Showing 33001 words to 36000 words out of 107087 words

Chapter 12 - AUREN GADO COMPLETE DOCUMENT Book by MATAR SOJA.txt

04 Dec 2024

5656

yaushe kafara sonta? This is not About yaya Ahmed ,this is about you, yes saboda naji yanda kukayi da salifa why kaki Amincewa da salifa ka amsa Naziya, why?
Zaburowa yayi ya nufota kamar zai shake ta, "baki Ajiye ni ba so don't question me again, kuma kije kiyi duk tunanin da zakayi I don't care, one last thing, in kinga ban Aure taba sai in bana raye, idan zaki iya zama ki zauna idan bazaki iyaba see your road. Yafada yana nuna mata hanya, juyawa tayi da gudu tafita ya bita da tsaki tareda cewa "useless.


Dakin momy tafada har bacci ya dauke ta Wanda ta dade batasamu tayi irin shiba domin rasuwar Ahmed, yau ma da taimakon maganin hawan Jinin da Aka bata ta samu yadan dauke ta, fadowar datayi tareda buga kofar yasa ta zabura tareda dafe kirji tana jin bugawar zuciyar ta yana karuwa, "kalu innalillahi, ke Fauziya lafiya kika bugamin kofa tareda fadomin daki kamar y'an fashi.
Kuka tasa mata mai karfi, kince zakiyi mai magana gashi yace sai ya Aureta, ni wallahi bazanyi kishi da yar talaka ba kuma Y'ar kauye. "Oh yanzu bazaki iya bari muyi maganar da safe ba? kinga bacci nakeji. "Allah bazaki runtsa ba Indai ni bazan runtsa ba."Toh baki Yarda dani bane Fauziya? nice fa, bazan taba Amince wa a hada min iri da jinin talaka ba, saboda soyayyar da Ahmed ke mata ya fadi ya mutu yabar ni don haka bazan Yarda ta dawo ta karasa min gudan da yarage ba, kina ganin Y'ar nan kinsan ta gaji maita daganin ta mayya ce.
"Ni Ina ganin yana sonta ne fa. "No no no ba wani so, yaushe d'an uwan nashi ya mutu ke baki san soyayyar dake tsakanin shi dashi bane ko Auren ki ya karba saboda sa bakin Ahmed badon niba, a duniya Khaleel zaiyi komai saboda Ahmed Inada Wannan yakinin, don haka kicire zancen Khaleel zaiso yarinyar nan bayan yanada mace kamar ke. "Hmmm ni ai baya sona kema kin sani Khaleel baya son kowacce mace baida lokacin mace, Ina tsoron ranar da zaiso wata irin su basu iya fadawa soyayya ba, ranar za ayi biyu kuwa domin zan iya kashe macen da duk Khaleel yaso, ni nayi dakon soyayyar shi don haka idan har akwai wadda Khaleel zai so to nice.
"Naji zo ki kwanta a nan don girman Allah kibarni in kwanta maganin nan aiki yakeyi ajikina. Da k'yar ta samu ta kwanta sukayi bacci.
Asubar Fari yabar musu kasar su batare da yajira sun tashiba, maid ya fadamawa tafada ma mommy ya tafi, Wanda saida tayi kuka sosai lokacin da yarinyar ta fada mata, wani gefe tana mai kewar Ahmed yaro mai biyayya, "Allah ya jikan ka yaron kirki", zabin ka ne kawai ya sabawa ra'ayina Amma kai d'a ne nagari Ahmed, Allah yakai haske kabarin ka.
Koda ta nemi wayar shi, lokacin yayi nisa a sararin samaniya, Wanda yatafi da kewar Abu biyu, Wanda yana fatan kafin yadawo yarage tunanin su domin samun zaman lafiyar zuciyar shi.


