Showing 159001 words to 162000 words out of 184930 words
Chapter 54 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt
sosai yake karatun Al'Qur'ani, babu dare ba rana, hakan kuwa sosai ya haifar masa da salama, acikin zuciyarsa, saidai kuma duk wani bugun numfashi dana zuciyarsa, tare suke tafiya da soyayyarta, ƙarya yake, shi yasani, ƙaryane, soyayyar Zahrah, tafita acikin zuciyarsa, lokaci guda, baisan wani irin kalan, zazzafar soyayya bace yakeyi mata.
Zaune yake akan kujera, ya lumshe kyawawan idanunsa, sallaman Abid ne ya karaɗe cikin falon, ahakali ya ware idanunsa, akan Abid.
Murmushi Abid, ya sakar masa, haɗe da ƙarasowa, wajen da Zaid ɗin ke zaune.
"Namijin duniya!" Abid yafaɗa yana me dafa kafaɗan Zaid.
(Namijin Duniya, na Aunty Mami, wacce bata karantaba, tayi missing)
Murmushin ƙarfin hali, Zaid yayi, haɗe dasa haƙori ya cije laɓɓansa, girgiza kansa kawai yayi, yana me tunano rayuwarsa ta baya.
"Yaushe kafara shan magani, batare da an tursasaka ba?" Abid yatambaya, yana me duba magungunan, dake zube akan wani table, dake aje gaban Zaid.
Murmushi Zaid yayi haɗe da duban Abid, cikin murya me sanyi yace.
"Please Abid, kasan banason yawan damuwa, ɗazufa kabar gidannan, yanzu kuma me yadawo da kai?"
Murmushi Abid yayi, haɗe da cewa
"Nazo ne, na maidaka gida, yajin ya isa haka, ka bar ƴar mutane, ita kaɗai, hakan kuma baidace ba"
"Zamana anan yafi min daɗi Abid, gaskiya banajin zan koma gidan nan" Zaid yafaɗi haka, da iyaka gaskiyarsa.
"Kada kace haka Zaid, bansan yakakeji acikin zuciyarka ba, amma tabbas nasan abun da kakeji bayayi maka daɗi, amma kuma, komawarka kusa da matarka, inaga zaifiyemaka wannan zaman kaɗaicin, da kakeyi"
"Banajin zan iya zama da wata Abid, Zahrah ce muradina, amma narasata" hanunsa yaɗauka, yakamo na Abid, ya ɗaura a dai-dai, saitin zuciyarsa, Cike da rauni yace.
"ji yanda zuciyata, take bugawa Abid, soyayyarta ne acikin ta, marar misaltuwa, inaso namanta da ita, amma nakasa, nakasa daina tunaninta, wallahi inasonta Abid, kataimakeni, inaso nadaina tunata, bazan iya jurewa ba, nasan kuma bazan taɓa samun madadinta ba!" tuni har ƙwalla suncika idanunsa.
Tsananin tausayin, abokinnasa ne yakamasa, haƙiƙa Zaid yana a zabtuwa, to amma haka tasa kalan ƙaddaran take, babu wani wanda ya isa sanja masa.
"Kayi haƙuri Zaid, kasaurari abun dazan faɗa maka, haƙiƙa soyayya na azabtar dakai, amma kaci gaba da daure zuciyarka, sannu a hankali, zaka manta ta, watarana, komai zai zama labari, inaso kayi ƙoƙarin mantawa da komai, ka je ga matarka, saboda itama tanada haƙƙi akanka, koba komai kai ɗin mijin tane, kuma Allah Zai kamaka da rashin, sauƙe mata haƙƙinta, tashi kaje kayi wanka kazo, nayi dropping ɗinka agida!" Abid yafaɗi haka cikin lallashi.
