Showing 66001 words to 69000 words out of 107087 words
Chapter 23 - AUREN GADO COMPLETE DOCUMENT Book by MATAR SOJA.txt
yafara daya sanin Abinda yayi mata, ko motsi bata iya yi, ba Abinda ke bashi tsoro irin jinin da yake gani, don haka cikin sauri sauri ya saka mata riga ya zura mata hijabi, karfe biyar da rabi, ya kin kime ta sukayi waje, Wanda yayi dai dai da Mommy ta fito, ta bishi da kallon wulakanci, " Ina zakaje yanzu da Asuba? " Mommy hospital she is bleeding. Please kisa maid ta goge kasan dakina ta gyara min gadon.
Tana lafe kamar matacciya a kirjin shi,
Tana jin komai saidai bazata iya motsi ba, " ka nuna min ban isa da kaiba ko, Toh listing to me, idan kuka Fita yanzu kadawo min da ita cikin gidan nan sai na tsine maka, daga inda zaku je ka kaita gidan ubanta, daga yau tabar gida na, kayi Abinda zaka iya nima yanzu zanyi nawa mulkin muzuba nidakai zamuga waye a sama.
Shiru yayi kadan har yayi gaba ya kuma tsayawa, "Mommy don't please. " nafada maka idan yarinyar nan tadawo ban yafe maka ba khaleel Allah ya isa nono na daka tsotsa. Juyawa yayi kawai ya Fita. Zuciyar shi na wani irin d'aci, tanajin komai don haka wasu hawaye kebin kuncin ta, a hankali ya Ajiyeta a motar ya share hawayen ta, bai iya cewa komai ba, burin shi dai ya kaita Asibiti a dubamai ita koma meye zai biyo baya, a natse yake driving, har ya isa family hospital dinsu, ba bata lokaci yasamu babbar likitar wurin doctor Asiya, ta karbeta, tace "Sir Ibrahim meye damuwar? Zuciyar shi daya yace "check her well she is bleeding doctor. "Tana da cikine? No is our first night. Yafada yana komawa gefe tareda nade hannu a kirji, kallon shi tayi ganin irin full confidence din da yake magana, ta girgiza kai, "this Ajebotas Hmmm", wayewa ce taja ko kudi ko rashin kunya? A ranta take magana, tace "excuse us Toh zan duba ta. Wani irin kallo ya mata yace "she is my wife. "I know but bazan iya aikina kana tsaye ba you have to go out. Fita kawai yayi domin yana cikin stress ya bar ta, masallaci ya nufa mafi kusa domin ya sauke farali.
Saida ya kwashi hour guda yadawo, lokacin har tasamu bacci an daura mata drip da Allurai,
Likita yasamu tace "we need to talk sir" let's go to my office.
Saida ya matsa gaban gadon da take kwance, fuskar ta harta fada a dare daya, wani irin tausayin ta yakeji, hakurin ta yayi yawa, a hankali yake fahimtar ita din batada hayaniya tanada hakuri mace ce mai biyayya, Naziya bazai iya hadata da komai ba yanzu a rayuwar shi, Kirjin ta ya shafo ya Fita,
A zaune doctor din take tana rubuce rubuce, yaja kujera yace " Any problem doctor? " yes sir, please kar akuma yimata irin haka, domin taji ciwo ta ciki shiyasa take bleeding, akiyaye gaba arika bi a hankali ba guduwa zaiyi ba you have just started ne, yanzu drip din da na bata zai taimaka mata tasamu karfi, at least tayi two weeks stitches din su warke. "Stitches? Ya tanbaya cikeda damuwa, " yes ba da yawa bane kadan ne, ka bata two weeks everything will be Aright. "Tank you doctor. Yafada ya Fita tana binshi da kallo, "yarinya dole kiji jiki irin wannan miji naki daga gani kin boni.
