Showing 153001 words to 156000 words out of 184930 words
Chapter 52 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt
sukayi ruwa da tsaki, wajen tsundumata, cikin halakan data faɗa, shikuwa saurayinta Ameer, wanda shiya fara saninta ƴa mace, ta zuba masa tsinuwa yafi guda ɗari biyu, da ƙyar ta iya lallaɓan kanta tashiga toilet donyin wanka..
Yajima acikin masallacin kafun ya dawo gida, abun dayajima baiyiba kenan, wai yaje masallaci yajima har haka, karatun Al'Qur'ani yayi, kuma da yardan Allah yaɗan samu salama acikin zuciyarsa..
Afrah najin shigowarsa cikin gidan, ƙafafunta yasoma rawa, take taji wani irin ciwon ciki ya kamata, mugun tsoronsa takeji, tun ada ma, balle yanzu kuma da wannan abun yashiga tsakaninsu, ta tabbatar sai yakasheta acikin gidannan, kuma ya kashe banza.
Yana shiga cikin ɗakinsa, ya ɗauki magungunansa yasha, tashi yayi yafice daga cikin ɗakin nasa, direct ɗakinta ya nufa.
Tanajin motsin ana buɗe ƙofarta ta miƙe zunbur, take wani irin fitsari ya zubo mata, tsabar tsoro, aikuwa tana jefa idanunta, cikin nasa, taji numfashinta, na shirin ɗaukewa.
Da rinannun idanunsa yake kallonta, ganinta da yayi yasake tuna masa ɓacin ransa, jiyake ya tsaneta, amma kuma yazama dole yayi mata tambayoyin dake cikin ransa..
"Zauna" yafaɗi haka cikin dakiya.
Jikin Afrah na rawa ta zauna aƙasan tiles.
Ƙafansa ɗaya yasanya, yataka kan gado, haɗe da ɗan ranƙwafowa.
"Dama ke karuwa ce?" first tambayar daya fito daga cikin bakinsa kenan.
Ƙirjin Afrah ne ya buga, take hawaye suka ɓalle akan fuskarta, kanta tashiga girgizawa alamar
"A'a"
Laɓɓansa ya cije cike da takaici yace.
"Da bakinki nakeso, ki bani amsa bada kai ba."
"A....a wallahi ni.....ba..ba..ka..ruwa..bace!" murya a sassarƙe tabashi amsa.
"Kinsan me ake ƙira da karuwa?"
Yatambayeta.
Dasauri ta kaɗa kanta, saikuma tatuna da abun dayace mata, baki na rawa tace "Karuwa itace mebin maza, wacce take zaman kanta"
"Good, ashe kinsan mene ake ƙira da karuwa, kenan ke ɗin karuwa ce?"
Da sauri tace "Wallahi niba karuwa bace"
"Idan ke ba karuwa bace, dan ubanki ina kikai budurciki!!!" amatuƙar tsawace yayi maganar, saboda ya matuƙar harzuƙa.
Guntun fitsarin da take ta riƙewane ya silalo, tsabar ta tsorata, ƙyarma tafara tamkar wata mejin sanyi, tsabar tsorata da yanayinsa da tayi, ta makasa ce dashi komai.
"Shirun da kikayi ya nuna alamar cewa eh ke cikakkiyar karuwace, mazinaciya, me kike nema arayuwarki, kina ƴar ƙaramar yarinya dake?" yatambayeta yana me ƙare mata kallo.
Kanta tashiga girgizawa, akaro na barkatai.
"Kayarda dani, wallahi niba karuwa bace, bantaɓa karuwanci ba!" tafaɗi haka tana kuka.
"Okay to tunda dai kince ke ba karuwa bace, ba naci ubanki, wataƙila zaki faɗamin inda kika kai virginity ɗinki" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin zare belt ɗin wandon jeans ɗin dake sanye a jikinshi.
Da gudu ta rarrafo ta ƙaraso garesa, zubewa tayi akan ƙafafunsa tana kuka.
