Showing 90001 words to 93000 words out of 107087 words

Chapter 31 - AUREN GADO COMPLETE DOCUMENT Book by MATAR SOJA.txt

04 Dec 2024

5674

ya gaida ta cikin girma ta tanbaya mai jiki yace Alhamdulillah jiki, kafin yayi shiru yakasa tanbaya ko tana nan. Aunty tace " ga mutuniyar nan. Ta Ajiye mata wayar tareda Fita Abinta tana cewa nabarki lafiya nayi wurin neman lada tsaya yanga ke.
Tana kallon wayar taki dagawa ya katse ya kuma Kira taki dauka, yace " tofa khaleel ka shiga uku yau. Ya Kira yafi sau goma taki dagawa haka ya hakura ya kyaleta dole yaje karbar hukunci in yana son yazauna lafiya da zuciyar shi, a daren dukan su basu runtsa ba, khaleel Kwana yayi tsuki ga takaicin su Salifa ga kuma fushin Naziya, ga wani horo da jikin shi kemai wai bazai runtsa ba tunda bata kusa saboda sabo da yayi, zaune ya tashi yanajin kamar yayi tsuntsu yagan shi a gaban ta saboda kewar ta, "kin lalatani kinaso kuma ki gujeni baby no way wannan fushin is unacceptable, bazai yuwuba dole gobe kidawo nan I can't take it.


Daren ya mugun yimai nisa, haka itama Amma saboda Yanayin kasalar da takeji daga baya tayi baccin ta, Assalatun farko yayi masallaci da badon kar ace lafiya ba zuwa zaiyi yayi gadin ta har gari ya waye ya ganta hankalin shi ya kwanta. Zama yayi yana gadin safiya, sai yanzu ya tuna da su Salifa ma, ya koma ciki tareda dakko key ya nufi kofar ya bude, suna shahsheme a kasa, Hajiya sharefa kugu yayi tsami ko motsi bata iyayi salifa kuwa hannun ta a kunbure Kwana tayi kuka saboda azaba daga gani ta targade ne. Suma sauran sai nishi sukeyi zasu iya rantsuwar ba mahalukin da ya taba musu irin wannan wulakancin na khaleel.


