Showing 21001 words to 24000 words out of 107087 words
Chapter 8 - AUREN GADO COMPLETE DOCUMENT Book by MATAR SOJA.txt
da gari ya Waye take jinta wani iri, mugun sanyi da zazzabi ke rufeta ma saboda damuwa, yau dai ba aiki domin komai odar momy tayo har Abinci,
Don haka tana kwance tana lazumi da carbinta na yatsa, Shigowa tayi cikin fada, "ke banason bakin ciki da kishi ki tashi ki shirya ki fito, kinzo kin kunshe a cikin daki kamar tsohuwar munafuka, Aure dai gobe insha Allahu sai an daura shi ko zaki mutu, in banda Abunki keda ko dadin Auren baki sani ba meye na kishi, don haka fito maza yanzu mutane natanbaya Ina uwar gidan Ahmed.
Tashi tayi cikin Sauri, tace "toh mommy, ta wuce bathroom ta sheko wanka, cikin kayan da momy ta bata ta ciro wani lafiyayyen leshi riga da sket kamar dinkin Amare ta saka, tana taje sumar ta taji Sallamar y'an uwan ta, Aunty Raliya da Aisha harma da Shukrah, wani irin tsallen dadi tayi domin Wannan ne karon su na farko a gidan nata, ta karbi d'an karamin goyon Aisha tace "Aunty my kalefa ya Kara wayau. Kallon ta sukeyi kawai domin sunga Alamar rama atareda ita ga kuma damuwa, basuce komai ba saida suka natsu shukrah ta tayata kwalliya ta murza dauri, sukace muje ki rakamu mugaida uwar mijin ki. "Toh tace suka fita, tana can kuryar dakinta da kawaye sai shewa sukeyi ita tafara Sallama wasu suka Amsa wasu suka zuba mata ido, suga Ina wannan kyakkywar ta fito, "mommy ga yayyina sunzo su gaisheki. "Toh sannun ku da zuwa, tafada tana gyatsina, kije dasu can dakin ki kisa Abasu komai domin akwai wadatar shi anan kuje. Tafada batareda tajira ko gaisawa suyi ba. Aisha dayake tanada fushi, har ta juya, Raliya ce ta tsaya tace "Allah yasa ayi a sa'a yakuma kade fitina, wasu sukace Amin. Ta juya Naziya tabi bayan ta,
Suna shiga dakin Aisha tafara sababi "wallahi Aunty Raliya wannan Matar batada mutunci yanzu dama Abunda ake fada gaskiya ne, gaskiya ni da malam zaiji magana ya raba Auren nan kawai. "Kinsan me zakiyi? Dakin bar nan saikije ki same shi kuyi magana kinji Aisha. Raliya tafada cikin haushi, wane irin Abu ne zaki tadawa yarinya hankali da mugayen kalaman ki, to sai me akanta farau da irin wannan uwar mijin? Don Allah kirika tausasa zuciyar ki. "Kiyi hakuri Aunty Abun ne yabata mun zuciya kalli yanda yarinya ta koma saboda fitinar wannan Matar, yanzu yarinya ko wata biyu kwarara batayi ba za azabgo mata kishiya wallahi ba adalci. "Ya isa bashi yakawo muba munzo ne mu debe mata kewa don haka don Allah ki daina mitar haka. Shigo musu da Abubuwan ciye ciye tayi ta baje musu tareda daukar kaleefa tana mai wasa,
Domin su dauke mata damuwa suka saki jikin su sosai tareda yimata hira tareda shawar wari, ta saki jiki a ranar, lokacin da aka fara taron ma tare suka shirya suka fito wanda tun shigowar ta gidan wannan ne karon farko data tako kofar gidan a yanzu ne take sanin Aljannar duniyar da take ciki, Suna fitowa khaleel na shigowa rikeda key cikin manyan kayan da ta lura yanzu yana kokarin sakawa, kallon ta yayi ya dauke kai tareda matsowa ya gaida su Aunty cikin girma yace kuzo muje inkai ku. Taso tace bazata shiga motar tashi