"Dan Allah kayi haƙuri, kayafemin, wallahi sharrin shaiɗanne, dakuma na zuciya, amma bantaɓa zaman karuwanci ba!" kuka take wiwi kamar wacce akace uwarta ta mutu.
Tsayawa yayi cak yana me kallonta, kuka take tsakaninta da Allah.
"Mene naka najin haushinta Zaid? mene naka nacewa zaka daketa? idan ita karuwace kai menene?" wata zuciyarsa ta tambayesa.
Rumtse idanunsa yayi haɗe da cije laɓɓansa, da ƙyar ya iya janye ƙafafunsa ya zauna, abakin gado.
Afrah dake duƙe a ƙasa tana kuka ya kalla.
Cikin wata irin murya a cushe yace. "Afrah!"
Dasauri Afrah taɗago fuskarta ta kalleshi, duk taɓata fuskar ta da majina, ansha kuka anƙoshi.
"Zo" yace da ita ataƙaice.
Babu musu ta ƙaraso gabansa ta durƙusa.
"Meyasa kika zaɓi banzatar da mutuncinki a waje Afrah?" tambayar dayayi mata kenan, sai dai wannan karon, ba acikin tsawa yayi mata tambayar ba.
Cikin kuka Afrah tasoma cewa "Bansan dalili ba, amma nabiyewa son zuciyata ne kawai, nabiyewa zugan shaiɗan da kuma shaiɗanun ƙawaye, najefa rayuwata a halaka, nasan irin wannan ranan zatazo, amma bantaɓa kawo cewa al'amarin zai kai har haka ba, domin wanda ya fara sanina amatsayin ƴa mace, yayimini alƙawarin aure, saboda haka bantaɓa kawowa araina cewa rashin kasancewata ba a budurwa ba zai kawo min wani abu, saboda na ɗauka wanda yafara sanina a cikakkiyar ƴa macena shine wanda zai aureni, ashe shima ƙarya yakemin, ba aurena zaiyi ba, yayi hakane kawai,dan na amince nadinga bashi kaina, aduk sanda ya buƙata!" taƙare maganar tana me tsananta kukanta.
Rumtse idanunsa yayi, haɗe da cije laɓɓansa, akaro na sau babu adadi.
"Banason kuka" yafaɗa ataƙaice yana me kawar dakansa gefe.
Duk da cewa kukan nacinta, amma haka ta haɗiye, tasoma ƙoƙarin yin shiru.
"Kinyi wanka?" yatambayeta still kansa na na kallon wani wajen.
"Eh" tafaɗa murya a raunane.
Miƙewa yayi daga zaunen da yake, haɗe da dubanta.
"Zanshiga na kwanta, banason naji koda motsinkine, ki zauna anan ɗakin, banason damuwa" yanakaiwa nan azancensa, yasakai yafice daga cikin ɗakin.
Afrah kam kan gadonta ta haye taci gaba da rera kukan danasani, ahaka har baccin wahala ya ɗauketa.
Zama yayi akan gado, haɗe da ɗaura idanunsa akan hotonta, hawayene suka zuraro daga cikin idanunsa, abune mawuyaci yadaina sonta, duk da yasan a yanzu ta haramta agareshi, kuma yana gudun ɗaukarwa kansa zunubi, amma kuma akan sonta, baya iya control ɗin zuciyarsa, akullum maganaɗisun ƙaunarta, ƙara fusgarsa take, saidai kuma kamar yanda yaɗaukarwa kansa alƙawari, zai ci gaba da addu'a har Allah yakawo masa sauƙi da sassauci acikin zuciyarsa akan soyayyarta..
