Showing 39001 words to 42000 words out of 107087 words
Chapter 14 - AUREN GADO COMPLETE DOCUMENT Book by MATAR SOJA.txt
ko tv Abun na burgeni sosai. Tafada tana dariya, Wanda ke karawa fuskar ta kyau, da zaka kalli fuskar khaleel da zaka hangota kamar manja saboda ja, "kai haba ai mace tafi mutunci da aikin likita Naziya, ni da badon anyi min kafa ba da tuni na jefaki school of nursing ma. Dariya tasa, wadda saura kiris ta tafi da numfashin khaleel, mikewa yayi tareda fita a zuciye, ya samu Malam a zaure, "Ibrahim harka fito? "Eh Malam magana zamuyi. "Bismillah Toh. "Nace ba laifi idan yau nadauke ta ta koma gidan mu? "Aa kaida Matar ka ai bawani laifi kawai ko yanzu ka so zaku iya wucewa, bari in fada ma mahaifiyar ta. "Toh zan tafi zuwa dare zan dawo in tafi da ita, ai badamuwa idan ba arakata ba ko? "Babu hakan shine daidai ma tunda ba Auren farko bane, Allah yabaka ikon rike Amanar dan uwan ka tareda sauke dukkan hakkin da ke wuyan ka. "Amin yace, yabi Malam suka koma ciki lokacin ta mike tsaye zata shiga dakinta, bin bayan ta yayi kawai,
Tana shiga taji mutum a bayan ta saida ta zabura, tayi baya kamar zata zube saboda tsorata datayi daganin shi, saurin riko hannun ta yayi domin zata fadi, ya fisgota zuwa jikinshi Wanda saida ta runtse idanun ta kafin tayi saurin ja baya tana fisge hannun ta, jitayi kamar ta warta mai mari, "me yasa zaka tabani? Ta fada jikin ta na rawa, "oh ba atabaki ne? Ai bansani ba, yafada yana bata Wani irin kallo mai cikeda ma'anoni tun daga sama har kasa.
Saurin bin jikinta tayi da kallo tareda juyawa tana shirin daukar mayafi, yayi saurin matsawa, " akwai Abinda zan iya yi idan har kika aikata Abinda ke cikin zuciyar ki, ni ba shashashan namiji bane, kina iya tsayawa a gaban Wani banza yanda kike so idan kinganni saiki rika neman Abun rufe jikin ki me kikeso ki boyemin?
"Kaga Ina jin kunyar ka don haka karka bari inbude baki infada maka maganar da bazaka manta daniba. "Say it am ready to hear. "Kaga kana cin Albarkacin Ahmed shi yasa kake yi mun Abinda kaga dama Ina kyale ka, not anymore, tunda kace zaka wuce gona da iri, karka manta kai kanin mijina ne, matsayin mijin da kake kokarin dorawa kanka zuciya ta bata karba ba ban Amince ba.
