Showing 72001 words to 75000 words out of 184930 words

Chapter 25 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt

09 Dec 2024

5715

neman ka bijirewa auren ƴar uwa kuma aminiyata da aka baka? Ashe dama wacce kake ikirarin kana so ɗin, ba cikakkiyar mace bace, sauran layine? kaban mamaki ƙwarai Sadeeq, amma bakomai ni na sakema har haka ta faru, kuma tabbas zanɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan ka, daga kai har sakaryar yarinyar da ka bawa soyayyarta amanna, bansan cewa rashin hankalin naka har yakai haka ba, ashe har zuwa kamun ƙafa wajen mutane kakeyi, akan cewa azo a bani baki, nabarka ka auri wacce tagama raba budurcinta ga mazan layi, hmmm wallahi kasaurari hukuncin da zan yanke, kuma tun wuri ka gaggauta cire tunanin auren wannan yarinyar aranka, domin kuwa bamai yi wuwa bane!" fuuu haka Hajiya ta juya ta fice daga falon nasa ranta amatuƙar ɓace...


Kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!"
Shine abun da yafito daga bakin Dr Sadeeq, wanda yasanya hannayensa gaba ɗaya ya dafe kansa... "Me yasa Aunty Raliya? meyasa zakimin haka?" yatambayi kansa cikin takaici dakuma ɓacin rai. Tabbas yasan Aunty Raliya ce ta sanar da Hajiyansa komai, domin kuwa lokacin da yake gaban Baffa Amadu ta ƙirasa, bai ɓoyemata ba kuma yashaida mata cewa yana gidan Baffa Amadu'n, ashe ita harta gane mai yakawosa, shine kuma tasanar da Hajiyarsu komai... Take idanunsa suka kaɗa sukai ja,, ba abun da yake masa ciwo kamar aibata Zahrah da akeyi, kowa idan yatashi sai yajefeta da sunan wacce ta watsar da mutumcinta a waje, alhalin kuma itama ba laifinta bane, ƙaddarace dakuma tsautsayi, domin kuwa shi kansa sheda ne akan abun da yafaru da'ita, tunda har kusan haukacewa tayi. Rasama me yake masa daɗi yayi, da wanne zaiji ne? da soyayyar Zahrah, ko kuma da fushin da Hajiyarsa keyi dashi. Gaba ɗaya ma ji yayi zazzaɓi nason kamasa don haka kawai sai ya koma ɗakinsa ya kwanta, ba abunda yake ambata sai sunan Allah, domin kuwa shi kaɗai ne zai iya kawo masa ɗoki,, dama kuma mu dashi muka dogara shine mai kowa kuma mai komai, sarkin da babu kamarsa, Allah kenan buwayi gagara misali, maiyin duk yanda yaso mai kuma ƙwacewa da kuma bayarwa alokacin da yaso, ga kuma duk wanda yaso.....


Zahrah kuwa tunda ta faɗa duniyar bacci ba'ita tafarka ba, sai gaf da'ana ƙiraye ƙirayen sallan magriba.. Kaitsaye banɗaki ta wuce taje tayi wanka haɗe da ɗauro alwala tazo ta kabbara sallan magriba.


Kayanta marar nauyi tasanya haɗe da ɗauƙan wayarta dakuma ledan da kayan siyayyanta ke ciki, tafito farfajiyar gidan nasu, zaune ta iske Inna tana faman ƙoƙarin kunna redio'nta, wanda koda yaushe take tare dashi kamar jaraba.


"Barka da dare Inna" Zahrah tafaɗa lokacin da tayi mawa kanta mazauni a kusa da Inna'n.


Inna bata amsata ba, saima kafe ledar dake hanun Zahrah'n da tayi da ido, Allah Allah take taga mene acikin ledar, domin dama bakinta ya bushe neman abun lasawa takeyi, kasancewar tuwo ta tuƙa abincin dare, bakuma tajin cinsa, tafison tasamu ƙwalam taɗan lasa, like o'o da o'o lol.


