Showing 54001 words to 57000 words out of 107087 words
Chapter 19 - AUREN GADO COMPLETE DOCUMENT Book by MATAR SOJA.txt
tasa mai karfi " na shiga uku" ni balkisu khaleel Asirin yafi kamaka wato yarinyar nan da biyu ta shigo cikin zuri'a ta, Amma anyi bakar kaddara, saboda ita kasaki fauziya nasani badon niba innalillahi, wallahi zabi yarage naka ko ka Auro salifa ko kasake ta ko in tsine maka Albarka. Mikewa yayi tareda cewa " mommy lallashin ki na ke yi ni ba Ahmed bane Amma nasan hakkin ki kuma nasan dokar da zan tsallake Allah ya hukunta ni don haka na zabi ki Auro salifa tazo ga filin gidan nan ba Abinda zata tsaremin saidai duk Abinda ya faru wallahi zunubin baya wuyana, domin Karin Aure yanada sharudda bazanyi Adalci ba bazan iya adalci ba Naziya daban ce. Ya fita domin duk zuciyar shi ta koma kanta, ya sani a cikin Kwana biyun sunyi mugun sabo yana ganin yanda yasamo kanta tafara sakin jiki dashi sosai.
Don haka jikin shi na rawa daga ciki zuciyar shi na kadawa haka ya fita zuwa part dinsu, tana zube kan kujera Kuka take Wanda batasan dalili ba kalaman khaleel nada nasaba da kukan ta, wato ita zaman yayan shi ta ke yi, komai ya na yi ne saboda d'an uwan shi, why zuciyar ta take son ya daina fadar hakan?why zuciyar ta ke kwadayin jin yace yana Auren ta because he wants her not because of his brother?. Dafata da yayi ne yasa ta dago idanun ta zama yayi tareda zuba mata ido ba tare da ya taba ta ba. "What happen ko wani Abu yafaru ne" ? ka mayar da ni gida. Tafada kai tsaye, kur yayi mata kafin yace " why? Ba asona a gidan nan kuma ai Mommy tace nima ka sake ni, kai ma baka ra'ayin zama dani sai don d'an uwan ka, please let me go. OK you can go bazan rikeki ba. Yafada yana daga hannu sama. But ki sani ba kotu ko Alkalin da zai iya datse igiyar Auren mu Naziya, babu kalmar da zatasa ni Ibrahim khaleel in sakeki. Fauziya has gone da gani sai ke yanzu, Alhamdulillah zan cika burin Yaya na, All his dream, bayason ya hadaki da wata mace and my dream is bigger than his, don't you feel akwai Abinda Allah ya boye a karkashin zuciyoyin mu, bakyajin wani strong feelings akaina Naziya, ba kya jin yes Am your real man?, nine farin cikin ki, bakya ganin cikin Kwana biyu munyi shakuwar da bamu yi zato ba? why kika saki jiki da ni in babu wani boyayyan Al'amari a zuciyoyin mu?, kinsan zuciya ta na kun she da sakonnin da take aikawa ta ki ki ke karba batareda kin sani ba?
"Wani Auren zakayi ai". Tafada tana kallon cikin idanun shi, "ba kya so ne? Samun kanta tayi da daga kai ta marairaice fuskar ta kamar zata kuma sa masa Kuka.
