Showing 147001 words to 150000 words out of 184930 words
Chapter 50 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt
ɗauke da nutsuwa, bawai ita ta ƙirƙiri hakan saboda burgewa ba.
Buɗe murfin motar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama, lumshe idanunsa yayi haɗe da kamo hanunta yasanya acikin nasa hanun cike da nutsuwa yake murza ƴan yatsunta.
"Nayi missing wannan kyakkyawar matar, nayi missing wannan kyakkyawar fuskan, haka kuma nayi missing wannan daddaɗan jiki me laushin, nakumayi missing wannan tausassun laɓɓan masu daɗin sucking, kuma ma nayi missing wasu abubuwana wanda suke sani nishaɗi sosai suke kuma.." da sauri tasa hanu ta toshemasa baki haɗe da shagwaɓe masa fuska..
"Ni dai dan Allah kayi shiru!" tafaɗi haka a sangarce.
"Ni dai gaskiya naƙi wayon bazanyi shiru ba saina ƙarisa!" yafaɗi haka cikin yanayi na kwaikwayon maganarta.
Ɗan ɓata fuska tayi haɗe da sanya hanu ta shafi ɗakalallen cikinta.
"Yunwa nakeji sosai fa, rabona da abinci tun breakfast"
Ɗan waro kyawawan idanunsa dake ɗaukar hankalinta waje yayi.
"Meyasa kikeson barin kanki da yunwa ne? kinsan fa bazan yafe miki ba idan har kika cutarmin da unborn ɗina" yayi maganar yana me kafeta da idanunsa.
Zaro idanu Zahrah tayi haɗe da kai hanunta kan cikinta da sauri, ta shafa wai ko zataji tudu.
"Unborn fa kace? badai ajikina ba?" tayi tambayar cike da zaƙuwar jin amsarsa da alama taɗan tsorata da kalaman nasa.
"Yes Unborn ɗina dana sa miki daren jiya mana, banaso wani abu yasameshi seriously!"
Wani ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da jingina bayanta da jikin kujeran motar, gaba ɗaya ya faɗar mata da gaba.
"Ita da take tsananin tsoron haihuwa, tun yanzu yafara mata wani zancen unborn" tafaɗi haka acikin zuciyarta..
"Ya naga duk kin wani firgice ne haka, bakyason baby ne?" yatambayeta adai dai lokacin da yake tada motar.
"A'a" kawai tafaɗa murya a sanyaye. Baice da ita komaiba yaja motar suka fice daga cikin makarantar...
Direct wani hotel suka nufa don cin abinci, a cewarsa bazai iya haƙuri har sukoma gida batare da tasawa cikinta wani abuba.
Bata iya cin komai acikin hotel ɗin ba, sai pepper meat da kuma kunun aya kawai.. Koda suka koma gida tuni bacci ya cika idanunta, kwana biyunnan sosai take ebo gajiya amakaranta, da ta dawo kuma tayi wanka shikenan sai bacci. Yaukam basu dawo da wuri ba sai gab da magriba, saboda haka bata ba bacci... Wanka tayi da ruwan ɗumi take taji gajiyan yasauƙa daga jikinta..
"dogon wando na pencil jeans ta sanya ajikinta, sai kuma wata riga wacce tsayinta yakawo har gaba da guiwanta, gefe da gefen rigan atsage suke har wajen ciki, gaban rigar kuwa akwai aninaye masu kyau, rigace me kyau irin wacce ake ƙira da shirt gown (my favorite) sosai rigannan tayi mata kyau ajikinta yayinda hips ɗinta kuwa suka bayyana afili, kasan cewar rigar nada tsagu ta kowani ɓangare dama da hagu, batayi ƙoƙarin kame dogon gashinta ba, tazura lufaya haɗe da hawa kan sallaya ta gabatar da sallan magriba.
Tana idar da sallan ta miƙe haɗe da fita zuwa falo. Buɗe ƙofarta yayi daidai da shigowansa cikin falon, shima dawowarsa kenan daga masallaci.
"Waw!!! Kinyi matuƙar yin kyau sosai fiye da kullum" yafaɗi haka yana me ware mata duka hannayensa alamar tataho zuwa garesa..
Wani irin sanyin daɗi taji acikin zuciyarta lokacin da taji kalamansa, babu musu ta ƙarasa garesa haɗe faɗawa cikin ƙirjinsa.
Kansa yaɗaura akan wuyanta haɗe da sanya harshensa yasoma yawo dashi yana lashe fatar wuyanta. Hanunsa ya ɗaura adai dai kan hips ɗinta, cike da zolaya yace.