Tun Zahrah batakai ga buɗe ledar ba inna tayi gajen haƙuri haɗe da fusge ledar daga hanun Zahrah tashiga dubawa.


Ganin cewa tarkacen su Chocolate's da kuma su biscuit's ne acikin ledar yasanya Inna jan uban tsuka haɗe da bankamawa Zahrah harara.


"Aikin kenan gayyar tsiya, mutum yasan bakacin abu, amma saboda tsinannen baƙinciki dakuma mugunta, ko da yaushe shiyake saya bini bini, bazai sayo abun da duka gida za'a amfana ba mcheeww!" cikin ƙufula Inna taƙare maganar, domin kuwa ita duk wannan shirmen banzan basonsu take ba, tafiso taga daƙwalen kaza, kokuma gasheshshen nama mai zafi, yauwa tanan tafi kauri, amma kwata kwata kayan kantin nan ita ba zaɓinta bane.


Da ƙyar Zahrah ta iya danne dariyan Inna dake cikinta aciki.


Buɗe ledan tayi gaba ɗaya haɗe sa sanya hanunta taciro wani ɗan madaidaicin cake wanda daganinsa kasan yasha madara.


"Ungo wannan Inna shikan nasan zaki iyaci, saboda kema nasayoshi" Zahrah tafaɗi haka tana mai miƙamawa Inna cake ɗin.


"Yauwa kokefa, amma da kya bani wasu tarkacen banza"


Take Inna ta ɓare cake ɗin, tahau ci har lumshe idanu take, domin dai sosai cake ɗin yamata daɗi.


Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da gyara zamanta, tasoma latsa wayarta....


Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, atare Inna da Zahrah suka amsa masa.


"Wai ana ƙiran Zahrah a waje" inji cewar yaron..


Wani irin faɗuwa Zahrah taji gabanta yayi harsaida tasanya hanu ta dafe ƙirjinta......


(🤔Miye Zaid yake sake shirya mawa Zahrah ne wai readers🧐.


Hajiya problem🤣 Team Dr saiku shirya kuyo gangami kuzo kuyi banbaki ga Hajiya kozata haƙura 😜)


(Ina jin bacci amma haka nayi tƴping ɗinnan, idan kunga tƴping eror kuyi haƙuri saboda typing ɗin dare nayi)


*Voted,Comment,and Share please..... Follow me on Wattpad @fatymasardauna


9:51 pm.....


(kuyi haƙuri banyi posting da wuri ba naje makaranta ne)
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*



*Written By*
*phatymasardauna*


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️


*Editing is not allowed📵*




*CHAPTER 59 to 60*


Wani irin faɗuwa Zahrah taji gabanta yayi har saida ta sa hanu ta dafe kirjinta daya fara dukan uku uku.....


"Jekace tana zuwa" Inna tace da yaron,, bamusu yaron yajuya yafice daga cikin gidan...


"Yadai lafiyanki kuwa naga kinwani dafe ƙirji?" Inna tatambayi Zahrah, wacce lokaci ɗaya yanayinta ya sauya.


"Bakomai" Zahrah tafaɗa a taƙaice domin kuwa ko tayi ƙoƙarin ganar da Inna halin da take ciki tofa bazata gane ba...


"Tashi maza kije, ba kyau yin watsi da baƙo, wata ƙilama da alkhairi yazo miki, domin na lura keɗin baki da ƙashin tsiya" Inna tafaɗi hakan lokacin da ta miƙe daga zaunen da take.


Cikin sanyin jiki Zahrah takoma ɗaki ta ɗauko ƙaton hijab ɗinta ta sanya.


Tun kafun ta ƙarasa fita daga zauren gidannasu zuciyarta tasoma bugawa, wanda batasan dalilin hakan ba.


