Showing 84001 words to 87000 words out of 184930 words

Chapter 29 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt

09 Dec 2024

5721

ɗauke da murmushi ya juyo zuwa gareta, haɗe da sanya hanunsa ya cire hular dake kansa, take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana, wacce take ɗauke da murmushi.


Jikinta ne yaɗauki rawa yayinda idanunta suka ƙara buɗewa take numfashinta yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, zuciyarta tashiga duka, ƙafafunta suka ƙage waje ɗaya, yayinda hawaye suka dinga fitowa daga idanunta tamkar anyi ambaliyan su.
Kallon yanda jikinta yake rawa Zaid yayi haɗe da dawo da kallonsa kan fuskarta jefa idanunsa yayi cikin nata. "ZAHRAH!" yaƙira sunanta da wata irin murya me sanyi, sakamakon ganin da yayi kamar cewa bata cikin hayyacinta...


"ZAHRAH" yasake ƙiran sunanta, de de lokacin ne kuma numfashin ta yashiga gudu yana neman ƙwace mata, aikuwa kasa fusgo numfashin nata tayi, lokaci ɗaya numfashinta yayi nasaran fita daga jikinta, take ta yanki jiki tafaɗi warwas a ƙasa, cikin mugun tashin hankali Zaid yayi kanta, haɗe da sanya hannayensa duka biyu ya ɗagota zuwa jikinsa, sunanta yashiga ƙira cikin tashin hankali dakuma ruɗewa, a matuƙar firgice ya sanyata acikin motarsa haɗe da shiga cikin motar da wani irin gudun gaske Zaid yafigi motar ya cillata kan titi... Gaba ɗaya ya ruɗe wani irin gudu yake shararawa baburuwansa da wanda ke gabansa ko bayansa, gaba ɗaya ya ruɗe sunan Zahrah kawai yake ambata, Allah yasa ba zuciyarta ta haɗiya ba..


Matsanancin gudun da Zaid yakeyi har ya wuce hankali, da wani irin gudu yashigo cikin asibitin yayin da ya ɗauko Zahrah caɗak a hanunsa tamkar wata ƴar tsana, haka yashigo da'ita cikin asibitin, ganin haka yasa Doctors sukayo kansa da sauri, hankalinsa a matuƙar tashe ya miƙa ta ga doctors sukayi emergency da'ita kai tsaye.. Taimakon gaggawa likitoci suka shiga bawa Zahrah domin kuwa bako maine ya haifar mata da ɗaukewar numfashin ba, face razana dakuma tsananin firgita haɗi da tsoro da suka rusketa alokaci guda, sannan yanayin yanda zuciyarta ke bugawa, yawuce mizani, idan har zuciyar tata tacigaba da bugawa da sauri sauri haka, tofa lalllai rayuwar Zahrah tana cikin haɗari...


(Niko nace idan Zaid yakashe mana Zahrah zamuci .... ko fans😂)


Iya ruɗewa Zaid ya ruɗe yakasa koda zamane, damuwarsa ɗaya shine Doctors ɗin da suke kan Zahrah, su sanar dashi meke faruwa, lallai idan har Zahrah tasamu wani matsala, to bazai taɓa yafewa kansa ba, sannan kuma babu uban da ya'isa yazauna lafiya, matuƙar likitocin nan suka kasa shawo kan matsalan Zahrah..


Kusan minti talatin likitocin nan sukayi suna ƙoƙarin shawo kan numfashin Zahrah, cikin ikon Allah kuwa sun samu komai yayi dai dai sai dai dole tana buƙatar hutu kodan zuciyarta ta samu salama...


Suna fitowa Zaid yayi kansu, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu.


Kallonsa ɗaya daga cikin manyan likitocin dasuke kan Zahrah yayi haɗe da dafa kafaɗunsa, "Ka kwantar da hankalinka, komai yayi dai dai, yanzu biyoni office ɗina"


Ba musu balle girman kai Zaid ya bi bayan liikitan.


