Showing 93001 words to 96000 words out of 107087 words
Chapter 32 - AUREN GADO COMPLETE DOCUMENT Book by MATAR SOJA.txt
"look kinga banason musu kitashi mutafi. Momy naji kuma tana gani so takeyi tayi magana ba dama,
Tashi ma tayi ta haye gadon dake dakin extra ta kwanta tareda jan net bayan ta saukewa momy nata, tabashi baya.
Abun ya matukar konamai rai don haka a zuciye yabar Asibitin, yayi gida.
Inba haka tayi ba bazai taba barinta ta Kwana da Momy ba ita kuma so take ta kula da ita saboda tasan a duniya batada ya'ya sama da Ahmed da shi gas hi ba Ahmed Khaleel kuma namiji ne, kuma bai kamata wata nurse na wani kula da itaba,
Don haka ta zamo mata ya' koda bazata godeba zatayi domin Allah.
Wani irin farin ciki momy keji ganin y'an da Naziya ta jajurce wuni guda tana bata kulawa. Sai dai rashin jituwar su yasa abun ya taba mata zuciya, ba Abinda take buri yanzu sama da ganin farin cikin khaleel da Naziya.
Gida yatafi kai tsaye badon yasan zai iya bacci ba, ya kwanta yanata fushi a kujera ga gidan bakowa cikin shi sai masu aikin shi tsoffi da yadawo dasu, harma da mai gadi bayan ya kora Wanda suka kawo.
Har karfe goma na dare yakasa natsuwa haka ya canja zuwa kanan kaya ya dauki key din motar shi ya kuma barin gidan.
Naziya Saida ta kuma shafe momy tsab da ruwan Addu'ar ta kunna musu waya tasa kira'ar sudais cikin suratul bakara tareda Ajiyewa kusa da gadon momy ta koma nata ta kwanta bayan taja mata bargo, murmushi kawai momy keyi najin dadi ya' daga sama wadda tafi ma d'an ta damuwa da ita, haka tayi baccin ta mai nauyi cikin salama tareda jin duk wasu igiyoyin da suka daure jikin ta suna kwancewa a hankali. Ita kanta Naziya tana bukatar hutawar domin d'an baccin ma da takeyi na rana yau bai samuba don haka tana kwanciya yayi awon gaba da ita,
Kamar a mafarki takejin hannun mutum a Kirjin ta tareda jin nishi kasa kasa, wai don ma yana controling kanshi karya samata ihu a Asibiti. Jin jikinta na canjawa yasa tayi saurin bude idanun ta, dayake akwai d'an duhu sai hasken dake shigowa kadan daga window domin tayi switching light din, mugun tsorata tayi jin mutum laulaye da ita gaba daya hannayen shi damke da kirjinta gam, sanin zata iya samai ihu yayi saurin rife bakinta yana rage murya tareda cewa " it's me baby.
"Hmmmm tayi saurin dafe kirjin ta ta zabura tana sauke rigar ta daya kwashe mata. Matsowa yayi ya janyota tareda zaunar da ita saman kafafun shi " hey relaxed, kinga fushina ba inda zaije nadawo because I can't sleep, the house is too big for me, please baby I really needs you kinsan bazan iya hakurin da nayi a bayaba, karki yimin irin wannan horon.
Y'an da yake magana ya mugun bata tausayi don haka ta d'an natsu a jikinshi,
"Kai wai bakajin kunyar idanun momy ne in taganka fa? Ni dai kayi hakuri inna dawo gida kabari momy ta warke.
"I said I can't why don't you understand?
Yafada cikin tsawa da fada, "you are my wife ya zaki rika garani saikace ba halalina ba how many times kikeso in lallaba ki?