Taka hannun salifan da yayi ne yasa ta saka Kara mai karfin da ta tashe su har mommyn tana "wannan y'a akwai ki da shegen raki saikace nima ba ciwon nan ne dani ba wannan akwai tambadadden.... Tayi tsit ganin shi duk suka mike tareda fara bashi hakuri " khaleel kabarmu mutafi yanzu kaga mun gyara ko ina wallahi bazamu kuma shigowa gidanka.... "Kuma nafada muku bazaku bar gidan nan a banza ba bayan kunyi sanadin kwanciyar mahaifiyata Asibiti", Kujera ya samu ya zauna tareda dora kafa daya kan daya yace yanzu inaso inji duk Abinda yafaru bayan bana nan kafin inbarku kufita gidan nan oya I'm all ear's. kayi hakuri bab.... "Kul kika kirani da wannan sunan ni ba sa'anki bane, call me sir khaleel ko sir Ibrahim. "Sir khaleel nidai naso in tafi mommy ce tasa ni zama wallahi ni na hakura da Auranka tunda naga baka damu dani ba, Amma mommy..... Ta bude mai bakin Jakar tsab momyn ta na mintsilin ta karta fada maganar takardaun Amma Kash tuni tayi b'ara, "takardun ka da managern ka yakawo suna nan ban tabasu ba wallahi. Dafe baki yayi yana mamakin greediness dinsu duk Abinda suke dashi wato bai ishesuba nashi suke hari da Dukiyar mommyn shi. "Wato 419 kuke yi kenan? Shine kukazo har gidana zakiyi in the name of Auren hadin zumunci, you know what? mommyna harga Allah so take zumuncin ku ya kullu shiyasa ta matsa mana domin Y'ar ki dagani har Yaya na, Ashe ku zuciyar ku sharri kuke nufin ta da shi, alright zaku ga karshen cin Amana kuwa. "Wayar shi ya ciro ya Kira manager yace ya zomai da police yanzu yanada y'an 419 a gidan shi. Tuni suka fara kuka mommy na rokon shi kawayen nacewa " mudai meye namu aciki kawai mu masoyane abarmu mutafi ba ruwan mu da rigimar gidanku, salifa kinga kunjefa mu a matsala daga Zuwa hutawa. Karku damu zaku huta a bayan kanta. Ya mike tareda Fita ya rufesu ganin suna kokarin biyoshi suna roko. "Mommy kinga masifar da kika jefamu ko nafada miki halin khaleel kingani bantaba zuwa prison ba yau zaki sa in shiga bayan inada Abinda zai isheni Rayuwa ta ko wacce kasa nakeso inada manyan babe da zasu kaini in more, now look what you have got us in to, wallahi bazan yafe miki ba mommy.
Ga Y'ar banza don wa nake duk wannan abun badon ke nake yi ba saboda banaso ki wahala.... "Oh really? All tanks to you now we are going to rot in jail".
Ke kibarni inji da kwankwaso na dakeyi kamar ya fita da gangar jikina.
Kuka tasa tace " ni hannu na bakya gani ya kunbura dakyar nake dagashi wallahi, nidai Allah ya isar min. "Gawa? Inji mommyn. "Ga duk Wanda ya tsargu. Tafada tana murguda bakin ta saboda tsantsar rashin tarbiya.
"Toh mu muyiwa wa Allah ya isa ke Ko uwarki ?, saboda jarabar ki yau kinja mana masifa mu bamuci ko fucika ba. Amma kunci ni shegu matsiyata la'anannu kawai jarababbun ba.. ai tuni dambe ya kaure suka fara jirgar ta mommy na ihu gashi bata Iya kwakkwaran motsi. Karku kashen ya'. Basu daina ba Saida khaleel ya bude kofar, sunyi mata lilis duk sun jijjimata da kunba, police yabawa izinin shigowa yace duk su kwashe su. Tana numfashin wuya dakyar haka aka jasu keeeee, aka watsa bayan mota, mommy sai rokon shi takeyi yayi biris, yanzu burin shi yaje yaga farin cikin zuciyar shi ko a wane halin take?


Wanda tunda ta tashi suka hada lafiyayya breakfast da Aunty suka shirya a basket, ta kintsa cikin wata tsaleliyar doguwar Riga Y'ar Oman ta nade kanta da mayafin, ba fushi yakeyi ba na ba dalili zai sha mamakin ta tayi kyau na fitar hankali dole duk Wanda ya ganta yasan Matar wanice, mijin Aunty a lokacin da zai Fita ya saukesu a Asibitin, tundaga harabar take baza idanun ta ko zata hango shi, Saida suka tanbaya dakin aka nuna musu, bashi ba Alamar shi yana can yana dealing dasu mommy, takara cika, sai a lokacin taga mommy, tayi matukar tausaya mata har wasu hawaye taji sun zubo a kuncin ta, kai Rayuwa d'an Adam ba bakin komai yakeba yanzu mommy Y'ar gayuce haka kwance ko motsi bata iyawa, matsawa sukayi bakin gadon ta dafa hannun ta, tace "Sannu mommy Allah yabaki lafiya. Ta bude idanun ta ta zuba mata ido sai hawaye, so take ta bude baki tafara bata hakuri Amma ba hali, hannu Naziya tasa ta goge mata hawaye, nurse ce ta shigo ta tanbaye ta za a iya bata Abinci? Tace eh su bata mai ruwa saboda bakin daya d'an juya.
Dama sunyi kunun gyada, "Aunty Raliya ta zuba mata, da taimakon nurses Suka d'an dagata saboda nauyin jikin ta jingina mata filulluka, cokali tasa tafara bata kunun Tanayi tana gogewa saboda dawowa yakeyi kamar jaririyar da ake koyawa cin Abinci, ido kawai take binta dashi da hawaye, sai sannu sukeyi mata, Aunty Raliya tace " kinga shirmen ki Naziya ki tsaya tunjiya saboda kula da ita kin kama kin tafi. "Aunty laifin shine ko bari baiyi na gantaba Ashe jikin yayi tsanani har haka ne, yanzu bazan koma ba zan tsaya da ita anan inkinje ki sa akawomin ko Kala biyu ne masu saukin sawa.