Babu musu Zaid yamiƙe, ya wuce cikin bedroom ɗinsa, dakansa ya haɗa ruwa yayi wanka, yana fitowa ya sanya, wasu riga da wando, masu kalan jinin kare, wato maroon colour, kayan suna da kyau, kasancewarsu, masu tsada, sosai kyawun sa yafito, acikin kayan, hmm ZAID, ZAID ne har yau, shiɗin na musammanne, irinsa basuda yawa, kuma wahalar samu garesu, shiɗin nadabanne, kyau dakuma ɗaukar hankali, yana a tattare dashi, Ajininsa hakan yake, wato burgewa, ga duk wanda yaganshi, duk da cewa yayi rama, amma kuma murɗaɗɗiyar surar jikinsa tananan, da turarensa me daɗin ƙamshi, ya feshe jikinsa, yana fitowa cikin falon, Abid yasaki murmushi, cikin sigar tsokana yace.
"Sabon ango kenan, sai ƙyallin amarci kake, gashi kuma kasha kyau"
Ƴar ƙaraman tsuka Zaid yayi, haɗe da wurgawa Abid harara.
"Nifa banason Iskanci, wallahi idan kasake ka kunnani, babu inda zani!" yaƙare maganar aɗan ƙufule.
"Sorry abokina, muje ko" Abid yafaɗi haka yana me tashi tsaye.
A motar Abid suka tafi, Abid ne ke jan motar, sai jan Zaid da hira yake, shi dai Zaid shiru yayi masa, haɗe da lumshe idanunsa, taya zai fassara abun dayakeji akanta?
Suna isa ƙofar katafaren gidan, Abid ya tsai da motarsa, haɗe da juyowa ga Zaid, hanunsa ya ɗaura akan na Zaid, cike da kulawa yace.
"Kamar yanda na faɗama tun a farko, tabbas saika daure, nasan kanajin ciwo, amma dan Allah karka cigaba da sanya, kanka acikin damuwa, basai na faɗa maka ba, nasan kasan cewa, akwai haƙƙi, da kuma alhakin Zahrah, dake bibiyarka, haka kuma idan har ka cutar da Afra, Allah Bazai barkaba, haka kuma haƙƙinta ma dake kanka, bazai barka, kayi rayuwa, me daɗi ba, please Zaid kayi controll ɗin kanka kaji!" cike da lallashi Abid ya faɗi maganar.
Ajiyar zuciya, Zaid ya sauƙe, haɗe da jinjina kansa, alamar yaji, buɗe murfin motar yayi ya fice, saida Abid yaga shigan Zaid gida, kafun ya tada motarsa yabar ƙofar gidan.
Tana zaune a falo, sanye take da riga da sket na kanti, gaba ɗaya tayi wani irin rama, duk da cewa dama tun asalinta, ba ƙiba gareta ba, haƙiƙa tana cikin damuwa, kwananta biyu kenan, bataji koda motsinsa bane, duk da cewa tana mejin tsoronsa, amma kuma tana buƙatar ganinsa, da sallama ɗauke a bakinsa, ya shigo cikin falon, Afrah najin sallamarsa, tayi saurin ɗago da kanta ta kalleshi, kallo ɗaya yayi mata ya kau da kansa.
Ƙarasowa cikin falon yayi, haɗe da zama akan kujera, cike da girmamawa, Afrah ta gaidasa, haɗe dayi masa sannu da zuwa.
Babu yabo ba fallasa, ya amsa mata, shiru ne yashiga tsakaninsu na ƴan sakanni.
Ƙirjinta na bugawa tace "Me za'a kawo maka?"
Kallonta yayi naɗan sakanni, da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yace
"Kawomin Ruwa"
Jikin Afrah na tsuma, ta miƙe don kawo masa ruwa, kamar yanda ya buƙata.
Ruwan Faro takawo masa haɗe da ɗan ƙaramin glass cup, har ƙasa ta durƙusa ta aje masa ruwan, a gabansa.
Ɗaukan goran ruwan yayi yakai bakinsa, saida yasha fiye da rabin ruwan, kafun ya aje goran yana shirin miƙewa tsaye ne, yaji Afrah tasanya hanu ta kama ƙafansa, fuskarsa ɗauke da mamaki, ya juyo da kallonsa gareta, gani yayi fuskarta, tayi chaɓa chaɓa da hawaye.
