Showing 54001 words to 57000 words out of 184930 words
Chapter 19 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt
da amsar kayan, sarai tasan Husnah bata da haƙurin yunwa ko kaɗan.
Ice cream kawai Zahrah tasha, yayinda Husnah kuwa ta cika cikinta da shinkafa. Yau darasi biyu garesu kacal, don haka suna fitowa kowa ya yi ƙoƙarin kama gabansa.
Waige waige tashiga yi ko zata hangosa, amma babu alamar komai irin motarsa, wayarta ce ta soma ƙara alamar shigowar ƙira, Number ne ke yawo a kan screen ɗin wayar babu suna, dama kuma batayi tunanin Numbern zai fito da suna ba, domin batayi saving numbern kowa ba, wama ta sani da zatayi saving number'nsa.
Har saida wayar ta kusa katsayewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran, "Zahrah! na gaji, da yawa, aiki yamin yawa, please ga nan driver na, zaizo ya ɗaukeki ya kaiki gida, kiyi haƙuri kinji ƙanwata!!" Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin kwantar da murya, da gajin yanda muryansa take fita slow kasan cewa a matuƙar gajiye yake.
A jiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa "Shikenan kahuta lafiya"
"Yauwa Ƴan mata na, ki kulamin da kanki" ƙit ya kashe wayar, ba tare da ya tsaya ya saurari mai zata ce ba.
Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da girgiza kanta, "Hmm wai itace ƴan mata, itakam yanzu ai ta wuce a ƙirata ƴan mata saidai sauran Zaid" tafaɗi hakan a zuciyarta, take kuma taji idanunta sun kawo ruwa. Dai dai lokacin motar Dr Sadeeq ta ƙaraso inda take tsaye, kasan cewar yayi mata bayanin cewa driver'n sane zaizo ɗaukarta, dan haka batayi wani jinkiri ba, ta buɗe murfin motar tashiga, ko kallon inda driver'n yake batayi ba, "ZAHRAH!" muryan Dr Sadeeq ya daki dodon kunnuwanta, saurin maida kallonta inda taji muryan tayi, ai kuwa shiɗinne kwance a jikin kujeran gidan baya, idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da ɗage giransa ɗaya sama, "Surprise!" yafaɗa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Murmushi itama tayi masa, haɗe dayin ƙasa da kanta, domin yanayin yanda yayi mata maganan, yasanya taji jikinta yayi sanyi.
"Dawo nan muzauna, ki bar driver yayi aikinshi"
Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da turo baki gaba, cike da shagwaɓa tace "Ni dai kabarni na zauna anan ɗin ma yayi!"
"Nace ki dawo nan muzauna ko!" yafaɗi hakan babu alamar wasa akan fuskarsa.
Cike da sakalci Zahrah ta dawo gidan baya inda yake zaune, ko kallonsa batayi ba saima langwaɓewa da tayi a jikin kujera. Har sukayi nisa a tafiyan babu wanda yace da ɗan uwansa ƙala, cikin shagwaɓa tace "Bakace min aiki yamaka yawa ba, amma mai yasa kazo?"
"Saboda ya cancanta nazo, ina da burin baki kyakkyawan kulawa a ko da yaushe, ko bakiyi farinciki da hakan ba?"
"Nayi farinciki sosai!" Zahrah tafaɗa kai tsaye, domin kuwa sam batason irin kallon da yake yawan yi mata a wasu lokutan.
Baisake ce da ita komai ba, shima sai ma komawa da yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran motar.
A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah'n, kallo ɗaya tayi masa haɗe da buɗe murfin motar tayi ficewarta, yana ganin shigewarta gida, yace driver ya ta da motar suje.
Bayan Sati Biyu....
Wani irin shaƙuwa ne mai ƙarfi yashiga tsakanin Doctor Sadeeq da Zahrah, kullum shi ke kaita mkaranta shi kuma ke ɗauko ta, sosai yake bata kulawa, baya son duk wani abu da zai ɓata ranta, ko ya sanya taji ba daɗi, ɓangaren Zahrah ma, sosai take kiyayewa dashi, tana iya ƙoƙari wajen ganin bata musa masa idan ya umarceta da tayi abu, ko kaɗan batajin wani abu a dangane dashi, tana dai yi masa biyayya tana kuma ganin girmansa, domin kamar yanda yace ta ɗaukesa, a matsayin ɗan uwa, to a matsayin ɗan uwan ta ɗaukesa, domin kallon yaya take masa, sannan kuma sosai wayarta take ɗe be mata kewa, yakanyi ƙoƙari wajen ganin ya ƙirata a waya, a kowani dare, sai dai hiran tasu bata tsayi suke sallama da juna, sosai rayuwarta tasamu canji, bakamar da ba, duk da cewa abune mawuyaci manta abun da ya faru da'ita, amma takanyi ƙoƙari ƙwarai wajen ganin ta gusar da duk wani damuwarta.