"Hmm first in history, naji mace na deciding yanda zasuyi zaman Aure itada mijinta, yafada yana rike gemun shi cikeda rainin hankali, "husband, yes I am your husband believe it or not, and secondly, ni nake tsara rayuwar da nakeso inyi, inaso kije ki bincika tarihi na kiji bana daukar ra'ayin Wani, I only did what I think is right, ya zakiyi rayuwa me kikeso me zaifaru dake, duk nine zanfada miki yanzu, wannan rufe rufen jikin da kike yi idan naso zan iya hanaki saka ko pant da breziya a cikin gida na, watch out wannan mijin da kike gani bakisan waye shiba, and third, later in the night you are going to my house, enough of all this hira da kikeyi da katon banza, so get ready in time, first in history miji zaizo ya dauki Amaryar shi, ya matsa gab da ita tareda cika mata fuska da hanci da tsadadden kamshin jikinshi ya hura mata iska yayi ficewar shi kamar Wani walkiya,
Ya sumar da ita da kalaman shi, saida ya fita ta zube akasa tana hade jikinta, she can feel his presence up to now, a dakin jikinta kamshin shi duk ya Kama, kalmar shi na ko pant da breziya sai yana ra'ayi zata sa ya tsaya mata arai, lallai tantiri take gani a gaban idanun ta na bugawa a jarida, zata iya rantsuwa kalmar bazata taba futowa daga bakin shi ba, yanda yake behaving like gentle man, now she is mistaken, infact batasan me zai yi nan gaba ba, kallon tsintsiyar hannun ta tayi tanajin nashi haryanzu a nata, Wani irin Yar takeji fiyeda yanda takeji idan Ahmed ya riketa, hannun shi kamar Wanda yake massaging dinshi da baby oil, saboda softness ko ita mace hannun ta baikai nashi laushi ba, she can still feels his heart beat, lokacinda ta fada na second biyar, zuciyar shi bugawa take da mugun karfi. Tashi tayi tareda kwabe kayan jikinta ta zubar akasa, ta datse kofar ta koma zubewa akasa, kallon shape dinta nayi, ta tsaru dakyau jikinta nada tsari da Wani irin kyalli abunka da fara, juyowa tayi ta zubawa tukunyar fulanin ta ido nasan cewa yes Ahmed yayi rashi babba da bai more way'ennan Abubuwan ba, a cike suke tam a girke zaune Alamar bazasu taba kwanciya ba, tashi tayi ta kalle su tasa kuka " am sorry Ahmed dana sani nabari kayi yanda zakayi dasu da nasan bazaka rayu da ni ba, bazan kasa kai maka hakkin kaba, yanzu tayaya zan iya bawa dan uwan ka kulawa, bazan iya ba kaine ka dace da duk wannan Abun ba kanin kaba, murje idanunta tayi tareda daura kuduri mai girma. Kiran da taji Inna nayi mata yasa ta zabura ta mike, wasu kayan tasa domin ta tsani way'ennan saboda kamshin shi da sukeyi, ta fita idanun ta sunyi ja. "Toh" Malam yace Anjima zaki tare gashi wannan Karon ko shiri ba'ayiba don haka na Kira yayar ku tace tana zuwa kije ki hada Abun bukatar ki. "Toh" tace kamar zatayi ihu saboda damuwa, gwara zama da mommy sau dubu da zama da khaleel a wurinta, a tunanin ta tagama zama a wannan gidan sai gashi rayuwa takuma juyawa da ita ta bahagon hannu.
Tunda yafita gidan su yana barin unguwar yayi tafiya mai nisa yayi parking a gefen titi wajen da ba hayaniyar komai ya Dora kanshi a jikin sitiyarin motar shi, wani irin numfashi yake fitarwa da sauri da sauri, yanajin kamshin turaren wutar da take Amfani dashi akaya, he can feel her chest a nashi har yanzu, runtse idanun shi yayi da karfi yana dukan iska, fauziya tasha rungume shi by mistake bai taba jin haka ba, wani irin racing zuciyar shi keyi, itace mace ta farko da ta fara sashi yaji shi a namiji, bayaso ya nuna mata rayuwar Aure sai yakoya mata sonshi, sai ya cire mata bakin cikin zamanta na baya sai ya bata dukkan farin ciki, so yake yazama bawan mace a Karon farko, Amma sai yayi amfani da nashi salon, "Am sorry Yaya, zuciya batada k'ashi, batada limit, I don't know when and how? I think tun ganin ta nafarko yes that's it, love at first sight.
"But kai take so, bana bakinciki because she love you, zan tayaka bata farin ciki I promise you bazan taba cutar da itaba that's my promise to you my brother.
Hour guda cur ya kwashe yana tunani a wurin kafin ya wuce ya samu kawun shi yafada mai yau zata tare, yasa Albarka tareda Bashi shawara akan zaman Aure, da kuma akan mahaifiyar shi, sai kayi da gaske, ina fatan kasan halin Hajiya balkisu fiyeda ni yanzu, don haka Allah yabaka ikon sauke duk wani hakki.
