Showing 117001 words to 120000 words out of 184930 words

Chapter 40 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt

09 Dec 2024

5751

kowa zai ɗauketa mahaukaciya wacce batasan me takeyi ba, amma kuma ayanzu tagane cewa wanda duk ya mata kallon mahaukaciya akan soyayyar da takeyia Zaid, to ko kaɗan baisan menene SO ba, SO shine wanda ke sauyawa mutum tunani alokaci ƙanƙani batare daya shiryawa hakan ba, SO shine wanda ke makantar da idanun mutum yazamanto bayaji baya gani, haka kuma tasanadiyar SO wasu ke salwantar da rayuwarsu, SO shike sawa kabi wanda baidace dakai ba, SO shike sawa amaka wulaƙanci amma kuma gobe ka koma inda aka wulaƙanta ka, SO shike sawa mutum yazalunceka amma kuma bazakaga laifinsa ba,kuma koda ma kagani bazaka iya juya masa bayaba, SO yana da matuƙar haɗari sannan yafi kowani abu saurin ɗaiɗaita tunanin meyinsa, SO shikaɗaine abun da zafinsa ke narkar da zuciya,,,,SO shine babban jagoran zuciya haka kuma shine raunin ta,, hanu ta sanya takuma dafe kanta wanda takeji kamar zai zazzago ƙasa,, hmmm kamar dai yanda Zahrah taga rana haka taga dare bacci sam yaƙauracemawa idanunta.....


(Kada kuga laifin Zahrah dan ta ci gaba da son Zaid, haƙiƙa Zaid ya cancanci Zahrah taƙisa mugun ƙi mawa kuwa, amma kuma SO bazai taɓa barin haka yafaru ba, wallahi Soyayya tawuce gaban kwatance, so babu ruwanshi da wai ancutar dakai ko ba a cutar dakai ba, shi so kaitsaye yake abunsa batare da yatambayeka shawara ba, nikam bana ganin laifin Zahrah dan taso Zaid domin shi so baya fita acikin sauƙi, sannan kuma zafinsa yanada matuƙar illa, ba'akanta aka fara ba, sau da dama zakuga namiji yana zagi dakuma dukan matarsa amma kuma duk da haka tanazaune dashi saboda tana sonsa, haka kuma saudadama zakuga Saurayi yayi amfani da soyayyar da budurwarsa takeyi masa ya yaudareta sun aikata zina, daga baya kuma idan ciki yashiga jikinta sai kuga yagujeta, saboda yasamu abun dayakeso daga wajenta, amma kuma idan harson gaskiya takeyi masa saikuga bata daina sonsaba duk dakuwa irin girman abun dayayi mata,, wallahi soyayyar gaskiya bata taɓa gushewa koda kuwa girman laifin da mutum ya aikata maka bazai misaltu ba, haƙiƙa idan banda sharrin SO babu wata mace da namiji zaiyi mata fyaɗe kuma ta dawo tacigaba da sonsa, wannan sharrin SO ne kawai wanda bashida magani😭 nidai nace ko guba baikai so hatsari ba, wallahi so mugune, inkun ganshi kukamaminshi kumai duka😰)


Ƙarfe 2 na dare ciwon Zaid yatashi sosai, abun gwanin ban tausayi, zuwa yanzu kam ciwon nasa yasoma fin ƙarfin tunanin Doctor's domin kuwa sai anyi tunanin cuta tayi sauƙi saikuma tadawo, yanzu haka bincikensu yanuna musu cewa zuciyarsa ce takumbura, gaba ɗaya hankalin Alhj Ma'aruf yakai ƙololuwa wajen tashi, Mum kuwa yanzu bata da aiki saina kuka dare da rana, hakanne ma yasanya Alhj Ma'aruf yanke hukuncin tattara Zaid ɗin sutafi Jermany, saboda ya ga abun yana nema yafi ƙarfin likitotinmu na nan, saboda koda yaushe Zaid cikin aman jini yake, lokaci ɗaya ya lalace yayi wani irin rama, kamar ma ba
Zaid ba.....


