da tsayawa a wani restaurant dake Jabi dan bazai iya matsawa ko'ina ba tare da yaci abinci ba,
cikin karairaya wata farar ingarmar budurwa ta matso kusa dashi tace alhj me kake bukata,
cikin ruďewar ganin jar fata gata a cike gaba da baya ko'ina sai rawa yakeyi a jikinta yace anytn special yanmata dan yunwa nakeji sosai,
ta ďan tsuguno kadan tace an gama ranka ya dade,
tayi gaba jikinta na girgiza alhj basheer ya bita da ido baki sake yana kallonta har ta bace ma ganinshi, ajiyar zuciya mai karfi yayi sannan ya gyara zamanshi dan ba karamin tafiya da imanin shi tayi ba, cikin yan dak'ik'u ta dawo dauke da plate din fried rice da pepper chicken sai peprsoup din kayan ciki a gefe da drinks,
alhj basheer da bai cika cin abincin restaurant ba sai gashi ya tsinci kanshi da cin abincin nan sosai, takardar bill ta kawo mishi yabi kirjinta da ya cika kamar zai faso cikin rigarta da kallo yace yanmata duk wadannan kudin ni zan biya,
tayi walll da ido tace alhj yayi kaďan ko, yayi wata kasaitacciyar dariya yasa hannu a aljihu ya ciro rafar dari biyar yace ya daiyi yawa ni kinga abinda zan iya biya nan,
tayi murmushi tasa hannu ta karba haďe tsugunawa, tace to an gode yallabai,
tayi gaba ya bita da kallo yana lasar baki kamar tsohon maye,
tashi yayi bayan ya gama goge bakinshi da tissue yana sakace ya yafito wani yaron da yaji an kirashi da John, da sauri yaron yazo ya tsuguna yace alhj any problm,
alhj basheer ya ďagoshi yace no young man ina bukatar taimakon ka ne,,
john cikin mamaki yace taimakon me alhj, alhj basheer ya jashi waje yace wannan yarinyar da take kawo abinci nake son sanin sunanta,
john yayi dariya yace OYIZA kake nufi,
alhj basheer yace ban sani ba wata fara kakkaura,
yace yes itace alhj sunanta "Safiya" Oyiza ake ce mata ita y'ar mai restaurant din nan ce,
bata cika zuwa nan ba sai in tazo daga lagos kuma I think gobe ma zata koma saboda tafi 1wk anan gurin,
ya fara waige2 ya ďan rage murya cikin gulma yace amma fa alhj bat--- maganarshi ta katse sakamakon kiranshi da yaji madam dinshi nayi,
da sauri yace alhj bari in tafi sai anjima ya ruga ciki da gudu,
alhj basheer a zuciyarshi yace ko bata dame ya ke so ya fada mishi oho? ya ďaga kafadarshi kawai ya dawo ciki dan yayi magana da mahaifiyar oyiza,
Guri na musamman maman oyiza ta bawa alhj basheer ya zauna tana yashe hakori cikin murna dan taga gurin ďana tarko,
cikin girmamawa suka gaisa, saida shuru ya đan ratsa na kusan 2mins sannan alhj basheer ya fara magana yace madam naga yarinya a gurinki ne kuma inaso,
wallhy da aure nake sonta ba yaudararku zanyi ba, ni in kin amince ma a cikin sati biyu a gama komai na maganar aure,
maman oyiza tayi ajiyar zuciya cikin gurbatacciyar hausarta tana girgiza kai tace anya kuwa gaskiya bazan iya ba bahaushe oyiza ba, kaiii bazan iya ba alhj hausawa basu cika rik'e mata ba,
yayi murmushi yace wasu dai madam ai ba duka aka taru aka zama daya ba,
tace ummm haka ne amma gaskiya--- alhj basheer ya katseta yace madam na barki kije kiyi tunani, zan dawo nan da 2days sai inji abin da kika yanke ya ajiye mata wasu kudin a gabanta sannan ya tashi ya tafi....
Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣
By Aysha Ya'u Kurah
Jujjuya kuďin maman oyiza takeyi cikin fargaba dan ita a tunaninta harka kawai zaiyi da ďiyarta su tatsi kudi su bar banza,
sai kuma gashi da aure yazo musu, ita kuwa sam bazata iya aurawa ďiyarta bahaushe ba tafi son kabilarta kuma dan garinsu wato OKENE, mikewa tayi ta shiga wani ďan lungu da oyiza ke yawan zama kullum in tazo abuja, waya takeyi tana dariya cikin murnar da uwarta ta kasa gane daga inda murnar ta samo asali,
zama tayi kusa da ita tana mata magana, oyiza tayi saurin katse wayar da takeyi ta kalli mamanta,
maman oyiza ta dafa ta tace sofy mun shiga cikin matsala,
oyiza ta haďe rai tace matsalar me mum, maman oyiza ta share gumin da ya tsatstsafo mata ta labarta ma oyiza duk yadda sukayi da alhj basheer, cikin damuwa tace ni bansan me yasa kika fito har kika kai mishi abinci ba, ke da ko ruwa bakya kai ma customers in kina gurin nan,
oyiza tayi dariyar farin ciki a zuciyarta tace thank uu "Chummy lord" ta kalli mamanta tace mum wannan shine matsala? ay wannan is a blessn to us,
kinsan irin dukiyar da yake dashi ne,
kuma kinsan abun dadin bai taba haihuwa ba,
maman oyiza ta saki baki tace a ina kika san bai taba haihuwa ba,
gaban oyiza ya fadi amma ta dake tace john ne ya fada min, mamanta tace koma dai menene ni bana son auren bahaushe, oyiza ta dafa mamanta tace mum karki fara wannan maganar ma saboda bazai yiwu ba, kawai in yazo kice mishi eh mun shirya yazo ayi maganar aure,
maman oyiza cikin bacin rai tace kina hauka ne,
oyiza cikin fushi tace yess am mad in dai akan kuďi ne, kuma duk wanda ya nemi shiga tsakanina da samun kuďi ko waye wil fc d consequences,..
Maman oyiza ta mike tace to zanga yadda za'ayi ki aureshi tunda ke baki da hankali kina zuwa 1yr ya koroki in dai bahaushe ne ki ma cire a ranki dan I swear bazan bari ya shigo ko gate din restaurant dinnan ba bare yazo jin wani feedbk ta wuce tana masifa,
Idon oyiza yayi jawur nan da nan fuskarta ma ta rikiďa ta zama jawur gunin ban tsoro, ta mike kamar walkiya ta wuce motarta taja tayi gida,
wani jan akwati ta bude ta dakko wani farin kyalle da wata jar baby kamar sassakar laka,
wani kirari tayi mai karfi da ya girgiza gidan da take ciki, cikin second uku wata mace ta bayyana a gabanta cikin jajayen kaya,
"fitsarin tsoro na saki ganin halittar wannan matar jikina take ya fara rawa idona ya ciko da kwalla a zuciyata nace duk "Badiyya" ce ta sani wannan bin diddigin gashi na kawo kaina inda zan halaka" dakewa nayi na fara karanto adduoin neman tsari, nan na samu kwarin gwiwar kai kunnena da idona gurin abun da sukeyi, oyiza na hango tayi ma matar da naji ta kira da "Chummy lord" sujjada (wa'iyazubillah) chummy tasa ma oyiza wani nannaďaďďen farin yadi a kanta tace "u are safe wit me by ur side",
oyiza ta ďago kanta zuciyarta a dake tace I