Showing 27001 words to 30000 words out of 184930 words

Chapter 10 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt

09 Dec 2024

5705

uwa rabin jiki, My lovely Sister ZAHRAH (MOM PHADEEL) nagode sosai da kulawa Allah yabar ƙauna, kisani.inasonki sosai tawan, inakuma ji dake, kijima kiyi lasting..*


*Chapter 23 to 24*


A ƙalla Zaid yakai kusan 50 Minute a cikin bathtub ɗin wanka, a sannu sannu yasamu ciwon kannasa ya lafa, duk da cewa bai daina ji ba, amma bakamar ɗazu ba,,,a daddafe yayi wankan tsarki dana soso da sabulu, domin kuwa wata irin muguwar kasala yakeji ajikinsa,, sanye yafito daga shi, sai rigan wanka, wacce ta tsaya iyaka guiwarsa,, kallo ɗaya yayi murmushinsa yayi haɗe da sanya hanunsa ya shafi gefen kumatun ta, " Me daɗi na !! " yaƙira sunanta da wata irin murya , idanunsa ɗaya yakashe tamkar dai tana ganinsa, doguwar rigarta dake yashe a ƙasa, ya ɗakko yasanya mata ajikinta, duk dacewa gaba ɗaya doguwar rigar a kece take,, wayarsa yaɗauka haɗe da karawa akan kunnensa, mintuna kaɗan wanda yake ƙira ya amsa wayar, "kuzo ku maidata inda kuka ɗauko ta " Zaid yafaɗa a taƙaice, haɗi da datse ƙiran, har yakai bakin ƙofar fita daga ɗakin, saikuma ya tsaya cak, dawo da kallonsa yayi zuwa kan fuskar Zahrah,, murmushi yayi, haɗe da murɗa handle ɗin ƙofar yayi ficewarsa,, yana fita farfajiyar gidan, yashige motarsa ƙirar Venza haɗe da bata wuta yabar gidan... Mintuna ƙalilan da tafiyan Zaid, waƴannan mutanen da suka kawo Zahrah, suka kuma da wowa, kamar yanda yashigo da ita awuya, haka yanzuma ya ɗagata a wuyansa yayi waje da'ita, aransa yana matuƙar mamakin yanda jikinta yayi faca faca da jini, tamkar anyanka kaza....


9:50 pm... Dai dai suka ƙaraso cikin unguwar su Zahrah, sai da suka kawo daf da ƙofar gidansu, kafun suka tsaya, buɗe murfin motar sukayi, haɗe da tunkuɗo Zahrah da bata numfashi waje, take ta zube a wajen,, sukuwa banka mawa motarsu wuta sukayi suka ƙara gaba...


"Gaskia Malam nifa hankalina yasoma tashi, haba dan Allah, ace yarinya tun shaɗaya'n rana ta fita, amma har yanzu kusan goman dare bata dawo ba, gaskia duk inda Zahrah tashiga jikina yana bani ba lafiya take ba, domin kuwa sam ba ɗabi'ar Zahrah bace yin dare a waje! "


Ajiyar zuciya Baffa ya sauƙe, domin shima zuwa yanzu abun yafara da munsa, ace tun rana da ta fita haryanzu shiru babu labarinta,,


"Haba Malam kayi shiru, kamata yayi kaje makarantar tasu kaji ko lafiya, amma ka wani tsaya ƙiƙam "


"kinga dan Allah kada kici kani da bala'i, tun ɗazu kintsaya akaina sai faman ɓaɓatu kikeyi, ca nai miki bazanje makarantar tasu induba ba ko me ?, ni banson baƙar jarfa !!" Baffa yaƙare maganar cikin faɗa,,


Gum Inna tayi da bakinta,,domin tasan nasa masifar ta taka nata, inyafara bala'i, sai yakai har gobe bai gama ba...


Miƙewa Baffa yayi daga zaunen dayake haɗe da ficewa daga cikin gidan,,,, kasancewar gari yayi duhu, ga kuma matsalan wutan lantarki da ake fama dashi, kusan koda yaushe ba wuta, yanzun ma dai hakanne domin kuwa gaba ɗaya layinnasu dulum yake babu wani gida mai ɗauke da hasken lantarki,, har Baffa ya gota saikuma yaga tamkar wani ƙaton abune yashe a ƙasa, cike da ɗar ɗar yafito da ƴar ƙaramar wayarsa Nokia, ɗan madannin sama ya danna take hasken tocila (flashlight) ya bayyana,, haska tudun dayagani yayi, aikuwa mutum yagani yashe a ƙasa,, "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un !!" Baffa yafaɗa gabansa na dukan uku uku, sake matsowa yayi don tabbatar mawa idanunsa, mutum ɗinne ko kuwa, wani irin razana haɗe da faɗuwar gaba ne suka dirar mawa Baffa alokaci guda, sakamakon tozali da fuskar Zahrah da yayi, "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Allahumma ajirni fil masibati wa'aklifni kairan minha, subahan Allah !!,, Salame Salame !!!" Baffa yashiga kwaɗa ƙira, aikuwa dagudu Inna mai kunnen jiyau, ta bazamo ƙofar gida, domin dai dawuya kaima Inna ƙira ɗaya bata jiba...