Washe Gari (Asabar)


*ƊAURIN AURE*


Tun ƙarfe 8 na safe gidansu Zahrah yake acike yayinda ƴan uwansu na nesa suka soma hallara don ɗaurin aure,, hayaniya ne ke tashi kota ina acikin gidan...


Ɗakin Zahrah na garzaya don inga awani hali take ciki...


Kwance take akan katifarta yayinda duka jikinta ke rufe da bargo, amma duk da haka bargon bai ɓoye rawan da jikin nata keyi ba, karkarwa kawai takeyi acikin bargon yayinda jikinta yaɗauki zafin zazzaɓi zau..


"Kitashi kisha maganin nan dan Allah Zahrah, kinga fa babu amfanin zama da ciwo batare da kinsha magani ba" Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da lallami..


Kai kawai Zahrah ta'iya kaɗawa alamar "A'a bazata sha ba" komagana ma yanzu bata iyayi saidai kawai ta kaɗa kai, hakan yafarune kuma saboda ciwon kai me tsanani da ta tashi dashi a safiyar yau ɗin,, duk yanda Husnah takaɗa ta buga akan Zahrah tatashi tasha magani ƙiyawa tayi, sai ruwan hawaye dake ta fita daga cikin idanunta, dole haka Husnah ta ƙyaleta..


10:30 tuni ƙofar gidansu Zahrah yasake cika da jama'a bamasaka tsinke, hayaniya ne kawai ke tashi tako ta ina, yayinda tsala tsalan motocin ango suka ƙaraso,, hmmm Dr.Sadeeq yasha kyau sosai cikin wata haɗaɗɗiyar gezina milk colour me matuƙar kyau da tsadar gaske, ɗinkin rigane da wando saikuma gare, amma kuma sunyi masa kyau sosai, yayinda ya ɗaura tsadadden agogo a hanunsa na dama, takalmin ƙafarsa kuwa ƙirar kamfanin GUCCI ne me matuƙar kyau,, ango fa yasha kyau iya kyau, sai yau nima nasake tabbatarda cewa shiɗin ma wani Handsome guy ne mezaman kansa, domin kuwa duk ƙwaƙwan mutum babu ta'inda zai kushesa, yahaɗu iya haɗuwa sonkowa ƙin wacce ta rasa😜, bakin ango fa yaƙi rufuwa sai murmushi kawai yake, yayinda abokansa keta tsokanansa,, shidai kawai murmushi yaketa zubawa, bazai taɓa iya misalta irin tarin farincikin dayake ciki ba, haƙiƙa yau yana cikin nishaɗi dakuma jin daɗi, yau takasance babban rana agareshi ranar da duk wani gauro da gauruwa suke jira, ranar da duk wani mai hankali da nutsuwa yake biɗar zuwanta wato RANAR AURE, shikam sai dai yace Alhmdlh yagodewa Allah mai kowa me komai daya nuna masa wanann rana... Baffa na hango shima yau cikin farinciki yake, yasha adonsa cikin farar shaddansa riga da wando dakuma gare, su uban amarya manya,,, 11:00 am dai dai dandazon jama'a suka shaida ɗaurin auren SADEEQ KHABEER SARDAUNA (Dr.Sadeeq) da amaryarsa FATIMA ADAM (Zahrah) akan sadaki naira dubu ɗari,, masha Allah ana kammala ɗaurin aure aka soma taya ango murna da Allah yasanya alkhairi, ae kuwa fuska asake haɗe da tarin annuri Dr.Sadeeq ke amsawa, hamdala kawai yakeyi acikin zuciyarsa shikenan Zahrah ta zama tasa mallakinsa halaliyarsa... Bayan angama musabahane kuma aka ɗunguma zuwa wani babban hotel wanda anan za'a gudanar da receiption....


