Showing 24001 words to 27000 words out of 50413 words

Chapter 9 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1785

zama Hajia ba mu sani ba. Raudha ce ta aiko ko?"


Innayi ta gyaɗa kai


"Ayya! ta yi abun kai"


Daga wannan rana Ado ya fara janye jiki daga kuɗin da ya ke ba da wa daga dubu ɗaya ya koma ba ta ɗari biyar a sati har ta kai yanzu kam sai ya bushi Iska ya ke ba ta kuɗi.




Zancen Raudha na aikowa Innayi kuɗi ya shiga har kunnen Halima, shikenan kuma ta samu kan Innayi, sai ta daƙonci ƙarshen wata yayi sai ta je gidan ziyara, da sun fara hira sai ta dinga sako zancen ba ta da kuɗi ko kuma yaranta za su sayi kaza a makaranta kuma ba ta da kuɗi gashi yanzu dama ta gama ƙarewa mijinta Alhaji Nuhu.
Tausayi irin na Innayi ya sa sai ta ɗau kuɗi ta ba ta wani lokaci har cikin kayan abinci tana ɗeba ma ta. Maimakon ita Haliman ta dinga kawowa mahaifiyarta sai ya zama mahaifiyartan ne ke ba ta.
Wani lokaci Sa'a ma kan aiko kuɗi ta wajen Ado a ba wa Innayi amma da kuɗin Sa'an da na Raudhan yanzu ya koma ba ta wani assasa komai da kuɗin, idan Halima ba ta karɓa ba matan Ado za su zo karɓan bashi wanda karɓa su ke yi ba sa maidawa. Shi kan sa Ado wani lokaci idan Sa'an ta turo kuɗi ta wajensa amfani ya ke da su idan ya ga dama ya gayawa Innayi cewa yayi amfani da kuɗin da aka ba ta, idan 'yan iskan na kusa kuwa shikenan. Ai kuɗin uwar sa ce dan ya kashe ba komai ba ne.


Raudha bayan wajen da ta ke PPA ɗin ta ta samu waje biyu tana yin lesson ana biyanta. Tunda maganar scholarship ya bi ruwa gara ta fara tara kuɗin da za ta koma makaranta da shi tunda ga yanayin gidan na su kowa nafsi-nafsi ya ke yi, kuma ta sa a ranta har Innayi ta koma ga Allah ba za ta taɓa bari ta yi aikin wahala wai dan ta samu kuɗi ba, duk wahalan da ta yi a baya ya isa yanzu lokacin jin daɗin ta ne...


Sau tari mu kan yi wannan kuskuren, wai dan wani ɗan uwan mu yana da kuɗi yana kyautatawa mahaifiyar mu ko na ce mahaifanmu sai mu da mu ke da rufin asiri sai mu ja gefe mu zuba ido mu bar wancan yai ta hidima shi ɗaya.


Ai idan shi ɗan uwanmu dubu goma zai bayar mu da bamu da kuɗi ko ɗari biyar mu ka bayar za mu samu lada kuma su ma iyayen na mu za su ji daɗi sosai, tunda sun san bamu da shi amma kuma mu na kyautata mu su...




***




Sai da Raudha ta yi wata shida kafin ta zo gida, ba wai ba ta son zuwa ba ne sai dai aikin da ta ke yi ne bai ba ta dama ba, gashi ɗan sarari da ta ke samu tana zuwa wajen wata mata inda ta ke koyon yadda ake ɗinka labule, pillow, bedsheet, duvet da sauran su. Hakanan tunda tana jin muryan Innayi kusan kullum hankalinta a kwance ya ke.


Ana gab da sallar Layya ta zo gida, Innayi dai ta yi kyan gani ba kaman kwanakin baya ba duk da kuwa ta ƙara tsofewa ko dan ba ta da jiki ne? Ko kuma dai saboda har yanzu ba ta da kwanciyar hankali...


Mamaki ne ya kama Innayi lokacin da Salisu da abokinsa Hassan su ka shigo da ragon da Raudha ta siya na layya.
Bayan sun ɗaureta ne Raudha ta tambayi Innayi ko ragon na da kyau?


