Showing 63001 words to 66000 words out of 184930 words

Chapter 22 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt

09 Dec 2024

5744

ki ajiye a wajenki, ko saboda gaba, domin naga ke kuka baya baki wahala, kinga duk lokacin da kika soma koke koken ki saiki share hawayenki da shi!"


Hararan wasa ta jefesa dashi, haɗe da murguɗa masa ɗan ƙaramin bakinta.


Dariya yayi domin sarai yana lure da'ita kuma yaga abun da tayi masa.


"Inazakije kikaci uban kwalliya haka? gashi kuma kinzo kinɓata shi da kuka." Yafaɗi maganar alokacin dayake ciro wayarsa daga cikin aljihunsa.


Turo bakinta tayi gaba, cike da ƙunƙuni tasoma motsa bakinta, da'alama wani abu takeson faɗa, "wai a hakanne nayi kwalliya, kawai dai yace banyi masa kyau ba" Zahrah tafaɗi hakan a cikin zuciyarta.


"Wayace miki hakane a zuciyata? ni na'isa nace kyakkyawar ƙanwata batayi kyau ba, to ma duk cikin garin Abuja wayakai ki kyau ne? babu fa!"


Dariya tasanya, wanda tajima batayi shiba, cab aikuwa ko da acikin makarantarsu akwai waƴanda suka fita kyau dayawa, balle kuma duka garin Abujan baki ɗaya.


Tsayawa yayi yana kallon yanda take dariyan, komai tayi ƙara kyau take.


Hanunsa ya sanya acikin aljihun wandonsa haɗe da ciro wani haɗaɗɗen choculate, ɓare ledan choculate ɗin yayi haɗe da miƙo ma ta. Kyawawan idanunta ta ɗago haɗe da watsa masa su, girgiza kanta tayi, alamar bata buƙata.


Kwaɓe fuska Dr Sadeeq yayi haɗe da marairaice idanunsa, take taji tsikar jikinta ya zuba, yayinda gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, domin kuwa hakan da yayi yasanya fuskarsa ta koma yanayi da fuskar Zaid, saurin ɗauke kanta tayi daga garesa, haɗe da sauƙe idanunta ƙasa, yabuɗe baki zaiyi magana kenan wayarsa tasoma ƙara, alamar shigowar ƙira, cike da girmamawa yaɗauki ƙiran ganin cewa ƙiran daga Hajiyarsa ce.


"Kana'ina?" Hajiya tatambaya a kausashe.


Baikai ga bata amsaba taci gaba da cewa "Koma mekakeyi kabari, Inaso kaje gidansu Salima yanzu, umarni ne ba shawaraba!" ƙit takashe wayan batare da tajira taji mai zai ceba.
Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da maida kallonsa ga Zahrah.


"Wani uzuri yatasomin, zantafi kikula da kanki!" yafaɗi maganar yana me miƙewa tsaye.


Miƙewa itama Zahrah tayi batare da tace dashi komai ba tashiga naɗe tabarman da suka tashi akai.


Wani irin kallo haɗe da murmushi mai tsayawa a zuciya yayi mata, kana yasa kai yafice daga zauren gidan nasu, yana fita yafaɗa motarsa yayi mata key.


Tanajin ƙaran tashin motarsa ta sauƙe a jiyar zuciya haɗe da komawa cikin gida.


Kamar yanda mahaifiyarsa ta umarcesa hakan yayi domin kuwa yaje gidan su Salima sungana da'ita, yarinyar bata da wani aibu, amma kwata kwata jininsa danata baizo ɗaya ba, domin kuwa sam bata burgesa kasancewarta mace mai rawan kai da shegen girman kan tsiya, har gwamma masa Zabba'u akan Salima, domin dai shikam Salima batayi masa ba. Haka dai suka gaisa sama sama, ko minti 20 baiyiba yabaro gidan nasu..


Bayan Sati Ɗaya.