Kasa zama akan kujeran da Dr ɗin yabasa yayi, babban damuwarsa shine yasan wani hali Zahrah take ciki.


"Nace ka kwantar da hankalinka, kazauna saimuyi magana ko" likitan yafaɗa yana me nuna masa kujera..


"Kaga Doctor bazamane yadameni ba, babban damuwana shine nasan wani hali take ciki" Zaid yafaɗi haka cikin damuwa..


"Zan faɗama ko wani hali take ciki, amma dole sai ka zauna"


Badon Zaid yasoba haka yazauna akan kujera haɗe da sanya duka hanunsa ya dafe kansa.


"Bawani babban abubane yake damunta, akwai abun da yafirgita ta ne, kuma dama anasamun irin haka, sau da dama firgici da tsoro, yakansa mutum yasamu ɗaukewar numfashi naɗan wasu daƙiƙu, amma idan tadawo hayyacinta komai zaidawo dai dai, sai dai kuma tana buƙatar hutu sosai, saboda haka bayau zaku samu sallama ba, dole sai kunjira zuwa gobe da safe, saboda yanzu haka akwai alluran damuka mata kuma suna sa bacci sosai"


Ajiyar zuciya me ƙarfi Zaid ya sauƙe, saboda jin bayanan Doctor da yayi, sun sauƙar masa da nutsuwa "Amma dole sai anan zamu kwana? me zai hana kabani ita mutafi gida, idan yaso saitayi baccinta acan" Zaid yafaɗi haka fuskarsa ɗauke da damuwa.


Murmushi Doctor yayi haɗe da cewa "Hakan bazai samu ba, saboda zata iya farkawa da kowani lokaci, bamu kuma san a wani hali zata tsinci kanta ba, bayan ta farka, saboda haka zamanku anan ɗin zaifi amfani" Doctor yafaɗi haka cike dason gamsar da Zaid.


Kai kawai Zaid yajinjina haɗe da kallon Doctor "Zan'iya ganinta kuwa? sannan kuma inaso akaita ɗaki na musamman konawane kuɗin ɗakin zan biya"


"Wannan ba'abun damuwa bane, zamu kaita ɗaki na musamman sannan kuma zaka iya ganinta, bana ƙira nurse sai a sanja mata ɗaki daganan saikaje ka ganta ko" Dr yafaɗi haka bayan yakara waya akan kunnensa. Cikin mintuna ƙalilan aka sanjawa Zahrah ɗaki inda aka kaita ɗaki na musamman.


Zaid ne tsaye akanta yana me ƙare mata kallo, karo na farko kenan daya farajin wani irin matsanancin tausayin ta acikin zuciyarsa, haɗe da wani shauƙi mai fisgar zuciya. A hankali yaƙaraso dab da gadon nataz haɗe da ranƙwafo da kansa dakuma ƙirjinsa zuwa gaf da'ita, lumshe idanunsa yayi haɗi da kai bakinsa gefen kumatunta ya yi mata kiss, haɗe da sa hanu yashafi gefen fuskarta, "I'm sorry Zahrah!" yafaɗi haka acikin maƙoshinsa. Karo na farko kenan a rayuwarsa daya soma bawa wata mace haƙuri.. Zama yayi a bakin gadon, haɗe da kama hanunta na dama yasanya acikin nasa hanun, a hankali yake murza hanunta haɗe da lumshe idanunsa.


Abu kamar wasa hankalin Inna ne yasoma tashi ganin Zahrah ta kwashe sama da awa ɗaya, a waje batare da ta shigo gida ba, gashi ta leƙa waje bataga ko da me kamannin Zahrah bane, kasa zama inna tayi gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, Baffa ne yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, ko amsa sallaman nasa Inna batayi ba tayo kansa tana cewa "Yau wa Malam gwamma da ka dawo, ko ka haɗu da Zahrah a waje kuwa?"