ba Amma ba hali domin sun Ansa har suna godiya, Aunty Raliya tace munko gode domin bamu san wurin ba, shukrah ce agaba ita dasu Aunty a baya fuskar ta turbune domin Allah dai yagani tamafi kaunar mommy akan khaleel, a harabar wurin ya Ajiyesu dai dai ana kawo Amaryar tashi fauzy wadda tasha ado kamar zataje gasa cikin tsaddun bridal dress, Washe baki tayi tayi saurin nufoshi "baby "kazo. "No banzo ba mutane nakawo am going back, yafada yana shigewa cikin motar ya datse, su Aunty sukayi mai godiya yace bakomai batareda ya ko kalli gefen Naziya ba, gaba daya kawayen ta sukayo mata cah, "angon kenan Fauxy gaskiya gayen nan yaje, Amma akwai wulakanci. "Ba ruwanku I love him like that. Tafada tana juyi tareda cewa suje, suka take mata baya tana yiwa su Naziya kallon banza,
An barar da kudi a wannan taron na gagaruman mata da hamshakai, to suma dai ba laifi domin sunyi kwalliyar su cikin mutunci ba wadda tasaka gyale dukan su hijabine, Wanda ya janyo suke musu kallon rashin wayewa da tsantsar kauyanci, su momy an barar da rawa da kudi itada sauran iyayen Amaren, su Naziya na gefe itada y'an uwan ta har akaci aka sude, fitar tata tasata cikin farin ciki at least tafito a cikin wannan gidan dayake kamar kurkuku a wurin ta.
aka yi komai suka yi gidajen su, tayi farin cikin kasancewa tare dasu domin sun Cire mata kadaici da damuwa, Wanda sukayi mata Alkawarin dawowa Washe gari yinin bikin, throughout ranar har dare batasa Ahmed a idoba, an zubawa Amaren kayan su a sababbin ginin nasu dake gidan, kowacce an narka mata dukiya fiyeda tunani, dama haka Hajiya bilkisu takeso.
Kayan Naziya da ko a ido bata taba ganin suba tuni antattare an zuba su a store an zuba na Amarya........ 🖊
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y'an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
🆓 page
1⃣5⃣&1⃣6⃣
.................. Ta kwana da matukar tunani a wannan daren, Rayuwar ta da Ahmed, distance relationship, hatred tsakanin ta da y'an uwan shi, musamman Khaleel, she don't really know why, bata kaunar ganin shi, idan akwai Wanda zata nunawa tsana itace mommy wadda ta hanata sakewa a Rayuwar Auren ta, but why him? So take ta nemo Amsar takasa, juyi takeyi cikeda mutuwar jiki, idan tace bata cikin damuwa tayi karya, Ace Auren ta wata cikin na biyu ba kwanciyar hankali, batasan dadin miji ba batasan dadin zaman Aure ba infact ba Abinda ta karu dashi sai girki da gyaran gidan, Wanda anayi ne domin a kuntata mata, basusan ta horu da aiyuka agidan ubanta ba, ba aikin da zai gagare ta, tsoranta daya a rayuwa kar a rabata da mijin ta, domin duk Abinda ke faruwa soyayyar shi bata ragu a zuciyar ta ba, sai ma karuwa da tayi duk wani moment ita da Ahmed idan ta kadaici cikin farin ciki take kasan cewa, idan tana tuno su, tasani duk ranarda ta samu freedom da mijin ta zaman su zai yi d'ad'in gaske. Bata cire tunanin wata rana zatayi farin ciki ba, Wanda tana fatan tayi nasara insha Allahu. Tashi tayi tareda yin sallah ta roki Allah akan ya cire idanun ta akan duk Abinda zai faru da kuma Wanda ya faru a baya, tareda neman juriya da nasara a rayuwar ta ta yanzu da kuma nan gaba.