Kusan ko da yaushe sai Doctor Sadeeq yazo gidan su Zahrah, amma kuma tundaga wannan lokacin baisake koda ɗago wani zance makamancin wancan ba, sai dai yana'iya ƙoƙarinsa wajen bata kyakkyawan kulawa. Sannan kuma dake ita ɗin me raunin zuciya ce take ta sake bashi yardanta akaro na biyu.


Ɓangaren gidansu Dr Sadeeq kuwa harsun fara shirye shiryen bikinsa, domin kuwa Hajiyarsa wannan karon bada wasa take ba, tace acikin 3 weeks takeso ayi bikin. Shi dai Dr Sadeeq idanu kawai ya zuba musu, domin kwata kwata baijin auren a jikinsa, da za'afasa auren to dazai fi kowa murna, saboda Zahrah yakeso Zahrah ce muradinsa, amma kuma haryanzu yakasa samun wani gamsashshiyar amsa daga gareta.


Ƙarfe 3 dai dai jirginsu ya sauƙa a babban airport ɗin dake cikin garin Abuja, motoci ne iri da kala har guda shida suka zo tarbansa, ciki kuwa hadda Dad ɗinsa, a hankali yake sauƙowa daga cikin matakalar jirgin sanyen yake da kayan sanyi hadda hula, yayinda fuskarsa ke ɗauƙe da wani haɗaɗɗen baƙin glass na maza, sosai yaƙara kyau da fari, kallo ɗaya zakai masa katabbatar da cewa yakai cikekke kuma gwarzon namiji, a gaskia yana da kyau da kuma kwarjini, uwa uba kuɗaɗe sun samu mazauni a jikinsa. Bakowacce mace bace zatayi tozali da haɗaɗɗen namiji kamar Zaid, kuma takau da idanunta ba, saboda Zaid yahaɗa duk wani abu da kowacce mace zata so awajen ɗa namiji, shidai matsalan sa ɗaya munanan halaiyansa. Yanda yake tafiya cike da izza shiyafi komai ɗaukar hankali, dakuma jan hankali zuwa garesa. Cike da farinciki Alhaji Ma'aruf yarungume ɗa'nnasa, duk da cewa babu wani shaƙuwa me ƙarfi a tsakaninsu amma yana matuƙar son Zaid.
Mota ɗaya suka shiga shida Dad ɗinsa, yayinda guard ɗinsu suka mara musu baya a cikin sauran motocin. Kwanciya yayi lamo ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, wani irin sanyi yakeji acikin zuciyarsa, koda wasa baitaɓa tunanin haka zai kasance dashi ba, kamarshi Zaid ace tunanin mace yahanasa sukuni harsaida yabaro duka abun da yakeyi ya dawo zuwa gareta, amma zaiyi maganin abun a yau bawai sai gobe ba yake da buƙatar ganin sugar baby'nsa, sai dai kuma wannan lokacin bada wasa yazo ba...


Zahrah ne keta kai kawo a tsakiyar ɗakinta, tabbas tayarda da duk wani shawara da zuciyarta ta bata, zuwa yanzu yakamata ace tayi abunda ya dace. Wayarta ne yasoma ƙara alamar shigowar ƙira, tana ɗaga wayar Dr Sadeeq yace "Gani na'iso ina ƙofar gida!"


"To" tace haɗe da aje wayar, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗi da cije lips ɗinta, dama ɗaya kawai take dashi kuma tabbas idan tarasa wannan daman to zaiyi mata wahala tasake samun wani daman.


Hijib ɗinta ta sanya, koda tafito tsakar gida bata taradda Inna ba tana kuma da tabbacin cewa bama ta gidan.


Zaune yake acikin motar tasa, dagani kasan cewa yana cikin damuwa, domin gaba ɗaya har rama tasoma bayyana a jikinsa. Murfin motar tabuɗe tashiga, bakinta ɗauke da sallama, amsa mata sallaman nata yayi haɗe da gyara zamansa yafuskance ta " Baki taɓa min irin wannan ƙiran ba, naƙosa naji wace maganace zaki faɗamin mai matuƙar mahimmanci haka" gaba ɗaya hankalinsa ya tattara zuwa gareta.