"Zahrah kuma, ina Zahrah'n take?" Baffa yatambaya cike da mamaki.


Nan Inna tashaida masa cewa tunɗazu tafita bata dawo ba,bayan tasanar mata cewa wani ne yaƙira ta a waje.


Take hankalin Baffa yatashi, domin kuwa Zahrah bata taɓa irin haka ba, har maƙota ya aika ko taje amma aka ce masa bata zoba, take Baffa da Inna suka zuba tagumi, sun marasa ta ina zasu fara, Inna cema takawo shawara akan cewa aƙira Doctor Sadeeq koshine yazo ya ɗauketa, aikuwa Baffa yayi na'am take yadannawa number'n Dr.Sadeeq ƙira, bugu biyu Dr.Sadeeq yaɗaga wayan,, shima bakaɗan ba hankalinsa yatashi jin dayayi cewa wai su Baffa basuga Zahrah ba, ae take yashiga motarsa yataho gidansu Zahrah'n duk da cewa dare yayi...


Kallon agogon hanunsa Zaid yayi a karo na barkatai, ƙarfe 10 na dare kenan, ajiyar zuciya ya sauƙe akaro na uku, haɗe da furzar da iska a bakinsa, kallonsa yakuma mayarwa ga Zahrah, wacce take ta sharan bacci, hakanan yatsinci kansa da sakin murmushi mai sauti, komai na Zahrah me kyaune, tafiyin kyau ma idan tana bacci.
Zama yayi akan wata kujera dake kusa da gadon haɗe da jingina bayansa da jikin bango, lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa sai yanzu ƴake tunanin ya makomarsa zai kasance idan Zahrah tafarfaɗo, domin kuwa ya hango muguwar tsanarsa acikin idanunta.


*23/December/2019*


*Follow me on Whatsapp and Wattpad*


*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI!!*


*Written By*
*Phatymasardauna*


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*CHAPTER 66 to 67*


Lokaci ɗaya hankalin Dr.Sadeeq yayi wani irin mummunan tashi, take ƙwaƙwalwar kansa tashiga charge, a iya tsawon sanin da ya yi mawa Zahrah, ita ba mace bace meson fitar dare, balle har tayi nisa da gida, sai dai kuma abun mamaki gashi yau annemeta an rasa, bayan ko ɗazu suna tare a waya shida ita, baikuma ji wani sauyi a tattare da'ita ba, sai dai kawai muryarta da yaji cikin sanyi. "To ina Zahrah taje?"
Yayi mawa kansa tambayar da bayi da amsa.. "Kodai Zahrah tayi hakane don batason aurena da'ita?" yakuma tambayar kansa, sai da zuciyarsa ta buga, shi kansa yatambayi kansa abun daya faɗar masa da gaba, kai amma Zahrah bazatayi haka ba, saboda ita da kanta ta tabbatar masa cewa ta amince da auren sa, saboda haka bazata bar gida saboda batason auren sa ba..
Kallonsa yamaida ga Inna wacce tayi tsuru tsuru da ido tamkar wata munafuka..."Da tazo fita bakiga wani alaman damuwa ko tashin hankali akan fuskarta ba?" Dr yatambaya cike da kulawa.


"Ƙwarai kuwa da damuwa tafita, saboda kwana biyun nan gaba ɗaya da damuwa take wuni sakamakon waƴansu tsinannun ƴan mata da suka zo, acewar ɗaya daga cikin su wai ita zaka aura Samira take ko Salma oho, haka nan suka zo hargida suka zagemu kaf, tamkar ma zasu mana luguden duka, to tundaga tafiyarsu dai take fama da ƙuncin rai har kawo yau, Allah dai yasa ma basune sukai mata wani abun ba" Inna tafaɗi haka cike da jimami..


Cike da mamaki Dr.Sadeeq yace "What Salima tazo har gidan nan taci muku mutunci?"