Wani irin murmushin farin ciki yayi tareda riko hannun ta ya dawo da ita kan kafarshi, " are you jealous? Kishina kikeyi? Girgiza kai tayi. "Toh in ba kya kishi na kibari in karo Auren. Ya kuma fada yana kallon kwayar idanun ta mai cikeda wani irin sinadari dake Kara narkar da zuciyar shi, Toh ka mayarda ni gida idan zakayi Auren. OK bari ranar da aka kawota zan mayarda ke saboda kin San kin batani bazan iya bacci ba tare da mace ba, before I don't care but now you spoiled Mommy's innocent child. Harar shi tayi ba tare da ta shirya ba, kaine ka ke lalatani ai. Dariya ya kwashe da ita yana rungume ta kam wani irin nishadi yake ji a zuciyar shi a duk lokacin da suke tare baya gajiya da kasancewa tare da ita,
Da wayau yacire mata hijabi. "Kinga wayon ya isa tunda kika yi kwalliyar bangani ba kinsa wannan katon hijab..... Hadiye miyan bakin shi yayi domin ganin kana nan kayan dake jikinta na boutique yellow riga da wando, kayan da ya siyo cikin akwatin da ya bawa yayan shi, Ashe shine zai Mora tun lokacin da ya siya kayan sun mugun burgeshi ne Amma a yau yaji zai iya biyan companin akan wannan adon, rigar nada guntun hannu ga wuyanta a bude sosai he can see her boobs kusan rabi sunyi wani irin kyau ga madai daitan hips dinta ma sunyi cif cif a cikin wandon kamar palazo ta saman ya kama ta kasan ya bude, fadin kyau da tayi bata baki ne, Abu na uku yanda ta saki sumar ta a gefen wuyan ta tayi kamar wata Amisha patel, domin jikin nata madai daici ne ba makusa, daskarewa yayi kawai kamar statue ya kashe ta da ido tagama kashe mai jiki, hannun shi na rawa ya daga zuwa sumar kanta ya shafa har suna lumshe idanun su atare domin sakon nashi yaje mata shi kuwa feelings din dake taso mai nata bazai taba kwatan tuwa ba.
Wani irin zubewa tayi a jikin shi kamar ruwa, wani irin murmushi ya yi mai cikeda farin ciki, yana jin dadin yanda small touch din shi ke affecting dinta, he is lucky ba zata yi wahalar koyan duk Abinda yake so tayimai ba, he is planning to spoil her so much, yanda ba zata taba mafarkin barin shi ba, so yake ya koya mata soyayyar shi yanda bazai sha wahalar samun kanta ba duk lokacin da yake bukata,
Hannun ta ta dora saman kirjin shi domin tana jinta cikin wani irin yanayi mara misaltuwa tareda natsuwa a duk lokacin da take jikin shi, gam ya rungume ta tareda dora bakinshi dai dai kunnen ta yana hura mata iska a hankali cikin wani irin salo, "my diamond", ki daina shige min haka zanyi Abinda zai hana ki zama fa yau, you have no idea how honey I am, you're driving me crazy babe, let's romance. Yafada yana mai tura harshen shi a cikin kunnen ta tareda shafa ko Ina na jikinta cikin wani irin salo, khaleel ya iya dora mace a network, tuni yasaka ta sakin jikin ta tafara shafa kirjin shi dake matukar burgeta saboda fadi, jitake dama ya cire rigar domin yanada soft gashi mai santsi dake Kara Kawata kirar jikin nashi, yanada tsarin mazajen duniya way'enda suka amsa sunan su, fadowar da mommy tayi cikin falon ne ba sallama tana ruwan masifa, to bita zai zai wato kina nan kin makalewa yarona kamar chewing gum, saurin zabura Naziya tayi kamar zata fadi, saboda kunya da kuma tsorata batayi zaton ganin ta ba, saurin rikota yayi yadawo da ita a jikin shi domin itace zata rufamai asiri in ba hakaba momy zataga Abinda bazata so ba, matsowa tayi tana salati tareda cewa " Amma wannan yarinyar kunyi nasara sosai Ina bacci kun asirce mun zuciyar da'. "Mommy Mommy" please meke faruwa why are you here? Toh fa wato banda damar shigowa cikin gida na duk lokacin da naga dama saida izinin Y'ar gidan malamai? " no mommy please ba haka nake nufi ba nasan zuwan ki akwai babban dalili. "Yes badon haka ba ba Abinda zai shigo da ni nan, Toh yama za'ayi kaso in shigo? ka narkar