"Dagaske kake Zaka aure ni?" Zahrah tajefo masa tambayar
dabai taɓa zata ba balle tsammani.


Kansa yashiga kaɗawa muryarsa har rawa take yace "Dagaske nake Zahrah, wallahi auren ki nakeso nayi, samunki a matsayin mata shine babban burina a yanzu." yafaɗi hakan da iya gaskiya'rsa


"So na kakeyi kokuma tausayina?" Zahrah takuma jifansa da wata tambayar.


"Sonki nake Zahrah, inamiki so mai tsanani, wlh inasonki da duka zuciyata!" Dr Sadeeq yabata amsa, cike da kulawa.


"Nayarda na Amince Zan aureka, muyi zama na har abada!" Abun da yafito daga bakin Zahrah kenan bayan tagamajin amsar da take buƙata daga garesa, cikin tsananin mamaki Dr Sadeeq yashiga kallonta, jin sauƙar maganarta yayi tamkar daga sama, kodai kunnuwan sa basu jiye masa dakyau bane?....


(To fa readers Ga Baba Zaidu yashigo Gari, ga kuma Zahrah ta amince da auren Dr Sadeeq, gashi kuma ɓangaren gidansu Dr anatashirye shiryen bikin Dr da Salima, koya zata kaya 🤷‍♀, please kusani a addu'anku wlh cikina ke ciwo sosai😥 idan kunga typing eror kuyi haƙuri gaba ɗaya banda wata isashshen nutsuwa ne 😭)


*10/December/2019*


*Voted,Comment,and Share please.... Follow me on Wattpad @fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI!!*



*Written by*
*Phatymasardauna*


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*


'''{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & mitivate the mind of readers}'''


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*



*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


*(This page is Dedicated to you HAROUN UMAR (H Umar) admin of 📖✍️BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION, inajinjinamawa ƙoƙarinka ako da yaushe haroun, kuma inagodia a gareka marar iyaka.)*


*CHAPTER 53 to 54*


Kasa motsa koda laɓɓansa yayi balle har yakai ga furta wata kalman, "dagaske ne abun da kunnuwansa suka jiye masa kokuwa mafarki yake?" yafaɗi hakan a cikin zuciyarsa.


"Kada kayi kokonto kokuma shakka, dagaske nake, na amince da aurenka, amma ina mai roƙon wata alfarma a gareka"...."Dan Allah kada ka wulaƙantani aduk yanda kasameni, kada kuma ka tozartani, nasan cewa tausayina yafi yawa acikin zuciyarka fiye da soyayya ta, saboda haka ina da tabbacin cewa ko gaba zaka iya sake samun wata mace,wacce itace zata kasance zaɓinka, kada haka yasa ka wulaƙantani dan Allah, kada kuma kacutar da rayuwata!" cikin sanyin murya ta ƙare maganarta ta, yayinda hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta,suna sauƙa akan ƙuncinta.


Jiyayi gaba ɗaya wani irin matsanancin farinciki ya lulluɓesa, gani yake tamkar wasa Zahrah take masa, amma kuma ba'abun mamaki bane, saboda babu abun da yagagari Allah.


"Bansan ta'ina kokuma tayaya zan fara godemiki ba Zahrah, kin gusarmin da duk wata damuwa dake damuna, kinbani farinciki cikin ƴan mintuna ƙalilan, kiyarda dani Zahrah, inamiki Soyayyace ta gaskiya bawai, irin soyayyarnan tako oho ba, zan'iya sadaukar da duk wani abu nawa akanki Zahrah, soyayyar da nake miki, yasanya bana ganin laifi ko kuma aibun duk wani abun da kikamin, burina da fatana shine murayu tare dani dake amatsayin miji da mata, kuma aƙarƙashin inuwa ɗaya, Inasonki Zahrah, kuma namiki alƙawari komai wuya komai tsanani bazan taɓa gujemiki ba, ZANRAYU DAKE Zahrah!!" Dr Sadeeq yafaɗa cike da matsanancin farinciki, jiyake tamkar yajawo Zahrah jikinsa yabata kyakkyawan runguma.