"Ƙwarai kuwa ashe dagaske kasanta, tabbas haka tace sunanta wai Salima, ita da waƴansu masu ƙoƙaƙƙun fuska, kamar an gasa nama"


Hanu Dr.Sadeeq yasanya yadafe kansa, lallai idan de har Salima bata ji kunyar zuwa ta zagar masa abar sonsa ba, to tabbas shima bazaiji kunyar zuwa har gidansu yaci mata mutumci ba, Uwa mahaifiyarsa kaɗai ze iya ɗagawa ƙafa akan Zahrah, amma duk wacce tace zata ci mutumcin Zahrah tofa shima zaici nata mutuncin, lallai yakamata ne yafara nemo inda Zahrah take kafun yasan matakin da zai ɗauka akan Salima. Sake dialing number'n Zahrah yayi amma still ce masa ake wai wayar akashe take, tun ɗazu yake ƙiran wayar anacemasa akashe wayarta ta take.. Tunanin ƙiran abokinsa inspector Adam ne ya faɗo masa, saboda yalura lamarin dole sai anshigo da hukuma ciki, tunkan suyi sake lokaci ya ƙure musu. Nan yashiga dialing Number'n inspector Adam amma har wayar ta katse bai ɗauka ba, sake ƙira yayi amma still bai ɗauki wayar ba, tsuka Dr.Sadeeq yayi haɗe da maida wayarsa cikin aljihunsa....


Asibiti


Sai yanzu tunanin halin da iyayen Zahrah zasu shiga yafaɗo masa arai, tabbas yakamata ne yasanar dasu halin da ake ciki, wayarsa yaɗauka haɗe da soma rubuta saƙo, domin bayason wayar da zaiyi yatashi Zahrah a baccin da takeyi, saboda haka gwamma yatura saƙo,a ganinsa hakan zaifi... wata number yaturawa saƙon, batare da yajira amsar da wanda yaturawa saƙon zai basa ba, ya maida wayarsa cikin aljihu.....


Dr.Sadeq ne yadubi Baffa dake a halin damuwa. "Banaje nasanarmawa ƴan sanda, akwai abokina inspector, inaga kawai gwamma naje gidansa na sanar dashi abunda ke faruwa, ina ga zaifi akan tsayuwan damuke" yafaɗi maganar yana me duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa, ƙarfe sha ɗaya na dare kenan agogon sa yanuna masa..


Sallaman da sukaji ana kwaɗawa a ƙofar gidan ne yaɗauki hankalinsu, ae ba shiri Baffa da Dr. Sadeeq suka ɗunguma zuwa ƙofar gidan, Inna ma ba'a barta a baya ba ta rufa musu baya.


Wani mutumi me shigar cute baƙaƙe suka gani tsaye a bakin ƙofar gidan, yayinda yarufe idanunsa da tabarau, da ganinsa dai zaka gane irin body guard ɗin nan ne.


"Waye kai?" Dr.Sadeeq yatambaya yana me ƙaremasa kallo.


"Saƙo aka bani nasanar daku cewa Zahrah bata da lafiya, yanzu haka tana asibiti.." baikai ga idar da zancen nasa ba, Dr.Sadeeq yace "Meyasameta sannan kuma a wani asibiti take?" duka tambayar yayisune alokaci ɗaya, kuma
cikin ruɗewa..


"Zaku iya biyoni muje" Body guard ɗin nan yafaɗa yana me nufar wajen da motar da yazo da ita ke fake.
Kallon su Baffa Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa su shigo motarsa subi bayan body guard ɗin, hakan kuwa akayi motar Dr.suka shiga yayinda Dr.yashiga bin bayan motar body guard ɗin. Gaba ɗaya ba acikin nutsuwarsa yake driving ɗin ba. Fargabane cike a zuciyarsa, bayi da wani buri da yawuce yaga Zahrah, yakuma ji meke damunta, har aka kawota asibiti batare da sanin su Baffa ba..
Suna shiga cikin asbitin wannan body guard ɗin ya kalli Dr.Sadeeq haɗe da cewa ya biyosa ciki, su Inna kuwa su jirasa, da su Inna sunso ƙi, amma sai Dr. Sadeeq yace su yarda su jirasu anan ɗin, badon su Inna sun so ba, suka tsaya daga waje... Suna shiga cikin wani corridor guard ɗin yaciro wayarsa, haɗe da karawa akan kunnensa.


