Showing 30001 words to 33000 words out of 184930 words

Chapter 11 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt

09 Dec 2024

5701

bansan kai wani irin mutum bane Zaid, idan kaso abu, to ko ta wani hali sai ka sameshi, Allah sarki, Innocent girl, tanacan tana fama, nasan kabata kaya da yawa, may be ma haryanzu bata san awace duniya take ba " Abid yafaɗa... Still murmushi Zaid yayi haɗe da gyara zamansa, wayarsa yajawo yashiga latsawa, amma fuskarsa ɗauke take da murmushi... Ganin haka yasa Abid sha re maganar domin yafahimci me abokinnasa yake nufi,, Jefi jefi suke hira da Abid.....


Washe gari... Har 9:00 am Zahrah bata farfaɗo ba, Doctor S.S yazo yasake dubata, yakumayi mata duk wani abu daya kamata, amma still ko motsawa batayi ba... Abu kamar wasa tun anasa ran farfaɗowar Zahrah har dai akasoma cire rai, domin kuwa yau kwananta biyu batasan inda take ba... Sosai Doctor Saddiq yake bawa Zahrah kulawa, kuma yau yake da yaƙinin farfaɗowarta insha Allah...


Ƙafantane yafara motsawa, sannu a hankali idanunta suka soma ɗan buɗewa, ƙwaƙwalwarta ne tashiga tariyo mata duk wani abu daya faru da'ita, wani irin ƙara Zahrah tasanya wanda yayi matuƙar firgita su Baffa da Inna dake zaune gefe da gadon da take kwance,, "Subahanallahi !!" Baffa ya faɗa cike da tashin hankali,,, ihu kawai Zahrah ke yi haɗe da fisge fisge, tamkar dai mahaukaciya,, Dagudu Baffa yayi waje don ƙiran likita,, duk yanda Inna taso riƙe Zahrah abun yagagara domin kuwa duk ta fusge ƙarin ruwan da akayi mata, cikin hanzari Doctor Saddiq yaƙaraso cikin ɗakin, cak yatsaya ganin yanda Zahrah ke ihu tana ta fusge fusge, wani irin mugun tausayinta yaji ya daki zuciyarsa,, tattaro duk wani kuzarin sa yayi yaƙarasa gareta, wani irin fusga Zahrah tayi, ai kuwa saiga Inna dake riƙe da ita, tafaɗi ƙasa warwas,, da hanzari ya kama hannayenta duka biyu, yana mai ƙoƙarin nutsar da ita, wani ihun takumayi wanda sautinsa ya zagaye kowani kusurwa na ɗakin, fuskar Zaid kawai take hangowa akan ta Dr Saddiq,


"Wayyo Allah na, Baffa kataimakeni zai kasheni, zai kasheni, wayyo !!!" abun da Zahrah take ta faɗa kenan cikin hargowa da son ƙwace kanta daga wajen Doctor Saddiq,, duk yanda Dr Saddiq yaso tayi shiru abun yacitura, domin da alama bata cikin hayyacinta,, wani irin cizo Zahrah ta gantsara masa ahannu, sosai yaji zafin cizon amma yasan tabbas yana saketa, guduwa zatayi, ko kuma ma tayimawa kanta rauni,, wani irin ƙara ta callara tana mai shirin turesa ta gudu, yayi saurin rungumeta ƙam acikin ƙirjinsa, wasu lafiyayyun cizo Zahrah tashiga gantsara masa akan ƙirjinsa, sake rungumeta yayi ƙaƙam acikin jikinsa, haɗe da rumtse idanunsa, yakuma datse lips ɗinsa da haƙoransa,, sosai yakejin zafi har cikin ƙwaƙwalwarsa, domin kuwa da iya ƙarfinta take cizon sa,, ganin cizo bazai wadatar ba yasanyata sanya hannayenta, duka biyu ta shiga dukansa tako ina,, tabbas duk wanda yaga abun da Zahrah takeyi yasan cewa bata cikin hayyacinta,, da ƙyar Dr Saddiq ya'iya danneta yayi mata wata allura wacce take kashe jiki, ta kuma gusar da ƙarfin jikin ɗan adam,, take tayi laƙwas haɗe da sulalewa daga jikinsa tafaɗa kan gado, kallonta yashiga yi gaba ɗaya tayi buji buji da tulin gashin kanta, gashi duk taɓalle maɓallan gaban rigarta, wanda hakan yabayyana kyakkyawar surar ƙirjinta,, saurin ɗauke idanunsa yayi daga kan ƙirjin nata, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, juyo da kallonsa yayi zuwaga kan su Baffa da suke tsaye cirko cirko, gaba ɗaya sunyi wani tsuru tsuru dasu, tamkar ace musu as su antaya a guje, bama kamar Inna,,


