Showing 42001 words to 45000 words out of 184930 words

Chapter 15 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt

09 Dec 2024

5711

ɗin ya nufa, tundaga fitowarsa acikin motar zaka gane cewa a matuƙar buge yake domin kuwa sai haɗa hanya yake gakuma zungureriyar kwalbar giya dake riƙe a hanunsa, yana shiga cikin katafaren falonnasa, yafaɗa kan kujera, haɗe da lumshe idanunsa,
"MY ZAHRAH!!" yaƙira sunanta cikin wani sweetness voice ɗinsa, sannan kuma cikin yanayi mai nuni da cewa mutum yana cikin shauƙi,, da ƙyar ya iya miƙewa yakai kansa zuwa ɗaki, yanashiga cikin bedroom, kaitsaye ya wuce bathroom saida ya amayar da gaba ɗaya giyan da yasha, kafun yasamu nutsuwa, amma duk da haka mayen giyan bai sake sa ba.


Buɗe drowern sa yayi, haɗe da fiddo wani irin ƙaton hoto wanda gaba ɗayansa aka rufesa da glass ma'ana akayi masa gidan glass, ba hoton kowa bane face hoton kyakkyawar fuskar Zahrah tana murmushinta mai burgewa.


Murmushi yayi haɗe da mannawa hoton kiss, cikin unique voice ɗinsa yace "Inakewarki My Zumata, haƙiƙa keɗin ta da bance, verysoon inanan dawowa gareki, har yanzu sha'awarki bata sakeni ba, banƙoshi dake ba babyna, kikulamin da kanki kinji Sweet Zahrah na!!" yaƙare maganar cike da tsananin shauƙi, domin kuwa wani irin feelings yakeji a ga me da Zahrah'n, yarasa maiyake damunsa akan Zahrah, aƙa'idansa idan yayi sex da mace sau ɗaya, to baya sake waiwayanta harsai idan ita tawaiwayesa, nan ma saiyaga dama ya amsa tayinta, amma yau gashi yana mugun kewar Zahrah saboda yasha zumanta mai daɗin ɗanɗano, haryanzu baisan menene so ba, sha'awa kawai yasani akan haka kuma ya dogara.


Haka Bacci yaɗauki Zaid yanata sambatu irin na mashaya yayinda yake rungume da hoton Zahrah akan ƙirjinsa, yana ji tamkar Zahrah'nce dakanta ya runguma a ƙirjinsa.


Washe gari bashine yatashiba sai ƙarfe 9 na safe, salati yasoma yi cike da ƙuncin rai, sam baisan maiyasa yake makara sallan asuba a kwana biyunnan ba, ( Nace Saboda Zina bata haɗuwa da ibada ) daƙyar ya'iya tashi yashiga bathroom domin gaba ɗaya jiyake jikinsa na masa ciwo,gashi kuma baida time ɗin da zaiyi gym, wanka yayi cikin mintuna ƙalilan, fitowa yayi sanye da rigan wanka ajikinsa, agurguje yamurza lotion ajikinsa haɗe da sanya hand dryer ya busar da gashin kansa, wata baƙar jallabiya yasanya haɗe da nufar inda darduma ke shumfuɗe, yatada kabbaran sallah, ko kunya bayaji.


(Tir da hali irinnaka Zaid, sallah da rana faɗe faɗe Allah yashirya)


Yana idar da sallah, ya buɗe ma'adanan clothes ɗinsa haɗe da zaro wasu riga da wando masu matuƙar kyaun gaske, koda yasanya kayan sosai suka amshi jikinsa kasancewarsu masu kalar fari, daga takalmi, belt harzuwa agogon dake ɗaure a hanunsa kalar maroon garesu, haɗaɗɗiyar rigar suit maroon colour yaɗaura akan kayannasa, take yafito a asalin Zaid ɗinsa, wato Abundance, Increase, Increment, Superabundance, Addition, Excess, Surplus, haƙiƙa Zaid kyakkyawane kuma cikakken namiji da ya isa ɗaukar hankali ko wacce irin mace ce afaɗin duniyar nan, haƙiƙa Zaid yana da kyakkyawar sura irinta cikakkun maza, haka kuma yanada matuƙar burgewa abubuwan da Zaid kedasu naburgewa suna da tarin yawa, tamkar yanda ma'anar sunansa ke da tarin yawa, shikansa yasan yayi kyau sosai, babu kuma abunda ke tashi a jikinsa sai tashin ƙamshi mai sanya nutsuwa da kuma sanya shauƙi,


