Showing 135001 words to 138000 words out of 184930 words
Chapter 46 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt
Cike da mamaki haɗi da tsoro Abid ya matso kusa da Zaid da ɗan sauri.
"Zaid meke damunka haka? yaushe kuka dawo? yajikin naka?" duka waƴannan tambayoyin Abid yayiwa Zaid su a lokaci ɗaya kuma duk amsarsu yake nema idan zai samu..
"Abid nakasa mantawa da ita, itace nutsuwar tunani na, banajin zan iya kaiwa lokaci me tsawo batare da na sanyata acikin idanuna ba, Inasonta sosai kai kasani!"
Kallon Zaid kawai Abid keyi yamarasa me zaice masa.. Kallon ɗakin yashiga yi sai alokacin ya Lura da maka makan hutunanta dake manne ajikin bangon ɗakin Zaid ɗin,wasu zane ne wanda Zaid ɗin yayi wasu kuwa hotunanta ne. Wani irin tausayin Zaid ɗinne ya tsirga masa me tsanani, shidai bazaice baitaɓa soyayya ba, amma kuma baita ɓayin kwatan kwacin irin wannan son me tsanani da Zaid keyi ba. Zama yayi akan kujeran dake fuskantar na Zaid, hanun Zaid ɗin yakamo haɗe da cewa "Kazama jarumi Zaid, kada kamanta fa yanzu Zahrah matar wani ce kuma...."
"Ya isheka haka Abid!!" Zaid ya katse Abid cikin tsawa sosai.
"Matar wani, Matar wani, abun da kuke ta faɗa kenan, meyasa ni bazaku duba halin danake ciki ba? shikenan don tana matar wani sai nadaina sonta? kafun wanda kuke ikirarin matarsace yasota nine nan nafara sonta, kada kataɓa tunanin zan daina son Zahrah Abid, bakuma zan taɓa samun nutsuwa ba harsai Zahrah ta zamo mallakina, kataimakeni Abid kazo muje gidanta mu ɗaukota tazo nan mu rayu tare nasan itama tana sona!" cikin murya me tsananin rauni yake faɗan maganar..
Kai kawai Abid yake girgizawa azuciyarsa kuwa wutar tausayin Zaid ne ta kunno, So yamakantar da zuciyar Zaid yasanya harya kasa tuna cewa Zahrah a yanzu ta haramta a garesa, shi duk iskancinsa baya tunanin Zaiso matar da take da aure, dukansu shida Zaid sunsani cewa shangiya da zina duk haramunne amma kuma saboda son zucia irin tasu suke aikatawa, yanzu kuma ga wani sabon saɓon da Zaid yafito dashi, yana goya masa baya akan komai, amma a wannan karon kam baya tunnin zae goya masa baya yaci gaba da son matar aure, haƙiƙa Zahrah takai macen da kowani ɗa namiji zai sota, amma kuma tunda ayanzu tazama mallakin wani babu amfanin Zaid yata takura kansa akanta. "Zaid!" Abid yaƙira sunansa araunace. Kansa kawai ya ɗago ya kallesa batare dayace dashi komai ba.
"Kada kaga laifina Zaid, mun hau wani mataki da yanzu dole ne mufaɗawa kanmu gaskiya, menene ribar da zakasamu idan kacigaba da dakon soyayyarta acikin zuciyarka? tazarar dake tsakanin ka da Zahrah a yanzu yanada matuƙar yawa, tana tare da mijinta kuma nasan zuwa yanzu tajima da zama shi kuma shima yazama ita, me yasa to kowannan bai isa yasanya kacireta acikin zuciyarka ba, akoda yaushe kada kana tunanin cewa wai Zahrah zata dawo gareka, so ne yasa mijinta ya aureta, kaga kenan haka nan kawai bazai rabu da ita ba, kasa aranka ma idan ƙaddara ta rabasu babu yiwuwar Zahrah zata amince ta aureka, kai da kanka kasan haka amma zuciyarka tana yaudaranka, haƙiƙa nima shaidane akan cewa har yanzu Zahrah tana sonka, amma hakan bawai yana nuni da cewa zata iya kashe aurenta ta aureka ba ne, kai koma da ace tafito agidan aurenta to bana tunanin Zahrah zata amince ta aureka, kamanta da ita Zaid, kasawa zuciyarka salama, akwai mata da yawa acikin ƙasarnan dama sauran wasu ƙasashen kasamu wata kabawa ajiyar zuciyarka, na tabbatar watarana komai zai zamo labari!" Abid yaƙare maganar yana me dafa ka faɗan Zaid almar son ƙarfafa masa guiwa..