Kuka Zahrah ta fashe dashi, wanda batasan dalilin yinsaba, ita ta amincewa kanta cewa zata auri Dr Sadeeq amma saitakeji tamkar dole tayimawa kanta.


Batayi zato ba saiji tayi Dr Sadeeq yajawota jikinsa haɗe da sanya hannayensa duka biyu ya rungumeta. "Inasonki Zahrah, kuma nayi maki alƙawarin bazantaɓa wulaƙanta ki ba har'abada, kidaina kuka kinji princess ɗina!" yaƙare maganar tasa cikin sigar lallashi.


Daddaɗan ƙamshinsa shiyaso birkita mata tunani don haka tayi saurin janyewa daga jikinsa, tana mai yin ƙasa da kanta.


Sam shikam ma yamanta da cewa hakan da yayi ba'abu bane mai kyau, gaba ɗaya murna yacika masa zuciya.


"Uh sorry baby, gaba ɗaya kece kikamantar dani komai!!" Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai dafe goshinsa.


Ƙasa ƙasa Zahrah tayi murmushi haɗe da kawar da kanta gefe, hakanan taji wani irin nauyin Dr Sadeeq ɗin yaƙaru acikin zuciyarta, haka kuma yaƙara girma acikin idanunta.


Wani irin kallo Dr Sadeeq yashiga yimawa Zahrah duk dacewa takau da kanta gefe, sai yanzu nema yake ƙara ganin haɗuwarta fiye da da, tabbas da Zahrah bata amince dashi ba to da ya tabka babban rashi, domin kuwa Zahrah tahaɗu, macece ita da kowanni Namiji zaiyi fatan mallaka.


Sam batayi tunanin kallonta yake ba, don haka taɗan juyo dan itama ta saci kallonsa, aikuwa karab idanunsu suka sauƙa akan najuna, da sauri Zahrah tayi ƙasa da kanta haɗe da cusa fuskarta tsakan kanun cinyoyinta.


Dariya Dr Sadeeq yayi cike da shauƙi haɗe da shafa sajen dake kwance akan fuskarsa. "Yaushe kika farajin kunyana? lallai zamu ɓata idan harkinajin kunyana!" ya faɗi hakan cike da zolaya.


Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba, haɗe da marairaice fuska cike da shagwaɓa tace "To bakaine kaketa kallo na ba, saikace baka sanni ba!"


Lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu a lokaci guda, irin wannan salon shagwaɓan ai saita sashi bacci batare da yashiryawa hakan ba,lol.


"Ki faɗamin laifi ne don nakalli abar sona? saidai kiyi haƙuri amma kallonki yanzuma na fara, tunda kinamin kyau, kina kuma burgeni!" yanayin yanda yayi maganar abun burgewa ne, ga macen da tasan daɗin soyayya.


"Nidai kada ka wani ce inada kyau, daɗin bakine kawai nasan kakemin!" still da yanayin shagwaɓa tayi maganan.


Lumshe idanunsa yayi haɗe da fitar da iskan numfashi daga bakinsa, yanayin shagwaɓan Zahrah yafi komai burgesa a tattare da'ita, haka kuma sosai yake sauƙar masa da kasala. "Princess!!" yaƙira sunanta dawani irin murya mai taɓa zuciya.