Wata mota ce tagani fake a ƙofar gidan nasu, kasancewar akwai hasken wuta, yasanya har kalan motar tana'iya hangowa.


Tsayawa tayi cak daga inda take, domin bazata sake tabka babban kuskuren da ta tabka a baya ba, batasan waye ba don haka bazata ƙarasa ba, idan wanda ke cikin motar yagaji ya fito, ya isketa daga inda take tsaye...


Cikin hanzari wani wanda baza'a ƙirasa da suna matashi ba, bakuma za'a ƙirasa da suna tsoho ba, yafito daga cikin motar hanunsa ɗauke da wani kwali, yayinda aka ɗaura wani kyakkyawan flower a saman kwalin... Ganin yanufota kaitsaye yasanya ta ɗan sake ja da baya..


"Sannu da fitowa ranki shi daɗe" mutumin nan yafaɗa..
"yauwa sannu" Zahrah ta bashi amsa a taƙaice...


" dama saƙone aka bani nakawomiki" wannan mutumin ya kuma faɗa cikin rusunawa haɗi da girmamawa, duk da kuwa cewa shiɗin ba yaro bane, domin yakusan haifar Zahrah'n ma, domin itama bawani yawan shekaru ne da'ita ba...


Cike da tsananin mamaki Zahrah, ta saki baki da hanci tana kallon mutumin dake tsaye a gabanta, yana miƙomata saƙon dake hanunsa...


"Wayekai?" shine kawai abun da ya iya fitowa daga bakinta, saboda gaba ɗaya kanta ya kulle...


Murmushi mutumin yayi haɗe da cewa "Ba'a bani daman sanar dake koni waye ba, kawai dai an umarceni dana kawomiki wannan saƙon, sannan dan Allah kada kice bazaki ansaba, saƙone mai mahimmanci, yanada kyau ki karɓa, sannan daganinki ke mai ilimi ce, kinsan bakyau maida hanun kyauta baya!" mutumin yafaɗi haka still yana mai sake miƙo mata kwali da flowern dake riƙe a hanunsa...


Kai Zahrah tashiga gyaɗawa, cike da tsarguwa tace " Kana da girma da kuma mutumcin da bazanyimaka gardama ba, amma kuma saidai kayi haƙuri, bazan karɓi abu daga wanda bansani ba, bankuma san menene nufinku a kai na ba" tafaɗi hakan da iyaka gaskiyarta....


"Hakane, amma ki ceci aikina, domin wanda ya ban saƙonnan nakawo zuwa gareki ya tabbatarmin da cewa, idan har baki karɓi saƙon ba, to abakin aikina, kitaimaka, ina da iyalai, kuma da aikina na dogara" mutumin yafaɗi haka cikin rauni.


Zaro idanu Zahrah tayi haɗe da jinjina maganar mutumin aranta, lallai kuwa kowaye ya aikosa yacika ɗan jin kai, ita kuma irin mutanen da tafi tsana kenan a rayuwarta wato mutum mai jin kansa....


Cike da kokonto haɗi da zullumi tasanya hanu ta karɓi abun da mutumin ke miƙomata.


"Zankarɓane kawai saboda kai, domin na fuskanci rashin karɓana zai iya sanyaka acikin matsala, amma koma waye ya turoka kace masa injini ya sanja hali, domin wannan ba hali mai kyau bane" daga haka tasakai tayi komawarta cikin gida..


Cike da murna'n cewa ta karɓi saƙon wannan mutumin yakoma mota haɗe da yi mata key yabar area'n unguwar tasu....


Zahrah tana shiga gida kaitsaye ɗakinta ta wuce, yayinda Inna ta rakata da idanu...