Wata tsuka me ƙarfi Zaid yaja haɗe da ture hanun Abid dake kan kafaɗansa... har abada bazai daina yiwa wanda yace yarabu da Zahrah kallon mahaukaci ba, wai Zahrah'nsa ake so yamanta ya daina sonta, sai yaushe mutane zasu gane cewa cire so bakamar cire takalmi bane? miƙewa yayi daga zaunen da yake haɗe da shigewa cikin bathroom ko sake kallon inda Abid ke zaune baiyi ba.. Ajiyar zuciya Abid ya sauƙe haɗe da gyara zamansa akan kujeran, yana nan yanajiran fitowarsa koda awa ɗaya zai share a banɗakin bazai tafiba saiyajirasa, Zaid bayason gaskiya wani lokaci, kuma kozai mutu saiya faɗamai gaskiya, ae soyayya ba hauka bane, son matar aure mezai jawo maka inbanda wahala da ƙarin zunubai....
Zaid kuwa yajima tsaye ruwa na fitowa daga shower yana dukan jikinsa.... Ɗaure da towel a ƙugunsa yafito daga cikin bathroom ɗin, kallo ɗaya yayiwa Abid yaɗauke kansa, Abid na kallonsa har yagama shafa man lotion ajikinsa...
"Saboda nace kamanta da Zahrah shine kake fushi dani? kai kanka kasan abun da kakeyi ba daidai bane Zaid sannan....."
"Ya isa Abid!" Zaid ya katsesa aɗan kausashe.
Murmushi kawai Abid yayi haɗe da sa kai yafice daga cikin ɗakin, yasan Zaid ya hau sama bazai taɓa sauraransa ba, wanda yayi nisa bayajin ƙira.
****
Tun fitarsa ta shige cikin kitchine yau bataso ya sayo musu abinci tafiso ta girka musu da kanta, fried rice tayi wanda taji zallan tsokan kaza, da kanta ta haɗa shaka ta sanya acikin fridge, takammala komai yanzu saura kawai tayi wanka.. Ƙaran wayarta take ta jiyowa, da sauri tanufi ɗaki inda wayartata take. Wata number ce special ke yawo akan screen ɗin wayar, ɗan tsayawa tayi tana ƙarewa number'n kallo, har ƙiran ya katse bata ɗauki wayarba, wani ƙiranne kuma sake shigowa.... A hankali ta ɗaga wayan ta kara akan kunnenta.
"Zahrah!!!" taji wata murya wacce bazata taɓa mantawa da itaba ta ƙira sunanta, jikinta ne yasoma rawa yayinda bugun zuciyarta yaƙara tsananta shin dagaske ne kokuwa kunnuwanta ne basuji da kyauba, kusan mintuna biyar ba asake cewa komai daga cikin wayarba haka kuma itama bata ce komaiba..
"Wa....y..e?"
tayi tambayar cikin wararrun kalmomi yayinda tsoro ke sake ɗarsuwa acikin zuciyarta.
"Zahrah na! me yasa zaki barni? kin barni cikin ƙunci da tarin damuwa, yazanyi da soyayyarki ne Zahrah, bazan iya rayuwa ba idan babu ke, please ki taimaki rayuwata dakuma zuciyar da ta jima da matowa akan ƙaunarki!!"
Jikinta ne gaba ɗaya yaɗauki rawa harbatasan sanda wayar ta zame daga hanunta ba, take ta faɗi ta tarwatse a ƙasa. Itakanta batasan sanda ta zame ta durƙusa guiwowinta a ƙasa ba, hawayene suka shiga fitowa daga cikin idanunta. "Zaid" shine sunan da take ta nanatawa acikin zuciyarta, sai yaushene Zaid zai barta ta huta tayi rayuwar aurenta cikin nutsuwa? anya kuwa Zaid baisamu matsalan ƙwaƙwalwa ba? ta tambayi kanta, shiru tayi haɗe da lumshe idanunta ƙirjinta kuwa har yanzu bai daina bugawa da sauri ba.
Cikin tsananin mamaki yake kallonta, da sauri ya ƙaraso inda take durƙushe haɗe da tsugunnawa yaɗaura hanunsa akan kafaɗunta
"Meke faruwa?" yatambayeta cike da kulawa.
Da sauri tabuɗe idanunta da suke a lumshe, batasan yaushe yashigo ba.
Kallonta yakeyi sosai da alama amsa yakeson ji daga bakinta.