"Barin taɓa naji ko ciko akayi, anaso a yaudareni"
Dariya ne yakamata. Cewa tayi
"Allah ya sauwaƙe inyi cikon hips, taɓa da kyau kaji hips ɗina ne da Allah yaban bawai soso ba"
Shima dariya yayi haɗe da sake matseta acikin jikinsa.
"Nasani to ko kema kina ɗaya daga cikin mata masuyin cikon hips ɗin tunda ai naga mata sunayi sosai"
Da sauri ta ɗago ta kallesa lokaci guda ta ɓata fuska.
"Wato mata kake kallo sosai idan kafita ko? harkasan ana cikon hips, hmmm thank you" tafaɗi haka tana me ƙoƙarin zare jikinta daga nashi..
Da sauri yasake matseta ajikinsa haɗe da tausasa muryarsa.
"Tuba nake madam, amma nisam mata basa gabana, inadake mezanyi da wata kuma daban, ke kaɗai ce kinkuma isheni, amma kinsan ba abun mamaki bane dan nasan hakan, saboda yanzu hakan ya yawaita sosai, wasu mata basa haƙuri da surar da Allah yayi musu, dole wai sai sunyi ciko, inakaranta labarai, ina kuma gani a Instagram, amma kema kinsan baruwana da duk wata mace ina da me daɗina mezanyi da wata me ɗaci!" yafaɗi haka cike dason shagwaɓata.
Aikuwa take ta hau dariya sosai taji daɗin kalamansa, amma kalman me ɗacin nan yabata dariya sosai, ko wace macece me ɗaci oho.
(Please maza kuna faɗawa matayenku kalamai masu daɗi, koda ita ɗin bata da wani kyau, ka hure mata kunne kace ai ita kyakkyawace, wallahi zataji daɗi sosai, kai inda halima kadinga ƙiranta da sunan me daɗi🤣🙈wallahi yanzun sai gaka ranta yayi fari ƙal, kuma always zakaga tana cikin farinciki, wayyo wayaga anƙira su O'O da sunan me daɗi, ai nasan sai sunkusa sumewa saboda daɗi😂😂😂)
Zama sukayi akan kujera haɗe da jawota ya ɗaurata akan cinyarsa, kansa yacusa acikin ƙirjinta, bayan ya ɓalle aninayen dake jere agaban rigarta, sosai ƙamshin dake fitowa acikin ƙirjinta yake yi masa daɗi, yanason ƙamshinta, domin kuwa yana sa masa nutsuwa sosai.
Lumshe idanunta tayi, tana mejin daɗin kissing ɗinta da yakeyi a ƙirjinta, hanunta ta sanya acikin gashin kansa tana yamutsawa a hankali. Ƙaran wayarsane yakaraɗe musu kunnuwansu, akasalance Dr.Sadeeq ya jawo wayartasa batare daya duba wanda ke ƙirannasa ba ya kara wayar akan kunnensa. Waro manyan manyan idanunsa waje yayi haɗe da cewa
"Dagaske kake?"
Banji me wanda yaƙirasa a wayar ya faɗa masa ba saiji nayi kawai yace
"Okay ganinan fitowa."
Kallonsa Zahrah tayi, tanameson jin ƙarin bayani daga bakinsa.
"Lumshe mata idanunsa yayi haɗe da ɓuɗesu alokaci guda.
"Friends ɗinane sukamin surprise wai suna waje, banaje na shigo dasu, please mintina kisanja wannan kayan kinji, ina kishinki sosai banason kowa yakallemin ke!" yaƙare maganar yana wani lumshe idanu, domin kuwa cike yake da shauƙinta.
Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da tashi daga kan cinyarsa tana cewa.
"Yanzu kuwa zan sanja kayan."
Ɗaki ta wuce shikuma yayi waje don shigo da abokansa.
Zama tayi akan gado bayan ta sanja shigarta zuwa riga da sket na material marar nauyi takuma yane jikinta da mayafi, tanajin hayaniyansu acikin falon.
"Maza kenan wai nan su fa taɗi suke, amma kuma yawancin zancen nasu kama yake da musu" tafaɗi haka acikin zuciyarta. Bata ida zancen zucin da take ba, Dr.Sadeeq ya shigo cikin ɗakin.
Hanunta yakamo haɗe da kai mata sumbata a goshinta.
"Ko wani irin kaya kika sanya sai sunyi miki kyau, kyau ajininki yake ƴan mata na!" yafaɗi haka yana me ƙare mata kallo.