Zama tayi akan katifa, haɗe da tsurawa kyakykyawan kwalin nan idanu, ba iya shi kaɗai bane, abun ɗaukar hankali, hadda wannan haɗaɗɗen flower'n dake samansa ma abun burgewane, alal haƙiƙa ma ita flower'n ne yafi ɗaukar hankalinta....
Cikin sanyin jiki tasa hanu ta ɗauki flower'n haɗe da matso dashi kusa da fuskarta....lokaci ɗaya ta zabura haɗe da wurgi da flower'n gefe, take idanunta suka kaɗa sukai jajur dasu, jitayi kanta yafara juyawa, tabbas bazata taɓa mantawa da wannan ƙamshinba har abada kuwa, ajikin mutum ɗaya tasan wannan ƙamshi, bayan shi kuma batasakejin ƙamshin a jikin kowa ba,, hannayenta ta sanya duka biyu haɗe da dafe kanta dayake sara mata,, tabbas irin ƙamshinsa fulawar nan keyi, take taji wani irin tsanar flower'n ya cika mata zuciya, san nan kuma tsanarsa tasake dawo mata sabuwa fil, cike da ɓacin rai ta ɗauki flowern haɗe da fita waje da'ita, ko son ganinta ma batason yi, kai tsaye wajen da suke aje shara ta nufa, cike da tsanar flower'n ta jefa ta cikin kwandon shara, haɗe da furzar da yawu akan flower'n duk wani abu da zai tuna mata da Zaid ta tsanesa...
Ranta a ɓace takoma ɗaki, ita dai Inna dake zaune a tsakar gidan haka ta saki baki galala tana ganin ikon Allah..


"Wallahi na tsaneka, tsana mafi muni, bantaɓajin tsanar wani a raina sama da wanda nakeyi maka ba, ya Allah kada ka sake haɗa fuskata da tasa!" tafaɗi hakan a bayyane, kuma cikin tuƙewar murya...
Gaba ɗaya ƙamshin da taji flower'n nan nayi ya ɗaga mata hankali, sabuwar tsanar Zaid yasake ɗarsuwa acikin zuciyarta...
Lallai da zataga wanda yasanya akawo mata flower'n nan da ta gargaɗesa da kada ya sake kawo mata komai nasa, don bata so, domin kuwa duk wani abu da zai sanya tayi tunanin Zaid bata ƙaunarsa, koda sunansa nema batason ji"


Kwanciya tayi lamo akan gado, tana mai da numfashi, ji takeyi gaba ɗaya ta tsani ɗakin nata, domin kuwa ɗakin gaba ɗaya ya ɗau ƙamshin turaren dake jikin flower' ɗin nan....


Wayartace tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ganin Dr Sadeeq ne me ƙira yasanya ta ɗaga wayan, cikin son ɓoye damuwarta..


"Inaƙofar gida" abun da Dr Sadeeq yafaɗa kenan, a cikin wayar, domin kuwa shima dai yauɗin yana cikin damuwa....


Babban tabarma ta shumfuɗa musu a tsakar gida, kafun tanufi ƙofar gida don yi masa iso..


Kusan tare suka shigo cikin gidan, tana gaba yana biye da'ita a baya.. Gaba ɗaya yagama karantar yanayinta, ya kuma gane cewa tana cikin damuwa.


Zama yayi akan tabarman da ta shumfuɗa musu, haɗe da tanƙwashe ƙafafunsa.. Gaba ɗaya nutsuwarsa ya miƙa zuwa gareta, ta hanyar zuba mata idanu....


Gyara zama Zahrah tayi haɗe da ɗaga idanunta ta saci kallonsa, aikuwa karab idanunsu suka sauƙa akan na juna.. Cikin son basarwa tace " Sannu da zuwa, ya hanya?"


Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da lumshe idanu..."Hanya ba daɗi duk nagaji da tuƙin ma, i hope you will find a driver that will take me home" cikin zolaya yaƙare maganar..


Kallonsa tayi kawai, haɗe da yin ɗan murmushi, shiru tayi batare da tace dashi komai ba...


"Meke damunki naganki haka, ko dai ciwon kanne?" Yatambayeta cike da kulawa..