"lafiya kuwa Malam kaketa zundumamin ƙira?, ai saika sa na.... Kasa ƙarasa maganar Inna tayi, domin kuwa idanunta ne suka sauƙa kan Zahrah dake kwance magashiyan a cikin turbuɗin ƙasa,, "ƙara Inna ta ƙwanɗara, haɗe da afkawa kan Zahrah tashiga jijjigata, "Zahrah ! Zahrah !! " Inna tashiga ƙiran sunan Zahrah, cike da firgici,,,, kuka sosai Inna tashiga rerawa tana mai ƙiran sunan Zahrah, amma ina Zahrah batasanma a duniyar da take ba,, Baffa ne yayi ƙarfin halin sa Inna ta cicciɓota sukayi cikin gida da'ita, gudun kada jama'a su taru akansu... Cike da tsoro Inna da Baffa ke kallon busheshshen jinin dake manne a ƙafofinta, "Nashiga uku Malam mai yasameta ne? kagafa taƙi buɗe idonta !" Inna tafaɗa cikin ruɗewa, " Ina zansani Salame ba dake muka tsintota a ƙofar gida ba, yanzu dai bana kawo ruwa ki zuba mata kozata farfaɗo "


Ruwa Baffa yakawo Inna tashiga zubawa Zahrah akan fuskarta, amma ina aiko alaman motsi Zahrah batayi ba,, " Mun shiga uku malam, kagafa haryanzu taƙi motsawa !" Inna takuma faɗa, cikin tsoro, "Banaje nataro mai taxi sai muje asibiti !!" Baffa yafaɗa cikin gaggawa domin yatsorita da al'amarin Zahrah'n....


Mintuna ƙalilan Baffa yadawo damai taxi, wata baƙar riga Inna tasanyama Zahrah, haka suka ɗebeta, aka sanyata acikin taxi kaitsaye suka wuce asibitin cikin gari.....


Mai taxi na fakawa Baffa ya arta a guje, yayi cikin asibitin, yanashiga yataradda wasu nurses suna zaune, bawani ɓata lokaci Baffa yasoma kora musu bayani akan cewa yazo da marar lafiya ne,, taɓe baki ɗaya daga cikin nurses ɗin tayi, haɗe da yi mawa Baffa kallon rainin hankali, cike da gadara tace " Bama karɓan marar lafiya sai anyanki kati " jiki na rawa Baffa yace " Kiyi haƙuri bansani bane, nawa ake yankan katin? kuma a ina ake yanka ?" bakinta takuma taɓewa haɗe da cewa " 1k ne sannan kuma acan wajen ake yanka " taƙare maganar tana maiyi masa nuni da wani waje,,


"menene kuma 1k yarnan ?" Baffa yatambaya,, cike da shaƙiyanci duka Nurses ɗin suka sanya masa dariya, "Hmm lallaima tsohonnan wato kai bakasan komai ba, amma kaɗauko marar lafiyanka kukazo asibitinnan, Hmm talaka baijira kansa ba, to abun da ake nufi da 1k shine dubu ɗaya " again nurse ɗin taƙara magana tana yatsine fuska... "To to to shikenan banaje na yanka " Baffa yafaɗa, cikin hanzari yanufi inda wannan nurse ɗin ta gwada masa, sosai Baffa yajima kafun yasamu ya yanki katin, saboda zalunci ma mai yanka katin dubu ɗaya da ɗari biyar takarɓa a wajensa, babu kuma yanda ya'iya haka yabayar, yana kawo katin yamiƙamawa nurse ɗin, yatsina fuska ta sakeyi haɗe da cewa aje katin a can, zuwa anjima maduba,,,


"Dan girman Allah ƴarnan kitaimakeni, wallahi ɗiyatace nakawo ko numfashi batayi, bansaniba ma ko tamutu kotana da rai !!" Baffa yafaɗa cike da tashin hankali, ganin suna neman aje katin daya basu,


