Showing 60001 words to 63000 words out of 184930 words

Chapter 21 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt

09 Dec 2024

5741

har ƙwalla sun soma cika mata ido.


Wani irin guɗa Inna tasa, haɗe da sake kama ƙuƙu, "Lallai kuwa, wannan babban al'amari ne, mai ɗauke da tarin farinciki, Allah yasa dai kin amince masa?" cike da zaƙuwa inna taƙare maganar.


"Bazan iya ba Inna, kuma ma ni yanzu babu batun aure a tsarina,zan zauna kawai naƙare rayuwata cikin ƙaddarata!" Zahrah tafaɗa lokacin da hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa.


Salati Inna ta sanya, haɗe da soma tafa hannaye.
"Amma kedai Zahrah anyi shashar banza, sokuwa marar wayo, ashe dai baki da hankali, yanzu a yanda kike ɗin nan, kin samu ance za'a aure ki a haka, kice wai baki amince ba, lallai yau nasake tabbatar mawa da kaina cewa ke wawuyace, to wlh baki isa ba, baki isa ɓarar mana da alkhairan da zamu samu ba, aure dole ko kina so ko bakya so, wato kinfiso kita zama damu, goɗo goɗo dake ba aure ko, to kisa aranki cewa aurenki da likita ba fashi, dole!"


"Babu wanda zai mata dole!" Muryan Baffa dake shigowa cikin gidan yakaraɗe kunnuwansu.


"Maikake shirin faɗa ne malam, kakosan me ta aikata kuwa, Likita fa yace yanason aurenta amma taƙi?"


"Ƙwarai kuwa duk na saurari zancen ku, magana ta gaskia Salame, baza'ayiwa yarinyar nan dole ba, yanzu lokacin ta ne, yakamata a bar rayuwarta tasha iska hakanan!" Baffa yafaɗi maganar sanda yayi mawa kansa masauƙi akan wani ɗan dakali dake tsakiyar gidan.


"Laaaa shikenan kuma, kakosan abun da kake cewa? kana nufin zuba mata idanu zamuyi, ba mu isa mu sata dole ba? wani shan iska kake ƙoƙarin samawa rayuwarta, sanin kankane cewa babu wani wanda zaizo yace zai jajiɓeta a yanda taken nan, don kawai likita ya rufa mata asiri yace zai aureta, saikayi ƙoƙarin hure mata kunne."


"Tashi ki koma ɗakinki kinji Zahrah, kiyi tunani mai kyau, idan kin yanke hukunci to kisanar dani!" Baffa yafaɗa cike da kulawa.


Cikin rashin ƙarfin jiki haka Zahrah ta koma cikin ɗakinta, yayinda take jiyo bala'in Inna a tsakar gida.
Jingina bayanta tayi da bango, haɗe da lumshe idanunta, saiyanzu take jin cewa bata kyautawa Doctor Sadeeq ba, amma kuma shima baikyautu ace yazo mata da magana mai nauyi kamar wannan ba, ko da wasa bata taɓa kawowa a ranta cewa wani zai sota anan kusa ba, gaba ɗaya ta cire soyayya a tsari da jerin rayuwarta, tabbas sai dai ta yaudari kanta, amma tasan bazata taɓa ƙara son wani ɗa namiji ba a rayuwarta, ta yarda da shawaran da Husnah ta bata, amma kuma abune mawuyaci, tarayyanta da Dr Sadeeq yazama mai ɗorewa, shin dagaske aurenta yakeso yayi koko shima wata manufartasa yakeson cimmawa? tatambayi kanta tambayar da bata da amsa, "Idan bakiyi aure ba, haka zaki dawwama Zahrah?" wata zuciyarta tayi mata wannan tambayar. hawayene suka shiga gudu akan fuskarta, lalllai akwai babban ƙalubale a gabanta.