Lokacin da labari ɗaurin auren ya'isa ga kunnen Amarya wani irin faɗuwar gaba wanda bata taɓa jin irinsa ba taji ya rusketa, shikenan yanzu tazama matar Doctor, zuciyar tane tashiga bugawa da sauri sauri yayinda har ƙirjinta yasoma amsawa, take taji wani abu maikama da tsananin tsoro ya lulluɓe mata jiki,ae kuwa sai neman ɗan kuzarinta tayi ta rasa,jitayi gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mutu laƙwas kamar ansassare mata su,, sake duƙunƙunewa tayi acikin bargo tashiga rera kuka marar sauti, ita bata tsani Dr.Sadeeq ba ko kaɗan, amma kuma tarasa meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarta....


(Kuyi haƙuri Team Zaid wallahi nima Allah jikina gaba ɗaya yayi sanyi sai dai kuma kunsan ita ƙaddara bata taɓa sanjawa dole saitazo a yanda Allah ya aikota😭 yanzu haka jinake kamar ruwan jikina ya ƙare😥)


Ƙarfe 2 dai dai jirginsu Zaid yatashi daga cikin garin Lagos Nigeria zuwa Jermany saidai shi Zaid sam baisan wainar da ake toyawa ba saboda baya cikin hayyacinsa kwata kwata, tunda suka baro Abuja har suka iso Lagos baisan inda kansa yake ba....


Ɓangaren ango kuwa reception aka gudanar gangariya, anci kaji ansha fruits juice kowa cikin sa yayi haniƙan sai dai godiyar Allah da sanya albarka...


Amarya kuwa koda ruwane takasa sanyawa acikin cikinta, rashin lafiya sosai ya tsananta a gareta, zuwa yanzu kam hawayen ma sun kafe sundaina fitowa, sai numfashin wahala da take fitarwa ta bakinta kawai,, kasancewar anata hidima yasa babu wanda yadamu da cinta kokuma shanta, Husnah ce kaɗai ke tsaye akanta tana bata kulawa.


"Dan Allah Zahrah ba danniba kitashi inrakaki toilet kiyi wanka kizo kisamu koɗan sabon kayane kisanya kingafa zuwa anjima za'a zo ɗaukarki!" Husnah tafaɗi haka tana me ƙoƙarin tada Zahrah dake kwance zaune.


Da taimakon Husnah Zahrah taje banɗaki tayi wanka, koda tafito wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar atamfa Husnah ta bata tace ta sanya, babu musu tasanya saigashi kuwa rigan tayi matuƙar yi mata kyau ajiki, da ƙyar Husnah ta lallaɓata tashafa mata powder haɗe da man leɓe, sai kace wata ƙaraman yarinya,,, komawa gefe Zahrah tayi ta takure bayan Husnah tagama shiryata, still Husnah maganar abinci tayi mata amma Zahrah tasake bushe idanunta tace ita sam bazataci abinci ba batajin yunwa (Ninaga jarfa saikace wanda aka mawa auren dole 😏)...


Ƙarfe 5 tsala tsalan motocin ɗaukar amarya suka shiga fakawa a ƙofar gidansu Zahrah motocine reras masu kyau har guda 15 suka zo don ɗaukar amarya yayinda motar da amarya zata shiga ta banbanta da duka sauran motocin don tafi duka sauran kyau..