*(So ba ƙarya bane, So gaskiyane, amma kuma wanda baitaɓa yiba bazai gane ya yake ba, haka kuma wanda baiyi zurfi acikin saba, bazai taɓa gane ya zafinsa yake ba, ba acire so alokaci guda, a sannu komai yake gushewa, ƙauna acikin jini take, bata taɓa gushewa, watarana a sannu so zai gushe, amma ƙauna tana nan. Ku yiwa Zaid da Zahrah uzuri, wallahi soyayya ta wuce gaban kwatance, idan kanason abu baka ganin laifinsa, shi so hana ganin laifi ne, meyin so shikaɗaine zai gane inda kalamaina suka dosa.)*
*(Yau fejin nasu Zaid ne, bazamu waiwaya gidan Doctor ba, team Doctor da Zahrah i'am sorry)*
*9/february/2020*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 108*
Kaikawo take tayi a cikin kitchine ɗin, sauri take ta kammala aikinta, tsaye take acikin kitchine ɗin, tana wanke wani plate dake riƙe a hanunta, sosai nayi mamakin ganinta a haka, rigace irin T-shirt me faɗinnan sanye ajikinta, duka duka tsayin rigar ko rabin cinyanta bai ƙarasa ba, bata kuma sanya wando dan rufe cinyoyinta ba, wani irin slipper ne me kyaun gaske sanye aƙafarta, wanda aka ƙawata samansa da wani kyakkyawan follower,
Irin yanayin shigar nata yasanya tayi kama da irin yaran turawan nan.
Sam bata ji motsin shigowarsa ba, hakan yasa bata kawo cewa akwai wani mahaluƙi dake kallonta ba.
Sake gyara tsayuwarsa yayi, haɗe da jingina bayansa, da jikin ƙofar fita daga kitchine ɗin, sosai tayi masa kyau, babu abun daya fi ɗaukar hankalinsa ajikinta, kamar hips ɗinta, ga santala santalan cinyoyinta, da suka bayyana kansu, gwanin ban sha'awa, gaskiya komai na Zahrah me kyau ne, ta cika mace hundred percent, yajima yana fata da burin samun cikakkiyar mace, me cikar halitta ka marta, a matsayin matar aurensa, sai gashi Allah Ya dubesa ya basa Zahrah.
Ɗan tsayawa tayi, haɗe da sanya hannayenta bisa ƙugunta, tana me sauƙe numfashi, a hankali, da'alama dai akwai gajiya a tattare da'ita.
"Kin gaji ko?"
Cike da mamakin jin muryarsa, acikin kunnuwanta, da tayi ta juyo, tana me fuskantarsa.
Murmushin sa me kyau, ya sakar mata, haɗe da soma takowa zuwa gareta.
"Yaushe kadawo bansani ba?" ta tambayeshi, cike da tsananin mamaki.
"Najima da dawowa, nadai tsaya kallon abar sona ne" yafaɗi haka yana me lumshe gajiyayyun idanunsa, sosai yakejin gajiya ajikinsa, baƙaramin aiki yau yasha a office ba.
"Sannu da dawowa!"
tafaɗa tana sakarmasa murmushi.
Jawota cikin jikinsa yayi, haɗe da rungumeta, kansa ya ɗaura akan wuyanta, wata ajiyar zuciya, me ƙarfi ya sauƙe.
"Nayi kewarki sosai my lovely wife!" cikin murya, me sanyi, ya yi maganar.
Murmushi takuma sakar masa, haɗe da langwaɓar da kanta gefe gudu. "Nima nayi kewarka Hubby na!" cikin salo ta ƙare maganar.
"Dagaske kema kinyi kewata my wife? nifa dukanki nayi kewarki!" yafaɗi haka yana meyi mata wani irin kallo, dake ɗauke da wani tarin ma'anoni masu yawa.
Ganin kallon dayakeyi mata, yasa tasaki murmushi me ɗan sauti, ƙoƙarin janye jikinta daga nashi tasoma yi.
Ƙam ya riƙeta, haɗe da sake mannata acikin chest ɗinsa, da alama dai bayason tacire jikinta acikin nasa jikin.
"Uh dan Allah, Kabarni na ƙarisa aikina, kuma mafa duk ƙauri nake, amma kaketa mannani a jikinka, kaɗan bari nayi wanka kaji!" tayi maganar cikin yanayi na lallashi, tasani sarai, idan dai ba lallashinsa tayi ba, to bazai bari ta kammala aikin data fara ba.