Dasauri tashiga goge hawayenta haɗe da tashi tsaye, kallonta yakeyi harta shige cikin toilet, idanunsa yasauƙe akan wayarta wanda ta tarwatse akan tiles gaba ɗaya ma screen ɗin wayar ya fashe, mamaki haɗi da ɗaurewar kaine matuƙa suka kamashi, "Meya faru? yaganta tana hawaye gakuma wayarta daya gani aƙasa a tarwatse" yayi mawa kansa tambayar cike da son sanin amsa. Tattare wayar yayi haɗe da komawa kan gado ya zauna zuciyarsa cike fal da tarin tambayoyi..
Zahrah kuwa tana shiga cikin toilet ta soma sauƙe ajiyar zuciya akai-akai, meta aikata hakane, gashi yanzu yazo ya ganta acikin halin damuwa, tasan dole ne shima saiya sanya kansa a damuwa, yanzu idan ya tambayeta metasan zata ce masa, wasu hawayenne suka kuma zubowa daga cikin idanunta, da sauri ta sanya hanu ta share.. Haka tayi wanka duk tanajin zuciyarta babu daɗi, ɗan ƙaramin towel ta ɗaura ajikinta, wanda yatsaya a iyaka cinyarta. A hankali ta buɗe ƙofar bathroom ɗin tafito, karaf idanunsu suka haɗe waje guda, da sauri ta kawar da kanta gefe, haɗe da nufar wajen drawer.. Kallon santala santalan cinyoyinta da suke bayyane a fili yashiga yi, wani iri yaji acikin jikinsa, da sauri ya ɗauke kansa..
Ganin da tayi cewa baya kallonta ne yasanya tayi saurin zura dogon wando na pencil jeans haɗe da wata farar top shirt me kyaun gaske ajikinta, yaune karo na farko da ta fara sanya irin waƴannan kayan ajikinta, ita kanta saitaga ta burge kanta domin kuwa hips ɗinta sunfito acikin wandon sunyi ɗas dasu kamar wanda aka zana.. Kasa daurewa yayi saida ya kafa mata idanunsa, sosai tayi masa kyau baitaɓa ganinta acikin irin wannan shigar ba, ta ɗau hankalinsa ƙwarai lallai Zahrah macece har mace komai nata me kyau ne... Tana tsaka da shafa turare ajikinta taji yaƙira sunanta. Tsayawa tayi cak daga abun da takeyi haɗe da juyowa sai dai bata kallesa ba ta amsa ƙiran dayayi mata.
"Zonan!" yace da ita ata ƙaice.. Ahankali tashiga takawa harzuwa inda yake, tana ƙarasawa garesa ta durƙusa a ƙasa haɗe da sunkuyar da kanta tana me wasa da yatsun hanunta.. Hanunta yakamo haɗe da jawota jikinsa ya zaunar da ita akusa dashi, cike da kulawa haɗi da lallami yashafa kumatunta yace "Kinyi kyau"
Tsintar kanta tayi dayi masa murmushi kawai...
"Meke damunki? Sannan menene dalilin dayasa naga wayarki a fashe gaba ɗaya kuma tatarwatse?"
Kanta tashiga girgizawa alaman babu
"Kinsan banason ƙarya, menene dalilin da yasa zaki ɓoyemin damuwarki? kada ki manta yanzu bake kaɗai kike iko da kanki ba, nima nan inada iko dake, saboda haka na cancanci ki sanardani damuwarki, ni mijin kine bazan taɓa son naganki acikin damuwa ba!" cike da lallashi ya ƙare maganar.
Mezata faɗa masa? tace masa Zaid ne yaƙirata a waya ko me? ko kuma tace masa hawayen da takeyi duk akan Zaid ne?
"Dagaske nake bakomai, na ɗaga wayar hanuna da kumfa shine ta suɓuce ahanuna tafaɗi" tsintar kanta tayi da basa wannan amsar, duk da cewa ƙarya ba ɗabi'arta bane amma yazama dole yau tayi, saboda sanar dashi gaskiyan lamarin daya faru bashida wani alkhairi saidai ma ransa ya sosu.
Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da jinjina kansa "Naji amma meyasaki kuka?"
Jitayi gabanta ya faɗi amma saita dake tace "Kuka nake saboda na fasa wayata"
Ɗan guntun murmushi yayi sam bai gamsu da maganganunta ba, amma kuma yazaiyi tunda ta ɓoyemasa gaskiya bazai tursasata ba..