"Dan Allah Kayi haƙuri, kada kajuyamin baya, inason nayi zaman aurena cikin salama, idan baka yafeminba, bazan taɓa jin daɗi ba, wallahi ƙaddarata ce tazo a haka!" kukane yaci ƙarfinta.
Wani irin tausayinta ne yakamashi, "Gwara taki ƙaddaran, tazo miki da sauƙi, akan tawa ƙaddaran" yafaɗi haka acikin zuciyarsa.
Hanunsa yasanya, ya kamo kafaɗunta, ya ta data tsaye.
"Ya isa haka, kidaina kukan nan banaso yana samin headache, kinci abinci ne?"
Kanta ta girgiza alamar "A'a"
"Okay, kinada abun da zakici ne ko kuwa?"
"Eh inadashi, na dafa abinci ɗazu"
"kici abinci!" yafaɗa ataƙaice, yana me nufar hanyar ɗakin sa.
Daɗine yakusa kashe Afra, sam bata tsammaci kulawa, har haka daga gareshi ba.
Zaid kuwa yana shiga cikin ɗaki, ya cire rigar dake jikinsa, ya wurga cikin wani dustbin, ɗin aje kayan wanki, yana shirin cire belt ɗin wandonsa ne, yaji anayi masa knockig ƙofarsa, wani irin haushine ya kamasa, a hasale ya nufi wajen ƙofar don ganin waye.
Yana buɗe ƙofar sukayi ido huɗu da Afrah, sai da taji gabanta ya faɗi, musamman da ta ganshi a tuɓe, amma kuma dolenta zata kau da tsoronta.
"Meye?" yatambaya yana me ƙare mata kallo.
"Ammm... dama abincine nakawo maka" tafaɗa tana me kallon plate ɗin dake riƙe a hanunta.
"Banaci!" yafaɗa ataƙaice yana me yunƙurin rufe ƙofar ɗakin nasa.
Dasauri ta kutsa kanta cikin ɗakin, cike da mamaki yake kallonta.
"Dan Allah kaci, kada kacemin a'a, Dan Allah!" tafaɗi haka tana me langwaɓar da kanta gefe, take idanunta sukayi rau rau dasu, da'alama kuka take son yi.
Ajiye abincin anan, yafaɗa yana me nuna mata kan sofa, cikin jin daɗi ta aje abincin, harta juya zata fita kuma, saita tsaya, haɗe da dawo da kallonta garesa. "Kayi haƙuri, ko badanni ba, kaci abincin" juyawa tayi tacigaba da tafiya, hartakai bakin ƙofar fita Zaid yace
"Afra"
Juyowa tayi garesa, ƙwalla yagani kwance acikin idanunta, da hanunsa yayi mata nuni alamar tazo, kanta aƙasa hartaƙaraso gareshi, domin gaba ɗaya, yacika mata idanu, sosai murɗaɗɗiyar surar jikinsa, ta ƙayatar da ita.
Bata tsammata ba saiji tayi, yasanya hanunsa, ya jawota jikinsa, rungumeta yayi, haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗanta, ya lumshe idanunsa, jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, hanunta duka biyu tasanya itama ta rungumesa, ƙam, haɗi da lumshe idanunta, wani irin shauƙi ke ratsata, ƙamshin sa mai matuƙar daɗi, shi yayi sanadiyar dulmiyata cikin wata duniya....
Yana rungume da ita amma kuma zancen zuci yake.