Gefen Naziya haduwa sukayi washe gari Wanda Aisha tabi bayan Naziya tareda cewa "gaskiya Innan mu Ki cire kara ki fadawa Malam gaskiya kar ya Yarda da had'in nan, domin tasha wuya a gidan nan batareda mun fada muku ba, nidai bana goyon bayan ta Auri wani kanin mijin ta, wane dadi ta tarar a gidan mijin nata da zata koma cikin shi?.
"Toh madallah naji ku kuma nasan inda tasamu zuga, Wato dukan ku kun canja hali banida labari? Malam ya fara fada kafin ya karaso ciki ya zauna, "Hauwa, ki zama sheda, da farko bani nayiwa Naziya zabin mijin ta ba duk da a Musulunce ni keda hakkin zaba mata mijin Aure a matsayin ta na budurwa, banyi hakan ba, can suka hadu dashi tace taji tagani, duk Abinda ta fuskan ta a gidan Aure kaddarar tata rayuwar kenan, kuma yanzu mijin ki ya tafi yabar wasiyya akan d'an uwan shi ya Aureki na fita hakkin ki a matsayi na na mahaifin ki ba neman shawarar ki nakeyi ba, Agaban ido na da na yaron nan ki kace wai bakya son shi, saboda rashin da'a, to ki rubuta ki Ajiye Indai Ina numfashi, daga ranar da kika fita takaba daga ranar zan daura miki Aure da Ibrahim don Allah Naziya kifito ki nunawa duniya ni Malam Abu nayi miki Auren da bakiso, don haka nagama magana. "Kayi hakuri Malam" inji Inna da sai yanzu ta fara magana, don Allah karkayi wani dogon tunani kazartar da duk Abinda yake dai dai, nasan duk hukuncin daka yanke kana da taka hikima. "Malam Kayi hakuri kokarin lallashin ta mukeyi wallahi. Inji Raliya, tashi yayi kawai ya kade babbar rigar shi ya fita, Wanda sai lokacin tasaki d'an karamin kuka tareda toshe bakinta kar Malam ya jita, "Akul Naziya, Aure na sama da shekara talatin idan kikaja min bacin rai saboda boyayyan bakin halin ki bazan yafe miki ba. A'a Inna ya haka? don Allah karkiyi saurin yimata baki. Inji Raliya, ba baki nake mata ba dawo da ita nake cikin hayyacin ta. Rarrafawa tayi da sauri ta rike kafar Inna. "Na tuba Inna wallahi bazaki kuma jin nace wani Abu ba akan maganar nan, ba zan kuma musu ba, ki yafemin don Allah Inna. "Allah yawa Rayuwar ku Albarka baki daya, Aisha kirika hakuri ke babba ce a saman ta in bazaki kwantar mata da hankali ba karki nemi tayar mata dashi.
"Afuwan Inna kuyafe mana. Tashi tayi itama tabarsu a cikin dakin, suna Kara tausar ta. Matsowa Raliya tayi tareda dafa ta tace " ki share hawayen ki, jikina nabani Naziya zakiyi farin ciki fiyeda Auren ki na farko, kinsan me? Girgiza kai kawai tayi badon tana farin ciki ba sai don tana gudun bacin ran iyayen ta, "saboda Khaleel daban yake bazaki gane ba sai nan gaba keda kanki zaki fadamin. Allah kadai yasan Abinda ke ranta amma ita tasan bazata taba son Khaleel ba domin jinin ta da nashi bai hadu ba, zaman ta da Ahmed soyayya ce sanadi Amma shi tasan zama ne bamai dadi ba. Haka suka wuni suka tafi gidajen su, Wanda daga nan ta Kama kanta tareda dukufa Addu'oi akan mijinta.
Wasa wasa aka fara aikin ginin malam Wanda batasan daga Ina Abun ya samo Asali ba, cikin wata guda har angine dakunan Al majirai sunkoma andawo gyaran cikin gidan Wanda aka rushe gefen da suke ciki aka bugawa Inna flat Dan madai daici Da bazai cinye filin tsakar gidan ba sai dakuna biyu a waje, daya na Malam daya nasu Naziya. Aiki ne dayaja kudi Abunka da akwai su gamasu aiki birjik, mamaki takeyi sosai akan Wannan gyaran Wanda saida takasa daurewa ta tanbayi Inna shin Waye yake musu irin Wannan gyaran ne? Tafada mata wasiyyar mijinta ce kanin shi ke isarwa, a ranar saida ta shiga daki tayi kuka sosai.
Tareda yi mai Addu'ar Allah yakai haske kabarin shi, tasan tayi babban rashi a rayuwar ta, a duk lokacinda ta tuna da kudurin shi nason ya huta da ita sai tayi kuka, yaso ya taba kirjin ta kamar me kunya ta hanata, Ina ma ana dawo da hannun agogo baya da ta Bashi dama yayi yanda yaga dama da jikinta kila data rage takaici, wani irin bakin ciki takeji idan ta tuna cewar Khaleel zata Aura domin tasani Malam baya magana biyu.