Zahrah na zaune wata Aunty Ladi ƴar uwar mahaifiyarta wacce tazo daga Niger tashigo cikin ɗakin babban mayafi me kyau ta ɗauka haɗe da rufe Zahrah dashi, miƙar da'ita tsaye tayi cikin farinciki tace
"Allah yayi yauzaki tafi ɗakinki amarya muje ɗakin Inna'n taki aimiki nasiha"
aitun kan aƙarasa ɗakin Inna Zahrah ta ɓarke da kuka wiwi, (Wayyo Allah, wallahi duk rashin daɗin gidanku randa zaka barshi saikaji ciwo acikin ranka harna tuna da nawa ranan 😭🙈)


Nasiha Inna da sauran matan dake ɗakin suka shiga yi mawa Zahrah akan tabi mijinta sauda ƙafa inayi bari na bari, komin ƙanƙantan ɓacin ransa ta gujesa, duk kuma wani abu datasan bayaso kada ta aikata, sannan kuma taji taƙi ji tagani taƙi gani, takuma riƙi haƙuri don shine tubali kuma gini haka ƙinshiƙin zaman aure, bawai idan anyi aure kullum soyayya ake ci ba, a'a watarana dole sai kunɓatawa juna, dole sai kunyi haƙuri kundanni zuciyarku tukun zamanku zaiyi daɗi, sannan kuma idan tasan tayi masa laifi kada tayi girman kai, tasameshi har ƙasa ta duƙa tabasa haƙuri, domin kuwa har kullum shine sama da'ita, yanzu amatsayin uba yake agareta bata da wani wanda yafishi,, wayyo Allah Zahrah tayi kuka sosai harda shiɗewa, Allah sarki sabo turken wawa duk da cewa Inna watarana tana hantararta amma yau duk saitaji babu daɗi tafiyan Zahrah'n saiga Inna tana hawaye tana jan majina, shikenan Inna kuma fa cin kaza ya yanke mata lol 😂.


Su Inna suna gama nasu nasihar aka garzaya da'ita wajen Baffa,, wayyo Allah Zahrah tana ganin Baffanta ta faɗa jikinsa haɗe da sake ƙara volume ɗin kukanta, Allah sarki take Baffa shima yasoma hawaye, daƙyar ya'iya daure zuciyarsa yayi mata nasiha, duk dai maganar ɗayace shine tabi mijinta sau da ƙafa takumayi masa biyayya akan duk abun dayace, sannan kuma tazamo me haƙuri akan dukkan komai, sannan kuma yaroƙi yafiyarta akan abun dayayi mata baya, tana kuka tace tajima da yafe masa kuma ita baimata komai ba, itama tanemi yafiyarsa yakumace ya yafe mata😭


Haka Aunty Ladi da Husnah suka fita da Zahrah tana kuka Husnah kanta kuka take, yanzu itama haka watarana za'a zo a ɗauketa daga gaban Momynta akaita can cikin wasu dangin😭...


Anasa amarya acikin mota sauran ƙawaye da ƴan uwa ma kowa yashiga motar da ransa keso, bayan komai yakammalane motocinnan suka gangara kantiti, atare suke tafiya wani abayan wani, sannan kuma komai anitse akeyinsa babu wani hargowa...


Direct gidansu Dr.Sadeeq aka wuce da amarya, domin kuwa 8:00 pm nayi za a wuce wajen diner...


Abun mamaki tarba me kyau Hajiya tamawa amarya dakuma danginta, ko kaɗan bata nuna musu ɓacin rai kokuma tsana ba, sai dai su Aunty Raliya dasuketa binsu da wani irin kallo dake nuni da cewa baƙaunarsu sukeyi ba, ɗaki guda aka warewa amarya, balaifi ɗakin yayi kyau sosai, akan gado Aunty Ladi ta zaunar da Zahrah, mintuna kaɗan da shigowansu ɗakin wasu ƴan mata suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye dakuma na sha abun gwanin burgewa, gaskiya sun samu tarba na mutumci daga Hajiyar Doctor......


Wayar Husnah ce tafara ruri ganin wanda ke ƙiran nata yasanya ta ɗaga wayar bawani ɓata lokaci


"Bestie'n mu how far?" abunda wanda yaƙirata acikin wayar yafaɗa kenan..