Tsaye yake a gaban tangamemen dressing mirror ɗin dake kafe a jikin bangon ɗakin nasa, yayi kyau sosai cikin riga da wandon shadda dake jikinsa, ba abun da jikinsa keyi banda tashin ƙamshi, hannayensa duka yazura a cikin aljihun wandon shaddan dake jikinsa, tabbas a kwai wani al'amari mai girma dake cikin zuciyarsa, haƙiƙa kuma akwai abun da yakeso ya furta,amma tayaya, baisan da wani manufa zata ɗauki zancen ba, baisan wani amsa zaiji daga bakinta ba, wannan shiya hanasa furta mata tsadaddan kalman dayake ta ɓoyewa tsawon lokuta, bayajin zai samu abun da yakeso daga gareta, bakuma yajin zai samu amincewarta, ya tabbatarwa kansa cewa, a yanzu lallashi take buƙata fiye da komai, sannan kuma bata buƙatar wata magana wanda zata zamo sanadiyar rugujewar ɗan farincikin da ta soma samu, sai zuciyar sa ta ƙarfafa masa guiwa, saikuma gangar jikinsa tayi sanyi laƙwas.
"Ba'asan jarumin Namiji da tsoro ba!" wata zuciyarsa ta furta masa hakan.
Ƙwarai ya yarda da cewa shi ɗin jarumi ne, amma kuma gurin da yake da muradin isar da saƙonnasa wajene mai rauni, dole zai fuskanci ƙalubale guda biyu, rashin nasara, ko kuma, yin nasara, wayarsa ya ɗauka ya sanya a cikin aljihunsa, kai tsaye ya fice daga cikin ɗakin nasa, yana shiga cikin motarsa ya bata wuta, kai tsaye unguwar su Zahrah ya nufa, sosai ya yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa, lallai yazama dole ya bayyana mata sirrin dake kwance cikin zuciyarsa, sai dai yasan balallai ta aminta da ƙuɗirinsa ba, amma zai jarraba ya gani.
A ƙofar gidansu yayi parking motarsa, haɗe da ciro wayarsa, ya danna wa Number'n Zahrah ƙira, sai dai harzuwa lokacin zuciyarsa fat fat haka take bugawa. tana ɗaga wayar yace "Ina ƙofar gidanku, dan Allah kizo ki sameni" banji mai tace masa ba, sai gani nayi ya mai da wayar tasa cikin aljihunsa, haɗe da sauke nannauyar ajiyar zuciya....
(Tofa readers, mai kuke ganin Doctor Sadeeq zai faɗawa Zahrah, da haryakejin tsoron faɗa mata, sbd baisan daya zata ɗauki maganar ba, to zadai muji kome nene a next page insha Allah! Ko ina Baba Zaidu kuma 🤷♀)
*3/December/2019*
*Voted,Comment, and Share please..... Follow me on Whatsapp and Wattpad @fatymasardauna

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother Khabier*
*🌈Kainuwa Writers Association*
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
(😂Yasin bansan haka Baba Zaidu yake da masoya ba sai kwana biyu da bana taɓo sa, ashe dai masoyan Zaid sunfi maƙiyansa yawa, kusha kurumin ku mutanen Zaidu yau zan taɓo muku chapter'n shi, su Munubia nasan anyi missing 🤣)
*Chapter 46 to 47*
Tana aje wayan ta ɗauko wani rover hijab ɗinta ta sanya a jikinta, koda tafito daga cikin ɗakin nata, zaune ta iske Baffa da Inna, a tsakar gida, domin dai dama dare yasoma rufawa, cike da ladabi tace " Baffa Doctor Sadeeq yana ƙirana a waje"
Gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa " to naji ƙaran tsayuwar mota ai, ashe dai likitane yazo, to adawo lafiya"
Muguwar harara Inna ta jefamawa Zahrah, cike da masifa tace "Wato ni banza bankai matsayin da zaki tambayeni ba ko? wato Baffanki kaɗai kika gani a wajen?"