Godiya yayi yatafi tareda wucewa gidan,
Bakowa duk sunfita, mommy taje wurin zarah domin neman mafita ita kuma Fauziya tayi gidan su,
Tabe bakinshi yayi ya shige dakinshi ya kwanta yana murmushi, yana hango yanda maganar shi ta sa takoma kamar gunki, "this is just the beginning baby. Tafin hannun shi ya kalla, yana jin kamar har yanzu yana rike da tsintsiyar hannun ta, yasan dole taji yanda yakeji shima, ya dauki lokaci yana tunani kafin yayi bacci mai dadin gaske,
Gefen Naziya kuwa tana zaune batada zabi Shukrah ta zana mata lalle jada baki gefe Aunty Raliya ta shirya mata lafiyayyar kaza tasata ci, zama tayi ta nagi kayarta tasan aikin banza sukeyi kawai yanda Ahmed yatafi haka shima zai gaji ya sallamo ta, ba Abinda zai shiga tsakanin su, sayi sa gama. Haka ta murjeta da dilka tas, zuwa magrib ta yi wanka da ruwan kamshi da yaji hade hade, suka bata sabon kaya ta saka, tayi sallah,
Ta dade a sujudarta tana neman Allah ya taimaketa kar ya bawa duk wani makiyinta sa'a akanta, bayan isha'i Malam ya shigo gidan ya zaunar da ita tareda yimata nasiha mai ratsa jiki.
"Naziya nasan zakiji a zuciyar ki banyi miki adalci ba, nasan bakya son wannan Auren, kuma nayi matukar mamaki da kike kokarin bujurewa hukunci na, shin kin manta bana yin Abu dakai, kin manta duk Abinda nake nema sai na nemi zabin Allah, na hango miki farin ciki Naziya idan har kin daure kin karbi kaddarar rayuwar ki, kije Kiyi biyayya Albarkar mu tare da Addu'ar mu tana tare dake, Allah yayi miki Albarka. Kuka takeyi kasa kasa hawaye sharkab a idanun ta, Inna ma tayi nata tareda sa ma rayuwar ta Albarka.
Sallamar shi ce tasa Malam ya fito tareda tarar shi cikin murna "sannu Ibrahim ka iso. "Eh Malam. "Toh Hauwa fito da ita ga mijinta, "wani irin nishadi yake jinshi a ciki, tun bayan mutuwar dan uwan shi yau ne yake jin kamar Ana wanke mai zuciya da ruwan madara.
Cikin manyan kaya yake sky blue yard na maza yanada wani kyalli kyalli kana iya hango farar singlet dinshi, gayen yasan sirrin ado, kuma duk shigar da yayi kyau take mai saboda cikar zatin shi, ko dago kai batayi ba data fito cikin katon hijabi kalar kayan jikinshi, Wanda yana kallon ta yayi murmushi cikin duhun daren, wannan fitinannen kamshin nashi duk ya cika musu tsakar gida,
Inna gaisawa sukayi tace bari insa Shukrah ta kwaso kayanta. "Abar kayan zandawo inkwashe su gobe. Yafada tareda yi musu sallama ya fita, komawa tayi ta rungume Inna tasa kuka, jikinsu duk yayi sanyi, Malam fita yayi yana cewa idan kungama Shukrah ta rakota waje,........ 🖊
*Wacce wainar zamu soya a gidan khaleel my fans, wane irin rayuwa ce zatayi tareda wainnan mutane ukun fauziya momy and khaleel, meye ra'ayinku akan kudurin Naziya? Waye zaiyi nasara a wnn tafiya khaleel or Naziya? " muje zuwa time will tell insha Allah*
*Matar Soja*
2⃣7⃣&2⃣8⃣
............. Tunda ya dauki hanya take kuka kasa kasa, ta cusa kanta cikin cinyoyin ta, kukan tausayawa kanta takeyi, domin batasan me zata tarar ba idan ta koma cikin wannan gidan. Yana yi yana waigota baice mata tak ba saida ya shiga cikin tangamemen gate din ya parker, kashe motar yayi tareda kallon ta yace "enough munzo gida", welcome back, ki sauka zanje insiyo miki kazar Amarci, ga part dinki can a bude ki wuce ciki kawai. dago kai tayi hawaye sharkab, "bazan shiga cikin wancan gidan ba" tunfarko ba aso zamana a ciki ba, yanzu ma bazan shiga ba inda nafara zama tun farko a ciki zan zauna. "Gidanki ne you can choose any place, go ahead sai nadawo. Ya ja baya tareda barinta tsaye takasa koda daga kafarta, sakawa takeyi da warwara ta Ina zata fara, Ina ta nufa can inda yace ko ciki ta tarar da Mommy. Juyawa tayi ta nufi hanyar main house, domin da zama da khaleel gwara zama da Mommy a wurinta yanzu.