Momy Saida ta farka saboda tsawar da ya bugawa Naziya, cikin ikon Allah ta bude bakinta tace "khaleel! Kamar daga sama sukaji muryar ta duk da maganar bawai ta bude sosai bane, da gudunsu suka matsa kusa da ita, Naziya tayi saurin gyara kanta ta kunna wutar dakin suka ganta tana kokarin mikewa, wani irin farin ciki ne yasa ya ji duk wani bacin ranshi ya kau ya rikota tareda cewa "momy you talk, kuna kintashi zaune? Cikin so much excitement, itama ta matso kusa da ita tace "sannu momy tana boye hawayen idanun ta domin tsoro biyu ne ya hadu mata, ga fushin khaleel ga tsoron Abinda Momy zata yimata tunda kuma daga gani sauki yazo, kallon ta tayi kafin ta kalli khaleel dayayi kicin kicin tace "meya miki kike kuka? Khaleel meyasa bakada hakuri da daren nan kana yiwa yarinya ihu duk da gajiyar da tayi..
Wani irin hawayen farin ciki ne ya Kara shatatowa daga idanun ta, batayi zaton haka daga momy ba, shikan shi yaji mugun dadi don haka yace " tanbaye ta ni ba Abinda nayi mata impact in kukane ma nine yakamata inyi ba itaba, do you know momy tundazu nake lallabata muje gida ta nace ita nan zata Kwana tare dake saboda taurin kai.
Hannun ta datakeji ya saku sosai guda daya ta mika tareda riko hannun Naziya zuwa kusa da ita, " Zo kinji daina kuka inbakya son zuwa ba mai matsa miki kinji, Amma in saboda nine kitafi gida ki huta kinga am OK zan iya gyara kwanciya ta zan iya tashi hannu na dayan nan ne da kafar hagun nan nakejin su a rike, Alhamdulillah nagode wa Allah nagode miki keda iyayen ki Naziya Allah yasa ki gama da duniya lafiya. "Amen Amen Sukace, farin cikin su baya misaltuwa a wannan lokacin, tace "in kina son binshi kije da safe kya dawo.
"Banason zuwa momy ni ina nan. Tafada batareda ta kalli khaleel ba,
Fuskar shi ya tamke yayi banza da ita,
Tace "kije kiyi kwanciyarki kinji kibarni dashi nasan kin gaji.
Wannan canjin na momy yafi komai faranta mata zuciya don haka bataso tayi Abinda zata bata mata rai har su koma Y'ar gidan jiya don haka ba musu ta wuce Abinta, momy tace ya tashi ya kashe hasken ya kunna musu na wayar shi magana zata yi dashi kar hasken ya damu Naziya zatayi bacci. "Ya tashi cikin murnar ganin momy taji sauki ga kuma canjin hali da ya lura tayi tuni ya goge mai duk wani fushi da yakeyi ya hakura da Abin da ya kawoshi ya zauna tareda gyara mata zama don tace ta gaji da kwanciyar jikinta na ciwo,
"Khaleel bansan ta ina zanfara magana ba. Tafada tana dukar da kanta tareda share hawayen ta da hannun ta mai lafiya, yayi saurin rikewa tareda girgiza kai ya share mata hawaye tareda cewa "don't say anything momy kinga jikin ki bai gama dawo wa dai dai ba, banaso kiyi tunanin kinyi mana ba sai dai ba, ke mahaifiyar muce dole mubi Abinda kikeso, am sorry for everything momy. Shafa fuskar shi tayi tareda murmushi "nice zan baku hakuri banzamo muku uwa tagari b.... Rufe mata baki yayi " enough for all this talk momy ki huta, komai ya wuce kawai lafiyar ki itace damuwa ta. "Khaleel Salifa..... "Leave everything to me momy am here don't worry yourself. "Akwai Abinda nakeso infada maka akan Salifa. "Nasan komai momy ki kyalesu I will handle everything. "Hmmm tom don Allah karka kai Naziya cikin gidan nan su cutar da ita....... 🖊
*Jumu'at kareem to All my fans Allah ya sadamu da Alkharin dake cikin wnn ranar Amen *
*Matar Soja*
6⃣1⃣&6⃣2⃣