Dariyane yakamata amma saita taƙaita dariyan haɗe da cewa "I'am fine sai dai gaskiya na gaji"


Murmushi shima yayi haɗe da cewa "Ina Amaryata Allah yasa tana lafiya, nayi kewarta sosai rabona da'ita fa tun ranan alhamis" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me gyara kwanciyar dayayi akan gadonsa...


"Kamar kuwa kasan kainaketa so kaƙira, wallahi yau tun safe Zahrah taƙicin komai kuka kawai takeyi, gashi bata da lafiya temperature ɗinta ya hau sosai" Husnah tafaɗi haka ga Dr.Sadeeq.


"Subahannallah, keda su waye aɗakin?" Dr. yatambayi Husnah cike da zaƙuwa..


Kallon waƴanda ke cikin ɗakin Husnah tashiga yi kafun tace


"Gaskiya munada ɗan yawa"


"Oh my God to shikenan, please anjima kikawomin ita ina cikin boys guaters kinji"


"To shikenan zan kawota insha Allah"


Daga haka suka kashe wayar murmushi kawai Husnah tayi bayan ta'ajiye wayar tata gaskiya azamaninnan idan mace tasamu wanda ke sonta kamar irin sonda Dr keyiwa Zahrah yakamata ta riƙeshi da kyau hanu tara tara domin samun irinsu wahalane dashi, saboda yanzu zuciyoyin yawancin mutane duk taɓaci da yaudara.........


*Inasonku masoyana na Wattpad irin sosai ɗinnan, ina yaba ƙoƙarin ku wajen min comment, Allah yabar ƙauna*


*Kuɗin ma ae nadabanne masoyana na Whatsapp inajin daɗinku sosai iya wuya muna jone Insha Allah*








*Comment*
*Share*
*and Voted please*





*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*CHAPTER 90 to 91*


Saida kusan gabaki ɗaya mutanen da suka kawo Zahrah suka soma watsewa zuwa wajen dinner, kafun Husnah ta matso kusa da amarya Zahrah wacce take aikin kuka. Hannayenta takamo haɗe da zama gaf da'ita.


"Please Zahrah kidaina wannan kukan, yanzu haka Doctor yace inkai masa ke yana boys guaters, kuma kinga babu amfanin kije wajensa kina kuka" Husnah tafaɗi haka ga cikin lallashi.


Zahrah dai bata kumace da'ita komai ba bata kuma daina kukan ba,, wayar Husnah ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Dr.Sadeeq ne keyawo akan screen ɗin wayar,, tana kara wayar akan kunnenta yace


"Yadai Husnah, najiku shiru"


Sake kallon mutanen da sukayi ragowa acikin ɗakin Husnah tayi.
"Gaskiya babu dama Doctor, saboda dazaran anga zamu fita za'ace ina zankaita" Husnah tafaɗi haka cikin ƙasa ƙasa da muryarta....


Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa
"Okay to bakomai zan san yanda za'ayi, ku shirya me meckup tana nan zuwa"


Cikin matsanancin ciwon kan dake ɗawainiya da'ita tashiga toilet ta ɗauro alwala, kan ƙaton darduman dake shimfuɗe a tsakiyar ɗakin ta hau ta kabbara sallah'n magriba,, tana idar da sallan meyi mata meckup ta ƙaraso, haka tanaji tana gani ta bada fuskarta aka zizara mata meckup wanda yaɗauki fuskarta sosai.. Yauma dai meyin meckup ɗinne ta shiryata tsab cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga (wedding gown) na wani tsadadden leshi me matuƙar kyaun gaske, riga ce doguwa har tana sharan ƙasa yayinda bayan rigar aka sanya wani haɗaɗɗen net me matuƙar kyaun gaske, sosai net ɗin da aka sanya abayan rigan yakuma ƙawata ɗinkin, lace ɗin yakasance light pink colour yayinda kayan ƙyale ƙyale najikinsa yakasance golding ash colour, sosai kayan yayiwa Zahrah kyau,,, haɗaɗɗen ɗaurin ɗan kwali aka tsantsara mata akanta, take tasake yin kyau,,,, yau dai kwalliya da kuma kyawun da Zahrah tayi haryafi wanda tayi a ranan kamu, komai nata yau na musamman ne tasha kyau sosai, ga doguwar riganta me ɗaukar hankali, daddaɗan ƙamshi kawai take fitarwa ajikinta me sanya nutsuwa,, duk da irin wannan kyawun da tayi sai dai fuskarta babu wani wadataccen walwala domin kuwa idanunta sunyi luhu luhu dasu, cikinta kuwa banda kukan yunwa babu abun dayake yi mata, amma kuma saboda masifar taurin kai irin nata taƙi sanyawa cikin nata komai na abinci.. Husnah ma yau zama tayi akayi mata meckup nagani na faɗa, sosai itama tayi kyau, tasha adonta cikin wata doguwar riga na golding white lace, idan ka kalleta dole ka ƙara domin itama tayi kyau sosai dama kuma itaɗin ma ko babu meckup tana da kyau masha Allah....