Cikin wata uku gidan nan yayi tsab bazaka taba gane shiba waje da ciki kowa sai ya yaba a unguwar, Almajirai sun samu gata domin odar katifu irin na yan boarding akayi musu Wanda a wanna dalilin yasa tsangayar take Kara bunkasa. A gefen gidan momy kuwa tun bayan tafiyar khaleel da sati biyu Fauziya ta tattara nata tayi tafiyar ta Tareda cewa "wallahi sai mijin ta yadawo zata dawo bazatayi gadin wata uwar miji ba, Wanda hakan ya taba mommy sosai domin tasa ran ita zata tsaya ta debe mata kewa, wani lokacin ta kanyi kukan rashin Ahmed don dai tana fita aiki ne Amma zaman kadaicin yana mugun tabata, watannin Sam ba masu sauki bane a wurin ta. Gefen Fauziya a kullum suna waya da khaleel yana kiranta tareda fada mata tayi hakuri idan yadawo komai zai dai dai ta, domin yasan cewa akwai hakkin ta a wuyan shi yana kokarin tursasa zuciyar shine kawai gudun hakkin ubangiji, bata taba fadamai cewa bata gidan ba, sai ranarda sukayi waya yafada mata yana hanya cikin satin bayan ya kwashe kyawawan watanni hudu a kasar ta China,
Kawai Mommy ganin ta tayi tana shiga part dinsu lokacin tafito zata tafi aiki, "A'a Fauziya andawo? " eh bakya kaunar indawo din ne to na dawo. "A'a murna nakeyi ai gidan shiru ni kadai, yanzu dai zanje aiki in nadawo mayi magana, ta bita da harara, "Y'ar sa ido kawai mtswew.
Wanda Mommy murna takeyi domin ita zaman Fauziya a gidan ta Kara mata girma yakeyi tareda mutunci a cikin kawayen ta don haka duk yanda zatayi zatayi taga ta rusa maganar Auren Naziya da khaleel, zakuma ta gyaro zaman Fauziya da khaleel Indai ita tahaife shi....... 🖊








*Matar Soja*
















🌻🌻AUREN GADO🌻🌻







*Matar soja ce*






Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
Y'AY'AN GATA
And now AUREN GADO,














Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y'an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,