Zaune yake akan derny table ɗin dake tangamemen falon Hajiyar tasa, plate ɗin abinci ne aje a gabansa, yayinda yake juya spoon ɗin dake cikin abincin dake gaban nasa a hankali, kusan mintuna 10 kenan da kawo masa abincin, amma yakasa koda kai loma ɗaya ne na abincin bakinsa, gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya garesa.
Cike da tuhuma Hajiya da tun ɗazu take kallon sa tace
"Wai meke damunka ne Sadeeq? gaba ɗaya yanayinka ya sauya, kowa yaganka yasan cewa kana cikin damuwa? gashi nace kaje gidan su Saleema, amma kayi banza da maganan bakaje ba har yau"


Ajiyar zuciya Doctor Sadeeq ya sauƙe haɗe da maida kallonsa ga mahaifiyar tasa.
"Inada damuwa Hajiya!" yafaɗi hakan cikin sanyin murya.


"Subahanallah! damuwa kuma Sadeeq, damuwar me?" Hajiya ta tambaya cike da kulawa, Allah yasani tana matuƙar son ɗan nata.


"Nasamu wacce nake so ne Hajiya!" Sadeeq yafaɗa cikin ɗar ɗar, don baisan ya Hajiyar tasa zata ɗauki al'amarin ba.


"Kasamu wacce kake so? wani irin magana ne wannan, wato so kakeyi kamai dani ƙaramar mace ko, to wallahi baka isaba, bazai taɓa yiwuwa ba, nariga dana gama magana da iyayen Saleema, har ƙanin mahaifinka yashigo cikin lamarin, saboda haka wannan batun kama dainasa tun kafun ranka yakai ƙololuwa wajen ɓaci, banason shirme!" Hajiya tafaɗi maganar a fusace, haɗe da tashi tabar masa falon.


Tabbas dama yasani ko da Zahrah ta amincewa aurensa, to balalle ne Hajiyarsa ta amince masa ba, amma yasan cewa yanamawa Zahrah so mai tsanani, kuma insha Allah, zai aure ta ya rayu da'ita har zuwa ƙarshen rayuwarsa, domin yaji hakan a jikinsa.


(Tofa readers kunji abun da Hajiyar Dr tace, shi kuma kunji abun da yace, koya zata kaya oho.... Kuyi haƙuri wlh yau ina busy! Shiyasa na muku kaɗan.)


*7/December/2019*


*Voted,Comment, and Share please..... Follow me on Wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
*Phatymasardauna*


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


'''{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*



*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*Chapter 50 to 51*


Cikin rashin kuzari yamiƙe haɗe da nufar hanyar barin falon, ko kaɗan babu nutsuwa acikin zuciyarsa, ko sake bi takan abincin nasa baiyi ba, haka yafice daga cikin falon. kaitsaye ɓangarensa yanufa. Shirya kansa yayi cikin riga da wando na suit. kaitsaye asibiti ya wuce domin kuwa akwai wasu patient da zai gani.


Gaba ɗaya tunanin Zahrah ya kulle, hartakai ta kawo ko makaranta taje ma bata da wani aiki saina tunani, ko karatun ma da ake koyar dasu bata fahimta, abubuwane sukai mata yawa, tayi matuƙar danasanin marin da tayi mawa Dr Sadeeq, haƙiƙa idanunta sun rufe, batare da tayi tunanin komai ba ta yanke hukunci, sai dai kuma har yanzu tunaninta daya gushe bai dawo gareta ba, takasa yanke hukunci, haka kuma takasayin tunani mai kyau, saidai tayarda da abu ɗaya. shine Doctor Sadeeq sam basa'an auren ta bane, yafi ƙarfinta. Yau kimanin kwana huɗu kenan da faruwar haka a tsakaninsu, tundaga wannan daren kuwa harzuwa yau, Dr baisake zuwa gareta ba, saidai fa kullum safiya, yana turo drivern sa akan yaɗauketa yakaita makaranta. amma zancen dai ɗayane, bata taɓa yarda tashiga motar, koma sauraran driver'n nasa batayi.