"Gaskiya Auta ragon nan ƙosashshene kuma zai yi mai"


Raudha ta yi murmushi ta ce " ragon layyan ki ne"


Innayi ta kalli rago sannan ta kalli Raudha sai hawayen farin ciki su ka fara zubo ma ta. Tunda ta ke ba ta taɓa yin layya ba, to ko mijinta Buba na raye ma ba kowani sallah ya ke yin yanka ba balle har ta yi tunanin ita ma zai mata layya.


Kowa ya ji labari sai ya dinga nunawa kamar Raudhan ta zaƙe dayawa a kan Innayi, har gani su ke kamar neman suna ta ke yi. Yayinda wasu kuma su ke tunanin wani halin banzan Raudhan ke yi ta ke samun kuɗi.
Iro ma da ya ji labari sai da yai mamaki daga baya ya ce ai ba komai bane tunda dai Raudhan ba ta da wani damuwa a kanta shiyasa ta ke da kuɗin yiwa Innayi layya.


Shin har akwai wani abun da za ka yiwa iyayenka har yai yawa ne?
Shin ko mi za ka mu su za ka iya biyan ɗawainiyan da su ka maka ne?...






Ranan sallah kuwa Raudha ta kawowa Innayi kayan sallarta. Wata leshi ne da ake yayin ta a lokacin. Dubu goma shabiyar ake sai da ta, sai dai ita Raudha wata ƙawarta 'yar bautar ƙasa ce ta siyo ma ta a Lagos dubu goma. Ta riga ta sa an ɗinka wa Innayi tun tana Yobe, takalmi mai kyau da hijab da ya tafi da kalar leshin Raudha ta haɗa ma ta da shi.
Innayi ba ta san kuɗin lace ɗin ba ta dai ji daɗi sosai da wannan kaya. Tare su ka tafi filin idi wanda tun a hanya ta ke ganin yadda ake kallonta. Duk wanda ka gani da irin lace ɗin to ya kai ne.


Innayi ba ta taɓa zuwa sallar idi ba sai bayan rasuwan Buba. Raudha ce ta kwaɗaita ma ta falalar shiyasa ta dage da zuwa. Amma tunda Buba ya taɓa hanata zuwa sau ɗaya ba ta sake tambayarsa ba har ya rasu, shiyasa tana da kaya ba ta da kaya duk ba ta da damuwa tunda duk hidimar sallan a cikin gida za ta ƙare shi.


A wajen idin ma chanjin kuɗi naira goma goma sabbi Raudha ta ba ta ta yi sadaka da su. Ba wanda zai gan ta a wajen idin nan ya raina ma ta, kallon wata Hajia ma ake ma ta...


Da su ka dawo daga idi, Raudha ta kira Ya'u ɗan anguwan su ya zo ya yankawa Innayi ragon ta. Babbar sallah ta wannan shekara ya matuƙar faranta ran Innayi, Raudha ta ma ta komai, sai godiyar Allah...




Bayan sallah da kwana biyar Raudha ta shirya komawa Yobe a lokacin ne kuma Sa'a ta haihu amma ɗan bai zo da rai ba. Da ya ke tun auren Sa'adatun sau ɗaya ta taɓa zuwa ma ta sai kawai ta ce Innayi su je Azare su ma ta gaisuwa kafin ta tafi.
Ranan Asabat su ka shirya tafiya da ke tsakanin Misau da Azare ba nisa ba kwana za su yi ba.




"Innayi ki sa leshin ki na sallah saboda ki fito a Hajia" Raudha ta yi maganar tana dariya.


Innayi ta yi shiru chan ta ce " barin sa wanda yayan ku ya siya min a sallar bara"


Yadda ta yi maganar ya tabbatarwa Raudha akwai matsala.


"Ba dai kin bawa Adda Halimah ba?"