A zaune suke a falon suna jiran me zaifaru domin sun sani tunda yafada ba canjawa, don haka suna jiran isowar ta, Sallama tayi a natse ta sawo kai, suka zubawa kofar ido domin ganin ita da waye, Fauziya Harda leke, sukaga ita kadai ce, mikewa sukayi gaba dayan su suka nufota tareda daka mata tsawa, " tsaya daga nan mai farar kafa", wato tsabar kin matsu kidawo cikin daula da kanki kika kawo kanki, Amma wannan yarinyar anyi mayya, to tsaya kiji, kurwar khaleel ba irin ta Ahmed bane, shi ba karen ki bane da zai rika rawa kina buga mai ganga, tunda sun nace anlika mai, kurwar shi kur yafi karfin ku, wannan naman shi da d'aci don kiji jinin dana bazai shawu miki cikin sauki ba Y'ar gidan malamai.
Shiru tayi saida mommy ta gama tsab ta gaida ita, "momy Ina wuni". Munafuka da ban wuni ba zaki ganni ba maras zuciya, yoh Ina zakiyi zuciya kina kwadayin a/c gidan Malam nakan buzu babu. Fauziya ce ta matso gaban ta tana huci "jaka akuya" in banda kina dakikiya ina ke Ina my Khaleel kema kinsan na wuce da Ajinki bare inyi kishi dake baki isa in hada miji dake ba.
Wani irin tafasa zuciyar ta takeyi, don haka saida ta gyara tsayuwar ta tace "Ai Akuya nada rana domin akan yanka naman ta aci haka jaki ma domin yakan dauki kaya ko banza kinga shima yanada rana, Amma mutum mai kwakwalwar kifi shine Wanda baisan darajar dan Adam ba, dake mace ce mai daraja bazaki tsaya kina zagin iyayen wani ba, kuma Alhamdulillahi duk rashi da talaucin mu baki gan mu kofar gidan ku muna barar Abinci ba, sannan mijinki dakike magana dashi da rashin shi duk daya a wurina, ni da zaki taimaka min da kinsa ya maida ni inda ya dauko ni yafimin kwanciyar hankali, kuma dake kin kai mace da kin taimaka tunfarko kin hana Auren nan, da banda masoyiya sama dake.
Wani irin daga hannu tayi zata zabga mata Mari taji anrike hannun ta carab, saurin juyowa tayi idanun ta a rufe ko gani batayi tace " mommy kibarni in daki Y'ar gidan talakawan nan ba kyajin mugayen kalaman datake fadamin ni sa'arta ce.
Jin an watsar da ita a gefe yasa ta dawo cikin hayyacin ta, ta ganshi tsaye fuskar shi ba fara'a, yace "I know you will react like lunatic, shi yasa na dawo, kuma ki godewa Allah da hannun ki yakai fuskar ta yau da sai kin kwana gidan ubanki, tunda bada kudin gwamnati muka gina gidan mu ba.