Kansa kawai ya jijjiga batare da yacemusu komai ba, yayi ficewarsa daga cikin ɗakin,, direct office ɗinsa ya nufa, da kansa ya haɗa tea mai kauri, kaitsaye ɗaki na musamman ɗin daya sa aka kai Zahrah yanufa, riƙe da kofin tea ɗin a hanunsa, baitaradda su Baffa a cikin ɗakin ba, don haka kansa tsaye yanufi gaban gadon nata,, kwance take flat daganinta kasan babu wani wadataccen ƙarfi ajikinta, saidai hawayene kawai ke ambaliya yana gangarowa ta gefen idanunta,,, "Zahrah" yaƙira sunanta, duk da yasancewa bazata taɓa amsa masa ba, saboda batacikin nutsuwarta...


Aje ƙofin tea ɗin dake hanunnasa yayi, haɗe da ɗaukar pillow yasanya a bayanta, da ƙyar yasamu ya iya jinginar da ita ajikin pillow'n, a hankali yake ɗiban tea ɗin cikin tea spoon yanakaiwa bakinta, duk yanda yaso ta buɗe baki tasha tea ɗin hakan yagagara, domin daya sanya mata ruwan tea ɗin acikin bakinta, zaidawo waje,, aje kofin yayi haɗe da harɗe duka hannuwansa akan ƙirjinsa, kallon fuskarta yashiga yi natsawon wasu mintuna, ajiyar zuciya ya sauƙe alokaci guda, haɗe da ɗaukar kofin tea ɗin yafice daga cikin ɗakin,, umarni yabawa wata nurses da tayi mawa Zahrah alluran bacci, domin duk yafahimci irin situation ɗin da take ciki a yanzun...


Gaba ɗaya ihun Zahrah ya karaɗe ɗakin, hankalinsu Inna gaba ɗaya atashe yake, kamar yanda tayi ɗazun, yanzuma haka takeyi, domin ihu da fusge fusge kawai take saidai yanzu, cewa take "Kutaimakeni, zai kasheni, wayyo Allah na, kutaimakeni !!!" abun da Zahrah take faɗa kenan cikin hargowa, da wani irin hanzari ta diro daga kan gadon, da take kwance, kaitsaye bakin ƙofa tanufa da gudun gaske, da sauri Baffa yasha gabanta, wani irin ƙara ta sanya, domin kuwa Zaid tagani tsaye a gabanta, amaimakon Baffa, wani irin ƙarfine yazomata aikuwa kyakkyawan hankaɗa tayimawa Baffa, saigashi jagwaf a ƙasa, dama bawani kuzari gareshi ba,, gaba ɗaya tayi buji buji da jikinta, ta tarwatsa gashin kanta, gudu kawai Zahrah take tsakaninta da Allah, daga zangar ta haɗu da mutane sai tasanya ihu, domin kowaye zatayi tozali dashi to fuskar Zaid take gani, akan tasa, hartakai bakin ƙofar fita daga cikin asibitin, cikin zafin nama ya cafko hanunta, wani irin ihu Zahrah tashiga kurmawa, tamkar wacce ake yankan naman jikinta, tun fitowarta mutane ke kallonta, atunaninsu mahaukaciya ce,, bai damu da ihun da takeyi ba, duka hannayen ta yahaɗe waje ɗaya, caɗak ya ɗagata haɗe da saɓata kan kafaɗarsa, yayi cikin asibitin da'ita,, wani irin ƙara tayi, take kuma jikinta ya sake numfashinta gaba ɗaya ya ɗauke,
Duk inda suka wuce sai ankallesu, wasu suna matuƙar tausayinta, da ƙuruciyarta amma hauka ta risketa, anasu zaton mahaukaciya ce..