"Aron shi kawai ta yi za ta dawo da shi"


Raudha kamar ta yi kuka ta ce " haba Innayi haba Innayi, tunda na ga Adda Halima na ƙwaɗa ɗinkin na san za a rina. Wallahi ko kaffara ba zan yi ba, ba aro ta ɗauka ba ta tafi da shi kenan"


"Yo abinki Auta ba na sa ba, ai shikenan"


"Shikenan Innayi ba ki isa ki sa abin arziƙi a jikin ki ba sai an miki baƙin ciki, wai hakan ma 'yar cikin ki"


Raudha ta ɗau waya ta kira Halima ta zazzageta duk da Innayi ta hana ta kiran amma ba ta saurareta ba, abin ya ba ta haushi kamar ta yi kuka.


Duk cikin zannuwan Innayi babu na arziƙi shiyasa wannan karan ta yi ƙoƙari ta siya ma ta abinda kowa ya gani ya san na zamani ne kuma yana da tsada.


Har su ka isa gidan Sa'adatu Raudha ba ta bar mita ba, har ƙaran Haliman ta yi a wajen Sa'an a kan ta ma ta faɗa ta dena ɗaukawa Innayi kaya...




***




Daf sun kusa ƙare bautar ƙasa Dr Ambi ya cikawa Raudha scholarship na Harvard Medical school. Tareda wata 'yar sa ya cika mu su, kawai kiran ta yai ya ce ta cigaba da addu'a akai ko Allah zai sa ta yi nasara. Raudha ta amsa amma ba ta sa rai a kai ba.


Bayan ta dawo gida ne ta gayawa Innayi a wani lokaci da su ka yi hiran batun komawa karatun da za ta yi.
Innayi ta dinga maimaita sunan makarantar har sai da ta iya faɗa HABAD a cewarta. Duk sujudin da za ta yi na sallar farilla ko nafila sai ta roƙi Allah ya sa 'yar ta Raudha ta samu tafiya wannan makaranta, yadda Raudhan ke zancen makarantan ya sa ta gane babbar makaranta ce sosai kuma makaranta ce ta mai rabo, amma ta ji a ranta 'yar ta Raudha za ta samu wannan rabo. Haka ta dinga duƙufa da addu'a ba dare ba rana.


"Allah ka sa 'ya ta Raudha ta samu tafiya makarantar HABAD"...




A wannan lokaci da Raudha ke gida ne samari su ka fara ma ta chaa. Tana da kyau gashi ta haɗa degree a ƙanƙanin lokaci dan kuwa shekarunta ishirin da ɗaya ta gama bautar ƙasa.
Cikin wanda su ke nacin neman ta ne Malam Iliyasu wanda lecturer ne a School of Agric da ke Bauchi ya samu daman gabatar da kan sa wajen su Ado.
Malam Iliyasu matashi ne dan a lokacin shekarun sa talatin da huɗu yana da mace ɗaya da yara biyu, ɗan asalin cikin Misau ne sai dai shi da iyalin sa su na Bauchi. A lokacin hidimar sallah ya ƙyalla ido ya ga Raudha nan ta ke kuwa soyayyarta ya shigeshi.


Ankai ruwa rana tsakanin Raudha da yayun na ta wanda su ke ganin Malam Iliyasu ba shi da aibu ta aureshi. Da ta kawo maganar cigaba da karatu kuwa su ka nuna sam ba su yarda ba gara ta yi aure idan ya so ta yi duk irin karatun da ta ke so a gidan mijin ta.
A ɗan hirarrakin da su ka yi da Malam Iliyasu shi namiji ne da bai yarda da aikin mace ba shiyasa koda matar sa tayi diploma amma kwalin na nan ajiye ya hanata neman aiki da shi. Tana da yaƙinin ko ta auri Malam Iliyasu haka itama za ta ajiye kwalinta a ƙasan gado ta dinga jiran man rabbuka, domin iya abinda zai ba ta shi kaɗai zai zama na ta.


Ba za ta iya ba, ba ta shirya rabuwa da Innayi haka ba. Da ace ma ita ɗaya za ta zauna sai ta yi tunanin idan ta auri Malam Iliyasu za ta tafi da Innayi gidan ta amma ba ita ɗaya ba ne.