"What ! bata numfashifa kace ? " su duka Nurses ɗin suka faɗa cikin ruɗewa, "ƙwarai kuwa " Baffa yabasu amsa... Ai da hanzari nurses ɗinnan sukayi waje, yayinda wasu sukatafi ɗauko wannan ɗan gadon da ake ɗaura mutanen da aka kawosu emergency akai,, akan wannan gadon aka ɗaura Zahrah da hanzari suke turata,don kaita abata taimakon gaggawa.... duk yanda suka so ceto rayuwarta abun yafi ƙarfinsu, ɗaya daga cikin Nurses ɗinne ta sharce gumin dake kan goshinta, ɗan nisawa tayi haɗe da kallon ƴan uwanta, cike da gajiya tace " gaskia inaga bazamu iya aikin nan ba, domin kuwa case ɗin fyaɗe ne, ba kuma hurumin mu bane, dole sai mundangana ga Doctor S.S domin wannan aikin sane " "Cab gaskia inajin tsoro mar'uda yanzufa time ɗin shin sane, kinaga yadace mukai masa wannan case ɗin ?, kuma ma idan yasan abun da muka aikata tun farko, wallahi bazamu share ba.." wacce ke tsaye gefen Mar'uda ta faɗa,, " gaskia saidai yayi haƙuri Aisha domin kuwa tabbas shiɗinne kaɗai zai iya kamo bakin zaren, banaje naƙirasa " Mar'uda nakaiwa nan a zancenta tafice daga cikin emergency room ɗin.....


Zaune yake akan tankamemiyar ƙujeran dake cikin haɗaɗɗen office ɗinsa, kyakkyawan matashin saurayine wanda aƙalla bazai wuce 30 years ba, sanye yake da riga da wando baƙaƙe, yayinda yaɗaura farin suit akai mai matuƙar kyaun gaske,, riƙe yake da wani file ahanunsa, yana dubawa yayinda yake shan coffee ahankali, da'alama abu mai mahimmanci yakeyi, farine shi amma basosai ba, sannan yana da ƙawataccen saje akan fuskarsa, yana da manyan idanu dakuma dogon hanci, wanda suka taimaka wajen bayyana kyawunsa, masha Allah shima dai kyakkyawane na nunawa sa'a....


Knocking ƙofar office ɗinnasa akashi ga yi, ajiye kofin coffee ɗin nasa yayi, haɗe da yamutsa fuska, cikin wata irin murya yace "yes, come in " Mar'uda ce taturo ƙofar tashigo, cike da girmamawa tace " sorry for disturbing you sir, we have an emergency patient"


" but i have closed for today, inama ƙoƙarin tafiya gidane " Doctor S.S yafaɗa cikin gajiyawa..


"Sir, the patient has been raped and she is unconscious !!"


" Suban Allah, fyaɗe fa kikace Mar'uda !!" Doctor S.S ya faɗa cikin kaɗuwa,, kai Mar'uda ta ƙaɗa alamar eh, miƙewa yayi cikin gaggawa yace " Muje "... Doctor S.S na gaba Mar'uda, nabiye dashi haka suka nufi emergency room ɗin,, yana shiga cikin Emergency room ɗin yaji ƙirjinsa ya buga, da sauri yaƙarisa kan Zahrah dake kwance tamkar gawa, take sauran Nurses ɗin nan suka shiga cikin taitayinsu, domin sun san Doctor S.S baya wasa, musamman ma idan akan irin wannan case ɗinne na fyaɗe... Taimakon gaggawa Doctor S.S yashiga bawa Zahrah, bayan yasanya Nurses sun haɗa masa kayan aiki, bakaɗan ba Doctor S.S ya tsorita, ganin irin taɓargazan da akayi mawa Zahrah a ƙasanta, domin sosai wanda yayi mata fyaɗen, ya ɓarkata,, "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un !!" kawai Doctor S.S kefaɗa acikin zuciyarsa, domin kuwa duk wanda yayi mata wannan abun yacika marar imani kuma marar tausayi, Doctor S.S nayi mata ɗinki amma zuciyarsa ƙuna da tafarfasa takeyi, "Haryaushene za'a ɗauki mataki akan banzayen mazajen da sukeyi mawa yara mata ƙanana fyaɗe ?, har yaushe za'adaina yi mawa mata fyaɗe ?, haryaushene wasu mazan zasu daina cin mutumcin mata tahanyar yi musu fyaɗe ?, ako da yaushe yana matuƙar jin ciwo acikin zuciyarsa, aduk sanda yaji cewa anyi mawa mace fyaɗe, tabbas da ace yana da wani babban iko, to da ya ɗauki tsattsauran mataki ga duk wani namiji da yayi mawa mace fƴaɗe" haka dai Doctor S.S yaɗinke Zahrah tsaf, bayan yagama ɗinketa ne, yayi mata treatment ɗin goshinta wanda yake a fashe, aƙalla dai Doctor S.S yakai kusan 1 hour yanayi mawa Zahrah teatment, allurai yayi mata kala biyu, saida yakammala yi mata komai kafun yafice daga cikin ɗakin bayan yabawa Nurses umarnin kaita ɗakin hutu, duk dacewa bata farfaɗo ba... "Suwaye suka kawota ?" Doctor S.S yatambayi Mar'uda fuskarsa babu alamar wasa,, inda su Baffa da Inna ke zaune Mar'uda tayi masa nuni,, cike da ɓacin rai Doctor S.S yanufi inda suke...