Zama yayi tareda yin tagumi ya zuba mata ido kamar zai cinyeta, " you deserve to be happy baby, why Mommy ta kasa gano cewa kedin kinfi sauran matan da take so ne , why she hate you? Kyakkyawar fuskar ta ya shafo yayi Ajiyar zuciya, tareda ciro wayar shi a Aljihu ya shiga contact yana searching numbers, ganin number da yake nema yasa yayi dialing, ringing biyu aka dauka, mikewa yayi ya matsa, " Aunty Ina Kwana. "Khaleel kaine ? Ince ko lafiya? "Lafiya Aunty sai dai muna Asibiti da Naziya yanzu, please inba damuwa inzo in dakko ki? " Toh meke damun ta haka harda Asibiti?
Bai taba sanin yanada kunya ba sai yau da yake magana da Aunty Raliya, don haka ya sosa keya yace zazzabi ne kawai. "Toh yanzu Baban yara zai Fita zanbiyo shi, wane Asibiti ne? Yafada mata, tace tana zuwa, yayi godiya tareda Fita yasamu doctor. Yace yana bukatar taimakon ta, "please sister din madam na zuwa you have to explain to her Ina so ta tafi da ita tasamu kulawa kafin in tafi da ita gida, kar asamu matsala gaskiya, two weeks is too much for me. Yafada da zuciyar shi daya, ido kawai ta bishi dashi tace ba matsala, yayi godiya ya tafi.......... 🖊
Not easy for me guys sorry please 🙏
*Matar Soja*
4⃣3⃣&4⃣4⃣
08032252760
08175479641contact this numbers for more information
............ A gida bayan fitar su da sauri ta fada dakin nashi, taga zani daya a kasa ga nakan gadon ma yayi kaca kaca, wani irin turnuki taji a zuciyar ta, wato khaleel da ace Asibiti ta haifeshi da tace anyi mata canje, ta manta da kana haihuwar Wanda yafika tsaurin ra'ayi, kwalawa mai aiki Kira tayi, ta nuna mata dakin cikin takaici " clean this mess right away. Ta Fita sai zagaye takeyi tana neman mafita tarasa ta Ina zata bullowa Al amarin khaleel, Zarah ta Kira tunda farar Safiya, " Aunty lafiya fa safen nan? Tafada cikin tsoro, " Ina fa lafiya zarah, ni bangane aikin malamin nan ba waya rana yayi wata rana kuma lamari ya barkace. " meyafaru Aunty? " khaleel..... Tafada mata komai in details. "Kema Aunty ke keja ki cire idanun ki aiki ai ahankali yake farawa kuma idan kika matsa za ayi biyu don tsab khaleel zai sallami salifa. "Bazaiyi ba don yana tsoron tsinuwa ta shiyasa ko yanzu na fada mai karta dawomin gida inba hakaba banyafe mai ba. "Kash Aunty me kikayi? Kinsan dai bazai sake taba, what up ya nema mata gida daban? Dafe kirji tayi ta tuna da kalmar shi bazai taba sakin Naziya ba, kuma tasan halin Abinta, "zarah kice na bato lamari? "Gaskiya Aunty wata rana bakya shawara kike aikata Abu, bakya yin Abinda ya dace. "Zan janye tsinuwar bari inkirashi in lallaba shi don karya sauke akan salifa. " zai aikata kinsani sarai bai barin Abu abanza.
Kashe wayar tayi ta fara neman shi jiki na rawa. Lokacin ya fito daga Asibiti domin duk hankalin shi na cikin dakin yanda yabarshi yasan momy bazata gyara ba, yaji karar wayar ta, dauka yayi kamar nothing happened, " khaleel Ina kakai yarinyar nan? Shine tanbayar da tafara yimai, yayi shiru kadan yace " Ina hanyar dawowa am close, ya kashe wayar.