Matsin Ado yai yawa har ta kai yana iƙirarin zai karɓi sadakinta a wajen Malam Iliyasu. Da ta ga da gaske su ke ta kai ƙara wajen mai garin Ajili wanda ta ke ganin zai iya shige ma ta gaba a wajen yayun na ta. Mai garin Ajili na lokacin kusan 'ya'yan kawunnai su ke da marigayi Buba. Bayan sun je Ajili anyi zancen ne su ka ba ta wata uku idan ba ta samu makaranta a lokacin ba dole za ta amince ta yi aure...




"Innayi idan ki ka ce na yi aure yau yau ɗin nan, zan amince na yi aure ko da ba na so amma idan ki ka amince na cigaba da karatu kamar yadda rai na ke so to kuwa wallahi sai dai kotu ta rabamu amma ba zan bari su Yaya Ado su min auren dole ba"




Innayi shiru tana kallon Raudha. Tabbas ta sani duk damuwar Raudha na son cigaba da karatu saboda ita ne, saboda ta inganta rayuwarta. Ta cika alkawarin da marigayi Baffah ya ɗauka ma ta wato ya gina ma ta gida ya kuma kai ta Makkah.


"Allah ya mi ki albarka Auta"
Raudha ta amsa da amin


"Raudha ina miki addu'a kuma na san Allah zai zaɓa miki mafi alkhairi a gareki. Idan cigaba da karatun ki akwai alkhairi a ciki to kafin watanni uku su cika za ki samu tafiya karatu. Idan kuma aure ne mafi alkhairi za ki ga auren zai zo mi ki da sauƙi kuma mijin da Allah zai ba ki zai zamo na gari, mai son ki, mai ƙaunar ki kuma mai tausayin ki"


Da wannan Raudha ta amince ta fawwalawa Allah lamarinta. Ana fara cika DE ta cika zuwa ABU tana neman MBBS a karo na biyu. Dr Ambi ya ma ta alkawarin zai yi duk yadda za ayi ta samu admission a ABU.


Allah mai jin ƙan bayi kenan, domin addu'ar Innayi ta karɓu Wata biyu da sati ɗaya bayan an gindayawa Raudha sharaɗi.
Dr Ambi da kan sa ya zo Misau ya ba wa Raudha labarin alkhairin da ya sameta.
Ta samu scholarship na zuwa makarantar Havard. 'Yarsa da ya cika mu su tare ba ta samu ba amma Raudha ta samu...


Da gudu Raudha ta shigo gida bayan ta gama magana da Dr Ambi da ya ke ƙofar gida. Innayi na Alwala sai ji ta yi an faɗo jikinta ana ihu da dariya.


"Innayi na samu admission, na samu scholarship na zuwa Harvard"


Innayi ta ɗaga hannu tana faɗin Alhamdulillahi...




********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels


WhatsApp Number: 08138873799




Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************




*RIBAR UWA*




*Na...Azizat*
*Wattpad@Azi_zat*






Chapter 10
(Free book ne)




*A crazy mother*








Tafiya ce za ta yi da ba ta san ranan dawowa ba. Duk ɗokin tafiyarta lokacin da abun ya matso sai ta ji ba ta son tafiyar. Innayi ce a ranta, ba lallai ne a kula da ita yadda ya kamata ba. Haka dai ta cigaba da shirye-shiryen tafiya, wani lokaci idan ta fara jimamin abin sai ta zauna ta yi ta kuka.


Da taimakon Dr Ambi ta je Abuja ta yi passport ɗin ta cikin sauƙi. Ana saura kwana biyar ta tafi ta je Azare gidan Sa'a. Duk cikin 'yan uwan na ta ita ce ta ke ganin tana da sauƙin kai kuma ta ke tunanin za ta iya fahimtar damuwarta.