"No bashi bane, ka wai dai gajiya ne, baisakeni ba haryanzu" tafaɗi hakan a taƙaice...


"Kansa yajinjina, haɗe da sake lumshe idanunsa, shi ɗinma ƙarfin haline kawai yasa sa yazo, amma tabbas damuwar dake damunsa tana da yawa.


"Meke damunka, naga gaba ɗaya kamar baka cikin farinciki?" Zahrah ta tambaya cikin siga da yanayi na nuna damuwa..


Wani irin sanyin daɗi yaji a zuciyarsa, badon komai ba, saidon kulawa da yasamu daga gareta.


Gyara zamansa yayi haɗe da bata duka nutsuwarsa...."Bazan ɓoyemiki ba Zahrah, tabbas inacikin damuwa, kuma duk akan kine, Ina tsananin sonki Zahrah, ina da burin baki farinciki a cikin rayuwarki, amma sai dai na haɗu dake a ƙurarren lokaci, inafata zaki fahimci abun da zance dake?"


Cike da ɗaurewar kai Zahrah take kallon Dr Sadeeq, domin kuwa sam ita bata fahimci inda kalamansa suka dosa ba.


"Mahaifiyata ta zaɓamin matar da zan aura, yanzu haka maganar da nakeyi miki, har ansanya mana rana, saura sati uku"


dummm haka Zahrah taji ƙirjinta yabuga, duk da cewa bata wani jin son Dr Sadeeq a ranta, amma bazata taɓa so kyakkyawan namiji mai nagarta kamarsa ya kuɓuce mata ba, take idanunta suka ciko da ƙwalla wanda batasan na menene ba.


"Dan Allah kada kiyi kuka kinji Zahrah na, nafaɗamiki hakane don kisan halin da nake ciki, amma bawai hakan nanufin bazan aureki bane ba"


Cike da kulawa yakama duka hannayenta biyu, haɗe da kafeta da idanu. Gaba ɗaya abun da yake wakana ya kwashe ya faɗa mata, hatta maganarsa da Baffa Amadu, saida ya sanar da'ita, sai dai ya ɓoye mata ƙiyayya dakuma maganganun da yayarsa da kuma mahaifiyarsa suka faɗa akan ta na ɓatanci.
Cigaba yayi da cewa "Ki kwantar da hankalinki, na miki alƙawari nan bada jimawa ba, zaki zamo mallaki a gareni, insha Allah zanzamo mijinki Zahrah!"


Hawayene suka shiga zirya akan fuskan Zahrah, cikin murya mai rauni tace " Dama nasan cewa nayi ganganci, domin kuwa kai ba sa'an aure na bane, nagode sosai da irin kulawa da kuma ƙoƙarin da kayi a kaina, bakuma zan taɓa mantawa da hakan ba, na yarda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, idan aurena dakai baiyi wu ba, na yarda haka Allah yatsara, tun da fari shiya gurɓatamin rayuwa, ya cutar dani, cuta mafi muni, ta yanda babu wani wanda zai lamuncewa haɗa zuri'a dani, tabbas daman nasan koda kai ka aminta da aurena, ba lallai iyayenka su aminta ba?....Kukane ya ƙwace mata sosai.


Sake damƙe hannayenta yayi acikin nasa, haɗe da kafeta da idanu, sosai tausayinta ya sake kamasa.


"Kinaso nasake shiga cikin damuwa ne Zahrah?" yayi maganar cikin tausasa murya.


Bata iya amasa masa ba, sai gyaɗa masa kai da tayi alamar "A'a"


"To idan har bakyaso nasake shiga damuwa, ki daina kuka kinji Zahrah na, insha Allah, zamu rayu tare dake, harma ki haifamin kyawawan babies, masu kyau kamarki, masu irin idanunki, da bakinki, harma da irin hancinki, da kuma..." sai yayi shiru, yana mai dariya ƙasa ƙasa.