2⃣3⃣&2⃣4⃣


.............. A katon filin jirgin yafito yana Takawa daya bayan daya kamar wani prince, sheki yakeyi yana wani irin haske, idanun shi dauke da katon eye glass, baka ko ganin kwayar idanun shi, fuskar shi dif take ba Annuri yakara haiba da cika ido, watannin hudu sunyi matukar taimaka mai wajen warkar da damuwar rashin dan uwan shi kadan, driver ne tare da manager dinsu ya tareshi, gaisawa sukayi ya shiga motar suka zuba mai duk kayan da yazo dasu, suna tafiya yana discussing harkar business din su Wanda an samu cigaba sosai a cikin watannin fiyeda shekarun baya, domin shi mai zafine kuma baida sanyi kamar yayan shi, yana bin diddigin komai ma'aikatan sun san an samu canjin boss ba wasa, kuskure kadan yagani ko yaji tun yana China zaisa ayi firing mutum a aiki.
Kamar daga sama suna zaune dai dai itada mommy suna hira mommy na Kara lallashin ta tareda alkawarin komai zaiyi dai dai idan yadawo tunda yafara sauraran ta. Kawai sukaji sallamar shi sama sama, wani irin zabura sukayi duka tareda sakin baki, suna mai welcome, zama yayi kawai gefen mommy ya gaida ita tareda dan sakin fuska, domin uwa uwace koda kuwa abola take yawo, he missed her domin fushin da yakeyi da ita yasa tunda yaje baya kiranta baya son ko jin muryar ta sai in ita takirashi, he know she is wrong, kuma shima he is wrong, domin ba Wanda yabashi damar watsar da uwar shi, riko Hannun ta yayi tareda sakin murmushi, "mommy am back. I'm glad my son, ya harkokin ina ji a bakin manager komai na tafiya normal. "Yeah Alhamdulillah. Wani irin rawar kafa Fauziya keyi ta matso tareda zama gefen shi tadafa cinyoyin shi dake cikin blue jeans dinshi sabo dal, "Baby wannan irin surprise haka dama kafada, am happy wallahi. Ture hannun ta yayi tareda mikewa yace" OK bari inshiga ciki zanyi wanka in huta, mommy please am hungry. Jikin ta narawa tace bari in hada maka meal din ka just five minute,Ta wuce murna fal cikin ta, tarar shi Fauziya tayi tace "darling muje part din mu mana nan akwai takura ba sakewa".
Mugun kallo ya watsa mata kafin cikin zafin rai yace "uban waye zai takuraki anan, now listing I know exactly what you are doing, ko ki dawo nan ko ki yi ta zama acan ke kadai, saboda bana ra'ayin zuwa wanna gidan if you are ready ga dakin ki can! Ya wuce abun shi.
"Kutumar uba wato dakin da Y'ar kauyen nan ta zauna yakeso ta dawo wallahi bazata dawo nan ba sai dai duk Abinda zai faru ya faru. Bin bayan shi tayi bayan ta gama dogon tunanin ta, lokacin harya tube ya daura towel, tuni taji wani irin feeling ya taso mata domin khaleel fa namiji ne complete ba algus ya ginu ya keru, wani fesar da zafin bakin ta tayi kafin ta matsa tana karairaya zata rungume shi.
Hannu yadaga mata "please, bana son disturbance, nagaji now get out.
Haba khaleel wane irin daukar Alhaki ne wannan? you're my husband why All this?, ko bankai mace bane, Auren mu wata hudu Amma ace ko hug baka bani damar yiba. "Go and ask mommy idan ta Amince da hakan saiki dawo now out. Yafada yana wucewar shi bathroom. Fita tayi kawai rai abace taci karo da mommy, me yafaru kuma kinfito da bacin rai? "Ba dole ba, yaza'ayi ace wai sai na tanbayi izinin ki zan rungumi miji na? gaskiya kekam a bincike ki kina wa yayan ki asiri ne wane irin biyayya ce suke miki kike cutar dasu, so kikeyi nima inyi rayuwa irin ta Naziya? wallahi ko kina so ko bakyaso sai kinganni da cikin khaleel. "Haba Y'ar lelen mommy zo kiji, ke baki iya siyasa ba keda zaki caba ado ki makalewa mijin ki, ya zakice banason hada iri dake Fauziya, duk soyayyar da nake nuna miki haba ki rika ragamin mana. "Nidai kiyimai magana yadawo gefen mu Ina jiran shi. "Jeki zanturo shi kin ji. Ko sauraran ta batayi ba ta fice, saida ya dauki kusan minti talatin yana kwance tareda runtse idanun shi a cikin ruwan, shi kadai yasan tunanin zuciyar shi, wani irin murmushi yayi na gefen baki, kafin ya fito ya dauraye jikin shi, ya daura towel ya fito, mommy da ya gani zaune da Abincin shi tana jiran shi yasa yace "oh my mommy am coming tank you, I really miss your cooking.
"Oh son kayi kasa kaya kazo kaci. Kananan kaya yasaka kafin yadawo yazauna, akaron farko yafara bata labarin komai kafin yayi shiru, domin tuno da dan uwan shi da yayi, "I promise, Yaya zanyi duk Abinda kake burin yi kafin nawa. Shiru tayi tareda dafashi, "khaleel, mutuwar Ahmed gibi ne babba a rayuwa ta and all tanks to wannan Y'ar gidan talakawan, look son kaga idan Har na isa dakai kar inji ka yarda da Auren yarinyar nan, idan kana so ka ciremin kewar dan uwan ka kabi Abinda nakeso. kallon ta kawai yayi ya janyo Abincin shi yafara ci, bai kuma cewa komai ba har ya cika cikin shi fal ya kora da juice, "mommy zan kwanta domin nagaji sosai, later zamuyi magana.
Kallon dan rainin wayau tayi mai kafin ta kwashe kwanonin ta tafita, wato duk maganar ta bata bukatar Ansa, saida yaga ta fita yaja numfashi, "am sorry mommy she is my wife now! Auren mu ya dauru tundaga ranar da tafita takaba, don haka soon zata tare agidan nan.
Baccin shi ya shaka bayan ya rufe kofar saboda bai son damuwar Fauziya.
Tana can ta cika tab tana jiran mijin ta ga mommy ko zancen batayi mai ba saboda damuwar Auren Naziya yafi tsaya mata arai. Bai tashi ba sai la'asar yayi sallah ya shirya yafito domin yanada Abunyi, part din yayan shi ya leka yaga ba kayan salifa, wayar shi yaciro tareda kiran manager yabashi umarni, akan ya nemo mai best company na furniture's a kano saboda he want to renovate the house, baya bukatar tsohon Abu a ciki, saida ya gama tsara komai ya fita daga gidan.