"Adda kin dai san halin Yaya Ado da Matan sa, ina tsoron kada na tafi Innayi ta shiga wani hali. Ba na so ta koma aikin wahala kamar yadda ta yi a shekarun baya, yanzu yadda Innayi ta ke, tana lokacin da hutu kawai ta ke buƙata da kwanciyar hankali"


"Gaskiya ne Raudha, zan yiwa Yaya Ado magana ya matsawa matan sa su dinga kula da Innayi sosai"


Idon Raudha ya ciko da hawaye ta ce "Adda idan ba na nan wai wanki da shara Innayi ke yi, sannan sai ita za ta dafa abin da za ta ci. Adda a shekarun Innayi bai ci ace ta dena zuwa gindin murhu ba?" Ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka.


Jikin Sa'adatu yai sanyi. Itama ba wai tana jin daɗin yadda Innayin ke zama ba ne, amma ya za ta yi tunda ba gari ɗaya su ke ba.


"Ki yi haƙuri ki bar kuka zan yiwa Yayan magana Insha Allahu"


"Adda ba Yaya kaɗai za ki yiwa magana ba har da Adda Halimah. Za ta zo wajen Innayi ta karɓi kuɗi ta karɓi kayan abinci amma ba abunda ta ke yi mata. Idan da tausayi ai ko Dija 'yar ta za ta dinga turota tana yiwa Innayi wanki duk sati"


"Abun kam ba daɗi. Insha Allahu zan kira Yaya Ado inyaso sai ayi fixing meeting mu je a zauna a tattauna komai kafin ki tafi"


Raudha ta cigaba da matsar hawaye saboda yadda abin ke ci ma ta rai.






***




Meeting dai da aka sa kowa ya hallara banda Idris wanda ya nuna shi ba shi da lokaci duk da kuwa meeting ya kama ranan Asabat ne.


Sa'a ce ta ba da shawaran a dinga haɗa kuɗi duk wata dan kula da buƙatun Innayi, Halimah da ke da ƙaramin ƙarfi za ta kawo ɗari biyar a wata, su kuma Sa'a, Ado, Iro da Idris kowa zai dinga kawo naira dubu biyu da ɗari biyar a wata. A hakan sai da aka yi ta ja kafin aka ajiye maganar kuɗi akan kowa zai kawo dubu bibbiyu amma ita Sa'a ta ce dubu biyu da ɗari biyar ɗin za ta bayar, jimillar kuɗi ya tashi dubu tara a wata.


Kai Jama'a! Wai mahaifiyar ka ce ba za ka iya cire dubu biyu da ɗari biyar ka ba ta a wata ba. Ƙila a wata kana amfani da adadin kuɗin ko fiye wajen shirme da shirirta ƙila ma harda kashesu a wajen aikata zunubi amma UWA da za ka ba ta ka samu lada sai hakan ya gagareka.




*true life story*


"Akwai wata Uwa da ta girma za ta kai shekaru 55-60. Sai ya zamana ba ta da lafiya kuma maganin da ake siya ma ta duk wata dubu bakwai ne. Tana da 'ya'ya da su ka manyanta kuma biyu daga ciki su na aiki. Watan farko aka haɗa dubu bakwai da ƙyar aka sayi magani, wata na biyu aka siya ana ƙunƙuni wata na uku aka sayi rabin maganin wato dubu uku da ɗari biyar. Jama'a Wallahil Azim a wata na shida babu wanda ya iya ciro kuɗi dan siyan maganin Uwar da ta tsugunna ta haifeshi. Kowa aka taɓa sai ya fara kukan tsadar rayuwa da kuma babu. Batun sauƙi yana tareda Allah, amma maganar magani wannan Uwa ta rasa mai siya ma ta cikin 'ya'yanta. Da ke sun ga jinyar ya fara sauƙi sai su ka basar, su ka nuna halin ko inkula akan uwar su"


A hakan sai mu ce ba ma ganin cigaba a rayuwar mu, a hakan sai mu ce 'ya'yan mu ba sa jin magana, a hakan sai mu ce musiba da fitintinu sun yi yawa. Irin waɗannan abubuwa da mu ke aikatawa muna ganin ba komai ba ne Wallahi babban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login