"Oga na faɗa musu sunma biyoni, yanzu haka munatare da wani inazaton ɗan uwanta ne, iyayenta kuma suna waje" Abunda Body guard ɗin yafaɗa kenan cike da girmamawa.


Tsuka Zaid yayi sakamakon jin abunda guard ɗin nasa ya ce, shirmen banza, cewa yayi yafaɗamusu bawai ya taho masa dasu ba, to yanzu dayakawosu ina zai sasu, wata tsukan yakuma yi, haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin bayan ya sake rufe Zahrah da bargo..


Cakume kwalan guard ɗin nan Dr.Sadeeq yayi cike da ɓacin rai yace "Bamason iskancin banza kace tana asibiti bata da lafiya, gashi munzo kuma kana ƙoƙarin raina mana hankali, wlh idan wani abu yasameta saina ɗaureka" Cikin ɓacin rai Dr.Sadeeq yafaɗi maganan domin kuwa yulura guard ɗin nema yake ya raina masa hankali....


"Idan har ka'iya ɗauresa, to tabbas zan iya yarda na ƙiraka da suna jarumi !!" muryar Zaid takaraɗe wajen, wanda yake ƙarasowa garesu cikin takunsa na isa..


Kallon Kallo aka shigayi tsakanin Zaid dakuma Dr.Sadeeq, wanda kowannensu da irin manufar tasa kallon.


Sama da 5 minute Zaid da Dr.Sadeeq suka ɗauka suna kallon juna, Zaid nayimawa Dr.Sadeeq kallon tsana, yayinda Dr.Sadeeq kuma kemawa Zaid kallon tuhuma, haɗe da son sanin koshi waye...


Kallon guard ɗin nan Zaid yayi haɗe da taɓe bakinsa cike da isa yanuna Dr.Sadeeq haɗi da cewa "Wan nan kuma waye?" yayi tambayar cike da rainin hankali, yana me ɗage kai sama bayan yajefawa Dr.Sadeeq wani irin kallo..


"Hmm ba buƙatar kasan koni ɗin waye, kai de zaifi kyau kasanardani ko kai waye, amma shishshigi baikamace kaba, saboda bakayi kama da me kula da lafiya ba, kafi kama da masu shiga inda ba'a buƙatarsu" Dr.Sadeeq yafaɗi haka shima yana me ɗauke kansa daga kan Zaid.


Murmushi Zaid yayi haɗe da kallon Dr.Sadeeq daga sama har ƙasa. Kansa kawai ya girgiza "Lallai bana buƙatar kowa, kasan yanda zakayi dasu" Zaid yafaɗi haka ga Guard ɗinsa, haɗe da juyawa yanufi ɗakin da aka kwantar da Zahrah, lokacinsa bana me aikin duba lafiya bane, lokacinsa muhimmine kuma sai me mahimmanci yake bawa...


Hasala Dr.Sadeeq yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarsa tana masa zafi, yana da sauƙi amma watarana abu kaɗan ke ɓata masa rai, a zuciye ya juya yafice daga cikin asibitin.. Su Inna dake tsaye a harabar asibitin suna ganinsa sukayo kansa da sauri suna tambayarsa ko Zahrah tana lafiya?


Kasa amsa musu yayi saima cewa da yayi, su shiga mota su yasauƙesu a gida... Bayanda suka iya haka suka shiga cikin motar jiki a sanyaye, saboda sunga gaba ɗaya fuskar Dr.Sadeeq ɗin ɓacin raine shumfuɗe akanta, kenan akwai abun dake faruwa.. Da wani irin gudu yaja motar suka fice daga haraban asibitin...