Washe gari aka tashi da shagalin biki, Wanda tun da safe jikin ta yagaza dauka daka kalleta kasan tana cikin tsananin damuwa da kadaici, Ahmed ya boyewa ganin ta baki daya, Wanda batada masaniyar baida lafiya ne, Saida khaleel ya kawo mai likita batareda sanin kowa ba.
Yana tareda d'an uwan shi har safe bai runtsa ba Abu biyu ke damun shi a zuciya, why yayan shi keda mugun hakuri? And wani gefe kuwa kanshi yake tuhuma, why why why? Domin shi karan kanshi da baida karfin zuciya cikin wata biyun nan da ya ga likitan zuciya, he is in big trouble, big mess Wanda yasani shi karan kanshi, he is a fighter domin duk Wanda ke yaki da zuciyar shi shine babban jarumi, Wanda kowa yasan yaki da zuciya Abune mai matukar wahala.
Dafashi da akayi yasa ya dawo cikin hayyacin shi tareda kallon yayan nashi, daya tashi zaune yana murmurshi kadan, kana ganin shi kasan cikin jinya yake. "All night bakayi bacci ba khaleel, why kuma kasan yau ranar Auren kane dole ka raya wannan daren. "Yaya ya jikin naka? "Alhamdulillah inajin sauki a jikina, ya Naziya kagan ta? how is she? " Yaya all you worried about is her? Why bayan ita bata damu da neman kaba if tasan Abinda ya dace me zai hana ta nemeka? "Kafada mata banda lafiya? "Nop Yaya. "Kaga batada masaniya, and please Khaleel take care of her, that girl deserve to be happy. "How Yaya bayan kaine zaka kula da ita she needs you more than me, kaine mijin ta. "I know khaleel. Ya Rungumo shi a jikin shi, yace "you have alot of responsibility, mommy, Fauziya and our company, I know you are stronger than me. "Yaya please stop All this you know you're breaking my heart, Yaya I have something in mind, Wanda bai kamaci in sakashi a zuciya ta ba I hate myself please forgive me. "What is that khaleel, me kakeso I promise to give it to you koda rayuwa tace saboda kaine farin ciki na. Wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro a kwayar idanun shi for the first time, yaji he need them, saboda sometimes tears heal some wounds.
"Noo Yaya bana son destiny din da zai zamo musayar rayuwar ka, I don't want that destiny, but Yaya is really painful, bansan yanda zanfada maka ba and please don't ask me too much question bazan iya amsaka ba. "Is OK bazan tanbaye ka komai ba, but dole inji dalilin zubar hawayen jarumin kani na, what is that, meye ya taba zuciyar the stone heart Ibrahim khaleel? "Yaya. "No am not asking the new ango but am sure kana kukan farin ciki ne yau zakayi Aure and you will last on bed more than me. Yafada yana daga gira daya, ya tuno da irin question din da yamai ranar da sukayi hira a dakin shi da Naziya. Dafe kanshi kawai yayi tareda sakin yayan nashi, "Hmmm yaja dogon Ajiyar zuciya, "I know kani na sai yafi thirty minutes. Mikewa yayi cikin sauri, am coming Yaya bari inje cikin gida. Yafita fuuu dagashi sai guntun wando yau ko singlet babu a jikin shi yama manta da taron matan dake gidan, burin shi ya ganshi a cikin gidan.
Dayake kowa na sha'anin gaban shi sannan kuma an Waye ba wani Abu bane don haka no one care, har ya shiga main palo, dai dai taci kukan ta tayi nak har wani zazzabi takeji ta fito jikinta kamar ba ruwa ba Wanda ya damu da ciwon zuciyar ta. Taga shigiwar khaleel fuuu ya wuce dakin shi, bayan shi ta hanga yana shigewa Wanda dole ta bishi taji inda zataga Ahmed domin ta gaza zuciyar ta tayi rauni, ta leka dakin khaleel din yafi sau goma tun jiya dukan su basa ciki, infact ko gyaran datayi bai baci ba.