"Tabbas, abun da Abid yafaɗa masa, gaskiyane, Afra itace matar da Allah Ya zaɓa masa kuma daidai dashi, wannan zaɓin Allah Ne, bazaɓinsa ba, kuma zaɓin Allah Yafi zaɓinsa, saboda haka, dole zai karɓi Afra amatsayin matarsa, kuma zai yi ƙoƙari wajen ganin, ya yi mata adalci, bayajin sonta aransa, amma zaiyi iyaka, bakin ƙoƙarinsa wajen ganin, yazauna da ita lafiya , idan ya rabu da ita, baisan wace buɗaɗɗiyar zai kuma samu ba, shidai yasan irin Zahrah ita kaɗaice, kuma yariga daya rasata, saboda haka dole zaiyi haƙuri da Afrah, kodan son kyautata masa daya lura tanayi"
******
Zaune take akan kujera, ta ɗaura ƙafafunta, bisa kan wani table na glass, dake cikin falin, wata ƴar ficikan riga maroon colour ne, sanye ajikinta, saman wuyan rigan net ne, yayinda hanun rigan kuwa, ya kasance na vest, wato siririn hanu, tayi kyau sosai acikin shigar nata, hanunta riƙe yake da kofi, wanda ƙe ɗauke da Banana Smothie aciki, sai kaɗa kanta take da alama, taji daɗin Banana Smothie'n da take sha, duk da cewa, har yanzu bata wani jin daɗin jikinta, amma haka ta daure, take abu kamar me lafiya, miƙewa tayi daga zaunen da take, haɗe da ƙarasawa gaban tangamemen tv plasma'n dake aje cikin falon, remote ta ɗauka, ta ƙara volume ɗin tv, ta aje remote ɗin kenan, wutan nepa ta ɗauke, gashi magriba ta somayi, ɗakin babu wadataccen haske, babu zato ba kuma tsammani, taji an sanya hanu an rufe mata idanunta, wani irin ƙara tasake alokaci guda, sai kuma ta yanki jiki tafaɗi ƙasa, da hanzari Dr.Sadeeq wanda shi yayi mata haka, yasanya hanu ya tarota tafaɗa cikin jikinsa, wayarsa ya laluɓo ya kunna torchlight, daidai lokacin ne kuma wutan nepan ya kuma, dawowa haske ya baibaye ɗakin, amatuƙar razane yashiga girgizata, yana ƙiran sunanta, amma ina ko motsi batayi ba, hanunsa yakai kan hancinta, yaji babu alamar shiga da fitar numfashi, tsorone yakamasa, haɗe da ruɗewa, akiɗime yashiga jijjigata, amma bata motsaba, saboda babu numfashi ajikin ta.....
*13/February/2020*
*✅ote me on Wattpad*
@fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Lovely Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*CHAPTER 110*
A matuƙar ruɗe yake girgizata, yana me ƙiran sunanta, sosai ya tsorita da al'amarinta, gaba ɗaya ya ruɗe, yama manta da cewa shi ɗin likita ne, sungumarta yayi acikin ƙirjinsa, direct sai cikin mota, a gidan baya yasakata, yafigi motar da wani irin gudu, saboda tsabar gudun da yakeyi, mintuna kaɗan, suka kawoshi, cikin asibitinsu, a ruɗe yaje wajan, abokin aikinsa Dr.Salim, yasanar masa abun dake faruwa, emergency aka wuce da ita direct, shikam Dr.Sadeeq kasa shiga cikin emergency room ɗin yayi, suke karɓan emergency patient idan aka kawo, amma kuma sai yau, gashi shine da kansa ya kawo, sai kaikawo yake tayi, aƙofar shiga emergency room ɗin, kwata kwata hankalinsa baya jikinsa..
Bayan Mintuna 30
Yana tsaye ajikin bango, idanunsa a lumshe suke, zuciyarsa kuwa, bugawa takeyi da ƙarfi, tamkar zata faso cikin ƙirjinsa, ta fito.
Dr.Salim da sauran doctors, ɗinne suka fito daga cikin ɗakin, har yanajin tuntuɓe, agarin saurin ƙarasawa inda suke.
"Salim ya ya take? tafarfaɗo ne? Meke damunta dan Allah? Allah Yasa tana lafiya?" Duka waƴannan tambayoyin, Dr.Sadeeq ya jerawa Dr.Salim su.
Murmushi Salim yayi, haɗe da sanya hanunsa, ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq.