"Ƴan mata kuma?" ta tambayeshi tana ɗan murmushi.
"Eh mana ƴan matace ke a wajena ae har gobe, kuma ke sabuwace a wajena, tunda har yanzu bangama lashe zuma na ba" yafaɗi haka yana me kashe mata idanunsa ɗaya.
Kunyansane ya kamata, amma babu yanda ta iya shidai duk irin kalamansa kenan.
"Ki kawowa baƙinmu drinks kinji"
"To" Kawai tacemai.
A tare suka fita ita tayi hanyar kitchine shikuma yayi cikin falon..
Hanunta ɗauke da wani ɗan madaidaicin trey wanda ke ɗauke da kayan drinks da kuma ƴan madaidaitan glass cups tafito daga cikin kitchine ɗin, kanta aƙasa tanufo cikin falon saida takawo cikin falon kafun ta ɗago kanta fuskarta ɗauke da ɗan murmushi, wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, lokaci guda idanunsu ya sauƙa acikin na juna, take ta saki trey ɗin dake hanunta yafaɗi ƙasa, ƙaran faɗuwarsa yajawo hankalin gaba ɗaya waƴanda suke cikin falon......
*(😳Waye Zahrah tagani🙆♀ badai Zaid bane yabiyota har cikin gida? kai ina ai Dr.Sadeeq yasan Zaid bazai barshi yashigomasa cikin gida ba, to waye ne wai??? 😂 kutaimaka kufaɗamin waye, bazan iya jiran next page ba😂😂)*
*(Kuyi haƙuri dan Allah jiya banyi muku update ba🙏🏻)*
*Vote and Comment please my lovely fans🙏🏻*
*4/February/2020*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 106*
Da sauri Dr.Sadeeq yataso ya taho gareta, durƙusawa yayi yashiga tayata tattare wajen, saboda har wasu daga cikin cups ɗin dake kan tray ɗin sun face. Bisa tsautsayi ta zo ɗaukan wani fasashshen cup kwalba ya caketa a ƴar yatsar hanunta, take ta saki wani ɗan ƙaramin ƙara, cike da kulawa Dr.Sadeeq yace.
"I'am sorry kibi a hankali, muga hanun yayi jini ne?" yaƙare maganar yana me kama hanunta wanda kwalban yasoketa.
Murmushin ƙarfin hali tayi haɗe da cewa
"Yayi jini amma baso sai ba" hanunta Dr.Sadeeq yakama yashiga hura mata iskan bakinsa ahankali, yama manta da cewa basu kaɗai bane a cikin falon.
"Sannu amaryarmu, munsa kin yanke da ƙwalba ko, i'am really sorry" wani daga cikin abokan Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana ɗan murmushi.
Murmushi itama ta ƙaƙalo haɗe
da girgiza kanta, alamar
"bakomai"
"Tashi ki gaishesu sama sama ae duk sune silar jin ciwonki" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me miƙar da ita tsaye.
Ɗan matsawa tayi wajen da suke zaune tashiga gaidasu cikin sassanyar murya, amma bata yarda ta kalli inda yake ba, shima kallo ɗaya yayi mata ya sadda kansa ƙasa, "Itaɗince dai duk da taƙara kyau hakan baihanasa ganeta ba" yafaɗi haka acikin zuciyarsa, zuciyarsa ne ke ingizasa daya ɗaga idanunsa ya kalleta, amma kuma yaƙi bin umarnin zuciyartasa saboda yasan hakan baidace ba.
Dr.Sadeeq dakansa yakawo musu wani drinks ɗin ita kuwa ta wuce ɗakinta..
Zama tayi akan gado haɗe da sauƙe wata irin ajiyar zuciya me ƙarfi, bazata taɓa manta wannan fuskarba, tabbas shine.
"To meya kawo JABEER gidanta kuma? kodai shima abokin doctor ɗin ne?"
tayi mawa kanta duka wa ƴannan tambayoyin, ganin da tayi cewa tunani bazai fishsheta bane, yasa ta miƙe ta ɗauko ɗan ƙaramin Al'Qur'ani'n ta tashiga karantawa a hankali...
Yanashigowa cikin ɗakin yajingina bayansa da jikin ƙofa haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.
Kallonsa tayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
"Yadai sai kace wanda yayi gudu?"
"laifine idan nayi gudu dan nazo naga matata?" shima yatambayeta yana me tsareta da idanunsa.