A kan gado ya shimfuɗeta, haɗe da rufamata bargo, wasu allurai yayi mata, bayan yasanya mata drip ɗin dazai taimaka wajen bawa jikinta kuzari, koda bataci abinci ba....


"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, ya Allah kataimaketa, haƙiƙa tanacikin mawuyacin hali, ya Allah kasa kada abun danake zargi yatabbata, Allah katsaremata ƙwaƙwalwarta, da kariyarka !!" Dr Saddiq yafaɗa cikin karyewar zuciya, haɗe da tsananin tausayin Zahrah,, sau da dama akanyi mawa yara ƙanana fyaɗe, firgici da tsoron da suke samun kansu ciki, yakan taɓa musu ƙwaƙwalwa, sai aga kamar sun zare, hakan yasa basa da wowa hayyacinsu cikin sauƙi,, a wannan rana dai Dr Saddiq da ƙyar ya iya barin asibitin, gaba ɗaya lamarin Zahrah ƴatsaya masa arai, tausayinta yakeji sosai....


Tsaf yagama shirya kansa cikin wasu mayun riga da wando, masu kyau da tsadar gaske, bakaɗan ba yayi kyau sai tashin daddaɗan ƙamshi jikinsa yake, SHU'UMIN NAMIJI kenan ganinka babu alkhari acikinsa, ƴar ƙaramar trolly bag ɗinsa ya shiga ja, bayan yaɗauki wayoyinsa da kuma duk wani abu dayasan zai buƙata,, wannan karan ko ɓangaren mahaifiyarsa bai jeba, motarsa ƙirar BUGATI yashige, yayin da driver yabamawa motar wuta, kaitsaye airport suka nufa, domin dai alƙawari Zaid yaɗauka yau bazai kwana acikin Nigeria ba, yawon shaƙatawa zai tafi New York City (America).. Yana shiga cikin jirgin baiwani jimaba, jirginnasu yaɗaga zuwa sararin samaniya.....


*((kuyi haƙuri page ɗin yau baida yawa...))*


*12/November/2019*
_________________________


*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written By*
phatymasardauna


*Dedicated To My Loveƙy Brother Khabier...*


*🌈Kainuwa Writers Association*


'''{United we stand and succeed our ambition is to intertain & motivate the mind of readers}'''
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*Wannan Page ɗin gabaki ɗayansa kyautane a gareku.*

*UMMIEE-ZARIA.*
*MRS MAI LAWAL.*
*MAMAN TEEMAH.*
*ZEE BLACK.*
*AYSHA HUMAIRA.*
*SA'ADAH GALADIMA.*
*MY ADIZATOU (Ummu Adnan.)*
*MARIYA...❤.*


*Chapter 27 to 28*


Tunda Zahrah tasume, bata sake sanin inda kanta yake ba, sai ƙarfe shida na yamma, alokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba, wannan karon sam batayi wannan iface ifacen da kuma fusge fusgen da tasaba yi ba, sai dai idanunta da ta tsayar waje ɗaya,wato kan ceiling ɗin dake saman ɗakin, hawayene kawai kefitowa daga cikin idanun ta, yana mai sauƙa a gefen fuskarta, "Zahrah !" Inna dake gefe taƙira sunan Zahrah.