Dariya sosai Mahmud yashiga yi, a lokacin da yagama jin matsalolin abokin nasa, haƙiƙa Sadeeq yabasa dariya, ko da wasa bai taɓa tunanin wai Namiji kamar Sadeeq zaiji tsoron furtawa mace kalmar soyayya ba.
Tsuka Dr Sadeeq yaja haɗe da ɓata fuska cike da takaicin dariyan da Mahmud ɗin ke masa yace
" Bawai nafaɗa maka matsalata bane don kasani a gaba kayita min dariya ba, mafita nake nema Mahmud, gaba ɗaya kaina ya kulle, inasonta banakuma tunanin zan'iya barinta, amma kuma naga alamomin cewa zan rasata a fili!" Dr Sadeeq yafaɗi maganar cikin son abokinnasa ya ƙarfafa masa guiwa.


Ƙoƙari Mahmud yayi wajen tsaida dariyar tasa haɗe da gyara zama
"Yazama dole nayi maka dariya Sadeeq, a matsayinka na likita bokan turai, ka kasa jure zafin soyayya, amma kuma ko kaɗan banga laifinka ba, sai dai kuma, akwai ƙalubale a gabanka!" Mahmud yaƙare maganar yana mai waina pen ɗin dake riƙe a hanunsa.


"Wani irin ƙalubale kenan Mahmud?" Dr Sadeeq yatambaya cike da zaƙuwa, saboda shi mafita kawai yake nema.


"Nasara ko kuma akasinta, sune babban ƙalubalen da zaka fuskanta, amma ina mai maka fatan nasara, duk dacewa banganta ba, amma nasan tahaɗu sosai, saboda nasan abokina ya'iya zaɓe!" Mahmud yafaɗi hakan cike da barkwanci, wanda hakan kuma halinsa ne.


"Bazaka taɓa canjawa ba Mahmud, kai ko da yaushe idan ana magana mai amfani saikayi yanda kayi ka sako wasa a ciki." Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai shafa suman kansa.


Ƴar ƙaramar dariya Mahmud yayi haɗe da ɗaukan cup ɗin juice ɗin dake gabansa yakai zuwa bakinsa.


"Babu amfanin ƙara tada zancen a gareta Sadeeq, tunda ta nuna maka bata sonka, inaganin kabata lokaci, ko ba komai zatayi tunani mai kyau, amma fa hakan danace bawai yana nufin kada kasake zuwa gareta bane, zaka iya zuwa gareta ako da yaushe, amma kada ka sake ɗago mata da zancen inaga haka zaifi!" Mahmud yafaɗi hakan cike da son ƙarfafamawa abokinsa guiwa.


Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe, haɗe da haɗiyar yawu, sai yanzu yasomajin sanyi a cikin zuciyarsa, domin kuwa da gaba ɗaya kansa ne ya kulle.
"Zanyi yanda kace Mahmud, sai dai kuma inajiyewa kaina tsoro, kada a gaba taƙi amsata, sannan kuma yanzu bansan da wani ido zan kalle ta ba!" Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin ɗar ɗar.


Dariya Mahmud yakuma kwashewa dashi a karo na biyu, lallai yayarda cewa so mugun abune, domin kuwa shi kaɗai ke sa jarumi kuma gwarzon namiji acikin tsoro dakuma ɗar ɗar.


"Yanaga jikinka gaba ɗaya yaɗau rawa, kada dai kabani kunya, tsoronta kakeji tun yanzu, idan kuma akayi auren yaya kenan?" Mahmud yatambaya cike da shaƙiyanci.


Tsuka kawai Dr Sadeeq yakuma ja, haɗe da miƙewa tsaye, domin idan yabiye ta Mahmud to baƙin ciki sai ya cika masa zuciya, domin kuwa halin Mahmud ne tsokana da yawan barkwanci.