"Nidai naƙi wayon, kuma ni banji wani ƙauri da kike ba, princess nadawo amatuƙar gajiye, gashi kuma ganinki ahaka yasake ɗaura min wani gajiyan, please kiyarda ko 30 minute ne kiban, ina da buƙatarki fa akusa dani...."
Bata bari ya ƙarasa zancen nasaba, tayi saurin toshe masa baki da tafin hanunta, shagwaɓe fuska tayi, haɗe da marerece idanunta, kanta ta girgiza masa akan kada yace komai.
Hanunsa takama, suka fice daga cikin kitchine ɗin, haka yake binta tamkar wani raƙumi da akala, suna shiga cikin bedroom, ta zaunar dashi akan gado, bathroom ta wuce direct, ruwan wanka me ɗan ɗumi, ta haɗa masa acikin bathtub, haɗe da sanya masa turaren wanka, me daɗin ƙamshi, acikin ruwan, take banɗakin ya gauraye da ƙamshi, tana fitowa daga cikin bathroom ɗin, ya kafeta da manyan idanunsa, durƙusawa tayi ta cire masa takalmi, da kuma safar dake ƙafarsa, ita da kanta tacire masa suit ɗin jikinsa, dakuma necktie ɗin dake saƙale a jikin wuyansa, Hanunta ta sanya, ta shiga ɓalle masa aninayen rigar dake jikin sa, ahankali ta zare masa rigar, shi dai haka ya tsaya, yana kallonta, yana me kuma lumshe idanunsa, lokuta zuwa lokuta, murmushine ya bayyana akan fuskarta, lokacin da idanunta, suka sauƙa akan faffaɗan chest ɗinsa, haƙiƙa yanada jiki me kyau, tasan hakan kuma, bazai rasa nasaba, da yawan gym ɗin dayakeyi ba.
Kallonsa tayi haɗe da sake sakarmasa murmushi, hanunsa ta kama daniyar janshi zuwa cikin toilet, da ƙarfi yajawo hanunnata, tafaɗa jikinsa, matseta yayi ajikinsa, haɗe da matso da fuskarsa gaf da tata.
"Ahakane zanje nayi wankan, bayan baki ciremin kaya ba?" yafaɗi maganar ƙasa ƙasa.
Cikin rashin fahimta tace.
"Wani irin kaya kuma, bayan wanda nacirema yanzu?"
Hanunta yakama, ya ɗaura akan belt ɗin dake saƙale jikin wandonsa, tsareta yayi da idanu, da'alama dai har wandon ma, so yake ita tacire masa da kanta.
Kunyan sane ya kamata, amma tasan wayon da zata masa.
"Naji zancirema, muje cikin toilet ɗin" tafaɗi haka tana nufar ƙofar toilet ɗin.
Jin abun da tace, yasanyasa, rufa mata baya, suna shiga cikin toilet ɗin tadawo baya, da sauri tafice daga cikin toilet ɗin, ta rufosa ta baya.
Dariya tashiga ƙyalƙyalawa, tana mejin daɗin wayon da tayi masa.
"I am sorry Hubby, kayi wanka kaji, banaje na kula da girkina, kada ya ƙone!" tafaɗi haka cikin muryar da ta tabbatar cewa zai jiyota.
Jin da tayi yana ƙoƙarin buɗe ƙofar toilet ɗinne, yasanya da sauri ta fice acikin ɗakin gaba ɗaya, tana dariya.
Murmushi me sauti shima yayi, kana ya girgiza kansa, waishi Zahrah zatayiwa wayo, hmmm.
Kwanciya yayi acikin bathtub ɗin , sosai yaji daɗin ruwan wankan data haɗa masa, ga ɗumi ga kuma ƙamshi me daɗi, a hankali gajiyarsa ta soma warwarewa.
Tana kammala girkin, ta zuba acikin manyan food flask, haɗe da jeresu cikin basket's masu hanu, sosai takejin, gajiya ajikinta, amma yazatayi, tunda ita tasanya kanta, duka kwanukan datayi aiki dasu, saida ta wankesu tas, kana ta gyara kitchine ɗin nata, lokaci ɗaya komai na kitchine ɗin, yadawo tsab dashi.