Al'adarsa ce kullum kafun yafita saiya bawa hotonta kyakkyawan sumba (kiss), to yauma hakance takasance domin wannan hoton nata yaɗauko, ya manna mawa kiss, haɗe da maidashi ya aje, kaitsaye yafice daga cikin ɗakin, ko sauraran kayan breakfast ɗin da aka aje masa akan derny table baiyi ba yasakai yafice daga cikin Aljannar duniyar falon nasa,, yana fita yashiga cikin motarsa, kai tsaye yawuce babban hotel ɗin dazasu gudanar da meeting, domin yau sunada gagarumin meeting, zuwa yanzu gaba ɗaya duk an hallara a wajen shikaɗai kawai ake jira, domin shida ma'aikatansa ne zasuyi meeting ɗin.


Nigeria


Yau kimanin sati guda kenan tunda Dr Sadeeq yazo baisake zuwaba, ɓangaren Zahrah kuwa sosai takesamun sauƙi acikin zuciyarta, sakamakon karatun Al'Qur'ani da tariƙe babu dare ba rana, zuwa yanzu ta dangana komai nata ga Allah, tasan ko ba daɗe ko ba jima zai bi mata haƙƙinta.


Zaune take a tsakar gidannasu tazuba uban tagumi, amma a zuciyarta karatu takeyi, Inna ce kishingiɗe a gefenta, tana koran sauron dasuka addabeta kasancewar dare yasoma rufawa domin kuwa har an idar da sallan magriba,,


Baffane yashigo cikin gidan fuskarsa ɗauke da fari'a, Inna ce kawai ta amsa masa sallaman da yayi, kallon Zahrah yayi haɗe da cewa "tashi ki ɗauko hijabinki likita na jiranki a waje"


Wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi, domin dudduniya a yanzu babu abun da zai ɗaga mata hankali kamar ace wai wani naƙiranta a waje, sam itakam tagama cire ƙauna da sake zuwa ƙiran wani, bata ƙaunarma koda sake fita waje ne,


"Wai ba magana nakeyimiki bane Zahrah kin shareni kuma bayan kinajina!" Baffa yafaɗa cikin faɗa faɗa,


Kuka Zahrah tafashe dashi haɗe da ɗago idanunta, ta kalli Baffa cikin muryan kuka tace "Baffa kataimakeni dan Allah, wallahi banso wani abu yasake faruwa da rayuwata !! "


"Ikon Allah, Malam kajita ko zata sake ɓarar mana da daman da muka samu na biyu, saikace akanta aka fara yin fyaɗe!" Inna tafaɗa cikin ɗaga murya,,


Da gudu Zahrah tajuya ta shige cikin ɗakinta haɗe da faɗawa kan gado tashiga rera kuka mai sauti, itakam batasan yanda zatayi da rayuwarta ba, batasan wasu irin iyaye bane Baffa da Inna, son zuciyarsu tayi yawa, kansu kawai suka sani, anya kuwa zasu rabauta da rahamar Allah ? cutar da maraya abune wanda ba kyau, kuma sunsani amma suke take saninsu, "Ya Allah kataimakeni !" tafaɗa cikin muryar kuka,


"Banni da'ita Salame nida itane, ai inbazata fita ba shi zaishigo cikin gidan " Baffa yaƙare maganar yana mai nufar ƙofar fita daga gidan.