"Haba Man, saikace ba doctor ba, duk kabi ka ruɗe, bawata babbar matsala bace bafa, kaida kanka ma zaka iya maganceta, amma duk karuɗa kanka"
Ajiyar zuciya me ƙarfi, Dr.Sadeeq ya sauƙe, sakamakon jin daɗin kalaman da Dr.Salim yayi.
"Masha Allah! kada kaga laifina, wallahi Salim, inasonta sosai ne, banason wani abu, ya sameta shiyasa" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me lumshe idanunsa.
Murmushi Salim yayi, haɗe da cewa. "Muje office"
Babu musu Dr.Sadeeq yabi bayan Salim, suka wuce office ɗin Salim ɗin.
Suna shiga suka zauna, su dukansu akan kujera ɗaya, murmushi Salim yayi haɗe da maida kallonsa ga Dr.Sadeeq, hanu yasa ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq ɗin, cikin son kwantar masa da hankali yace.
"Kada ka damu Sadeeq, ba wani abu bane, tsananin tsorone kawai, ya sata suma, amma bayan haka babu wani ciwo dake damunta, sai dai naga tana da hawan jini, amma kuma gaskiya abokina, ka iya aiki, wai ma watanku nawa da aure ne yanzu?"
Harara Dr.Sadeeq, ya jefawa Salim. "Wannan wani irin iskanci ne Salim? me ya haɗa ciwonta da tambayan watannin auren mu? yanzu ba lokacin wasa bane, ina tsananin son matata, bana ƙaunar naga wani abu yasameta, idan akwai wani abu bayan wannan, ka sanar dani, idan kuma kaƙi zan bincika da kaina, daɗin abun nima likita ne" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me ƙoƙarin miƙewa tsaye, sarai yasan iskancin Salim, iya shegensa yayi yawa, gwamma ma yaɗauki Zahrah'nsa, kawai su koma gida, inyaso shida kansa, zaiyi checking ɗinta agida, dama ruɗewan da yayine, yasanya ya kawota asibiti.
Hanunsa Salim ya riƙe haɗe da cewa.
"Meyayi zafi kuma? daga tambayar watannin aure, yanzu duk ba wannan ba, miye tukuicina wanda zaka ban, idan nafaɗama wata magana me daɗi?"
"Tukuici kuma? wace magana me daɗi kenan? nida matata bata da lafiya, har akwai wata magana da za'a faɗamin wacce zatayimini daɗi? nace maka kadaina min wasa ko Salim, yanzu ba lokacin wasa bane." Injicewar Dr.Sadeeq.
"Koma dai menene can maka, kuma tukuicina ne sai ka bani, ina tayaka murna, saboda madam ɗinka, tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki, na wata biyu!" Salim yaƙare maganar yana faɗaɗa fari'ar, dake kan fuskarsa.
Zama daɓas Dr.Sadeeq, yayi akan kujera, haɗe da sanya hanunsa, ya kama duka kafaɗun Salim, cike da tsananin farinciki yace "Dagaske kake Salim? Zahrah na ɗauke da ciki na ajikinta? Kafaɗamin gaskiya, dan Allah karka yaudareni!"
Dariya Salim yayi haɗe da cewa "Wallahi ba wasa nake maka ba Sadeeq, da gaske matarka, kuma Zahrah'n ka, tana ɗauke da ciki, sannan kuma yana da kyau, ka kiyaye ɓacin ranta, dakuma duk wani abu, da kasan zai sanya ta tsorita, saboda yawan tsorita zai iya haifar da zubewan cikin.."
Kafun ma Salim yaƙarisa zancensa tuni, Dr.Sadeeq ya sulale ƙasa yayi sujjada, na tsananin nuna godiyarsa ga ALLAH, Haƙiƙa ya matuƙar jin daɗin, wannan albishir ɗin da Salim yayi masa, rungume Salim yayi cike da farinciki.
"Thank you so much Salim, haƙiƙa yau kasani farinciki sosai, kuma kaima insha Allah, zan saka farinciki, ta hanyar baka tukuici, wanda zakaji matuƙar daɗinsa" yanakaiwa nan a zancensa ya sake Salim, haɗe da ficewa daga cikin office ɗin, direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa.