Tunda yagama dasu cikin gaggawa yayi wanka ya shirya cikin d'an kareriyar shadda Arsh guntun Riga tasha dinkin gayu na maza, ya fito yafada mota, hankalin shi ya kasu kashi biyu, mommy da Naziya, don haka ya yanke hukuncin zaije Asibitin first ya dubata don yasan inyaje wurin Naziya zai iya mantawa da kanshi acan, koda ya isa Asibitin yasha mamaki, Wanda tundaga kofar dakin kamshin ta yafara yimai welcome, wani irin Ajiyar zuciya yayi tareda murmushi kadan yace " my happiness tunkafin ya ganta....... 🖊






*Matar Soja*














5⃣9⃣&6⃣0⃣












................ Ita kanta ta san ya isowa tunbai karaso ba, don haka tuni ta Kara hade fuskar ta tamau domin tayi mugun daukar fushi dashi, tuni ya ji wata natsuwa ta ziyarci zuciyar shi, cikin takun kasaita ya shigo, hade da sallama kasa kasa idanun shi a sama, domin ba Abinda yake buri sama da yayi ido biyu da ita, yayi matukar kewar ta, sai jera Ajiyar zuciya yakeyi tunda ya sauke idanun shi akanta, gangar jikin shi tuni ta amsa gayyatar ganin ta da tayi tank God ma manyan kayane a jikinshi, a bu biyu yanzu zai hanamai rungume ta ya rafe zafi, nafarko Aunty Raliya na biyu momy, don haka ya saita kanshi yayi gyaran murya, tareda gaida Aunty, tamai ya gajiyar hanya da mai jiki, ya Amsa cikeda jin kunyar ta.
Kafin ya matsa gab da gadon, taki ko dago kanta sai bawa momy kunun take tana gogewa, he wants to touch her amma no way, don haka ya waske yana fisgo maganar "momy sannu. Ido ta juyamai Alamar amsawa, fita Aunty Raliya tayi domin amsa waya, yayi Ajiyar zuciya yayi saurin riko hannun ta batareda damuwa da idanun momy ba saboda he can't help it, tayi saurin dago kyawawan idanun ta masu rikita shi tace " meye haka agaban momy please stop. Tafada tana karkata kanta, " why kika ki tafiya gidanki kikatafi na Aunty Raliya? Hannun ta take kokarin kwacewa amma takasa don rai ita tasan kunya, momy Naji Nagani wani irin dadi takeji y'an da yarinyar ta nuna mata kulawa ga kuma Alkunya da zata iya mikewa itama zata basu wuri su zanta da junan su, Amma ko yanzu abun mugun faranta mata rai yakeyi har ya nuna a fuskar ta, "let me go please. Tafada" I want sai kin fada min dalilin da kika tafi gidan Aunty kuma nakiraki kinki daukar wayata kuma kinki kunna taki why?
Dago kanta tayi ta kalle shi cikin fushi tace ka sakarmin hannu idan kai bakajin kunyar idanun momy ni inaji please let go. "Never ever, if I let you go in zauna da wa? "Your second wife da kakeson kasancewa da ita that's why ka koreni batareda kama bari na duba lafiyar Momy ba jiya that's why na koma inda dama ka dakko ni kafin mubar kasar nan, ni nasan matsayina banda wani value a wurinka, kuma am not here because of you, nazo saboda nadamu da lafiyar momy tana warkewa shikenan.
Wani irin kallon what is wrong yake mata, momy feels bad saboda itane duk wannan mis understanding din ita tajawowa d'an ta, kallon Naziya tayi taga ita din dai data raina ita tafi dacewa da d'an nata ga hakuri da tarbiya, don haka taji duk duniya ba Abinda takeso yanzu kamar ta warke ta gyaro kuskuren ta,
Mikewa tayi da cup din ya Kara rikota, " Naziya please stop it, ko so kike ki dagamin hankali um? Dagowa tayi taga momy ta rufe idanun ta, ta ce "I said let go of me. Shima kallon momy yayi kafin ya Kara matsota cikin rage murya sosai dake dauke da damuwa, "meye nayi kike kokarin horani haka please am sorry koda ni bansan laifina ba kiyafe min but I can't handle your anger on me.