"Gwamma nayi tafiyata zaifi min, kayi dariyanka ka ƙoshi, ai nine nakawo kaina office ɗinka, kana da right ɗin da zaka iyamin komai" Dr Sadeeq yakare maganar yana mai gyara zaman suit ɗin dake jikinsa.


Ko sake sauraran Mahmud dake ta faman dariya baiyi ba, yayi ficewarsa daga office ɗin Mahmud ɗin.


Cikin ɗan kuzarin da yasamu yake tuƙa motar tasa, yanzu kam yagama aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa. Kai tsaye gida ya koma, wanka yayi haɗe da shirya kansa cikin wani haɗaɗɗen riga da wando na jeans masu kyaun gaske, sosai kayan sukai masa kyau a jiki, suka kuma fito da asalin kyawu da kwarjininsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turare. Makullin motarsa ya ɗauka haɗe dasakai yafice daga cikin ɗakin.


Zaune take akan ƴar katifarta, daga ita sai wata riga marar nauyi, jakan kayan shafanta ne aje a gabanta, da'alama daga wanka tafito, domin kuwa wani sashi na jikinta ɗauke yake da danshin ruwa. Kallo ɗaya zakai mata kafuskanci irin ramar da tayi lokaci guda, gaba ɗaya ta zabge ta faɗa, hips da breast ɗin tane kawai suke a cike a jikinta. A hankali take shafa Vaseline ɗin dake riƙe a hanunta, Yanayin yanda take shafa vaseline ɗin idan ka gani, kace dole akai mata. tana gama shafa mai ɗin, ta murza powder kaɗan akan fuskarta, haɗe da shafa kwalli a cikin idanunta, take fuskarta ta tasakeyin fayau, yayinda idanunta, suka sake bayyana girmansu a fili,kasancewar kwallin yana taimakawa wajen bayyana girman ido.


Kallonta tamayar kan ɗan ƙaramin agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe 5 na yamma kenan, kuma dai dai lokacin sukayi da Husnah cewa zataje ta sameta a gida. Cikin rashin kuzari, ta miƙe haɗe da ɗaukan kayanta riga da sket na atamfa tashiga sanyawa, duk da cewa atamfar mai sauƙin kuɗi ne, amma hakan baihana ta yi mata kyau a jikinta ba. Wani irin zazzaɓi takeji yana sanɗan jikin ta, idan ba don tariga da tamawa Husnah alƙawarin cewa zata zo yau ɗin ba, to tabbas da ta ɗage zuwa gidansu Husna'n saboda bata wani jin daɗin jikinta, takumasan cewa damuwace kurum tayi mata yawa.


Inna ce tashigo cikin ɗakin, adai dai sanda Zahrah ta gama sanya hijab ɗinta.


"Au ashema kinsan da zuwansa kenan?" Inna tatambaya tana mai ƙarewa Zahrah kallo.


"Banganeba Inna, zuwan waye kuma?" Zahrah taje fawa Inna tambaya cikin rashin fahimtan inda kalaman Inna'n suka dosa.


"Naga kinshirya tsab kamar kinsan da zuwansa, to koma dai menene kije yanajiranki a waje!" Inna tafaɗi hakan tana mai ƙoƙarin barin ɗakin.


"Waye Inna? kuma ni shirin nan da kika ga nayi, gidansu Husnah zani, amma waye ke nemana ?" Zahrah takuma tambaya cike da son ƙarin bayani.


"Waye kuwa zaizo neman ki a yanda kike ɗinnan, ai sai dai shiɗin da har ya yarda zaiyi JIHADI ya aure ki a haka, amma wai saboda son zuciya da butulci irin naki, kike neman watsa masa ƙasa a idanu!" Inna taƙare maganar dai dai sanda tayificewarta daga cikin ɗakin.