Shigowarsa, yayi daidai, da buɗe idanunta, wani irin ƙawataccen murmushine, kwance akan fuskarsa, ƙarasowa yayi, kan gadon ya ɗagota, haɗe da rungumeta, tsam acikin ƙirjinsa, wani irin daɗi yakeji na musamman, kwanciya tayi luf acikin jikinsa, cikin muryan shagwaɓa tace.
"Hubby me mukeyi a asibiti?"
Sake matseta yayi, acikin jikinsa, haɗe da sanya hanunsa, yashiga shafa bayanta, cikin wata irin murya yace.
"Bansan dame zan iya biyanki ba Zahrah, haƙiƙa ke ta musammance, kinkawo min farinciki, na musamman, kinsani acikin wata duniya, me ɗauke da wasu surruka, wanda suke da wuyar mantawa, Inasonki My Wife! ina tsananin ƙaunarki, nagode miki sosai, Allah yayi miki albarka!" "Inaasoonki!!" yakuma faɗa, in a slow sound, yana me sumbatar goshinta.
Mamakinsa ne yacika Zahrah, ita sam bata gane me yake nufi ba, kyawawan fararen idanunta, ta zuba masa da'alamu tanason jin ƙarin bayani daga garesa.
Hanunsa yasa ya shafi gefen kumatunta, idanunsa ɗaya, ya kashe mata, haɗe da cewa.
"Verry soon, ni da ke, zamu zama parents!"
"Parents?" ta maimaita sunan abakinta, da ɗan mamaki.
"Yes, ni dake munkusa zama iyaye, saboda kina ɗauke da, ciki!" yafaɗi haka yana murmushi.
Waro manya manyan idanunta tayi, haɗe da sanya hanu ta shafi kan ɗakalallen cikinta.
"Ciki! inada ciki fa naji kace?"
"Eh kina ɗauke da cikina, yanzu haka ajikinki, saura lokaci ƙanƙani kizama mummy's boy"
Wani irin madaran farinciki ne, taji yana ratsa duk wani ƙofar sadarwa dake jikinta, ko kusa koda wasa bata taɓa, kawo hakan acikin tunaninta ba, rungumeshi ta sakeyi ƙam ƙam, haɗe da sakin wani irin murmushi, gaba ɗaya sai tanemi ciwon jikin nata ma ta rasa, "Ashe itama zata zama Mama? lallai ALLAH Abun godiya ne" tafaɗi haka acikin zuciyarta.
"Babyna mu koma gida ko?" yatambayeta, cike da tarairaya.
Dama ita uwar shagwaɓa ce, aikuwa tuni ta narke masa, haɗe da kaɗa masa kai, alamar
"Eh"
Karɓo musu takardan sallama yayi, haɗe da dawowa cikin ɗakin, ɗagata yayi caɗak, yasanyata acikin ƙirjinsa, haka yanufi ƙofar fita, daga cikin ɗakin, shagwaɓa tasakamai, akan cewa ya sauƙeta ƙasa, zata iya takawa da ƙafafunta, amma fir yaƙi, waishi bayasone ko kyakkyawan motsi tayi, bayaso tasha wahala, haka suka fito cikin asibitin, kowa sai kallonsu yake, abokan aikinsa kuwa, dariya kawai sukeyi masa, sam basuyi mamaki ba, domin kuwa duk wanda yasan Dr.Sadeeq, to yasan,cewa, yana matuƙar ƙaunar Zahrah'n shi, domin ko da yaushe sunanta, nanan raɗau acikin bakinsa.
A hankali yake tuƙa motar, tana manne ajikinsa, ji yake kamar ya maidata cikin jikinsa, wani irin sabon ƙaunarta, yakeji na huda fatarsa, yana shiga cikin jikinsa.
"Me zakici na saya miki my lovely na?" ya tambayeta, cike da kulawa.
Harshe tasanya, ta