Yana dukan sitiyarin yana fesar da numfashi, " I will fight this battle alone Yaya Ahmed, Allah ya jikan ka ya biyaka da Aljannah. Yafada yana jin duk wani damuwar sa ta gushe da ya tuna da cikin ni'ima da farin cikin da ya Kwana, Aure dadi, Naziya karshe ce a cikin mata, tuni yafara kewar ta yaji kamar ya juya ya koma ya rungume ta, jin kanshi yakeyi a sama, koda ya shiga gidan ya parking, masu aiki na gaishe shi yana amsawa cikin fara'a da wani irin Annuri. Gefen momy ya wuce, tana tsaye tana zagaye taja doguwar Ajiyar zuciya ganin shi, ta tashi, matsowa yayi fuskar shi a sake ya zauna a gefen ta " momy good morning, dazu na Fita ba a natse ba. Kallon fuskar shi tayi tana hango sheki da Annuri tareda kwantaccen farin ciki a fuskar shi,
"Khaleel Ina ka kai ta? Answer me? " Momy in her condition Ina yakamata inkaita inba hospital ba? And forgive me if I did anything wrong to you, Ina so inyi miki biyayya momy nima one day kiyi min Addu'a exactly yanda kikewa Yaya na, idan nabata miki rai, forgive me bakin ki guba ne dafi ne, fushin ki damuwa ne, Ina sonki mama na, please ki tayani son Abinda nake so, Momy kin tanbaye ni why I marry Naziya without rejection? How can I reject the woman I love more than my life? Momy Ina son Naziya tun Yaya na na Auren ta batareda nasan zan mallake taba, kince karta dawo cikin gidan nan, bazan dawo da ita ba, insha Allahu I will obey you Momy. Ya zabura ya kama hanyar dakin shi takasa cewa komai, sometimes sai zuciyar ta taso tausar ta saita kasa so take ta bashi hakuri Amma tunanin Alkawarin da tayiwa kawarta da kuma ego dinta ya hanata tana kallo harya shige dakin lokacin maid din na kokarin shinfida mai wani bedsheets, wani irin tsawa ya buga mata " ke uban waye yace ki taba min kaya? Get out.
Jikinta na rawa ta fice, ya kwashe zanin gadon masu stain ya kwabe ya shiga bathroom da kanshi ya wanke su tas Abinda bai tabayi ba wanki irin wannan,
Saida ya gama ya dawo cikin dakin ya canja bedsheets da kanshi, ya daura towel ya shiga bathroom saida ya hada ruwa mai zafi ya shiga ciki shima domin shikan shi yana bukatar su, kwanciya yayi yana wani irin murmushi mai cikeda da ma'anoni, "baby this is your work fa, kinsani gashi, all my joint are paining me, what a sugar. Yafada yana sude lips domin he can still feels her sweetness,
Imagine yake idan ta warke how he is going to spoil her, yanda bazata iya rayuwa batareda shiba, " we are going far away from all this problems. Ya dauki dogon lokaci a cikin ruwan kafin ya fito, zama yayi gaban mirror ya fara kalkale ko Ina na jikinshi, kafin ya fito dakin, saida ya gama nazari kafin ya fito da wata farar shadda, " am ango today. Ya zura harda hula ya ciro agogon shi ya daura tareda katon Azurfan shi,
Kamar ka sace shi ka gudu, haka ya baza kamshi, ya kwashi wayoyin shi ya fito harda nata,
Yana fitowa tana sawo kai cikin karai raya da sanabe, lokacin da tayi arba dashi saida ta kusa zubewa saboda ya tafi da imanin ta, " wow is he really my husband? Oh my gosh. Kamar invisible haka ya ganta, ya fito da wayar shi dake Kara ya yi saurin picking, "Aunty kinzo ne? OK gani nan zuwa. Yafada yana wuce ta cikin sauri.
Kamar doluwa haka ta tsaya har ya bacewa ganin ta yabarta da fitinannen kamshin shi.