"A'a, amma ae abun bana gudu bane, tunda dai batashi sama zanyi ba inanan tare dakai" tafaɗi haka tana me gyara zamanta.
Takowa yayi yaƙaraso gareta, zama yayi gab da ita haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta.
"Ya hanun naki?" yatambaya yana me ƙoƙarin kamo hanun nata wanda taji ciwo dan ya duba.
"Da sauƙi bayama min zafi sosai"
Iskan bakinsa ya hura ahanun kafun yaɗago ya kalleta.
"Amma nayi mamaki ƙwarai da abun daya faru ɗazu, ko dai tuntuɓe kikaji ne?"
Da sauri ta shiga kaɗa kanta. "Bankula da gabana bane alokacin danake tafiya shine kawai na buge da kujera" batasan sanda ta mulmulo wannan ƙaryan ta rantaɓa masa ba.
Kansa ya jinjina haɗe da sanya hanunsa ya rungumota zuwa jikinsa.
"Nagodewa Allah ma dayasa bakece da kanki kika faɗi ba, tray ne kawai ya faɗi, da bansan inda zansa kaina ba" yafaɗi haka yana me shafa gashin kanta da hanunsa.
Ɗan shirune yashiga tsakaninsu kowannensu da abunda yake saƙawa acikin ransa, tabbas bazata iya haƙura ba sai ta tambayeshi waye Jabeer agareshi, to amma tace masa me? tace masa me ya haɗasa da Jabeer tsohon saurayinta ko kuma me? bari dai tayi masa wani wayon, tafaɗi haka acikin ranta...
Ɗan sake gyara zamanta tayi haɗe da cewa. "Amm wai duka waƴannan abokanka ne?"
Murmushi yayi batare daya ɗago ya kalleta ba yace "Eh"
Kanta ta jinjina haɗe da sake cewa "Dukansu fa nake nufi"
Murmushi yakumayi saidai a wannan karon ya ɗago idanunsa ya kalleta.
"Eh dukansu abokaina ne, meya faru?" yatambayeta yana me tsareta da idanunsa..
Murmushi ta ƙaƙalo haɗe da cewa
"Babu ko mai kawai dai naga sunyi yawa ne, kuma naga wasu daga cikinsu banga fuskokinsu a wajen bikinmu ba shiyasa"
"Ae mu maza ba irinku bane munfiku yawan jama'a, wasu daga cikinsu basu samu daman zuwa bikinmu ba shiyasa bakisansu ba, kamar Jabeer baisamu halattaba saboda baya Nigeria yana Polland yana karatu, kuma baijima da dawowa ba, sauran kuma wani uzururruka ne suka hanasu zuwa, kinsan maza da sabgogi" yafaɗi haka yana me sake kwanciya acikin jikinta.
Yanzu tasamu amsar da takesonji cikin sauƙi, kenan dama Jabeer baya Nigeria ne shiyasa bainemeta ba, da sauri ta yi watsi da tunaninsa haɗe da ƙoƙarin zame Jikinta daga cikin nasa jikin.
Ƙara rungumeta yayi batare daya bata daman tashi ba, kallon cikin ƙwayar idanun juna suka shigayi, kallon tsananin SO Dr.Sadeeq keyi mata, yayinda ita kuma nakasa fassara wani irin kallo takeyi masa, na ƙauna nane ko na SO oho, Lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu alokaci guda, yanayin yanda taga idanun nasa sun mareraice shiyasanya taji tsikar jikinta ya tashi, aduk sanda ta kalli cikin idanunsa takanji wani abu na ratsa har cikin ɓargonta, hakanne ma yasa bata ɗaukan lokaci me tsawo tana iya kallon cikin idanunsa, sosai idanunsa keyi mata kyau.
"Baby bacci nakeji!"
yafaɗi haka cikin murya me sanyi, yana me sake lumshe idanunsa.
"Ɓacci a wannan lokacin? Yanzu fa lokacin sallan isha ne"
ta faɗi haka cike da mamakinsa, tasan dai shiba mutum ne dayake da saurin bacci ba.
Hanu yasa yaɗan murza idanunsa, kansa kawai ya kaɗa mata batare dayace da ita komaiba yakoma jikinta ya kwanta. Yana lumshe idanunsa ladanin masallacin kusa da gidansu yasoma kwaɗa ƙiran sallah'n Isha. Jiki babu ƙwari haka yayi alwala yawuce masallaci..
Koda ta idar da sallah batayi yunƙurin tashi akan sallayan ba, zama tayi tana me rero karatun Al'Qur'ani ahankali.