................Bai fada mata komai ba akansu kawai gyada mata kai yayi, sukaci gaba da magana kasa kasa, tana tanbayar shi me yasa yake son takurawa Naziya, "khaleel kabi yarinyar nan a hankali karka kure mata hakuri fa. "Momy so kike ki shagwaba ta inkina fadar irin haka please karki fada Agabanta taji, nifa ba Abinda nayi mata impact ita yakamata kiyiwa fada tana juyani y'an da takeso. Yafada yana d'an daure fuskar shi, murmushi MOMY tayi na farin ciki da kwanciyar hankali ta dafashi da hannu mai lafiya. " kasan bazan bari kasa min ita kukaba, wannan yarinyar farin ciki yakamata tayi ba kuka ba, khaleel kataba ganin ta daga kai tamun koda kallon banza, duk da Abubuwan da na rika yimata? Ka duba yarinyar nan iya zuciyar ta ta tsaya jinyata batareda ta duba duk cin mutuncin da nayi mata ba a rayuwa. Takarasa wasu hawaye na nadama na biyo kuncin ta, "duba kagani mahaifin ta batareda ya duba duk halin da na jefa Y'ar suba ya kuma daukar ta yabaka, saboda karfin Alkwari da soyayyar da sukeyi wa d'an uwan ka, yau maganar da nakeyi Albarkin Naziya nakeyin ta, da bata cikin rayuwata nasan wulakanta zanyi khaleel Hajiya sharefa tayi mun Abinda bantaba zaton kawa zata iya yiwa kawarta ba,All I want zumunci tsakanin mu ya Kara karfi Ashe.... Hmmm Salifa kuma..
Takarasa kalmar kuka na kufce mata. Tashi yayi ya rungume ta " is OK Momy please komai ya wuce ki manta dasu, kuma nima ki yafemin da na bijire miki kuma natafi na barki.
"Aa bakayi laifi ba khaleel hakan shine ya kubutar min da Rayuwar ka da lafiyar ka nagode da baka Yar da ka hada Rayuwar ka data Salifa ba, danayi danasani na har abada da hakan ya faru domin sam batada tarbiya. "Please Momy ki kwanta ki huta ya isa haka. Yafada yana gyara mata kwanciya ya rufeta tareda komawa kan kujera ya zauna, dafa fuskar shi yayi yana shafawa tareda kallon gefen Naziya dake juyi duk tanajin hirar su takasa bacci saboda farin cikin canji da saukin momy.
Ya dauki lokaci kafin ya ja numfashi ya mike ya koma inda take kwance, gefenta ya rab'a tayi dif kamar tana bacci ya kwanta yana kallon saman dakin na tsawon lokaci kafin ya juya ya rungume ta tsam yana Ajiyar zuciya.
Kai khaleel maye ne wallahi tafada a zuciyar ta, wato koda da idon momy dai sai yayi y'an da yakeso, bakin shi ya Dora dai dai kunnen ta cikin rage murya sosai yace "I no you are not sleeping Hajiya, are you happy momy na takamin birki akanki, Hmm duk wayan Amarya dai sai ansha manta don haka ki gama gudun ki zamu hadu. d'an motsawa tayi domin gadon karami ne Wanda ta zungureshi badon taso ba ya Kara manneta yana runtse idanun shi, "kinsan dai baki kyauta min ba ko? This is the worst punishment for me, gaskiya ina kwaruwa Umm.
Shiru tayi mai Saida taji hannun shi ta saman rigar ta yana kokarin zurawa tayi saurin juyowa domin bashi gargadi da ido, yayi saurin cafke lips dinta, yana kallon kwayar idanun ta, tareda juya mata ido Alamar tayi mai shiru. Ya dade yana shan bakinta kamar mayun wacin Zaki tana kallon tsantsar jaraba kafin ya cire ya dora bakinshi saman wuyan ta yana lasa tareda mayarda numfashi nadan lokaci. Tashi yayi ganin hakan bazai taba yimai ba ya dagata tareda cewa " let go. batason hayaniyar su dashi a gaban momy don haka tabishi tana mai gyara mayafin rigarta, ta dauki wayarta tana dubawa kusan karfe daya na dare.
Cikin Asibitin shiru sai hasken wuta ta ko ina ya bude motar shi ya zaunar da ita kafin ya shiga ya rufe ruf, fuskantar ta yayi tareda janyota zuwa kafar shi ya dora kanshi saman kirjin ta yana Ajiyar zuciya.