da Dukiyar ka akan Y'ar gidan matsiyata tunda kasan ba zaka samu Abun Arziki ba ga y'an mata nan na fita kunya ya'yan Arziki bana tsiya ba sai sauran d'an uwan ka. Jin yadawo dai dai ya saketa tareda cewa "wuce ciki Ina zuwa". Domin kuka takeyi mai cimai zuciya domin kalaman mommy na da ciwo, don haka bata tsaya komai ba ta wuce ciki, bata taba ji ko ganin uwa mai hali irin na mommy ba, bata ko bata damar gaisuwa a duk lokacin da suka hadu don haka take shakkar haduwar su da ita a kullum, Ada tana ganin zama da Mommy yafi mata da khaleel amma tagano cewa khaleel din wani irin inuwa ne dake sanyaya mata zuciya da ruhi, shidin bangone Wanda idan ta jingina sai tajita cikin tsaro da Aminci,
Saida yaga ta shige ya maida hankalin shi kan mommy "meya faru yanzu momy?" Na Kira uban da ya daure maka kayi Abinda kaga dama na fada mai yau ko gobe nake son adaura maka Aure da salifa, ban Amince da zaman ka da wannan Y'ar ita kadai ba, tunda ka nace bazaka rabu da itaba, in har inada sauran mutunci na uwa a idonka kar ka fada mai ba tare da Amincewar ka bane inba hakaba ba zaka yi farin ciki a rayuwar ka ba khaleel. Ta juya ta fita fuuu. Yasani akwai hakkin ta na uwa kuma dole Tayi mai baki ya kamashi, don haka zaiyi yanda take so Amma bazata samu Abun da duk take so ba domin in har bai iya kula fauziya ba, ba yanda za ayi ya iya kula wata salifa don haka su zuba. Zama yayi tareda dafe goshi yana murzawa yarasa mafita, saida ya dauki lokaci ya mike zuwa cikin dakin, tana zaune tuni ta share hawayen ta ta dauki wayar ta tana karatun Auren Soja inda take ganin uwar miji tagari, gaskiya yasmin tayi sa'ar uwar miji, yaushe ita zata samu hakan a wurin Mommy?ta ga ta bata dama ta nuna mata ba ta da wani mugun nufi a tare da zuri'ar ta, kaddara ce ta Rayuwar ta wadda takeson ta rungume ta da hannu bibbiyu, domin ta Yarda Auren ta da khaleel shine mukaddarin rayuwar ta, *AUREN GADO* ne wadda zai juye ya zama hasken rayuwar ta, farin cikin ta, domin da mommy tace ya saketa sai da ta jita kamar numfashin ta zai tsaya, wane irin saurin shakuwa tayi dashi ba tare da ta shirya ba, tanaji kamar sun dade dashi fiye da Ahmed sometimes tana mantawa da wani Ahmed ma,
Sallama yayi ciki ciki ya tsaya tareda yin Ajiyar zuciya ganin ta tana sha'anin gaban ta bata kuka, dago kanta tayi ta amsa tare da cewa "Mommy ta tafini ne? " yes. Yafada yana matsowa ya zauna tareda fuskantar ta yace " my diamond, zan angwance fa, kinsan ni d'an gata ne Yaya na mata biyu yabarmin yace in more, ta farko na dauka a bude take amma itama dal take a Leda ga kuma Amarya wadda ranar da ta Kwana Washe gari yatafi ya bar ni da ita, my brother really loves me. wani irin kallo take yi mai Wanda bai gano fassarar shiba. Ki tayani murna idan na Kwana nan gobe zan canja sheka, wo ni d'an gatan Yaya na. Yafada yana kwanciya agadon tareda mirginawa kusa da ita. Saurin sauka tayi kasa, "me zakaci"? Saurin juyowa yayi ya zuba mata ido kamar ya mareta, he hate this character of her I don't care about him, that means shike haukar shi akanta a kullum, ke wai me kika mayarda ni ne idan Ina important magana ki rika kawo min shirme ko banda lokaci sai na cin Abinci? Am telling you Aure Mommy zatayi min yau ko gobe why can't you show your concern? Yanzu ta gano shi yanayi ne purposely saboda ya gani ko zata damu to bazata nuna mai ba ai da wayon ta. "Ikon Allah" me kake son inyi? Yanzu gashi ka fada Mommy take so kayi Auren kaima what is new? Na saba da hakan Wanda nayi Auren soyayya dashi ma an Auro mai ita hankalina bai tashi ba sai yanzu da kai kafadamin kana Aure na ne saboda cikon burin Yayan ka , Toh me zanyi dukkan mu zabin shine kuma umarnin Mommy zakabi don kasamu tsira don haka banda damuwa she is welcome.