Cikin sanyin murya Zahrah tace "Kiyi haƙuri Inna, naga shi ya kamata na sanarmawa hakanne, tunda ya na nan!"
"Wuce kije ƙiran da yake miki kinji Zahrah'u, barta Salame yau masifa take ji dashi" Baffa yaƙare maganar yana mai wurgamawa Inna harara.
Bata kuma sauraran abun da Inna zatace ba tasakai tayi ficewarta daga cikin gidan..
Duk da cewa babu wadataccen haske a wajen, amma tana iya hango kyawun da kayan jikinsa sukai masa, "gaskiya Dr kyakkyawane shima" tafaɗi hakan a cikin zuciyarta.
Da sallama ɗauke a bakinta ta ƙaraso inda yake tsaye, cike da fari'a Dr ya amsa mata sallaman da tayi haɗe da cewa "Wato sai anjamin aji kafun a fito ko?"
Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa "Bawani batun jan aji, ni a hakan ma inaganin na fito da wuri"
Shima murmushin yayi haɗe da cewa "Kinyi kyau!"
Still murmushi tayi, cikin son kawar da zancen da yayi na cewa tayi kyau, tace "Lafiya kuwa naganka a dai-dai wannan lokacin?"
Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da maida nutsuwarsa gareta "Maganar danazo miki da'ita Zahrah bata tsaye bace, yana da kyau mushiga mota, sai mu tattauna ko?"
Ɗan jim Zahrah tayi, haɗe da cije lips ɗinta, "Shikenan amma inafatan bazamu jimaba, kafasan banson fitowa waje da dare"
"Insha Allah, bazamu ɗau tsawon lokaci muna magana ba!" Dr yafaɗi hakan lokacin da yayimawa kansa masauƙi a cikin motar tasa, bayan ya kunna ƙoyin wutar dake cikin motar take haske ya gauraye cikin motar.
Gyara zama Zahrah tayi, haɗe da tattaro duka nutsuwarta "Inajinka" tafaɗa a taƙaice.
Wani irin numfashi Dr yayi, haɗe da fitar da iska daga bakinsa, sai yanzu yakejin cewa, bazai iya furta abun da yakawosa ba, gaskiya yanajin nauyi, baisan tayaya Zahrah zata karɓi muradinsa ba, kada maganar da zaifaɗa ma ta yazamo sanadiyar rugujewar nishaɗin da yake gani akan fuskarta yanzu, "Ta'ina zanfara?" ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
"Lafiya kuwa, naga kayi shiru?"
Zahrah ta tambaya, cike da mamakin yanda yayi shiru, bayan yace akwai maganar da zasuyi.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗi da maida kallonsa gareta, saida ya tattaro nutsuwarsa kafun yace...
"Yazakiji idan wani yazo miki da batun soyayya a wannan lokacin Zahrah?" abun da ya iya fitowa daga bakinsa kenan, domin a gaskia shikam yarasa ta'ina zai fara.
"So kuma? wani irin so?" Zahrah ta tambaye shi cike da mamakin kalaman nasa.
"So na Aure Zahrah!" yafaɗi maganar cikin ɗar ɗar.
"Au..r..e.. Kuma Likita? Aure fa kace, dama akwai wani wanda, zaiji kwaɗayi da sha'awar aure na ne? hmmm a gaskia bana tunanin haka, domin kuwa babu wani wanda zai so ni da rayuwata, a yanda nake ɗinnan!" Zahrah tafaɗi hakan da'iya ka gaskiyar ta.
"Kada kice haka Zahrah, akwai mata masu rauni da yawa irin ki, amma an auresu, kuma anzauna dasu, ke me yasa zaki yanke ƙauna da...."
"Dan Allah kadaina min wannan zancen Doctor, banjin zan sake son wani ɗa namiji a duniyar nan"
Zahrah ta katse shi da ga maganar da yakeyi, ci gaba tayi da cewa
"taya kake tunanin zansake kai kaina tarkon da ya ruguzamin rayuwa, shi So ɗin dakake faɗa yanzu, shine ya ruguzamin rayuwa ta, ya rabani da duk wani farinciki na rayuwata, shin idan kace min na sakeyin So, kamin adalci kenan? " Tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.