Dr Sadeeq ne tsaye a jikin motarsa yasha sky blue ɗin shadda sai tashin ƙamshi yake,


Baffa yafito fuska a sake kai tsaye yanufeshi, "Yauwa likita ka'iso saikuyi maganar acikin gida ko, kasan mutumiyar taka sai a hankali" Baffa yafaɗa still washe da baki, like namesake ɗina (fatiwasha lol), ba musu Dr Sadeeq yarufa masa baya suka shiga cikin gidan.


Yauma dai a tsakar gidan yazauna duk da cewa babu yawancin haske a tsakar gidan amma akwai hasken farin wata.


"Wai Zahrah bazaki tashi kije bane, nacemiki gashi yashigo har cikin gida, dan Allah Zahrah kada ki watsamana ƙasa a ido, kidubi girman mutumcin dayayi miki sanda kike ciwon hauka kitashi kije " Inna tafaɗa cikin lallami.


"Ciwon Hauka kuma Inna?" Zahrah ta tambaya cike da mamaki domin dai ita a saninta batayi wani ciwon hauka ba,


"Ƙwarai kuwa kedai tashi kije kawai" Inna ta faɗa still cikin lallami, bawai don tasoba haka tasanya hijab haɗe da ficewa daga cikin ɗakin.


Tun fitowarta a cikin ɗakinnata ya kafeta da idanunsa, har taƙaraso can gefe dashi ta zauna, haɗe da takurewa waje ɗaya tana matsan ƙwalla,


"Saiyaushe zaki daina kuka ne?" Dr Sadeeq yatambaya cikin tattausar murya,


Shiru tayi bata amsa masa ba domin jin kalamansa take tamkar zuban narkakken dalma acikin kunnuwanta,


"Matsowa yayi gaf da ita, har tana iya jiyo ƙamshin turarensa, babu wani tsoro kokuma ɗar ya sanya hannayensa akan kumatunta yashiga share ma ta hawaye, sosai jikinta yaɗauki rawa domin tayi matuƙar tsorata da hakan,


"Banason kukanki Zahrah, nasani dole kina buƙatar ayi miki uzuri, kinajin ciwo da damuwa a cikin ranki, kuma kinada buƙatar kyakkyawan kulawa, kidaina min kallon wani bare kokuma na daban, kiyi mini kallon ɗan uwanki, wanda zaki iya gayawa damuwarki, inaso kifaɗamin duka damuwarki kinji ƙanwata, nasan zakiji sanyi idan kika faɗi ko kaɗanne daga cikin damuwarki !!" Dr Sadeeq yayi maganar cikin lallashi dakuma tausasawa,


Kuka takuma sanyawa mai sauti, domin kuwa tabbas abun daya faɗa ɗin hakanne, tana buƙatar mai kulawa da'ita, tana buƙatar ɗan uwa mai ɗaukar damuwarta, saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, sakamakon jin hannayensa da tayi akan nata,
Kai ya jinjina mata batare da yace da ita komaiba, yana kallonta tayi kuka harta ƙoshi, a hankali take sauƙe ajiyar zuciya, kofin ruwan dake gefensa ya ɗauka, haɗe da kawai bakinta, babu musu taɓuɗe baki ta soma sha, domin kuwa yanda zuciyarta ta bushe tana buƙatar ruwan,, saida tasha fiye da rabi kafun ta tsagaita da shan ruwan, sosai taji zuciyarta tasoma dawowa daidai nutsuwarta kuma yasoma sauƙa,,


"Yaushe zaki koma makaranta ?" Yajefomata tambayar kansa tsaye, kallon mamaki tabisa dashi, domin kuwa ko a wasan mafarki bata sake kawo sake zuwa makaranta acikin zuciyarta ba, itakam ai duk wani farinciki yawuce mata,


"Kada ki yarda da abun da zuciyarki takecewa, ba'akanki aka faraba, haƙiƙa abune mai ciwo amma idan kika daure zuciyarki, zaki iyayin rayuwar farinciki kamar kowa" Dr Sadeeq yafaɗa cike da son ƙarafafa mata guiwa,