Tana shigowa cikin ɗakin, bata ko kalli inda yake ba, da sauri ta faɗa cikin bathroom, sam bataso ma yaganta a haka, wujiga wujiga da ita, duk ƙamshin kayan girki take, ruwan ɗumi ta tara tayi wankanta, take itama taji rabin gajiyarta, ya kama gabansa, towel ta ɗaura ajikinta, haɗe da buɗe ƙofar bathroom ɗin tafito.
Tsayawa tayi tana kallonsa, Tsaye yake agaban dressing mirror, yayi matuƙar kyau, cikin sky blue ɗin, shaddan dake jikinsa, agogo yake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa, yayinda tulin gashin kansa ke ta faƙan ƙyalli, da'alama dai yasha gyara, da man gashi, na musamman, akan fuskarsa kuwa, ƙawataccen sajensa ne, ya samu waje, ya kwanta luf akan ƙuncinsa.
"Wallahi duk wanda yace Dr.Sadeeq, bai haɗu ba yayi ƙarya" Zahrah tafaɗi haka acikin zuciyarta.
Dawo da kallonsa yayi gareta, fuskarsa ɗauke da murmushi yace. "Sannu da fitowa, Hajiyar wayo"
Itama murmushin tayi masa, haɗe da takowa zuwa garesa, hakanan ta tsinci kanta, da matuƙar son rungumesa, lokaci ɗaya ta faɗa jikinsa, haɗe da ɗaura kanta akan ƙirjinsa, shima dama nema yake, sosai ya matseta acikin jikinsa, tare da sanya hanunsa, akan bayanta, yana shafawa, a hankali, lumshe idanunsu, sukayi su duka, suna masu, sauƙe ajiyar zuciya.
"Kayi kyau sosai Hubby!" Zahrah tafaɗa cikin murya me sanyi.
"Nagode my princess!"
yabata amsa, yana me faɗaɗa, murmushin dake, kan fuskarsa, yanason Zahrah har acikin ɓargonsa, so sosai yakeyi mata, ko kaɗan baya fata Allah, Ya nuna masa, ranan dazai ɓata mata, alƙawari ya ɗaukarwa kansa, cewa Insha Allah, Bazai taɓa wulaƙanta Zahrah ba, koba komai itaɗin farincikinsa ce, sannan kuma tana da, wani irin girma, na musamman, acikin idanunsa, itace mace ta farko, daya fara sani, acikin rayuwarsa, itace macen data fara, jiyar dashi wani daɗi, wanda bai taɓa sanin akwai irin shi, acikin wannan, duniyar ba, Zahrah ta shayar dashi zumanta, wanda ɗanɗanonsa, keda wahalan mantawa, duk da cewa bai sameta, amatsayin cikakkiyar budurwa ba, amma haƙiƙa tanada wani, matsayi na musamman agareshi.
"Hubby!!"
taƙira sunansa cikin wani irin cool voice.
"Ummm princess ɗina, ya akayi ne?" yayi maganar yana me duban fuskarta.
Murmushin dake ƙara mata kyau, ako da yaushe idan tayishi, tasakar masa, haɗe da zare jikinta daga nasa, body lotion ɗinta tajawo tasoma shafawa, batare da tace da shi, komai ba.
"Na lura tunda nace miki, yau zamu fita, kike ta ɓare ɓare, kodai ma nace na fasa ne" yafaɗi haka yana me jingina kansa da bango, alamar nazari.
Da sauri ta juyo ta kalleshi.
"Dan Allah, Hubby karkace ka fasa, kaga fa har na kammala abincin!" tafaɗi haka a shagwaɓe.
Murmushi yayi haɗe da cewa "Cigaba da abun da kikeyi, wasa nake miki"
Murmushin jin daɗi tayi, haɗe da ɗaukan powder, tasoma shafawa akan fuskarta.