"Kunkuwa san mekukeyi ? taya zakubanzatar da ɗiyarku, har aimata mummunan fƴaɗe irin wannnan ?, ko kunsan wani irin haɗari ƴarku tashiga, a sanadiyar wannan fyaɗen da akayi mata ?, maiyasa iyaye kuke sakaci da rayuwar ƴaƴayenku mata ne?, shin bakusan cewa ranan gobe, Allah zai tambayeku game da amanarsu daya baku ba ? ".. Doctor S.S yajero musu tambayoyi cikin matsanancin ɓacin rai,, jikin Baffa da Inna ne yayi laƙwas, domin su sam basuma san cewa fƴaɗe akayimawa Zahrah'n ba sai yanzu, take Inna tasoma share ƙwalla hadda shashsheƙar majina,, wani irin kallon tsantsar takaici Doctor S.S yayi mawa su Baffa haɗe da cewa "Kubiyoni Office " yanakaiwa nan a zancensa yanufi hanyar office ɗinsa,, haka su Baffa suka rufa masa baya jiki ba ƙwari, domin kuwa dukansu sun kaɗu dajin cewa wai fyaɗe akayimawa Zahrah, to waye ? suka tambayi kansu... Zama yayi akan kujera gaba ɗaya jin zuciyarsa yake ba daɗi, wani irin masifaffen haushin iyayen yarinyar ma yakeji, da ƙyar ya iya daure zuciyarsa, yace "Ya akayi abun yafaru ?" gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa "Wallahi likita bansani ba, nidai natafi wajen sana'ata, dana dawo kuma sai bantarar da Zahrah a gida ba, shine kuma daga baya nataradda ita yashe a ƙofar gida !" Baffa yaƙare maganar yana matsan ƙwalla, laɓɓansa ya cije cike da takaici, domin gaba ɗaya abun ma yalura rashin kula ne yajawo, amma tun da shi ba ɗan sanda bane bai dace yatsare su da tambayoyi ba, " Yanzu dai maganar gaskia ƴarku tana cikin hatsari, tana matuƙar buƙatar taimako, wanda yayi mata fyaɗe yayi mata rauni sosai a gabanta, wanda yaja dole akayi mata ɗinki, amma ba'anan matsalar take ba, ba lallai ƴarku, ta farfaɗo yau ba, zata iyakaiwa gobe koma fiye da haka, sannan baizama lallai ta dawo cikin hayyacinta ba kodama ta farfaɗo ɗin, saboda ana yawan samun irin waƴannan matsalolin, dayawan mata idan aka musu fyaɗe yakan taɓa musu ƙwaƙwalwa, sai dai ako dayaushe fatanmu shine komai yazo da sauƙi ".... Bakaɗan ba hankalin su Baffa yatashi jin abun da Doctor ke cewa, ya ilahi wani irin iftila'i ne ya faɗo cikin rayuwarsu haka ????......


((Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru abubuwane sukaimin yawa, Zee black nagode da kulawa...))


*10/November/2019*


*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*Dedicated To My Brother Khabier....*


*🌈Kainuwa Writers Association*


*((United we stand ans succeed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers))*


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Chapter 25 to 26*


"Yanzu likita ya za ayi kenan ?" Baffa yatambaya fuskarsa ɗauke da damuwa, ajiyar zuciya Doctor S.S yasauƙe haɗe da cewa " asamu wanda zai kwana da'ita, kafun gobe Idan Allah yakaimu " yanaƙare zancen, yasoma tattare files ɗin dake baje kan table ɗin dake gabansa..