Ko gizau Zahrah ba tayi ba, balle Inna tasaran zata amsa mata, gyra tsayuwa Inna tayi haɗe da jinjina kanta, tabbas tasan koma meyafaru da Zahrah sune sanadi, domin kuwa basu riƙe amanar da iyayenta suka basu kafun su rasu ba.
Dr Saddiq ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo, bakinsa ɗauke da sallama, yayinda Baffa ke biye da shi a baya, "Yauwa likita kazo ko? ta farka amma kwata-kwata bata magana!" Inna tafaɗa cike da damuwa.
Ɗan guntun murmushi kawai Dr Saddiq yayi,haɗe da nufar inda Zahrah'n ke kwance, kallonta yayi na ɗan wasu mintuna, kana yajuyo da kallonsa wajen su Baffa... "Inaso Za'ayi mata gwajin ƙwaƙwalwa, domin sake tabbatar da lafiyarta, saboda haka zanturo Nurses su ɗauketa " Dr Saddiq yafaɗa.


Sosa kai Baffa yashiga yi, cike da damuwa yace "To kamar nawa ake buƙata likita? kuma naga tunda mukazo ka ke bata kulawa, amma banji anyi min maganar nakawo ko sisi ba, fatana Allah yasa gwajin ƙwaƙwalwar bashi da tsada !" Baffa yafaɗa cikin karyewar zuciya, domin kuwa idan gwajin yana da tsada tofa sai dai ahaƙura, saboda bashi da kuɗi.


Kallonsa kawai Dr S.S yayi batare da yace dashi ƙalaba, ya sa kai yayi ficewarsa daga cikin ɗakin.


Mintuna kaɗan da fitarsa, wasu nurses su biyu suka shigo, ɗaukan Zahrah sukayi, suka ɗaurata kan wani gado mai ƙafafun taya, suka fice da'ita, ba don idanunta da suke buɗeba, tabbas da idan ka ganta zakayi zaton gawace, domin kuwa babu abun dake, motsi a jikinta, sai hawaye kawai dake ambaliya a cikin idanunta...


Alhmdlh anyi mawa Zahrah gwadin ƙwaƙwalwa lafiya, saura kawai ajira fitowar result.
Babu abun dayake ɗaga mawa Dr S.S hankali a yanzu, kamar yanda take yawan firgita, gashi hawaye sun kasa daina zubowa daga cikin idanunta, babban abun damuwar kuma shine bata um balle um um, ko motsawa bakinta bayayi, sannan kuma waje ɗaya idanunta suke kallo, wato sama.


Result ɗin gwadin da'akayi mata yafito, kuma masha Allah, ƙwaƙwalwarta tana nan lafiya, babu abun daya sameta, kawai dai tashiga halin firgici ne, kuma dama ana yawan samun irin haka...


"Likita ya sakamakon, Allah yasa bata samu wani matsala a ƙwaƙwalwarta ta ba ? " Baffa dake zaune cikin office ɗin Dr S.S ya tambaya.


"ku kwantar da hankalinku, sakamako yayi kyau, domin kuwa brain ɗinta nanan lafiya"


"Alhamdulillah, Allah mungodema !" Baffa yafaɗa cike da jin daɗi,


"Kaine Babanta mahaifi ?" Dr S.S yatambaya sanda yake ƙoƙarin cike wani file dake gabansa.


"A'a bani na haifeta ba, ƴar ɗan uwana ne da ya rasu, amanarta yabarmin, gashi yanzu bansan wani tsinannen bane ya aikata ma ta wannan abun ba !" Baffa yaƙare maganar yana matsan ƙwalla.


Kallon sa Dr S.S yayi na tsawon wasu mintuna, kafun ya kau da kansa gefe, "Dawa take mu'amala, saurayi ko aboki ?" Dr S.S ya kuma tambaya.