Batayi wani kwalliya sosai ba, janbaki da kwalli kawai ta saka, saikuma mascara, wanda sakasa yazamemata sabo, dazaran ta goga akan eye lashes ɗinta, sai kaga kamar eye lashes ɗin kanti tasanya, sosai kuma tayi kyau.
Wata haɗaɗɗiyar abaya gown, wanda aka sanya mata, acikin kayan aure, taciro ta sanya, sosai rigan ta amshi jikinta, da ɗan madaidaicin vail ɗin rigar, ta yane kanta zuwa wuyanta.
Wani flat shoe, me igiyoyi ta zura a ƙafafunta, kana ta fice zuwa falo, domin dama tuni Dr.Sadeeq ya jima, a falon yana jiranta.
Yana ganinta, ya lumshe idanunsa, yayinda murmushi ya faɗaɗa akan fuskarsa, cike da zolaya yace.
"Baƙuwa mukayi ne? sannunki da zuwa, ɗan ƙaraso ki zauna anan" ya ƙare maganar yana meyi mata, nuni da gefensa.
Dariya ne yakama Zahrah, tsayawa tayi agabansa, haɗe da ɗanyi masa fari da idanu.
"Yadai malam ko ka ƙyasa ne?" taƙare maganar tana me kama ƙugunta da duka hannayenta.
"Sosaima kuwa, gaskiya kinyimini, minti biyu please!" yafaɗi haka, yana me kashe mata idanunsa ɗaya, haɗe da ɗage giransa sama.
Dariya suka saka, su duka biyun, haɗe da miƙa masa hanu suka tafa.
Riƙe da hanun juna, suka nufi dinning area, plate ta ɗauka ta zuba musu fried cous cous, dakuma sauce egg, wani plate ɗin takuma ɗauka, ta zuba musu pepper soup, take gurin ya gauraye da ƙamshi. Harshensa yasanya ya lashe laɓɓansa, haɗe da ɗan lumshe idanunsa.
"Babe abincin nan fa zaiyi daɗi, tunkafun naci, har naji taste ɗinsa acikin bakina"
Dariya kawai tayi, haɗe da turo masa plate ɗin abincin gabansa, zama tayi akan cinyarsa, da hanunta take eban abincin, tana kaiwa bakinsa, idan tasamai abincin abaki, sai ya tsotse mata yatsunta kaf, kafun yake sakewa, ita dakanta taciyar dashi, kana itama taci, suna kammalawa ta tattara komai dake, wajen takai kitchine, fitowa tayi daga cikin kitchine ɗin, hanunta ɗauke da baskets guda biyu, aje baskets ɗin tayi akan dinning table, kallonta tamayar kansa.
"Yakamata muje ko, kaga dare fa yanata ƙarayi"
Wayarsa dake riƙe ahanunsa, yajefa acikin aljihun rigansa, haɗe da ɗaukan duka baskets, ɗin yanufi hanyar fita daga cikin falon, da sauri ta wuce cikin ɗaki, ta ɗauko hand bag ɗinta, kana ta rufa masa baya.
Saida suka hau titi, kafun ya dawo da kallonsa gareta.
"Ina zamu fara zuwane, gidan Hajiya ko kuma gidan Inna?" ya tambayeta.
"Mufara zuwa gidan Hajiya, inaga zaifi ko" tafaɗa tana kallonsa.
Kansa yajinjina, kana yaci gaba da tuƙa motar..
Yana danna horn, mai gadi ya wangale masa makeken gate ɗin gidan nasu, tura hancin motar tasa yayi zuwa cikin gidan.
Tana fitowa acikin motar, ta ɗauki ɗaya daga cikin baskets ɗin ta riƙe a hanunta, hanunsa yamiƙo alamar ta bashi basket ɗin ya ɗaukar mata.
Waro idanunta tayi, haɗe da cewa "Karufamin asiri, kabarni na ɗauki basket ɗinnan, salon nabaka, Hajiya taganka tace na mallake mata ɗa"
Dariya maganarta ta ta basa.
"Ko