A hankali ta ɗago idanunta ta kallesa, batare da ta amsa masa ba, ganin idanunsa a rufe, yasanya taɗan tsaya ƙaremawa fuskarsa kallo. "Duk kallona ɗaya da zaki yi bazai tafi a banza ba, sai kin biya kuɗi, gwamma ma kisani!" Dr Sadeeq yafaɗi haka batare da ya buɗe idanunsa ba.
Saurin ɗauke kanta tayi daga kallonsa haɗe da cewa "Niba kallonka nake ba"


"Zaki iya rantsewa cewa bani kike kallo ba?" yaje fo mata tambayar da batayi zato ba.


kanta tashiga girgizawa haɗe da cewa "Ai bankalleka sosai ba, kaɗan nakalleka!"


Dariya Dr Sadeeq yasanya wanda harsaida dimple ɗinsa suka bayyana, yanzu yayarda cewa Zahrah yarinyace ƙarama, kuma zakayi saurin kamata idan tamaka laifi.


Ƙoƙarin buɗe murfin motar Zahrah tasomayi, cikin mamaki Dr yace "ina zaki?"


"Zankoma gida ne, dama magana zan faɗa ma, shiyasa na ƙiraka, kuma nafaɗa ma, inada karatu, gobe muna da test a makaranta" Zahrah tafaɗi hakan dai dai lokacin da ta gama sanya ƙafafunta waje.


"Shikenan to My Princess kikulamin da kanki kinji, inasonki sosai!" Dr Sadeeq yafaɗa cike da kulawa.


Wani irin muguwar kunyarsace takama Zahrah, bashiri ta wuce cikin gida tana mai rufe fuskanta da tafukan hanunta.


Shima Dr ɗin murmushi yayi cike da jindaɗi, lallai idan ya auri Zahrah yakasance mutum mai sa'a, acikin satinnan insha Allah, zai sanarda ƙanin mahaifinsa azo a nemamasa auren Zahrah, a wajen Baffa.


"Aurenka da Salima fa?" Wata zuciyar ta jefo masa wannan tambayar, wani irin bugawa yaji ƙirjinsa yayi, gaba ɗaya amincewa dashi da Zahrah tayi yasanyashi manta halin da yake ciki na batun auren sa da Salima. Jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, tabbas akwai ƙalubale a gabansa, domin kuwa yanada tabbacin cewa Hajiyarsa bazata taɓa sanja maganarta ba, gashi har ansoma shirye shiryen bikinsa da Salima, kuma shi a tsarinsa bai sha'awar auren mata biyu, Zahrah ita kaɗai ta'ishesa rayuwa, amma kuma tabbas yasan zai fuskanci matsaloli da yawa daga ƴan uwansa, matuƙar ya jajirce akan cewa Zahrah yakeso ba Salima ba, to amma dole zai jarraba sa'ansa, domin a gaskiya baijin cewa zai'iya haƙura da Zahrah.
Cike da sanyin jiki yayimawa motar tasa key, haɗe da nausawa kan titi.


Suna isa katafaren gidannasu, adai dai parking space motar tasu ta tsaya.


Bawani jinkiri Zaid yabuɗe murfin motar yafito, batare da yatsaya sauraran Mahaifinnasa ba, yanufi ɓangarensa kai tsaye.


Komai dake cikin ɓangaren nasa a gyare yake tsab, tamkar akwai wani wanda ke rayuwa a cikinsa, hakan kuma yasamo asaline da yawan gyara part ɗin da akeyi duk bayan kwana biyu, kasancewar Zaid mutum ne da bayason ƙazanta.


Direct bedroom ɗinsa yanufa, yanashiga yasoma rage kayan dake jikinsa, rigan wanka irin na maza mai gashi gashi a jiki yasanya, haɗe da sanya badroom slippers a ƙafafunsa, kai tsaye wajen fridge ɗin dake aje cikin ɗakin yanufa, maltina can yaciro haɗe da ɓalle ɗan ƙarfen da aka rufe bakin can ɗin dashi, yakai bakinsa, tunda yakai maltina can ɗin nan bakinsa bai ɗauke ba harsaida yatabbatar da cewa bakomai ciki ya shanye, cikin dustbin ɗin dake aje a ɗakin ya jefa can ɗin. Bathroom ya wuce haɗe da sakarmawa kansa shower. Wanka yakeyi amma gaba ɗaya tunaninsa baya garesa, yanaga shugar baby'nsa, amatuƙar matse yake da sha'awarta, haryanajin bazai iya daurewa yakai zuwa wani ɗan lokaci mai tsawo batare da'ita ba.