Fisgewa tayi ta yi bathroom domin dauraye cup din da spoon, ya runtse idanun shi tareda dafe kai " oh my god khaleel ka boni. Yafada tareda binta cikin sauri, tana kokarin fitowa ya maida ita tareda datse kofar, "kallon shi tayi fuskar ta a tamke "meye haka Aunty Raliya zata iya shigowa kuma kasan momy dai Nagani ko? " Hmm so what? In zaki yi kokarin horani da irin wannan new attitude din ya kikeso ni inyi behaving, tell me? Look am not use to this, and I can't take it any longer please forgive me if I wrong you.
Ji tayi yakara tunzura ta wato shi baisan laifin shiba, don haka cikin zafi ta dago tareda cewa " ba Abinda kayimin kawai bana son damuwa leave me alone OK.
"Hhhhh story, rubbish, you are insane Naziya, leave you alone, ni khaleel? You are dreaming wallahi, ban hakura dakeba tuntuni sai yanzu da kika gama shigewa cikin rayuwata kika yimin dalla dalla, hannun shi yasa cikin sauri ya fisgo kugunta ya hade ta da Kirjin shi, Saida yaji kamar ya shekara bai kusance taba saboda shauki da kewar ta, "Ahhhhhh Hmmmm. Yafada tareda kankameta kamar zai mayarda ita cikin jikin shi, kokarin kwacewa takeyi ya hanata dole tayi lakwas tana sauraran bugawar zuciyar shi tareda rawar da jikin shi keyi kamar bai saba rungume taba" baby banyi bacci ba jiya kinsaba min da yin bacci kina saman kirjina bayan kin shayarda ni zumar ki tareda madarar ki mai rikita kwakwal war mutum, why kike fushi dani why kika barni nikadai jiya why kike son ki gujeni bayan kinsan zuciya da gangan jikina bazasu dauka ba?
Samu tayi ta fisge haka kawai taji yanaso ya tayar mata da feelings a Asibiti a banza yabarta da Abin kunya, tana juyawa ya kuma hade jikin shi da bayanta yasa hannu ya rungumo Dukiyar fulanin ta tareda matsawa kadan yana gwama numfashi, "Am honey, kinji let go home yanzu zamu dawo please baby. Yafada yana goga mata jikinshi, she can feel how hard he is, tayi saurin bude kofar domin takai gab ta fisge ta gudu.
Matsawa yayi baya kadan ya dafe bango tareda runtse idanun shi ya dade a wurin kafin ya d'an dawo hayyacin shi,
Ta gyarawa momy kwanciya tareda komawa gefe taja kujera ta zauna, Aunty Raliya tashigo, Wanda har lokacin bai fitoba, tace "ni zantafi nabar yara Allah yakara lafiya Ina khaleel din? " gani Aunty yafada kanshi kasa domin yasan for sure yadago fuskar shi zata ga canjawar idanun shi, yace "bari muje in sauke ki tom, "Aa Wallahi ga mota nan megidana ya aiko yaron shi Allah ya bata lafiya.
Godiya yayi mata Naziya ta rakata ya zauna tareda bin bayanta da Kallo yana tausaya wa kanshi, Saida Auntyn ta tafi tadawo,
Still fuskar ba walwala, ya kalleta cikin da tausayin kanshi yace " muje ne? Banza tayi mai ta dauki Jakarta karama ta ciro wayar ta ta kunna.
Tafara game, karkace kai yayi yana kare mata Kallo tundaga fuskar ta har zuwa kirjinta har kafafunta data zame takalmin ta dora daya kan daya, jajur dasu mulmul, ya hadiyi miyau Kut a zuciyar shi yace " kinada Abinda duk zakija min aji yarinya is your time. Haka suke zaman kurame Wanda har doctor ya shigo tareda duba momy yafita, suka cigaba da zaman haka badon zuciyar shi nasoba sai dan baida yanda zaiyi, idanun ta akan su momyn khaleel din ma kebata tausayi yanzu da tanada baki da ta lallashi Naziya domin ta rikemata yaro hankalin shi ya kwanta,
Sallamar su Shukrah da malam harma da Inna da sadiq ne yasa ta zabura cikin matukar murna ta nufesu, shima mikewa yayi cikin girma mawa ya gaida surukan nashi, malam yace yamai jikin? Sukace Alhamdulillahi.
Matsawa tayi zata rungume Inna tace " ke bani wuri ingaida mai jinya mara kunya. Shukrah tayi dariya tace Aunty nidai Rungume ni nayi kewar ki. Suka rungume juna yana kallon duk wani motsinta kamar ya sace ta ya gudu yakeji, ganin ta yakeyi kamar ma bai taba Rayuwa da itaba,