Saida Momy ta fito rikeda jaka zata tafi aiki taganta a tsaye kamar wata yar kwaya tana bin kamshi, "Salifa lafiya?
"Hmmm Momy. Tafada tana matsowa cikin salon iya shege, " kin iya haihuwa what an Angel. Tafada tana rungume ta, " kingan shi kuwa? He look very handsome and classy, wow I love him wallahi yafi Ahmed komai wow gwara da ya mutu na Auri wannan......... "Ke meye haka banson hauka, agaban Idona kice gwara da Dana ya mutu? Banson rashin hankalin ki da rashin iya magana. " Allah ya baki hakuri Momy yau ba kida laifi ganin khaleel yasa ba Abinda zai batamin rai yau. Ta rungume ta, " Momy kisa yau yazo gareni please. Cireta tayi a jikinta " matsa min zanje aiki karinyi latti. Kawai ta iya fada domin Abun ya mata wani iri wannan idanun ta budewar su ya wuce misali,
Fita tayi tabarta tana faman tsallen shauki da son khaleel, momy da kanta ta shiga motar ta ta tayar idan ka kalleta zaka gano cewa jikinta a mace yake yau, kawai maganar da Khaleel ya fada mata ce ta dameta musamman kodai ba ita ta haifesu ba? D'an cikinta na tantaba akanta, is she that bad? Me tayi musu wrong a rayuwa da har yafada mata irin wannan maganar? A haka ta tafi jikinta yayi matukar sanyi.
Asibitin ya shiga, saida ya nemi likitar, tace ta sallameta ruwan ya kare kawai zata rika yin sit bath ne, akai akai har dinkin ya warke, nama yiwa Y'ar uwar ta bayani. Tafada tareda rubuta musu wani cream mai saurin warkar da ciwo, ya karba, ya Fita, saida ya d'an tsaya a kofar dakin da take domin kunyar Aunty Raliya yakeji sosai kafin yayi ta maza. Yana tura kofar, ta dukar da kanta kasa domin basai yace komai ba wannan fitinannen kamshin nashi ya isar mata da sakon isowar shi, sallamar shice ta biyo baya, Aunty ta mike daga kan kujerar ta amsa fuskar ta cikeda fara'a. "Harka iso khaleel? "Eh Aunty yafada yana mai kallon cup din hannun ta dake dauke da kunun gyadar da Aunty tazo mata dashi.
Juyawa tayi tafita kawai domin basu space, Wanda hakan yakeso dama, tun shigowar shi yake satar kallon ta,
Tayi mai kyau so yake ya matsa jikinta har wani irin fisgar shi gangan jikinshi keyi zuwa gareta, don haka Aunty na Fita ya daga kafa cikin sauri ya isa gefen ta ya zauna tareda karbar cup din ya Ajiye, taki yarda su hada ido dashi domin ita kam tasan kunya duk Abinda ya faru Ina taga karfin zuciyar hada ido dashi,
Ji kawai tayi ya rungume ta gam a gefen kafadar shi, "Am sorry baby nasa anyi miki stitches, ba laifina bane, lafin kine you are so sweet, so so sweet that I can't control myself, you deserve a gift, but not here, ya dago kanta ta runtse idanun ta, ya ce " please open your eyes kinji I want to see them. Kara runtse idanun tayi don kunya takeji, " oh come on, meye kunya a tsakanin mu yanzu, kin zama ni nazama ke we shear the same bond same blood I can feel you all over my body and my soul,
Lafewa tayi luf a kirjin shi, bata bude idanun ta ba kuma batace komai ba,
" why are you always silent? Talk to me feel free, complained let me know what is going on in your heart even once please, Momy a kullum tana miki fada duk kalmar ta akanki batada dadi it hurt and touch me, ke kuma you don't even react, why?