"Kada kice haka Zahrah, kefa musulmace, kuma ke mace ce, nasan kina da sanin cewa, kyautatuwar rayuwar ƴa mace shine aure, haka kuma rayuwar ƴa mace bata cika hundred percent sai da aure, haka kikeso ki ƙare rayuwarki ba aure? ko kin manta cewa cikar mutumcin mace shine a ganta gidan mijinta? yin Aure shine burin kowacce mace ta ƙwarai, nasan kema wannan shine burinki, kada shaiɗan yayi amfani da abun da yafaru dake, ya ruguza miki rayuwa, ya hanaki aikata sunna!"
"Hakan shine burina amma ada, wa zai aureni a yanzu? waye zai ɗaukawa kansa duhu? waye zai ɗauki sauran da wani yaci ya rage, sauran da wani ya tarwatsa, ya zuba ƙazantarsa, acikin cikinta, waye zaiyi hakan? bazan yaudari kaina ba, nasan babu wani wanda zai aureni a yanda nake, bantaɓa aure ba, amma kuma niba budurwa bace a yanzun, ya cuceni yariga ya karɓe abun da nake burin bawa mijina na sunna, waye zai yarda da haka?"
"Nine nan Zahrah, Nasan komai a kan ki, kuma zanyarda da duk wata ƙaddaranki, nine wanda zan sharemiki hawayenki, kece damuwata bawai budurcin kiba, kiyarda dani dan Allah!!" Doctor Sadeeq yafaɗi hakan cikin jajircewa..
Kamar sauƙan aradu haka Zahrah taji sauƙan kalamansa a cikin kunnuwanta, cak ta tsaida kukan da takeyi haɗe da, da hangame baki tana kallonsa, gani take kamar ma baya cikin hayyacinsa, ƙaryane tayaya za'ace Namiji mai aji, kamar Doctor yace wai ya amince da ƙaddaranta zai aureta, wannan ba gaskia bane,
"Kada kiyi shakka ko kokonto, ba yaudara'nki nake ba, dagaske nake har cikin zuciyata, don Allah ki bani dama Zahrah, burina da fatana kawai ki amince min!"
Kai Zahrah ta shiga girgizawa, cikin tsananin ɓacin rai da danasin sauraransa da tayi tasoma cewa " Nayi Babban kuskure, haka kuma na tabka nadaman baka daman shigowa rayuwata da nayi, ashe dukanku haka halinku yake, macutane ku azzalumai, ashe bazaku taɓa sanjawa ba, dama ɗaya kawai idan aka baku, sai ku nemi shigo da manufarku, kaicona da abun da Zaid yayi mini baikasance IZNAH ga rayuwata ba, kaicona dana sake aminta da kai, kaicon zuciyata, kafita a rayuwata dan Allah, kaje banaso nasake ganinka ko kuma jinka, katafi kayi nisa da ni, kabarni na rayu cikin salama dan Allah!!" gaba ɗaya hawayen ɓacin rai yagama wanke mata fuska, ƙoƙarin fita daga motar ta somayi, cike da tashin hankali Doctor Sadeeq ya riƙo hanunta, ko kaɗan baiyi zato ko tsammani ba, saijin sauƙar mari yayi akan kumatunsa, Zahrah ce ta ɗaukesa da lafiyayyen mari, babu abun da ke kwance akan fuskarta banda tsananin ɓacin rai,
"Koda wasa kada kasake ƙoƙarin taɓani, mayaudari, dama haka kuke bakuma zaku canza ba!!" fuuuuu haka Zahrah tafice daga cikin motar tamkar kububuwa.
Tamkar statue haka Dr Sadeeq ya tsaya, komai nasa daina aiki yayi, sai numfashinsa dake fita da sauri, ganin komai yake tamkar al'amara, wai yau shine Zahrah ta mara da hanunta, a hankali yasanya hanunsa ya shafi kan kumatunsa inda Zahrah ta wankesa da mari, ko kaɗan baiga laifin Zahrah ba, kuma baiji zafin marin da ta masa ba, babban damuwarsa da tashin hankalinsa, shine yanda yaga Zahrah tana kuka wiwi, sannan kuma ranta yayi matuƙar ɓaci, tabbas da yasan abun zai ɓaci har haka, to da baiyi gigin furta mata kalmar cewa zai aure ta ba, ko da na minti ɗaya ne bayason ɓacin ran Zahrah, yanzu yasan haka zata kwana tana kuka, maiyasa? maiyasa na kasa jurewa? ni nake burin faranta rayuwa da zuciyarta, amma sai gashi da kaina nasake ruguza farinciki'nta maiyasa? yatambayi kansa da ƙarfi, cike da haushin kansa ya sanya hanunsa duka biyu ya daki siterin motar tasa, wani irin haushin kansa yakeji, yayi dana sanin sanar da'ita abun dake cikin zuciyarsa, "mai yasa na yarda nazamo LOSER?" ya tambayi kansa cikin ƙunan zuciya, yakusan 10 minute yana zaune a cikin motar, da ƙyar ya'iya tada motar yabar cikin unguwar tasu...