Komawa sukayi gefe itada Shukrah su kuma suka matsa jikin gadon suka fara gaida ita, "Sannu Hajiya Allah yasa kaffara ne. Inji Inna da sai yau suka hadu da juna ido da ido, kallon iyayen Naziya takeyi tana hango tsantsar datti jantaka a fuskokin su, malam yace "kulu ciromin Ruwan zam zam din nan da kunnen magaryar. Yafada yana zama gaban gadon, a wurin ya balle Y'ar Karamar robar Inna tabashi cup ya juye ya fara Addu'a a ciki tareda mutsika ganyen magarya yace Naziya zo ki karba ki juye a gora kuna shafa mata a hannu da kafafun ta har fuska sau uku a yau.
Malam ya dade da sanin wasu mutane basuda yadda shiyasa bai hado komai ba yayi wannan agabanta idan taji sauki bakinta ya bude zai iya bata wani, a take Naziya ta yi y'an da malam yace Wanda tunda ake shafa mata a kafafun takejin wani irin sanyi hade da jin jikinta na rage nauyi kamar tace kar Naziya tadaina, a ranta nadama takeyi mara Amfani wasu hawaye take fitarwa na rashin bakin da zatayi godiya,
Khaleel kamar ya goya su yakeji y'an suka nunamai karamci da kulawa, yana Kara godiya da Allah ya hadashi da surukai nagari, basu dade ba suka tafi, yarage daga shi sai ita, matsowa yayi yace "am hungry madam in baza abani Abincin cikin rigaba abani Abincin da zanci. Yafada yana rage murya tareda kashe mata ido, mikewa tayi ba musu ta zubamai Wanda su Inna suka kawo shinkafa da naman zabbi,
Ta hado mai da ruwa mai sanyi domin akwai dispenser a dakin ta Ajiye ta juya.
"Kinsan tun jiya banci komai ba kuma kinsan bana iya cin Abinci nikadai yanzu kizo muci. "Ni ba wannan nakeso ba. Tafada tana tura baki. "Oh lobster or crabs? Yafada cikin mamakin y'an da ta juya cin wainnan Abubuwan. "Ni shrimps nakeso. Iyakar gaskiyar ta tafada, ya fara cin Abincin shi Saida yayi kat yasha ruwa, ya gyara zama, zuwa tayi tadaga plate din ta saka a, basket tadawo tareda tsayamai akai, "yunwa nakeji nima. Tafada cikin fushi domin yasan sarai me takeso, " bude idanun shi yayi yace ga Abinci nan kici in kuma nine muje sai kin koshi.


Komawa tayi can kusa da momy ta zauna, Abinta ta share shi, tashi yayi ya fita, Wanda yana fita y'an uwan shi suka shigo daga gidan kawun shi. Haka tayi ta karbar baki bayanan har zuwa magrib ta rage ita kadai, ta kuma shafewa momy jiki da ruwan Addu'ar, anan take shinfida dadduma tayi sallah domin kayanta a yalwace suke, bai shigo ba sai bayan isha'i.
Ya matsa tareda gaida momy kafin ya ce ta tashi lokacin tafiya yayi su tafi gida don ba akwana anan. "Ba inda zanje inbarta ita kadai intana bukatar wani Abu fa? " nurse na nan. "Am not going nama fadawa doctor zantsaya kuma ga ruwan maganin ta Anjima zankara shafa mata, kai katafi.
Kamar ya dora hannun shi a kai ya buga ihu yakeji,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login