Shiga yayi ya kalli gadon cike da wani irin zafi zuciyar shi keyi Wanda bai taba jin irin shi ba, ya fisge zanin gadon ya jefar tareda zubewa kasa yasaki wani irin kuka mai karfi kadan Wanda ba Wanda zai jishi,
Tayi matukar tsorata da kuma jin mamakin kukan namiji, tun dosowar ta kofar dakin kuma tanada yakinin a cikin dakin khaleel yake fitowa, wake kuka haka? Bude kofar tayi cikin Sauri, ya dago fuskarshi karab cikin idanun ta, tayi matukar girgiza, bata taba kawo zata ganshi yana kuka ba, meye yasa shi kuka haka ? The great mai girman kai, this is serious, kokarin juyawa tayi kawai domin a tunanin ta koma meye ba hurumin ta bane. "Wait. Yafada cikin sanyi tareda mikewa yana share hawayen shi, tsayawa tayi cak har ya iso wurin, hijabin dake jikin ta tarike gefen shi gam tana jiran taji me zaice, saida ya matsa ya tura kofar ya datse, ta zaro idanun ta, "meye na rufeni a dakin ka, bana son rainin wayau ka bude min kofa intafi. Tafada bakin ta na rawa kamar zatayi kuka, "Hmmm, me kike nema? "Mijina. Tafada kai tsaye batareda ta kalli y'an da ma yake ba, "bakida lafiya ne? Saurin dago kanta tayi ta kalle shi akaron farko tun shigowar ta, da gudu ta datse makullin idanun ta, "Auzubillahi. Tayi saurin ja baya, Wanda Abun yayi mugun batamai rai fiyeda tunani,
Bata taba ganin bear chest din namiji ra'ayil aini ba sai yau ga kirjin nashi da shegen fadi da wata irin suma mai tada tsigar jikin mace,
Fisgo hijabin ta da yayi cikin zafin rai yasa tafara istigifari tareda bude idanun ta tana mai kallon that's why I hate you, "you are behaving like baki taba ganin namiji ba kaya ba, kina Abu kamar wata saliha, look karki daukeni jahili ko mara sanin iyakar shi, I know my limit shiyasa kike tsaye agaba na batareda wani Abu yafaru dake ba, ni kikeyiwa a'u'ziya? kamar Kinga shedan. Cikin tsiwa da zafin zuciya tace "meye banbancin ku da shi, kana ratsa mata tsirara bayan kasan haramcin Abun sannan wuce limit! yes you cross All the limit da ka rikemin hijabi now let me go. Tafada cikin karaji, saurin sakin hijabin yayi tareda sai daita kanshi yana shafo sumar kanshi tareda d'an naushin iska.
"Am sorry, kiyi hakuri am worried ne because my brother is sick tun jiya. Saurin natsuwa tayi tareda sakin jiki tace "Ina yake? Jikin ta na rawa, yana part d'in mu na waj... Ko gama sauraran shi batayi ba ta bude kofar ta fice da sauri,
She knows it shiyasa itama batada lafiya, saboda Ahmed d'in ta is sick,
Tana fita ya datse kofar tareda zubewa kasa ya hade kai da guiwa, "khaleel you are so dead. Ya furta yana sakin Kara.