Yana shigowa ta rufe Al'Qur'ani'n domin dama takai ƙarshen suran da take karantawa.
Direct bathroom ya wuce, tanajin ƙaran ruwa tasan wanka ƴakeyi.. Bawani jimawa sosai yafito daga shi sai towel ɗaure aƙugunsa, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauƙe kanta, har yau bata iya jure ganinsa a haka, tashi itama tayi ta wuce bathroom ɗin donyin wanka.
Dogon wandon jeans kawai ya sanya ajikinsa haɗe da feshe jikinsa da turarensa me daɗin ƙamshi.. Kwanciya yayi lamo agadon haɗe da lumshe kyawawan idanunsa.
daga ita sai wani ɗanƙaramin towel tafito ɗaure ajikinta, yanzu kam bata wani jin kunyarsa sosai, tana iya fitowa gabansa a haka, sai dai idan taga ya kafeta da idanu, sai taji gaba ɗaya tayi wani irin da ita. Kallonta yayi yakuma sake lumshe idanunsa, yayi imani idan yaci gaba da kallon wannan haɗaɗɗiyar surar tata zata iya zautar dashi.
Turare kawai ta shafa ajikinta, ko sleeping dress batasanya ba, yau kuma da towel takeson kwana, kashe musu wutan ɗakin tayi ta kunna musu na bacci, wanda bashida haske sosai.
A maimakon tanufi gefensa ta kwanta, sai ji yayi ta haye kansa.
"Wayyo mama lutiya zata karyani!" yafaɗi haka aɗan shagwaɓe.
Sake sakar masa duka nauyinta tayi akansa, haɗe da cusa kanta cikin wuyansa.
"Kai nauyinka baisa na karye ba sai nine zan karyaka, ko kamanta kafini nauyi" taƙare maganar tana me manna masa wani irin hot kiss akan wuyansa.
Lumshe idanunsa yayi sosai yaji kiss ɗinnata ya ratsa shi.
"Wai yaushe kika zama haka ne princess?" yatambayeta, don harga Allah kwana biyun nan yana mamakinta.
Cikin rashin fahimtar maganan nasa tace "Bangane ba"
"Naga ne kindaina jin kunyana, sannan kuma nima da nake da kunyan nema kike ki lalatani ki maidani marar kunya"
Cizo takaimasa akan ƙirjinsa, wanda yasanya sa sakin wata ƴar ƙara.
Yana dariya yace
"To ƙarya nayi ai gaskiya nafaɗa, yanzu bakyajin kunyana ko kaɗan, har kaya kike cirewa a gabana..."
Wani cizon takuma kaimasa batare da ta bari yaƙarisa abunda yakeson faɗa ba, da sauri yatureta takoma ƙasansa shikuma yazama yana samanta, yayi mata rumfa da kirjinsa, duka hannayenta yakama yariƙe acikin nasa.
Cikin dariya ta soma ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikinsa don talura cizon da tamai yakeson rama wa.
"Dan Allah kayi haƙuri bazan ƙaraɓa!" tafaɗi haka aɗan tsorace dan ta lura dagaske cizonta zaiyi.
"Ae babu maganar haƙuri yarinya, aƙirji kika cijeni, nima kuma dan haka aƙirjinki zan cijeki" yafaɗi haka yana me warware towel ɗin dake jikinta.
Cikin dariyan data kasa hanashi fitowa tashiga yi masa magiya amma yace sam shi sai ya rama.
Yana ɗaura bakinsa akan ƙirjinta, tayi shiru lokaci guda ta shiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, harwani lumshe idanunta take tsabar daɗin abun da yakeyi mata da takeji, shikuwa dagangan yayi mata haka so yake ya tsokalota sai yayi mata wayo yayi baccinsa, hanunta tasanya ta ɗago kansa, wani irin kallon tayi masa wanda ya rikirkitasa, bakinsu ta haɗe waje ɗaya, atare suka soma sucking lips ɗin juna, shida yake shirin mata wayo sai gashi ya susuce alokaci ɗaya, har yazo yafita ɓuƙata..... Bargo yaja ya rufe musu duka jikinsu, yana kwance akanta bacci me daɗi ya ɗaukesu.....
*****
*_ZAID_*
Tunda aka sallamosu daga asibiti baice da kowa ƙala ba, haushin kowa yakeji, tuƙuƙin baƙin ciki zuciyarsa keyi masa, ji yake yatsani kowa, bayamaso wani yashigo cikin lamarinsa..
Zaune yake a cikin falonsa, dagashi