Ta kureshi kamar ya dora hannu akai yakeji ya kurma ihu cikin sauri ya duro tareda fisgota rashin sanin madafa yasa ya cafke bakinta da ke fadamai Abun haushi yafara tsotsa cikin mugunta harda ciccizawa yakeyi idanun ta a waje ga zafi gashi takasa ture shi saida yayi son ranshi ya tureta tareda nuna ta da yatsa, " karki kuma furtamin kinyi Auren soyayya a rayuwar ki me kike nufi da nawa Auren, what is wrong with me? Niba namiji bane ko bankai ki soni kiyi kishi na ba? Look ni inada kishin Abinda yake nawa koda ace ke zabin Yaya na ce now you are under me, ikona ce ke you must love me, dole kiyi kishina dole. Yafada yana fita saboda takaici yarasa Ina zai saka ranshi kishin ta yayi yawa a zuciyar shi,koda yayan shi ne ta Aura Abun na tabashi kuma duk da yasan ita din tashi ce zuciyar shi taki convincing dinshi sai ranarda yaga tazamo shi yazamo ita, don haka he is ready to make her his completely.
Zama yayi tareda yin dariya, this guy is strange, kalli yanda yake reacting itafa ta ma gano shi yanzu kamar yanda yake fada akwai boyayyen Al'amari a kasan zuciyoyin su ita mace ce don haka bazata taba bada kai da sauri ba dole shine zai sauke wannan ego din ya fada mata zuciyar shi, tagano shi fiyeda yanda yake tunani, tana sane da kalaman fauziya akan yaki kusantar ta, ace mace wayayya like her yakasa kulata Amma ita daren farko yanuna mata shifa namiji ne kuma yanada lafiya, Wanda ita sheda ce domin idan ya rikice mata har tsoro takeji.
Part din Mommy ya nufa Wanda yayi dai dai da shigowar motar kawun su, yayi saurin boye fushin shi ya nufeshi, suka gaisa yace " muje cikin gidan Ina Hajiya"? Mommy na ciki Ya fada suna tafiya, tana zaune a falon tana kada kafa, suna sallama ta mike tareda cewa " gwara daka iso domin jini na nagab da hawa saboda bakin cikin khaleel. Kallon ta yayi kawai domin yasan korafinta baya karewa, mommy me nakuma yi kince in Amince da zancen Auren salifa koda bana ra'ayi na Amince now what? Oh fadamai kakeyi nice nasaka khaleel nagode kaji shiyasa nake kukan Rashin Ahmed. Tasa kuka, tareda zama, kawun nasu ma zama yayi ba tare da yace uffan ba, saida sukayi shiru yace " Toh nidai nasaba da mugayen kalaman ki balkisu ba tun yau ba idan na yanke hukunci akan yarana kice namiki shishigi kuma idan fitinar ki ta tashi sai kin nemo ni kuma kinsan bakina ba shiru zaiyi ba, don haka ni na isa nace khaleel bazai yi irin Auren da ki ka yi wa Ahmed ba, kina maganar nadama Hajiya balkisu har yanzu baki san Annabi ya faku ba, da zaki gano ita wadda kikeso din ranar da kika Aurota aranar ya Kwana asibiti, da Naziya ce da baki kauna da kince itace ta kashe miki yaro, Amma da yake bakya tsoron Allah kinyi mukus, yanzu ko mutuwar Ahmed bai isheki ishara ba, duk bakiga ya dace ki kyale komai ki barwa Allah ikon shi ba, naji kin kashe Auren da kika kulla ba tare da