Da taimakon mai aiki tasan inda Ahmed din yake Wanda shine karon farko data shiga wannan part din Wanda ya kamata ta kasance a ciki, tundaga falon take zuba ido domin tasan dukiyar dake ciki bata malam bace, infact ko kudin labulen dake cikin falon zai siya kaf kayan dakin ta, wani irin karyewa zuciyar ta tayi takasa daga kafarta daga nan ta zube, shikenan tata takare za ashiga tsakanin ta da mijin ta domin tasan burin mommy ya cika ta Auro mai burin ranta,
Jin kukan ne yasa yafito daga bedroom ya ganta a wurin da gudu ya karaso gaban ta, "Naziya Naziya, ya zube tareda rikota zuwa jikinshi, "Am sorry please, Allah yagani kukan ki yafi komai daga min hankali please kiyi hakuri komai nada dalili believe me, dago kanta tayi ta ce"harda guduna kadawo dakin Amaryar ka tun bata tareba, Ahmed meye ribar zama na a karkashin inuwar Aurenka? "Soyayya ta Naziya, soyayyar kice Ribar Auren mu, Wanda nayi miki Alkawari muddin baki tare cikin gidan nan ba bazan taba samun farin cikina ba kece walwala ta kece farin cikina, am sick Naziya saboda damuwa datayi min yawa zuciya ta na ciwo. , Hawayen ta tayi saurin sharewa, "Ahmed Ina son zama dakai, ka koyamin sonka duk da bamu zauna tare ba, halin ka hakurin ka tarbiyar ka, Ina son halayen ka, kaddarar rayuwar mu, nadauka am not blaming you for that shine kaddarar mu, please karkayi ciwo zan shiga damuwa kaji, tafada tana shigewa cikin jikin shi da kanta kuma a karon farko, taji ta iya sakin jiki dashi batareda kunya ko nuku nuku ba, Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara zaman shi dakyau tareda rungume ta gam a jikin shi shima, "Wow Naziya sarkin kunya yau ta rungume ni haka? What a lucky day, kice intashi ingirgice kawai mu shige daga cikin dakin mu yau. Sunne kanta tayi cikin kirjin shi tana jin kunya, tareda kokarin tashi ta gudu, "no karya ne yarinya kinkawo kanki don haka let go inside ki bani Abinci inci domin rabona da Abinci tun shekaran jiya, "why? Tafada cikin damuwa, "because am worried about you kullum Ina tunanin Ina shiga hakkin ki idan namutu ubangiji zai tanbayeni hakkin ki Naziya, kiyafemin kinji. "No bakayi min komai ba, muje in hada maka Abincin kaci, akwai komai a ciki ne? "Yes let go, yafada yana Rungumo kugunta. Ya dade a tsaye yakasa shigowa falon yana ganin yanda take shigewa jikin Ahmed, komawa yayi kan kujera ya zauna tareda runtse idanun shi gam only God knows what is going on in his mind,
Dagewa tayi ta shirya mai girki lafiyayya domin takara zama expert yanzu saboda shine kawai aikin ta a gidan, yana biyeda ita har cikin kitchen din, yana shige Mata harta gama yace suje falon domin yaji muryar khaleel na waya, kuma shima tunjiya baici komai ba saboda yaga yayan shi baici ba, tayi mugun jin haushin shi domin ya katse musu lokacin mai dadi ta hanyar zuwa musu gida,
Fitoda komai yana tayata, yana zaune a wurin batareda ya motsa ba, idanun shi a rufe har suka jera Abincin, tana gefen Ahmed yasa hannu ya cire hijabin jikinta batareda ta shirya ba, doguwar riga ce a jikinta mai kyau ta kanti, wadda ta d'an kamata shiyasa take yawo da hijabin, saurin kallon shi tayi tareda narke fuskar ta "kana so ingudu ne? "No wife inaso inyi kallon matata ne, Kinga yanda kikayi kyau, and,,ya matsa daidai kunnen ta ya rada mata "this your chest baby please agama abani hakkina I need them very badly.
Hannu tasa ta datse fuskar ta tana girgiza kai, "Allah zantafi fa. Cikeda wata irin murya mai daukeda tsantsar shagwaba mai burge y'an maza, Wanda saida khaleel ya daure ya kalleta, a yau yake ganin dariyar ta da kyau hade da farin cikin ta, he feels a little happy one side, ga dimple d'in ta wow,. "Yaya Am hungry yafada domin katse moment din, "let eat brother, ta zuba musu tareda cewa "wannan Abincin