"Kada kayi ƙoƙarin yaudarana domin kuwa sam banda wani sauran farinciki, yaruguzamin duk wani burina, to yanzu inaso kasanar dani shin menene amfanin karatuna bayan zuciyata cike take da ƙunci? kuma miye amfanin farincikina bayan rayuwata ke waye take da duhu ?, zanfaɗama damuwata domin nayarda dakai, inajin ciwo mai zafi a zuciyata bankuma san ranan warkewarsa ba, shin maiyasa zaka ce nayi farinciki bayan kasan cewa bazantaɓa samuba ?"


Ɗan gajeren murmushi yayi haɗe da matse hannayenta gam acikin nasa, "Saboda inada yaƙinin baki farinciki mai ɗorewa, amma saikin daina sakanki a damuwa "


Wani irin kallo tawatsa masa wanda yake nuni da cewa tana buƙatar ƙarin haske akan maganganun nasa.


"Zahrah ke yarinyace mai ɗauke da tarin ƙuruciya, kinaga yadace kibar rayuwarki tatafi a haka ?"


Dr Sadeeq yatambaya yana mai kafeta da idanu.


"Haka Allah yatsaramin, BAZAN BUTULCE BA, yadda da ƙaddara yana da kyau, NAYARDA DA ƘADDARA TA, saidai kuma bazan mantaba har abada, babu mai aurena, babu kuma mai tallafawa rayuwata, zanƙare rayuwata acikin ƙunci, idan har kaɗaukeni ƴar uwa kamar yadda kafaɗa, to inaso ka yi tunani shin wacce ta tsinci kanta acikin mummunar ƙaddara irin tawa akwai sauran farinciki da yarage mata?, ni yarinyace haryanzu bangama sanin rayuwaba, amma tabbas nasan mai kyau dakuma marar kyau, saboda haka rayuwata a gurɓace take, yariga daya ruguzata, bakuma zata taɓa kafuwa ta tsaya da ƙafafunta ba har abada, BANI DA ZAƁI likita amma akwai Allah ya isarmin komai!!" gaba ɗaya hawaye yagama wanke mata fuska, wannan karan ba iya zuciyarta bace tayi rauni hadda tashi zuciyar, lallai ƙaddaran Zahrah mummuna ce, amma kuma yazama dole yatsaya yakawar mata da duk wani duhu dake rayuwarta shi mai iya dawo mata da farincikin tane idan harzata amince, amma yasani Zahrah ta yanke ƙauna gaduk wani ɗa namiji,


"Likita ga abinci ko" Inna takatsemusu tunanin da sukeyi su dukansu.


Inna tana aje abincin tajuya tashige cikin ɗaki, kallonsa yamaida kan ɗan ƙaramin bakinta dake bushe, sannan yakuma maida kallonsa kan idanunta, a matsayinsa na mutum mai karantar yanayin ɗan adam, take yakaranci halin da take ciki, bayajin yunwa ko kaɗan domin saida yaci abinci kafun yafito, amma saboda dalili ɗaya yasa yajawo kwanon abincin gabansa, shinkaface ƴar gida jalof, ko mai batajiba ballantana albasa, amma haka ya share, yakai loman abincin cikin bakinsa, taunawar farko yaci karo da dutse amma haka dolensa ya basar (readers likitafa yagamu da girkin manya Inna, lol🤣).