yaro ya Amince ba tun farko, wannan badamuwa ta bace yarage naki Allah ne ke nuna miki komai cikin sauki inda ke mai kwakwalwa ce Amma toshashshiyar madiga....... "Ya isheka Muhammadu", don bazan ce Alhajin ba, ko ince modu kamar yanda kowa ke kiranka tunda kaki Kama furfurar ka, kuma kuji nan, wallahi in har ban Aurawa khaleel salifa ba sai in ba na numfashi, kuma kai kaji idan baka Aureta ba banyafe maka ba duniya da lahira mu zuba ni da ku shege ka fasa. Ta mike fuuu ta shige dakinta tareda mugayen kud'uri, "kawu kaji me tace? Ya fada cikeda damuwa domin kalmar ta girgiza shi, naji khaleel kuma mahaifiyar kace bamuda yadda zamuyi da ita, sai Addu'a, yanzu dai ya za'ayi? Ko ka Amince ne a daura Auren? "Eh kawu ayi mata yadda takeso ai ba akaina zata zauna ba,
Yafada tareda ayyana wani kud'uri a zuciyar shi, Wanda shikadai yasan tsiyar da ya shuka, haka ya raka kawun shi tareda zancen zai samu iyayen yarinyar ai shi namiji ne zai iya rikesu duka don haka karya damu, koda kawu ya tafi bai iya komawa part din Naziya ba, dakin shi na nan ya shiga ya canja tareda barin gidan,
Direct gidan malam yaje.......... 🖊
*Matar Soja*
3⃣7⃣&3⃣8⃣
08032252760
08175479641 contact this numbers for more information
........... Sun dade suna tattaunawa da malam akan rayuwa Kafin ya koromai zancen Karin Auren da Momy keson yi mai, Sai da yayi shiru malam yace "yanzu meye matsalar ka? Baka da muhalli ne, ko baka iya daukar nauyin mata biyu ne? Kuma meye dalilin sakin ita dayar Matar taka ba akan ka'ida ba? Yanzu dai nasan ba mata hudu ba Kanada karfin da zaka ciyar da Unguwa guda ma, sannan lafiya kana da ita, sauran ka Adalci, karike Amanar su tsakanin ka da Allah kabi umarnin mahaifiyar ka kasamu tsira kamar d'an uwan ka. Haka suka dade sai karfe kusan biyar yabar unguwar, tun fitar shi take jin ba dadi domin ta saba dashi yanzu tafara sanin dadin Aure zaman ta da khaleel, shine ya nuna mata ita mace ce mai daraja da lafiya a tareda ita, domin duk lokacin da ya kusanto jikinta bata iya misalta dadin da takeji hade da nishad'i, kewar shi ta dameta sosai har waya ta dauka sau ba adadi' tana dubawa tareda tunanin kiran shi sai takasa, to me zatace mai inta Kira? Ganin zata damu da yawa yasa ta janyo wayarta ta fara karatun littafin ta, y'ay'an gata yasata cikin nishadi' sosai, saida taga yamma yayi ta mike ta shiga kitchen, ta shirya mai dinner lafiyayya irin wadda tasan yakeso, Kafin tayi wanka, duk Abinda takeyi a yanzu bin zuciyar ta ne domin tana samun farin ciki ba tare da tayi tsammanin samun shi ba a cikin wannan Rayuwar Auren.
Yana tafe a hanya yana duba waya, wato ba zata iya neman shi ba koda zai shekara baya gidan? Don haka saida yayi magrib ya shigo cikin part din, lokacin tayi wanka ta saka simple gown tana zaune tana lazimin ta, ya yi sallama ciki ciki, tareda wucewa gefen