"Bata mu'amala da kowa sai wani yaron arziki, shine ma yace yana sonta, kuma hargida yataɓa zuwa ya gaisheni, a zahirin gaskia bana tunanin shi zai yi mata wannan aika aikan" Baffa yafaɗa da ƙwarin guiwarsa.


"Maiyasa kake tunanin shi bazai iya yi mata haka ba ?" Dr S.S yakuma jefo mawa Baffa tambaya,


"Saboda shiɗin yaron kirkine kuma ɗan babban gida ne, mutane masu dattako" (readers kuji Baffa fa da sharri )


"Zaka iya tafiya, anjima zanzo na bata maganinta" Dr S.S yafaɗa a taƙaice, domin kuwa wani irin taƙuƙin takaicin Baffa ne ya cika masa zuciya,


Sumi sumi haka Baffa yafice daga cikin office ɗin, yana matsan ƙwalla.


"Wai maiyasa mutane suke wasa da amana ne ? idan har ɗan uwanka bazai iya riƙe maka ahalinka, idan baka raye ba, to waye zai iya riƙe maka su da gaskia dakuma amana? ƴar ɗan uwanka tamkar ƴa take a wajenka, idan baka nuna ma ta soyayya ba, to wazai nuna ma ta? irin su Baffa ne suke ɓatawa mutane suna, kuma suke tozarta marayu, ya Allah kabamu ƴan uwa masu amana, wanda zasu kula da namu ko bama raye Ameen." Dr S.S yafaɗa acikin zuciyarsa,


Yau kwanan Zahrah Biyu kenan bata magana, hawaye har sun gaji da fitowa daga cikin idanunta sun kafe, duk kuwa yanda su Baffa suka so ta faɗi koda kalma ɗaya ne, hakan ya gagara, domin kuwa ko kallonsu batayi balle su sa ran zatai musu magana. Sosai Dr S.S yake ƙoƙari wajen kulawa da'ita, baya wasa da lokacin shan maganinta, domin yana da yaƙinin zuwa yanzu, ɗinkin da akayi mata a ƙasanta ya warke.


Zaune yake a kan ɗaya daga cikin kujerun falon mahaifiyar sa, sanye yake da riga da wando na maroon ɗin bugaggiyar shadda, bakaɗan ba kuwa yayi kyau acikin kayan, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa a kwai damuwa a tattare dashi, domin kuwa tun ɗazu aka aje masa plate ɗin snacks a gabansa, amma yakasa ɗaukan ko da ƙwaya ɗaya ne, yakai bakinsa, duk da kuwa snacks ɗin abune mafi soyuwa a garesa,,


Hajiya ce tsaye a kansa, tayi kusan minti ɗaya da zuwa amma sam baisan da zuwan nata ba,


"Saddiq!" Hajiya taƙira sunansa.


"Na'am, Hajiya sannu da fitowa!" Dr S.S yafaɗa cikin girmamawa.


Zama Hajiya tayi haɗe da kallonsa cike da kulawa tace " Wai meke damunka ne Saddiq ? ina lure da kai gabaki ɗaya kwana biyunnan bana gane kanka, idan kafita aiki baka dawowa da wuri, ga yawan tunani da kakeyi, meke faruwa ne ?" Hajiya ta tambaya.


Gyara zama Dr S.S yayi, domin sam baya ɓoyewa mahaifiyar tasa matsalarsa,ko ta me cece kuwa, cike da damuwa yace "Hajiya wata yarinya aka kawo hospital ɗinmu, duka dukanta bazata wuce 18 to 19 year ba, yarinyar tana matuƙar baƙatar taimako, domin kuwa, wani ne yayi raped ɗinta, ahalin da ake ciki yanzu, ko magana batayi, narasa wace hanya zanbi nashawo kan lamarin!" Dr S.S ƴafaɗa cike da raunin murya,


"Subanallahi fyaɗe kuma Saddiq ?"