Kunyane ya kama Zahrah haɗe da dariya, duk da kuwa cewa tana cikin halin damuwa, sai kawai ta kawar da kanta gefe, gaba ɗaya jinta take a tsarge sakamakon hanunta da ke saƙale acikin nasa...


"Zantafi saboda naga dare yasoma yi, amma saikinmin alƙawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma za kisa kanki a damuwa ba, idan kikayi haka zanji daɗi sosai"


Abune mai matuƙar wuya, a dake ka sannan a hanaka kuka, amma tabbas zata jarraba wajen daure zuciyarta.


"Bazanyi kuka ba" tafaɗa cikin muryar da bata fita sosai, da badon yana kusa da'ita sosai bana ma to tabbas da bazaiji maitace ba..


"Kinyi alƙawari?" yatambayeta


"Eh" tafaɗi haka bayan taɗanyi jim.....


"Yauwa Zahrah na, nasan ai kina da cika alƙawari, taso muje mota na baki magungunanki" babu musu ta miƙe daga zaunen da take, haɗe da rufa masa baya.


Murfin motar ya buɗe haɗe da fiddo wata ƙatuwar leda.


"Ungo magungunan suna ciki, akwai bayanin yanda zakisha a jiki, please ki kulamin da kanki kinji" yafaɗi haka cikin lallashi, haɗe da miƙa mata ledan dake hanunsa.


Kasa amsan ledar tayi, saima kawar da kanta gefe da tayi.


Murmushi Dr Sadeeq yayi, domin kuwa sarai ya fuskanci hakan da tayi metake nufi.


"Kiyi haƙuri ki karɓa kinji Zahrah na" yakuma faɗan hakan cikin lallashi.


Baki Zahrah taturo gaba haɗe da cewa ...
"Kasan tun ba yauba nafaɗama cewa banaso domin kuwa hidiman da kakemin yayi yawa, mai yasa bazaka bari haka ba!" ta tambayesa cike da sakalci..


"Saboda kina da mahimmanci, kinkuma cancani namiki fiye da haka, amma yanzu dai banso kice a'a ki karɓa kinji" still cikin lallashi yayi maganar.. Badon ranta yasoba haka ta karɓi ledan.


"Saida safe" tace dashi cikin sanyin murya haɗe da juyawa ta nufi hanyar shiga gida.


"Kada kimanta kin ɗauki alƙawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma zaki shiga damuwa ba, kada ki karya alƙawari kinji mai kyau na!"


Murmushi kawai tayi masa haɗe da ɗaga masa kai alamar taji.
Yana ganin shigewarta cikin gida, shima yashiga motarsa haɗe da bata wuta yabar unguwar tasu..


Tanashiga cikin gida, Inna tayo kanta haɗe da fusge ledar dake hanunta, babu magana ba komai ta shiga zazzage ledan akan tabarma, kallonta kawai Zahrah ta tsayayi cike da takaici, sai yanzu take godewa Allah dayasanya ba Inna bace ta haifeta, domin kuwa da Innace ta haifeta to tabbas da nan gaba kaɗan zuciyarta zata fashe, saboda wannan halin da Inna keyi ba hali bane na iyayen ƙwarai, batama tsaya ganin menene acikin ledar ba, ta wuce cikin ɗakinta, domin ita dama ba wannan bane a gabanta, yanzu babban damuwarta shine, yanda zata samo maganin matsalarta.


Ɗaukan kwalin nan da aka kawo mata tayi, haɗe da soma kiciniyar buɗewa, kasancewar bakin kwalin a nane yake da wani gam me kyau..


Tana buɗe cikin kwalin wani tsadadde kuma kyayyawan agogo na mata ya bayya, gefen sa kuwa wani irin awarwarone haɗe da zobe masu kyaun gaske, wanda dagani kasan na gold ne, domin kuwa kyawunsu kaɗai ya'isa ya bayyana haka, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da mai da murfin kwalin ta rufe kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login