Wasu irin siraran hawayene suka samu nasaran gangarowa daga cikin idanun Zahrah, tabbas gaskia Inna ta faɗa, babu wani mai nemanta sai shi ɗin shi kaɗai, kuma tabbas tayadda shima JIHADI yayi kamar yadda Inna tafaɗa, ashe dagaske ne itakam ƙaddaranta tayi mata mummunan zane a goshinta, saurin share hawayenta tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin.


Tsaye yake a jikin motarsa yayinda kansa ke duƙe a ƙasa, ɗan makullin motarsa ce riƙe a hanunsa yana kaɗawa, wannan karon kam sosai yake yaƙi da zuciyarsa don bayaso tasake sanya masa tsoro kokuma ɗarɗar.


A hankali take taku cike da nutsuwa har ta ƙaraso garesa, ɗan nesa dashi ta tsaya haɗe da yimasa sallama cikin sassanyar muryarta wadda bata fita sosai.


Lumshe idanunsa yayi haɗi da buɗesu a lokaci guda, badon komai ba sai don yanda sassanyar muryarta ta daki jiki da zuciyarsa.


"ZAHRAH!" yaƙira sunanta cikin murya marar fidda ƙaƙƙarfan sauti.


"Um!" Zahrah ta amasa masa batare da ta'iya motsa bakinta ba, haka kuma kanta a duƙe yake tunda tazo bata'iya ɗaga kai ta kallesa ba.


Kallonta yashiga yi tundaga ƙasanta har sama, tabbas duk da cewa a cikin hijab take, amma hakan bai hanasa hango rahamar da tayi ba, take yaji zuciyarsa tayi sanyi, tausayinta yasake kamasa.


"Inaso kimini iso cikin gida, inaga maganar mu acan zaifi, domin ina buƙatar zama!" yafaɗa cike da ƙosawa da tsayuwan da yakeyi.


Sumi sumi haka ta juya ta nufi cikin gida, harta shige cikin gidan bai ɗauke idanunsa daga kanta ba, "Wallahi Zahrah ta haɗu, komai nata mai kyau ne!" yafaɗi hakan a fili, cike kuma da shauƙin soyayya.


Jim kaɗan Zahrah tafito, tana mai wasa da yatsun hanunta, "Kashigo!" kawai ta'iya furtawa cikin murya mai sanyi. Tana gaba yana biye da'ita haka suka doshi cikin gidan.


Katuwar tabarma tabaje musu a hanyar zaure, yayinda ta je ta zauna a can ƙarshen tabarman ta takure waje ɗaya, tamkar amaryar da aka kaita ɗakin miji yau yau, lol.


Murmushi Dr Sadeeq yayi bayan yayimawa kansa mazauni, dole dai shi zai ci gaba da zama jarumi ako da yaushe.


" Miye haka? ai ko da yanka naman jikin mutane nake, ya kamata ace kin matso kusa dani, balle ma kuma ni ba'abun da nakeyi, ko na taɓa miki wani abune ?" Dr yafaɗi hakan cike da kulawa.


Saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, domin yadawo mata asalin Likitan da tasani, kuma gaba ɗaya ya sauya wasu ɗabi'un nasa.


Giransa ɗaya yaɗage sama, haɗe da cewa "Yadai, ko nayi wani sabon laifi ne akan wancan banda labari?"


Girgiza kanta tashiga yi ita kaɗai tamkar ƙadan garuwa, domin ita tama rasa maizata ce dashi domin kuwa da wani salon yadawo.


"Matso kusa dani mana!" yafaɗa cikin sanyin murya, mai ɗauke da lallashi.


Cikin rashin kuzari, ta koma tsakiyar ta barman ta zauna, bayan ta haɗa jikinta duka ta takure waje ɗaya.


Ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe haɗe da sanya hanunsa yashafi ƙasumbar dake kwance akan fuskarsa.