Ganin bazai ce komai ba tace" please meye haka wai? Idanun shi da sukayi ja ya dago tareda kallon ta na d'an lokaci kafin ya sanya hannu ya kwantar da kujerar motar yace " keep quit my friend, tunda bakisan damuwa ta ba Allow me to sleep OK. Kwanto da ita yayi kan kirjin shi ya rufe idanun shi Alamar baccin zaiyi da gaske. Kafin kace me yayi bacci ta tsaya tareda sauraran Ajiyar zuciyar shi a natse,. Mamaki ya bata batareda ya tabata ba yasha baccin shi har Asuba, Wanda momy ma batasan fitarsu ba tasamu bacci mai cikeda kwanciyar hankali da kuma saukin da taji a jikin ta,
Ganin Ana kiran salla ga jikinta yayi ciwo domin ya kanan nad'eta ya hanata motsi sam, ta d'an bubbuga shi, ya bude idanun shi, baccin bai ishe shiba tace "Ana kiran salla fa. Mika yayi tareda ita a jikinshi yayi salati tareda karanto Addu'ar tashi daga bacci. "You see is All your foult jiya bansamu bacci ba yau ma bai isheni ba saboda rashin jinki da munje gida nasan zanyi bacci mai dadi.
Batace mai komai ba tafara kokarin sauka a jikin shi, riketa yayi " wai ke meke faruwa ne? Kin zama kurma ne da kike bina da idanu ba magana, ko fushin ne da bansan laifina ba haryanzu? "Muje muyi sallah mutane sunfara fitowa. Sakinta yayi saboda lokacin sallah suka koma dakin, har lokacin momy bata tashi ba sabon brush ta bude tayi kafin tayi alwala ta fito. Tasamu baya ciki, domin dole sai yaje gida he can't pray batareda yayi wanka ba domin yasan ya fitarda Abubuwa duk da bai samu Abinda yake soba.
Sallah tayi ta zauna akan dadduma tayi ta Azkar dinta har gari yayi haske.
Likita yayi matukar mamakin saukin jikin momy lokacin da ya shigo, yace is a miracle a dare daya ansamu improvement sosai domin duk nauyin jikinta ya sauka saura gefe dayan kawai Wanda yace a hankali shima zai warke idan taci gaba da shan magani. Tayi godiya da kanta.
Karfe takwas Aunty Raliya ta kuma zuwa da basket din Abinci ta ga Naziya da momy suna hira sama sama ta rashin sabo domin Naziya kunyar momy takeji ita kuma so take tajata a jiki sosai.
Abun ya matukar farantawa Aunty Raliya rai, ta ko saki jiki da momy sukasha hirar su tanata godiya da sa Albarka, ta sake ta d'an ci Abincin da Raliya ta kawo,zuwa karfe goma Tace zata tafi sai ta kuma dawowa, Naziya ta mike tace zataje tayi wanka ta canja tadawo ta Kira nurse tareda bata umarnin ta kula da momyn kafin tadawo, suka fita tare, momy taso tace ta Kira khaleel mana ya kaita Amma batason ta kuma yi musu katsalandan a rayuwar Auren su tasan komai zai tafi dai dai, Allah dai yabata lafiya.
Saida suka fita aunty Raliya tafara yimata fada, meyasa zata ce zata bita? "Aunty ai yasan zan bukaci wankan yatafi batareda niba don haka bazanje gidan ba nidai muje gidanki, ai kayana da na dawo suna can. Shiru tayi kawai kanin mijinta da yakawota ya mayarda su, koda ta tafi tayi wanka ta shirya ta natsu ta karya. bata samu bacci mai dadi ba jiya saboda nacin khaleel don haka Saida ta kwanta na kusan hour biyu.