Tun fitar ta takaba ta murmure tayi tas da ita ba ruwan ta da komai fitama batayi dama kuma ita bamai yawo bace, tana cikin gida tana taya inna aiki ko tana chat a wtstp domin yana rage mata tunani da kewar Ahmed dinta, a kullum ta kalli yanda baya duniya Amma ya inganta rayuwar su Abin na mugun faranta mata zuciya, hatta da dakin su an saka musu gado da sabuwar katifa, dama basuda talaucin Abinci domin Malam ba mutum bane da ke zama, nema yakeyi iya karfin shi, a zaune take yanzu a karkashin bushiya itada shukrah suna hira sama sama tana chat, tana cikin adon ta cikin riga da sket na shadda orange sabuwa da Aunty Raliya ta dunka mata na fita takaba, dinkin yayi kyau sosai yayi cib a jikin ta, jikinta ba ko mayafi dankwalinta yadan zame kadan kana hango kwantacciyar sumar ta agaban goshin ta, yanzu Almajirai basa shigowa gidan saboda duk Anfitar dasu waje, suna sakewa sosai, Inna ce ta fito dauke da robar gyada mai bawo ta zauna itama a wurin, "Shukrah sa hannu mu bare gyadan nan da ita zamuyi sanwar dare, waccan inta dauki waya bata ji bata gani. Ajiye wayar tayi tana Dariya, "kai inna ai zan Ajiye tunda ga aiki, Amma inna me yasa bakya son a bare miki gyada a injin sai barar hannu? "Kyuiya ke damun ku yanzu" mu da Ina mukaga wainnan Abubuwan, ko nikan masara sai mu niketa a dutse, Yanzu aiku yan gayune, inkai gyada ta injin a farfashemin rabi yabi bawo. Sallamar da akayi ne yasa suka amsa tareda dagowa, Inna ta saki baki tareda cewa" maraba da mutanen ikko, mai sunan Malam kaine a gari?, dukan su sakin fuskar su sukayi, Shukrah ce tafara cewa " Yaya Sadiq oyoyo kaine? Matashi ne kyakyawa ba laifi ya matso wurin da suke Shukrah ta Bashi wurin zama ya zauna ya gaida Inna tareda gaisawa da Naziya tareda yimata gaiduwar rasuwar mijinta, Sadiq Almajirin Malam ne da yazauna a gidan kusan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login