"Maiyasa zakisa kanki a damuwa Zahrah? yawan kuka dakuma yawan tunani marassa amfani, basa haifar da komai sai gajiyar da ƙwaƙwalwa, please banso kina wahalar da ƙwaƙwalwarki, nasan cewa abaya banine sila ba, amma yanzu nine sila.!" ɗanjim yayi kana yaci gaba da cewa..." Kiyi haƙuri Zahrah, nasan bankyauta ba, amma inaso kimanta komai, inaso ki fuskanci karatunki, ki maida hankali sosai kinji ƙanwata, bawanda zaimiki dole, ke mutumce kuma kowani ɗan adam yana da ƴanci, kema kina da ƴanci, saboda haka ki daina kuka kinji ƙanwar Likita!" Yanayin yanda yaƙare maganar kaɗai ya'isa yasanya zuciya hucewa daga cikin fushi.


Kuka kawai Zahrah ta fashe dashi mai sauti, domin kuwa sai yanzu nadaman abun da ta'aikata a garesa yadawo mata sabo fil. A hankali ta ɗago idanunta da suke ɗigan hawaye tamaida kallonta garesa, wannan fuskar ta mara? ta tambayi kanta, tabbas batayiwa kanta adalci ba, Dr Sadeeq baicancan ci mari daga gareta ba. kukane yakuma ƙwace mata, don batasan tayanda zata soma basa haƙuri akan abun da tayi masa ba.


Cike da damuwa ya dawo kusa da'ita, har suna iya juyo ƙamshin turaren juna.


"Subahanallah Zahrah kuka kuma? kinfasan banaso, kidaina kuka kinji, ki faɗamin idan ganina ne bakiso, yanzu zantafi Zahrah, nazo ne dama nabaki haƙuri akan abun da yafaru tsakanina dake, kiyi haƙuri Zahrah haka bazata...." Kasa ƙarasa maganar yayi sakamakon Zahrah da ta sanya duka hannayenta biyu ta toshe masa baki.


"Dan Allah kada ka ƙasƙantar da kanka awajen wacce bata dace ba, bata kuma cancanta ba, bakaine yakamata kabani haƙuri ba, nice yakamata na baka haƙuri, bai kyautu ace na mareka ba, nayi nadama Doctor, dan Allah kayi haƙuri, bansan yanda zanyi ba ne banda zaɓi, kayafemin!" Zahrah ta ƙare maganar cikin kuka, haɗe da karyewar zuciya.


Take yaji tausayinta yasake ninkuwa acikin zuciyarsa.


A hankali ya sanya hanu yazame hannayenta dake kan bakinsa, domin kuwa hakan da tayi masa har ya sanya tsikar jikinsa sun soma motsawa.


"Kinaso nayi haƙuri?" Dr yatambayeta.


Kaitashiga kaɗawa cikin kuka alamar "Eh"


"To kidaina kuka, domin kuwa daina kukanki shikaɗaine zaisanya nayi haƙuri nakuma manta da komai, kuma ko dama ni Zahrah batayi mini laifi ba, ƙanwata bata laifi a wajena, saboda haka share hawayenki kinji!" yaƙare maganar yana me miƙomata wani farin handkerchief wanda yafito dashi daga cikin aljihun wandonsa.


Karɓan handkerchief ɗin Zahrah tayi, cike da shagwaɓa tashiga share hawayen dake gudana akan fuskarta, ajiyar zuciya kawai take sauƙewa akai akai domin kuwa ko ba komai tarage wani nauyi dake maƙare a gefen zuciyarta.


"Yauwa ƙanwata, kinga kinfi kyau idan kina murmushi dakuma dariya, inaso akoda yaushe kikasance cikin farinciki!" Dr yafaɗa cikin nishaɗi, domin kuwa sosai yaji daɗin yanda Zahrah ta sauƙo daga fushin da takeyi dashi.


Tana gama share hawayen nata ta miƙamasa handkerchief ɗinnasa.


Kai yagirgiza alamar a'a haɗe da gyara zamansa "Nabaki kyauta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login