"Saboda wayarki ta fashe kawai shine kike kuka? har yanzu dai ke yarinyace ƙarama Zahrah, amma mene abun kuka, idan kikace na saya miki wata kina ganin bazan saya miki bane?"
Kanta ta jinjina alamar "A'a"
"To indai hakane miye na kukan tunda kinsan zansaya miki wata wadda ta fita, kitaimaki zuciyata ki daina sa kanki acikin damuwa please, inasonki banason naga wani abu ya ɓata ranki!"
Raunannun idanunta ta ɗago ta kalleshi, wannan maganar daga cikin ƙahon zuciyarsa yake fituwa, tabbas ita kanta ta gamsu da ƙaunar da doctor yakeyi mata ɗari bisa ɗari, ya cancanci tasakamai da farinciki ne bawai akasin haka ba..
"Ki kwantar da hankalinki, gobe Insha Allah namiki alƙawari zamuje dake ki zaɓi irin wayar da kike so, shikenan?"
Kanta ta ɗaga tana ɗan murmushi, kamar da gaske maganar wayarce a cikin ranta.. Miƙewa yayi yafaɗa toilet, tanajin sauƙar ruwa aƙasa ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, bataso doctor yasan cewa Zaid yafara bibiyar rayuwarta. Sumu sumu haka ta fice falo.
Tana zaune tayi jigum ya fito daga cikin ɗakin, sanye yake da blue ɗin wando kalan nata, sai dai nasa na maza ne babu ado kamar nata, saikuma farar polo shirt, murmushi tayi domin kuwa yayi mata kyau sosai, shima murmushin yayi mata haɗe da kashe mata idanunsa ɗaya...
Ita da kanta ta zuba musu abinci, yanaci yanata zuba mata santi, har batasan lokacin da tarin damuwar dake cikin ranta suka kau tasoma ƙyalƙyalewa da dariya ba ...
****
Zaid ne zaune agaban Dad ɗinsa ya sunkuyar da kansa ƙasa, magana Dad ɗin keyi masa amma kuma kwata kwata bayajinsa, hankalinsa da tunaninsa sunyi nisa sosai wajen tunanin Zahrah, muryarta dayaji ɗazu shiya kara rikita masa tunani, baisauraran Dad dake yimasa bayani amma duk da haka yaji abun da Dad ɗin yafaɗa na ƙarshe, cike da ƙuncin rai haɗe da tsananin mamaki yake kallon Dad ɗinnasa cikin wata murya me ɗaci yace
"Aure fa kace Dad? ni ɗin, kuma da wata ba Zahrah ba?"
Cikin takaici Dad yake kallon Zaid ɗin, wato tunkan ayi nisa ma yafara nuna masa cewa hakan bazai yiwuba kenan.
"Natabbatar kajini, kuma aure babu fashi!" Dad yafaɗi haka a ƙufule, domin kuwa shima yafara gajiyawa da halayyan Zaid na rashin hankali, taya zaka je kana yiwa matar wani soyayya me tsanani irin haka.
Wani murmushi Zaid yayi me matuƙar ciwo haɗe da sanya haƙoransa ya ciji laɓɓansa.
"Bazan iyaba Dad, kaima kafi kowa sanin hakan, aduniyar nan mace ɗaya kawai nakejin zan iya rayuwar aure da ita, bakowa bace kuma Zahrah ce, saboda haka please Dad maganar wani aure na da wata kabarshi don banaso, idan kuma ka matsa shikenan, amma idan kuka tsinci gawanta nayi mata mugun illa kada ku zargeni kufara zargin kanku" yana kaiwa nan azancensa ya tashi tsaye yafice daga falon mahaifinnasa.. Baki a wangale haka Dad yabi Zaid da kallo har yaɓacewa ganinsa..
"Lallaima kuwa Zaid ya ɗauko babban al'amari, amma kuma wannan karon sam bazai lamunta masa ba aure dole sai yayi masa, acikin satin nan ma kuwa" Dad yafaɗi haka acikin zuciyarsa...
Zaid kuwa yana fita a ɗakin Dad direct motarsa yashiga, dagudun gaske ya ja motar yafice daga cikin gidan, tafiya yake akan titi amma zuciyarsa ƙuna takeyi masa, har wani ɗaci yakeji a maƙoshinsa, wayarsa ce tayi wani ɗan gajeren ƙara alamar shigowar saƙo (Message), da sauri ya ɗauki wayar ya duba, domin kuwa tun ɗazu dama saƙon yake jira, adireshi ne na gidan da Zahrah take aka turo masa.. Wani mugun murmushi naga yayi haɗe da ɗan dukan kan steering motar, lallai dole zai cimma burinsa ne kota halin yaya kuwa...