Bayan yafito a wanka yashiga shirya kansa cikin, haɗaɗɗun riga da wando masu kyau da tsadar gaske, gaskia komai na Zaid me kyau ne, domin kuwa kowani kaya yasanya saiya yi kyau, bakuma kayanne yake masa kyauba, shi ɗin kansa ne yake mawa kayan kyau,lol.


Haɗaɗɗen takalminsa sau ciki ƙiran kamfanin Gucci yasanya, aƙafansa, bayan ya ɗaura tsadadden agogon nan na Rolex a hanunsa mai kyau da burgewa. Daddaɗan ƙamshi ne kawai ke fita daga jikin shi, ƙamshine mai wahalar mantawa.


Black facing cap, yasanya akansa, domin kuwa yanayin garin ana ɗan busa sanyi, duk dakuwa cewa daga cikin sanyin yafito.
Wayarsa yaɗauka haɗe da car key ɗinsa, kai tsaye yafice daga cikin ɗakinnasa. Ɓangaren Mom ɗinsa yanufa. Hajiya Safara'u ne tsaye a gaban ƙatoton teburin cin abinci, yayinda Alhaji Ma'aruf ke zaune tana serving ɗinsa, batasan da shigowarsa ba saiji tayi ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗarta, cike da soyayyar mahaifiyarta sa yace "Barka da gida Momy!"


Cike da tsananin farinciki itama ta rungumesa haɗe da basa sumba a kan kumatunsa, "Barkanka da dawowa my son, ya gajiyar hanyar?"


"Alhmdlh!" Zaid yafaɗa a taƙaice, bayan ya janye jikinsa daga na mahaifiyartasa. Ƙoƙarin juyawa yakeyi, Mom tace "Inakuma zaka my son ba abinci kazo ciba?" cike da kulawa ta tambayesa.


Ɗan ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa "Banajin yunwa Mom, idan nadawo zanci!" baijira jin maizasu ceba yasakai yafice daga cikin falon.


Da kallo kawai Mom tabisa har yafice, fuskarta ɗauke da damuwa, itakam ta rasa wani irin haline da Zaid, sam ba'a iya gane gabansa da bayansa.


"Miye abun shiga damuwa Hajiya Safara'u? zuwa yanzu yakamata ace duk wani hali na yaronnan Zaid kin gama saninsa!" Alhaji Ma'aruf yafaɗi hakan cike da nuna kulawa ga matar tasa.


"Nasan halinsa Alhaji, amma kuma ace mutum shi baya taɓa sanjawa, ko da yaushe fa Zaid bayason zama a cikin mu, sannan kuma sam baya sakewa damu!" Mom tafaɗi hakan cike da damuwa.


"Zauna muci abincin mu, aishi ba ƙaramin yaro bane, yasan me yakeyi!" Alhaji Ma'aruf yafaɗi hakan yana mai kama hanun Mom yazaunar da'ita a kusa dashi.


Zaid kuwa yana fita daga ɓangaren mahaifiyartasa, kai tsaye wajen motarsa yanufa, koda driver yanemi da yabarsa ya tuƙasa, ɗaga masa hanu yayi alamar baya buƙata, shida kansa yayimawa motar key, ya harbata zuwa kan titi.


Tafiya yake cikin nutsuwa yayinda airpiece ke saƙale a kunnuwansa, wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ganin cewa babban manager'n company'nsa dake nan gida Nigeria ne ke ƙiransa yasanya shi ɗaga ƙiran. Banji mai Manager'n nasa yace masa ba, sai gani nayi ya'aje wayan, haɗe da buga dogon tsaki, lokaci ɗaya yakarkata akalar motar tasa zuwa wata hanya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login