Gyara zama Baffa yayi haɗe da kallon Dr.Sadeeq wanda da'alama tunaninsa baya jikinsa.


"Meyake faruwa ne Likita? kashiga kakuma fito da ɓacin rai, ina Zahrah'n takene me yasameta?" cikin damuwa Baffa yayi tambayar domin shi gaba ɗaya kansa ya kulle.


Daure zuciyarsa yayi haɗe da cewa "Tana nan lafiya, gobe da safe zamu zo mu ɗauketa"


Ajiyar zuciya Baffa yasauƙe me ƙarfi yagodewa Allah da ba wani abun bane yasamu Zahrah, to amma ae da anbarsu sun ganta...


A ƙofar gida Dr.Sadeeq ya sauƙesu haɗe dayi musu saida safe yaja motarsa yayi gaba..


Suna shiga gida Inna ta kalli Baffa haɗe da cewa "Anya kuwa Malam bakaganin cewa akwai matsala?"


"Bawai gani nakeba, tabbas ma nasan akwai matsala Salame, sai dai fatana ɗaya shine Allah yatsare Zahrah, amma tunda Likita yace gobe da safe zamu koma asibitin, saimu jira zuwa goben idan Allah yakaimu"


"To Allah yakaimu" Inna tafaɗa jiki a sanyaye... Da "Ameen" kawai Baffa ya amsa.


Kamar yanda Zaid ya kwana a zaune, haka Dr.Sadeeq yakwana juyi, gaba ɗaya kansa ya kulle, yarasa meke faruwa, baisan waye wannan gayen ba, amma tabbas yaji tsanarsa fiye da misali, amma babban abun tambayar shine me yasamu Zahrah har aka kawota asibiti? sannan kuma meke tsakaninta da wannan mutumin? tambayar dayake buƙatar a amsa masa kenan, amma babu wanda zai amsa masa, tambayar da ta kuma hanasa bacci kenan...


Ƙarfe bakwai na safe Zaid yasa aka turo masa nurses guda biyu, suka zo dankula da Zahrah, saboda yana buƙatar yaje gida yayi wanka.....


Tamkar amafarki haka fyaɗen da yayi mata yasake dawowa cikin idanu da ƙwaƙwalwarta, wani irin nishi tayi haɗe da sakin ƙara mai sauti, lokaci guda kuma ta ware idanunta da suka cika tab da ƙwalla, da sauri nurses ɗin nan sukayo kanta.


Kallon Nurses ɗin tashiga yi, haɗe da soma ƙaremawa ɗakin da take ciki kallo, tabbas idan ƙwaƙwalwarta bata juye ba, zata iya cewa nan ɗakin asibiti ne sannan kuma waƴan nan dake tsaye a gabanta nurses ne.


"Barkanki da tashi, me kike buƙata yanzu a kawomiki?" ɗaya daga cikin nurses ɗin nan ta tambayi Zahrah cike da kulawa...


"Idanunta dasuke zubar da ruwan hawaye, ta ɗaga ta kalli nurse ɗin haɗe da girgiza kanta alamar batason komai.
Hanun nurse ɗin takamo duka biyu haɗe da fashewa da wani irin kuka me ciwo, da'alama wani abu takeson faɗawa nurse ɗin.. Dai dai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, Zaid ne yasha adonsa sai zuba ƙamshi yake.
Tsayawa yayi cak daga bakin ƙofar sakamakon ganin yanda Zahrah take kuka..


"Me kukayi mata?" yajefawa nurses ɗin tambaya cikin yanayi na rashin yarda dasu.


"Bamuyi mata komai ba,ranka ya daɗe tashinta kenan tasoma rusa kuka" su duka biyu suka haɗa baki wajen faɗan maganar...


Tamkar wanda aka zuba mata narkakken dalma haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login