Sai lokacin ta dago tareda kallon shi cikin ido " me kakeso inyi? In Rama? " you have the right. Yafada yana mata wani irin kallo. " girgiza kai tayi ba tarbiyar da aka dora mu akai ba kenan, babba kullum adai dai yake yaro ke laifi, me tayi wrong? Saboda tanaso ku Auri mata dai dai da Rayuwar ku? She is right tanada dama kuma uwace ta isa, kuma ra'ayi da burinta takeson cikawa, kayi mata biyayya please give her what she want.
Hade fuskar shi yayi, " do you know what that means? " yes ka sake...... Bakin shi yayi saurin dorawa akan nata ya fara tsotsa cikin zafi zafi, har tanajin yana cizon lips dinta da d'an mugunta saida ya dauki lokaci ya janye, " don't repeat that, it hurt to hear from your mouth, na tsani kalmar rabuwa dake ko a mafarki, don't even imagine that again, Aure na dake mutu ka raba takalmin kaza ban rabu dake tun farko ba sai yanzu, mahaukaci ne ni, rabuwa dake yana nufin rabuwa da numfashi na, zan iya rabuwa da kowa bazan iya rayuwa babu ke ba.
Wani irin sanyaya mata zuciya da gangan jikinta kalaman shi sukeyi, duk sun warkar da wani ciwo da damuwar ta, yes da zata iya bude baki data fadamai itama bazata iya rayuwa bashi ba, tsanar da taji wasu Amare na yiwa Angwayen su just saboda sunyi musu biji biji ita ba haka bane a zuciyar ta, she love him more, yes tana son khaleel saboda shi din namiji ne tsayayye d'an ra'ayi in yace yes baya canjawa, ba kamar Ahmed ba, shine ya cika burinta shine yazamo mata mijin da ke share hawayen ta da damuwar zuciyar ta, yes she love him koda shi baya sonta, domin ita har yanzu gani take yanayi ne domin yayan shi,
Jin hannun shi a saman kirjinta yasa ta zabura ta kalle shi, kashe mata ido yayi tareda rada mata" Allow me, I missed them tunfa jiya yafada yana maria raice fuskar shi kamar wani jariri,
Ture hannun shi tayi "Aunty na jira. Dafe kai yayi ya duro, " kinga kinja mun shanyata. Hannu yasa ya sauketa, yace "walk slowly karki karamin wasu kwanakin kisa in suma.
Shiru tayi kawai don yaci ta gano cewa shifa baisan kunya ba, hijabin ta ta gyara ta zura silifas dinta, Aunty Raliya tayi sallama, yace "ya gama kimtsawa Aunty muje. Gaba yayi cikin sauri, sukuma suka biyo shi, satar kallon shi takeyi, yana tafiya, a karon farko tana hango mazantaka da jarumtar shi komai nashi Abin burgewa ne, sai Ajiyar zuciya takeyi har suka isa wurin dalleliyar motar shi,
yanzu take lura da lamarin shi, a koda yaushe sabuwar mota take ganin shi da ita, saboda Alfahari ko rashin sanin Abinda zaiyi da kudi ne ya janyo?
Saurin zagaya wa yayi ya bude mata gaba tareda kallon ta yace "here. Zagaya wa tayi a natse take tafiya domin zafin da takeji, a hankali ta zauna, Aunty Raliya tuni ta shige baya. Saida ya fita cikin Asibiti yace "Aunty kinyi magana da doctor? " eh tafada min komai yanzu ba damuwa muje gidan nawa da ita, Amma banson malam yasani don zai iya yin fada. " no ba Wanda zai sani, in one week ma zanzo indauke ta. " Allah ya kaimu. Tanajin su batace komai ba sai sauke hannun ta da tayi gefen break, Wanda kamar jira yakeyi ya dora kyakkyawan hannun shi akan nata, ya damke tareda murzawa kadan, kallon shi tayi cikin sauri tareda nuna mai Aunty da ido, yagane me take nufi ya basar tareda dauke kanshi yasa a titi, tuki yakeyi cikeda nishadi da farin ciki,