Faka motan yayi yana me ƙaremawa gaban gidan kallo, gidane me kyau da kuma aji, dagani kasan ankashe kuɗi wajen tsara gidan, amma Zaid dake kishi yacika masa zuciya sam baiga wani kyawun gidan ba, saima ji da yayi ya tsani gidan.. Idanunsa ya tsaida akan tankamemen gate ɗin gidan tamkar wanda yake karantan wani abu, a hankali ya buɗe murfin motar tasa yafito waje, cikin takunsa na isa yashiga takawa harzuwa wajen gate ɗin....... (🤔Anya zaishiga kuwa?hmmm inaga dai yau Zaid aƙasam kanta zai kwana😂)
*(Kuyi haƙuri dan Allah kwana biyu kunjini shiru wallahi neighbour ɗitace tarasu ranan friday da dare shiyasa kuka jini shiru, naji mutuwar ajikina wallahi sosai shiyasa nakasa koda yin typing ɗinne ma, please kusata a addu'anku Allah ubangiji yayi mata rahama, yasa aljanna tazamo makoma a gareta Ameen thumma Ameen. Ina me ƙara neman afuwarku sosai 🙏🙏🙏)*
*Tuesday 28/January/2020*
*Fatymasardauna*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 100 to 101*
Tsayawa yayi yana me ƙarewa gate ɗin kallo, idan da zaibi son zuciyarsa ne, to tabbas da shiga cikin gidan zaiyi, amma kuma saidai wata zuciyar tana gargaɗinsa da kar ya shiga cikin gidan, bawai kuma don yanajin tsoro ba, kawai dai yana me tausayawa kansa ne, yasan idan yaga Zahrah dole sai ciwonsa yasake motsawa, duk da yanzun ma bawai ciwon nasa ya kwanta bane, komawa yayi cikin motarsa yazauna, haɗe da Kifa kansa akan steering motar, lumshe idanunsa yayi sai kawai ga hawaye suna fitowa daga cikin idanun nasa, wai yau shi Zaid ke kuka akan mace, lallai rayuwa juyawa take, gashi shikam tajuyo masa da saɓanin tunaninsa... Ƙarar motar dayaji shi yasanya sa ɗago kansa yakai kallonsa wajen gate ɗin gidan, ko ba a faɗa masa ba yasan motar RIVAL ce (wai Dr.Sadeeq ne rival ɗin nasa) balle ma kuma yagansa acikin motar, wani irin abune yazo ya tokarewa Zaid maƙoshinsa, baƙinciki, haushi, takaici, da kuma tsanar doctor ne duk suka haɗe masa waje guda. Ji yake kamar yafita acikin motar yaje ya shaƙo sa kozaiji salama acikin ransa.. Har motar doctor tashige cikin gidan bai ɗauke idanunsa akan gate ɗin ba, da sauri ya rumtse idanunsa lokacin da motar tagama shigewa cikin gidan aka kullo gate ɗin gidan, da ƙarfi ya danne lips ɗinsa haɗe da buga steering motar, yanaji yana gani wani zai yi masa rayuwa da Zahrah'nsa. "Yanzu Allah ne kaɗai yasan shigarsa mezaiyi mata, wata ƙilama rungumeta zaiyi, wataƙila kuma har kiss zaice zaiyi mata" wata zuciyar tafaɗa masa haka. Da ƙarfi ya shiga dukan steering motar, yana me jijjiga kansa, ƙwaƙwalwarsa bazata iya ɗaukar masa wannan tashin hankalin ba, jiyake komai na duniyan nan najuya masa, Allah yasa abun da zuciyarsa ta faɗa masa bahakanne zai kasance ba, bazai taɓa iya jurewa ba, hanunsa ya ɗaura adaidai saitin zuciyarsa haɗe da sake rumtse idanunsa, zafi yakeji haɗe da zogi acikin ƙirjinsa, da ƙyar ya'iya tada motar ya cillata kan titi a zafafe, gudu sosai yakeyi akan titi babu ruwansa da waƴanda suke gabansa ko suke bayansa, idanunsa sun rufe sosai.. Ikon Allah ne kawai yakawoshi gida, amaimakon yawuce ɓangarensa sai ya wuce ɓangaren mom ɗinsa..
Hajiya Safara'u ce tsaye agaban dinning table tana shirya abinci, batare da sanin shigowarsa ba saiji tayi anrungumeta ta baya, ƙamshinsa kaɗai taji tagane cewa tilon