Tuƙi yakeyi amma gaba ɗaya jinsa yake wani iri, duk wata ƴar walwala da kuzarinsa sun ƙaura daga garesa, sosai fyaɗen da akamawa yarinyar yataɓa ransa, hakanan yakejin matsanancin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarsa,gaskia wasu mazan basu da imani, ka suma ƴar ƙaramar yarinya kamar wannan, ka danneta kakuma yi mata fyaɗe da ƙarfin tsiya, idan kai akamawa taka kuma bazakaji daɗi ba, ya Allah kasakama bayinka,... Horn biyu yayi kacal maigadi ya wangale masa tankamemen gate ɗin gidannasu, a parking space yayi parking motar tasa, haɗe da fitowa, kai tsaye ɓangarensa yanufa, domin yana da yaƙinin zuwa yanzu su Hajiyarsa sunshiga, ko yaje ɓangarensu bazai tadda suba,


"SADDIQ!!" wata ƴar dattijuwar mata dake tsaye a bayansa taƙira sunansa,, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Doctor S.S yayi haɗe da juyowa, ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi yayi ya aza akan fuskarsa, "Hajiya barka da dare" yafaɗa cike da girmamawa, "Yauwa barka dai, sai yanzu kake dawowa ?" sunkuyar dakansa ƙasa yayi haɗe da sanya hanunsa abayan kansa yashiga shafa ƙeyarsa, "Hmm da kyau, duk nasan mai yajawo hakan, rashin iyali ne, kuma wallahi komai yakusa zuwa ƙarshe, a wannan karon ko kana so ko baka so,yazama dole kafitar da mata ko kuwa, in zaɓa maka cikin ƴaƴan ƙannena, bazanci gaba da sanya maka idanu ƙato dakai ace baka da mata ba !!" Hajiya tafaɗa cikin faɗa, "Kiyi haƙuri Hajiya Insha Allah nan ba da jimawa ba komai zai dai dai ta"


"Koda yaushe haka kake cewa, inanan inasa ido, idan naji shiru kuma kasan sauran " Hajiya tafaɗa, juyawa tayi kaitsaye tanufi ɓangarenta, shima nasa ɓangaren yanufa, jinsa yake amatuƙar gajiye, wanka yayi haɗe da bin lafiyar gado ya kwanta, abu na farko daya fara ziyartan idanunsa bayan yarufesu, shine hoton fuskar Zahrah, sosai hoton fuskarta keyi masa gizo,acikin idanunsa, da sauri yabuɗe idanun na sa, a zuciyarsa yana mai mamakin faruwar hakan, dayaga abun bana ƙare bane, kawai saiya dangana hakan, dacewa tsananin tausayinta ne yajawo hakan......


ZAID kuwa yana barin Zahrah kai tsaye TRANSCORP HILTON yanufa, domin dai yauma yana da meeting a can... Bayan sunkammala meeting ɗinne, kai tsaye yawuce ɗakinsa dake ɓangaren V.I.P,, yanashiga yasoma rage kayan dake jikinsa, direct bathroom yashige yasakarmawa kansa shower,, wani irin sanyi da nishaɗi yakeji a cikin zuciyarsa, tun bayan abun daya shiga tsakaninsa da Zahrah, yakejin ransa yayi fari, nishaɗi kawai yakeji acikin zuciyarsa, gaskia yau yasha zallan madarar daɗi, domin kuwa sosai ɗanɗanon Zahrah yayi masa hundred percent, yanason mace mai ɗanɗano sosai... Yana fitowa daga wanka, wayarsa dake aje kan gado, tasoma ƙara haɗe da kawo haske, alamar shigowar ƙira, saida wayar tasa takusa katsewa kafun yaɗauki wayar haɗe da karawa akan kunnensa, "Shigo ciki" Zaid yafaɗa a taƙaice haɗe da cilla wayartasa kan gado,, Abid ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo,, rungumar juna sukayi, kamar yanda suka saba koda yaushe idan sun haɗu,,


"Daga ina haka ?" Zaid ya tambayi Abid, murmushi Abid yayi haɗe da zama akan hamshaƙiyar kujeran dake gefen gadon ɗakin, " yau nasha sweet abokina, wata babe nasamu mai zafi, inagayamaka tashayar dani zuma !!" Abid yafaɗa cike da nishaɗi,, Dariya sosai Zaid yayi hadda ƙyaƙyatawa, shiru kawai Abid yayi yatsaya yana kallon Zaid, domin dai Zaid baya dariya abanza, abune mai wuya kaga dariyansa, sai dai idan ya ƙulla wani abun... " Final !!" Zaid yafaɗa yanamai cije laɓɓansa,, zaro idanu Abid yayi cike da mamaki yace " what ! ? badai kanaso kacemin harka gama da Zahrah ba ??" ƙayataccen murmushi Zaid yayi haɗe da cewa "Tuntuni harma anwuce wajen " dariya Abid yayi haɗe da cewa " Har yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login