Yauma dai ango tare da amaryarsa zasu wajen dinner kowa yariga daya tafi harsu Auntie Raliya kuwa....


Husnah ce riƙe da hanun Zahrah suka fito compound ɗin gidan inda motar ango ke jiransu.


Shikam gaba ɗaya kwana biyunnan salon kyawun na Zahrah namatuƙar tafiya da imaninsa babu ma kamar yau, gaba ɗaya komai na surar jikinta ya bayyana bama kamar hips ɗinta yafito raɗau acikin rigan..


Husnah ce ta buɗe murfin motar dayake zaune aciki, sai da ta tattaro ƙasan rigan Zahrah'n kafun Zahrah ta'iya shiga cikin motar ta zauna,, lumshe idanunsa yayi haɗe da shaƙan daddaɗan ƙamshin daya kawowa hancinsa ziyara, wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi ya sauƙe,, kallonsa yakuma dawowa dashi kan tauraruwar da haskenta yacika idanunsa,,, murmushi yasakar mata me ƙayatarwa, yayinda ita kuwa kanta ke duƙe aƙasa tama kasa ɗago idanu ta kalleshi,, hanunsa ya sanya ya ɗago haɓarta, sai alokacin ta iya jefa idanunta cikin nasa idon, wani irin abu yaji acikin jikinsa, ita ɗinma hakane, da sauri ta rumtse idanunta,, abun daba ta tsammata ba, sai jitayi ya jawota jikinsa, haɓanta yakuma ɗagowa da hanunsa na dama, haɗe da sanya ɗayan hanunsa yashafi gefen kumatunta


"My Princess!"
yaƙira sunanta cikin wata muryarsa me sanyi. a hankali ta ware idanunta acikin nasa idanun, ƙasa ƙasa yayi da idanunsa haɗe da maida kallonsa ga ɗan ƙaramin bakinta dayasha lipstick, murmushi yakuma sakarmata haɗe da sake jawota ya ɗaurata akan cinyarsa.

"Kinyi kyau fiye da kullum my princess!" yafaɗi haka still yana me shafa gefen kumatunta da hanunsa, wani irin kunyarsane yakamata tunda take dashi baitaɓa yi mata irin kallon dayakeyi mata a yanzu ba, haka kuma baitaɓa jawota yaɗaurata akan cinyarsaba sai yau. Marairaice fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa,, sweet ɗin dake cikin bakinsa ya cire, haɗe da ɗago fuskarta ya sanya mata acikin bakinta, kallonsa tayi da ɗara ɗara idanunta, kansa ya jinjina mata yana ɗan murmushi, ahankali tashiga juya sweet ɗin acikin bakinta, dama kuma tunsafe babu wani abu daya shiga bakinta inbanda ruwa, sai wannan sweet ɗin daya bata yanzu,, hanunta yakama yashiga murzawa ahankali haɗe da kafeta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login