"Eh Hajiya, shiyasa abun yake damuna" Dr S.S yafaɗa,


"Allah sarki! Allah ubangiji ya cigaba da tsare mana ƴaƴanmu, amma iyayenta sun maka case ɗin a kotu ne ?" Hajiya ta tambaya.


"A'a Hajiya banjin zasu kai case ɗin kotu, domin kuwa talakawa ne basu da wani ƙarfi " Dr S.S ya faɗa cike da tausayawa.


"To Allah yabata lafiya, amma miye na jefa kanka acikin damuwa haka Saddiq? irin wannan matsalolin naga dama an riga da an saba kawo muku, sai dai Allah yarufa asiri kawai, bakaci snacks ɗinba mai yasa ?"


"Zanci Hajiya ko zuwa anjima ma" Dr S.S yafaɗa lokacin dayake miƙewa daga kan kujeran dayake zaune,


"A'a ina zaka kuma ?" Hajiya ta tambaya.


"Lokacin shan maganin Zahrah yayi Hajiya, zanje ne na bata" yaƙare maganar yana mai duba wrist watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.


"Zahrah! wacece kuma Zahrah ?" Hajiya ta tambaya,


"Itace yarinyar da akayi raped nata dana gaya miki"


"To to adawo lafiya"


"Ameen Hajiyana!"


Yana fita yashige cikin motarsa kaitsaye hanyar asibitinsu ya ɗauka....


Kamar koda yaushe zaune take akan gado, yayinda idanunta ke kafe a waje ɗaya, ruwan hawayene kawai ke tsiyayowa daga cikinsu,


Da Sallama ɗauke a bakinsa yaturo ƙofar ɗakin, harya ƙaraso tsakiyar ɗakin, batasan ma da zuwan sa ba,


Aje abubuwan dake hanunsa yayi akan ƴar ƙaraman drowern dake gefen gadon, "Zahrah!" yaƙira sunanta cikin kwantar da murya, bata amsaba kuma bata juyo zuwa garesa ba, dama kuma yasan hakan zai iya faruwa, domin bata taɓa amsawa idan yaƙirata, bakuma ta tankamai komai zaice, duk da kuwa yasan tanajinsa.


Magungunan da yakamata tasha ya ɓare, haɗe da zubasu acikin hanunsa, goran ruwan daya shigo da shi yaɗauka, haɗe da ƙarasawa gareta, hanunta yakama yana ƙoƙarin sanya mata maganin , wani irin firgita tayi haɗe da fasa ƙara, wanda yajanyo hankalin Baffa da Inna dasuke zaune a waje, da hanzari suka shigo cikin ɗakin, da gudu Zahrah taƙarasa jikin Inna ta rungumeta, wani irin kuka mai tsananin ban tausayi tashiga rerawa,, sai kawai Inna ma ta fashe da kuka, tana mai tausayin Zahrah har cikin zuciyarta, domin kuwa lokaci ɗaya gaba ɗaya ta lalace, ta rame har duhu saida fatarta tayi, "kice su fita Inna dan Allah! kice masa kada yasake zuwa inda nake natsanesa! natsani duk wani Namiji! na tsanesu kice su fita, ko kuma inkashe kaina!!" Zahrah taƙare maganar tana mai ɗaukar wani Scissors dake aje kan wani ɗan ƙaramin table.


"Suhanallahi Zahrah mekikeyi haka ?" Baffa yafaɗa yana mai ƙoƙarin matsowa gareta,


Ihu Zahrah tasanya mai ƙarfin gaske, haɗe da saita scissors ɗin dai dai saitin cikinta, da iya ƙarfinta taɗaga zata cakawa kanta, cikin matuƙar zafin nama, Dr S.S ya murɗe hanun ta, haɗe da bata wani kyakkyawan mari akan kumatunta, "saboda hauka zaki kashe kanki ne? wani irin rashin hankaline wannan!!?" yatambaya cikin faɗa.


Zamewa tayi ƙasa tana mai rushewa da wani irin kuka mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login