"Khaleel banson dibar Albarka agabana kake tarewa wannan yarinyar fada, me kakeson nuna mana ne, tafimu mutunci da daraja kenan, Toh ahir dinka dani wallahi zanyi maganin ka da duk Wanda ya daure ma gindi ka kwaso min wannan yarinyar cikin gidana. "Mommy me tayi daga shigowar ta kuma agaban idanun ki take kokarin marar min mata, wallahi da abakin wanna igiyar da kuka daura mara Amfani yau. Baki dukansu suka saki sunkasa furta komai, ya juya gefen ta" kema bakyaji na nuna miki part dinki inda bamai damunki kin shigo nan, kinga bazan iya tare miki fada kullum ba let go to your part. Matsawa tayi tana tura baki ni anan zan zauna bana son can. "OK as you wish, ya riko hannun ta ya nufi hanyar dakin shi da ita tana kokarin kwacewa, Amma karyarta domin ta riku, har wani hadota yayi da gefen shi ya wuce da ita cikin dakin tareda kulle kofar yabarsu a sume, suna shiga ta fisge tareda nunashi "karka kuma kokarin tabani banaso. "Ni kuma inason tabaki kuma bake zaki yanke wannan hukuncin ba nine zan yanke hakan ko Ina bukatar tabaki ko banayi nine zan zartar da hakan.
Juyawa tayi domin ta fita yayi saurin shan gaban ta ya rufe kofar da key ya cire yayi gaba Abin shi, "kazo ka budeni intafi dakina. "Excuse me? Kinada wani daki ne bayan wannan da kuma gidan da kikaki shiga? "Yes dakin mijina da na saba zama. Dawowa yayi da sauri gaban ta, ta zuba mai ido shima cikin kwayar idanun ta yake kallo tareda dage gira daya, "repeat that", "say it again, yanzu in nuna miki am your husband and believe me zakisha mamaki na. Ja da baya tayi kadan, "nifa bazan Kwana daki daya dakai ba. "OK zamu gani yau, ni kuma bazan Kwana ni kadai ba as far as you are my wife, muje zuwa inga who will win. Kallon dakin takeyi tana tunanin lokacin da ta shigo cikin shi suka zauna akan gadon yana shayar da ita kalamai masu dadin gaske, namiji Dan soyayya yayi a rayuwa, she is missing him so much waye zai maye mata wannan gurbin? Har wani tsigar jikin ta ke tashi idan tana tuna lokacin da yake taba ta.
Kallon gadon tayi taga ba Wanda ta sani bane, karewa dakin kallo takeyi yanzu take realizing an canja komai new, jin motsin shi yasa tayi saurin juyowa, tagan shi yana kwabe kayan jikin shi tayi saurin bashi baya tareda cewa "ai dama bakajin kunyar yawo tsirara a cikin mutane" ka girma bakasan ka girma ba. Bai tanka taba saida ya cire duk manyan kayan yarage dagashi sai boxer, ya fito ainihin namijin shi, tsarin jikin shi a bayyane kirar shi broad chest din shi murdadden hannun shi irin na ainihin maza naturally, Wanda duk macen da ta kalle shi sai ta afka mai lokaci daya, shiyasa fauziya takasa hakura dashi har gobe tana mafarkin kwanciya a wannan kyakkyawan jikin har safe,
Matsowa yayi tareda dafe west dinshi ya zo har gaban ta, zare idanun ta tayi tareda saurin runtsewa bayan ta mai kallo daya tana girgiza kai "wai kai meye haka kakeyi baka kojin kunya"?
Wani irin mugun murmushi yayi, that's exactly what he is looking for a wurin mace me kunya, and its going to be so much fun, domin duk namijin da ya Auri mace mai kunya zai mori kuruciya da rayuwa mai cikeda nishadi, "open your eyes or.....
Ja baya tayi tareda girgiza kai "kaga don Allah kasa kaya kuma ni kabarni intafi part din da kace. "You are late, now listing to me, open your eyes ko in cire boxer din and believe me kema sai kinyi necked irin nawa mun tsaya aga Wanda yafi kyau ba kaya. Da mugun gudu ta bude idanun ta tareda kallon shi cikin ido way'enda ba duk mace ke iya resisting kallon cikin suba, but sunfi mata saukin kallo akan jikin shi, ita da Ahmed bai taba mata irin haka ba Amma wannan marar kunyar Hmmm.
"What did you said? Bana girma? Yafada yana matsowa tareda yin murmushin gefen baki, irin na muguntar nan, da kuma enjoying each and every moment with her. Tana ja da baya har ta cimma kofar bathroom dinshi ta manne yana biye. Saida yaje gab ya kalli kofar, "just say it ba