"Zo muci" yafaɗa a taƙaice,


Saurin kallonsa tayi haɗe da girgiza kanta, domin ita yanzu abinci baya gabanta, damuwarta ma abincine a wajenta,,


Babu alamar wasa akan fuskarsa kaitsaye yanufi bakinta da hanunsa wanda yake ɗauke da ƙwayoyin shinkafa domin da hanu yakecin abincin,,


Saƙare haka tayi tanakallonsa domin wannan shine karo na farko a rayuwarta da wani ɗa Namiji ba muharraminta ba ya taɓa yunƙurin bata abinci a baki,


Kai tagirgiza masa alamar bataso haɗe da kawar da kanta gefe,


"Kinaso muyi faɗa kenan, kuma hakan nanufin baki ɗaukeni ɗan uwaba, nasan wunin yau bakisa komai a cikin kiba, sbd haka banason gardama, idan kuwa kikace bahaka ba, to akwai alluran da na taho da'ita, yanzu sainasa Baffa da Inna su riƙemin ke na yi miki har guda uku!! " yaƙare maganar in a serious tone, aikuwa ya faɗar mata da gaba domin kuwa tsoron alluran da takeyi haryazarce tunanin mutane, "Haaaa" Dr Sadeeq yafaɗa still yana kusanta hanunsa ga bakinta, tamkar dai za abawa ƙaramin yaro abinci.


"Basaikabani ba zan iya ci!" Zahrah tafaɗa cikin raunanniyar muryarta,


"To ci ingani" Shima yafaɗa yana mai turo mata kwanon abincin gabanta, ahankali ta sa hanu ta tsakuri abincin, tamkar wacce akace ta tsakuro garwashin wuta da hanunta, daƙyar ta iya buɗe baki ta kai loman abincin bakinta, murmushi yayi haɗe da sanya hanunsa acikin kwanon abincin yasoma ci, duk da cewa ba daɗin abincin yakejiba, adole Zahrah take kai loman abincin bakinta bayanda ta'iyane kawai,,


Lomanta huɗu ta soma kwarara amai a wajen tamkar zata amayar da ƴaƴan hanjinta, miƙewa tayi daga tsugunen da take domin tasoma ɓata jikinta da amai, aikuwa wani irin jiri ne ya ɗe beta take ta faɗa kan Dr Sadeeq dashima yake yunƙurin tashi tsaye,, gaba ɗaya yatarota tafaɗa cikin ƙirjinsa, yayinda aman dake jikinta ya gogu ajikin kayansa,,


Da sauri su Inna da Baffa suka ƙaraso wajen domin tundaga ɗaki sukejin ƙaran amannata, "Lafiya likita maiyasameta kuma ?" duka suka tambaya cikin ƙosawa, da'alama dai sungaji da lamuranta.


" Bakomai inaga olsa (ulcer) ce kawai ke damunta " Dr Sadeeq yafaɗa yana mai ƙoƙarin shimfiɗeta a akan tabarman da suke zaune,


Saidai gaba ɗaya ba ƙarfi a jikinta, saboda haka duk ta narkemasa a cikin jiki, yayinda shikuwa zuciyarsa ke tsananta bugawa, addu'a yake a zuciyarsa Allah yasa ba abun da yake zargi bane ke damun Zahrah idan kuwa abun da yake zargine tabbas babban tashin hankali na gaba...


(Wani tashin hankali munbanu readers 😲, Allah yasadai bacikine da ita ba, da Zaidu ya yi aiki mai tsada 🤣 )


*Breakfast na baku kuji daɗinku*



*23/November/2019*


*Voted, Comment, and Share please....follow me on Wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*


*🌈Kainuwa Writers Association*


{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*Chapter 38 to 39*


A hankali Doctor ya kwantar da ita, cikin sanyin jiki yanufi motarsa don ɗauko jakarsa ta aiki, domin dama daga office yake yabiyo tagidannasu,, Allah yasa ba abun dayake hasashe bane yake shirin faruwa, lallaiko idan har ya zamana Zahrah ciki ne da ita, to fa shikansama yashiga tashin hankali, bawai ita kawai ba, domin yasan ɗan guntun tsarin daya shirya rugujewa zaiyi, to ina kuma ga Zahrah wacce bata gama warkewa daga ciwon dake jikinta ba, kuma ace taƙara faɗawa cikin azabar wani ciwon, tabbas yasan tashin hankalin da zata shiga sai ya take wanda tashiga a baya,, jiki a saluɓe haka Dortor Sadeeq yadawo cikin gidan, zuwa lokacin har Inna ta ɗauketa takaita cikin ɗaki.