Zahrah kuwa tana shiga gida, kaitsaye ɗakinta ta wuce, zamewa tayi a ƙasa, tashiga rera sabon kuka, lallai tayarda cewa Ƙaddaranta mai girma ce, daga wannan sai wannan, bata taɓa zato ko tunani'n haka zai fito daga bakin Dr Sadeeq ba, ko da wasa bata taɓa ayyana wani abu a ranta ga me da shi ba, maiyasa zai zo mata da wannan maganar a daidai wannan lokacin? maiyasa zai sake maida ita uƙubar da tayi nasaran samun bakin fita daga cikinsa? tabbas yanzu kam tayarda cewa duhu yasamu mazauni a cikin rayuwarta
"Bawanda zai soni a haka, shima nasan ba sona yake ba, wata manufarsa kawai yakeson cimmawa, ashe ƙaddarorina suna da yawa?" ta tambayi kanta cike da ruɗu.
Sanin bata da amsar bawa kanta, yasanya ta cigaba da kukanta, ganin hakan bazai fishsheta ba yasanya ta ɗauro alwala tazo ta fara gabatar da salla, haɗe da miƙamawa mai kowa mai komai duka lamuranta...
Koda Doctor ya isa gida, baije koda ɓangaren mahaifiyarsa bane, kai tsaye ɓangarensa ya nufa, gaba ɗaya jiyakeyi duniyar ta masa ƙunci, saboda cimma muradinsa yasake sanya Zahrah a damuwa, kwanciya yayi lamo akan gado, zuciyarsa cike da tarin tunanuka kala kala, gaba ɗaya kalamanta ne suke yawo a ƙwaƙwalwarsa, babu kalman da tafi tsaya masa a rai kamar inda takecewa " Natabka nadamar baka daman shigowa rayuwata da nayi, katafi ba naso na sake ganinka ko kuma jinka!!" wannan kalamannata sunfi komai ɗaga masa hankali, sam shikam ya ma manta da marin da tayi masa, saboda bai ɗauki marin a matsayin komaiba, shidai shiga damuwarta ne bayaso, baisan wani irin so yake mawa Zahrah ba, bayason ganinta a cikin damuwa, ba kuma yason ɓacin ranta, amma tayaya Zahrah zata fuskancin hakan? Yanaso ya aureta yakuma inganta rayuwarta, ba budurci'nta bane abun so a gareshi ita kanta ce abarsonsa, haƙiƙa kowani namiji yana burin auren mace yasameta a budurwa, shima kuma yana burin hakan, amma son da yakemawa Zahrah, yasanya zai iya karɓanta a yanda take.. Haka Doctor yayita saƙawa da kuncewa, da ƙyar bacci ɓarawo yayi nasaran ɗaukarsa.
Ɓangaren Zahrah ma dai hakanne takasance da ƙyar ta'iya runtsawa a wannan dare....
*TURKEY*
*ZAID* ne zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera, sanye yake da riga long slive, white colour yayinda wandon jikinsa ya kasance baƙi, suit ne baƙi ɗaure a saman kayan nasa, sosai yayi kyu a cikin shigartasa, hanunsa riƙe yake da wani dogon kofi na glass, bakomai ne acikin kofin ba face giya, a hankali yake sipping giyar tasa, yayinda ya ɗaura ƙafansa ɗaya kan ɗaya, gefensa kuwa Abid ne zaune shima dai irin shigar Zaid ɗinne a jikinsa, sai dai shi nasa kalan sun kasance blue, "Lokaci fa yana tafiya Zaid, yakamata ace yau munkoma New York, amma bansan dalilinka nacewa muzauna anan ba, ni fa duk yanda instanbul takai ga haɗuwa da daɗin zama, batakaimin new york