Khaleel kuwa bayan ya shirya Saida yaje office dinshi yaga meke tafiya domin baisamu sukunin lekawa ba ya d'an dauki lokaci kafin ya dawo Asibitin, Samun momy yayi da Aunty Zarah da tadawo jiya ta samu labari a wurin Aunty Raliya domin duk ta damu bata samun wayar momyn Kwana biyu, fuskar shi ya tamke ya shigo kamar yaga kashi don Allah yagani ya tsani Matar nan shiyasa ya mugun raina ta, hawaye takeyi tana Sannu aunty Allah ya wulakanta sharefa da zuri'ar ta matsiyata. Sallama yayi ciki ciki ya samu gefe daya ya zauna ta juyo cikin fada " khaleel Amma wallahi kai bakada kishin mahaifiyar ka, yaza ayi ace Suyi ma Aunty irin wannan Abun Amma ka zuba ido ka kyale su?
"Zarah kije ke kidauki mataki da kanki dama kece mai babban kaso a duk Abinda yake faruwa a rayuwar gidan mu, don haka karki manta inkin tashi yimusu hukunci ki hada da kanki kema kina bukatar hukuncin.
"Kingani ko Aunty wallahi Ibrahim ya mugun raina ni sai kace ba kanwar uwar ka nake ba kayita zuba min magan ganu son ranka, wallahi zandauki mataki akanka mtsww. "Hope dai badani kike wannan zancen ba da kuma tsakin, domin Zaki iya fuskantar bacin raina fiyeda tunanin ki, girma na kikayi ko kece kika haifeni da zanbaki girma? Look we don't need you here just leave, go and fix your life first, don munafunci ina kike lokacin da ita yayar taki ke bukatar taimako? Were are you? Sai bayan ta samu sauki ki debo dogayen kafafunki kizo kina kawo mana sanabe were are all your relatives, sai lokacin da munafunci ya tashi ku cikawa mutane gida, look am not like Ahmed duk wadda tasan ba zumunci zai kawota gidan muba she is not welcome, kowace ta tsaya gidan tsohon mijinta, especially you Amara.
Tuni Aunty Zarah ta hadiye bala'in ta ganin ya hau yana faman surfa mata that means ajiraye yake da ita, momy ce tace " khaleel that enough OK. Yace "Sorry Momy were is that girl? "Taje ta yi wanka ta canja tadawo. Dama yasan zatayi hakan wato bazata iya fada mai Abinda take bukata ba sai kawai Tayi Abunda taga dama don taga yana sonta yana lallaba ta, OK zai nuna mata koda yana son mace kuma baya daukar wulakancin ta why take mai yawo da igiyar Aure any how? Haushin ta ne ya saukewa Zarah tass tun ma baiji meya faru ba.
Komawa yayi kan kujera yana Danna wayar shi fuskar shi kamar hadari, momy ta kalle shi tace " khaleel bansan me ke ranka ba, Amma na rokeka haukar da kamun yanzu ta iso kar yarinyar nan tadawo ka rufemin ita dafada.
Shiru kawai yayi domin yakai wuya, zarah kuwa mamaki take ciwon ne ya janyo momy har take damuwa da Naziya haka?
Kallon ta Tayi tareda yin murmushi kawai. Domin ta Riga tadawo hanya sambal bata fatan ta kuma karkacewa,
Aunty Raliya tasa aka dawo da ita bayan ta tashi ta shirya cikin kana nan kayanta ta zura katon hijab saboda shigar domin duk native wears dinta na gidan khaleel, harda socks ta sa baki,
Bayan ta zura after dress a sama saboda koda zata bukaci cire hijabin a Asibiti,
Wata irin uwar kasala takeji da tashin zuciya, da batasan dalilin shiba don haka duk sai jikinta ya mugun mutuwa, koda ta shigo cikin Asibitin zuciyar ta tashi takeyi sosai musamman kamshin pharmacy dake tashi a Asibitin,
A cikin natsuwa ta shiga dakin bakinta daukeda sallama yana nan zaune a wuri daya, muryar ta da yaji tuni zuciyar shi ta sauka yaja numfashi tareda zuba mata ido, ta matsa tareda gaida momy da Aunty Zarah da ta zuba mata ido itama tana ganin mugun canji da murjewar da Naziyar Tayi,
Ta koma kusa dashi