Tana kwance akan ƴar katifarta, sai faman sauƙe numfashi take a hankali, dagani kasan aman da tayi ya galabaitar da'ita sosai, zama yayi gaf da'ita, haɗe da kama hanunta, lokaci guda yaji jikinta yaɗau zafi sosai, kayan aikinsa dake cikin jakarsa ya ciro ya fara yi mata ƴan gwaje gwaje,


Wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe sakamakon gano abun dake damun Zahrah da yayi, duk da cewa baiyi mata gwajin ciki ba, amma a iya ɗan bincikensa da yayi ya gano cewa bata ɗauke da ciki, ulcer ce kawai tayi mata mummunan kamu, sakamakon yunwa daya samu mazauni acikin cikinta.


Kallonsa yamaida kan Baffa haɗe da cewa " Bawani babban damuwa bane ulcer ce, yanzu zanje na ɗauko wasu allurai a asibiti sainazo nayi mata, insha Allah komai zaiyi dai dai"


"To likita Allah yayi albarka muna godiya sosai !" Baffa yayi maganar cike da yabawa ƙoƙarin Dr Sadeeq.


Miƙewa Dr Sadeeq yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, yana fita su Inna ma suka mara masa baya.


Kwanciya tayi lamo tamkar wacce ruwa ya ƙare mawa a jiki, gaba ɗaya jinta takeyi bata da kuzari, gawani irin zafi da ƙuna da ƙirjinta keyi mata,,


Koda Dr Sadeeq ya ɗauko magunguna da Alluran da yakamata ace yayi mata, sai da ya biya ta wani katafaren wajen sai da kayan marmari yasaya mata dangin su apple da su inabi hadda abarba, bai tsaya anan ba hadda fresh milk saida yabiya ya saya, gudu yashiga sharawa akan titi, burinsa ɗaya shine yaje yabata taimako mai kyau, sosai yakejin tausayinta, saboda ta cancanci a tausaya mata, daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa idan yatuno da cewa ba ciki bane da'ita, sai yaji wani irin sanyi da nishaɗi na ratsa zuciyarsa, wanda ya alaƙanta hakan da cewa bayason tasamu ciki saboda zata sake shiga wani hali marar daɗi. (kuji shifa😏 wai hakane reaɗers?)


Mintuna ƙalilan ya iso ƙofar gidannasu.
Koda yanemi Inna da tayi masa iso zuwa ɗakin Zahrah'n, cewa tayi yashiga kai tsaye ai anzama ɗaya su yanzu ɗan uwa suka ɗaukeshi (hmm)


Yanda ya barta haka yataradda ita sai dai yanzu idanunta a lumshe suke, "Zahrah!!" yaƙira sunanta dai dai lokacin da yake ƙarasawa kusa da'ita.


A hankali ta buɗe idanunta tasauƙesu a kansa, ɗan guntun murmushi yayi mata, wanda yasanya gabanta mugun faɗuwa, domin kuwa murmushin nasa yatuna mata da murmushin Oga Babba (ZAIDU manyan maza, lol), take taji wani irin abu ya toshe mata maƙoshi, yayinda zuciyarta tayi ƙunci.


Aje ƙatuwar ledan dake hanunsa yayi, haɗe da zama akan katifarta ta, "Tashi ki zauna" yafaɗa yana mai kafeta da ido, kai kawai ta girgiza masa alamar bazata iya tashi ba, ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya ɗagota zaune, duk da cewa yana matuƙar jin shock idan yataɓa jikinta, amma babu yanda zaiyi dole hakan shine mafita.


Ledar daya shigo da'ita ya buɗe, haɗe da ɗauko apple guda ɗaya ya miƙa mata, kallonsa kawai tayi haɗe da kau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login