Showing 30001 words to 33000 words out of 50413 words

Chapter 11 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1780

ranta irin Raudha...




Yadda ka treating iyayenka da 'yan uwanka haka zai sa matarka ta daraja su ko kar ta daraja su...






*RIBAR UWA*




*Na...Azizat*
*Wattpad@Azi_zat*






Chapter 11
(Free book ne)




*An evil daughter inlaw*






Da ke Huwaila ba ta san kan Asibitin ba da ƙyar su ka samu su ka yi gwajin bayan anyi ta mu su kwatance. Daɗin abin Likitan da yai gwajin yana jin Hausa ganin da Huwailan da Innayin duk sammakal ne shiyasa ya mu su bayani dalla-dalla yadda za su gane tareda cewa su dawo washegari su karɓi result ɗin su kaiwa Likitan da ya turo su. Innayi ta ma sa godiya.
Lokacin da za su fita ne Likitan ya ce "Mama ina yaranki maza ne su ka barki kina yawo ke ɗaya?"


Innayi ta ce " 'ya ta ba ta ƙasar, tana karatu a Hawad"


"Hawad?" Likitan ya maimaita dan bai gane ba


"A ƙasar Amelika ta ke, makarantan koyon likitanci ne irin na ku" tana maganan ne cike da alfahari, idan akwai wanda ta ke alfahari da shi cikin 'ya'yanta to Raudha ne.


Likitan yai murmushi tareda addu'an Allah ya sa 'yarta ta gama karatu lafiya. Bayan fitan su da ɗan mintina yana duba computer kwatsam sai ƙwaƙwalwarsa ta ankaro ma sa ma'anar abinda Innayi ta faɗa wato Hawad, ashe Havard ta ke nufi, yai dariya yana ƙara maimaita sunan...






Bayan sun dawo gida Huwaila ta dafa mata spaghetti sannan ta tafi, kafin ta tafi ta ce " Inna sai dai fa ki ƙara haƙuri saboda gaskiya sha'anin Anty Fa'iza sai ahankali. Ba ta da daɗin sha'ani"


Innayi ta ce " ba komai, na gode Allah ya saka da alkhairi"




Da ƙarfe biyu da rabi Faiza ta dawo gida, ko ta kan Innayi ba ta yi ba. Innayin ne ma ta fito tana ma ta sannu da zuwa wanda ta amsa a fiska ɗaure.
'Yarta Mufeedah ta fara tambayar kowaye Innayi. Da ke rayuwar ƙarya su ka ɗauka wa kan su, da Hausa da Fulatanci duk babu wanda su ka koyawa Mufeedah, turanci su ke mata kuma dashi ta tashi ɗan gara Hausa wani abin ta na ɗan ji amma ba ta iya mayarwa.
Maimakon Faiza ta gaya ma ta ko wacece Innayi sai ta ce ma ta ta tambayi Daddyn ta idan ya dawo.


Yarinyar ta kalli Innayi ta ce "who are you?"
Innayi ta ma ta murmushi ta ce "Allah ya miki albarka"...




Da Huwaila ta shigo da yamma ta ma ta bayanin ta dafawa Innayi spaghetti da rana, Faiza ta haɗe rai ta ce kar ta ƙara yi mata girkin da ba ta sa ta ba.


"Anty Faiza na ga ba za ki dawo ba sai..."


"Huwaila ba na son shishshigi. Ki yi abinda na ce kawai"


Huwaila ta ja bakinta ta yi shiru...


Ƙarfe shida saura Idris ya shigo gidan amma bai leƙa Innayi ba sai da ya dawo daga sallar Isha.


Tambayarta yai ko ta je asibiti, ta gaya ma sa yadda su ka yi da Likita. Ya ce Allah ya ƙara lafiya.


Yau dai tuwon Semovita da miyar kuɓewa Faiza ta yi, ta kawo wa Innayi abincin ba yabo ba fallasa.


Ko kafin su kwanta sai da ta yiwa Idris ƙorafi akan ita fa ya san yadda zai yi Innayi ta tafi ƙarshen sati dan ba za ta iya ɗawainiyar Uwar sa ba...






***


Washegari still Huwaila da Innayi ne su ka je su ka ƙarɓi result su ka kai wajen Likita, amma da ke ba su zo da wuri ba dole sai tafiya su ka yi akan washegari za su dawo.


A yammacin ranan ne kuwa Raudha ta kira Idris, da farko Ado ta kira shine ya sanar ma ta abinda ke faruwa, ta ji zafin rashin gaya ma ta da ba su yi ba tun farko, shine ta kira Idris ɗin.
Sun jima suna tattaunawa kafin daga baya ta ce idan ya koma gida ya haɗata da Innayi...




Daren ranan bakin Innayi har kunne saboda farin ciki. Sosai su ka yi taɗi da Innayi, har ta ke sanar da ita aikin da ta ke yi a free time ɗin ta. Innayi ta rinƙa saka ma ta albarka. Bayan sun gama wayan ne Idris ya tambayeta yadda su ka yi a Asibiti ta sanar da shi ya ce gobe zai haɗa ta da wani saboda ya ji bayanin da Likita zai yi. Innayi ta gyaɗa kai kawai...




Da sassafe alert ɗin kuɗin da Raudha ta turo ya shigo, da ke yana da domiciliary account in dollars kuɗin ya shigo, yana ganin kuɗin ya lissafta su a ƙwaƙwalwarsa wanda ya zamo a kuɗin Nigeria dubu goma shatara da ɗari uku.


Kai tsaye kitchen ya wuce wajen Faiza yana gaya ma ta adadin kuɗin


"Hmmm ko mi ta ke yi har ta ke samun kuɗi haka oho. Ni dai na san karatun Likitanci da wuya ba sa samun lokaci ma bare ace wani aiki ta ke yi"


"Honey ƙila gwamnati ke biyan su fa kin san da scholarship ta tafi"


Faiza ta ce "Hmmm"....






AbdulWahab wani yaron maƙotan su Idris ne yana karatu a Jami'ar ATBU, shi ne ya raka su Innayi da Huwaila asibiti wajen Likita. Likitan ya mu su bayani da cewa gwajin da aka yiwa Innayi ya nuna babu abinda ya samu kan ta sai dai za ta dawo bayan wata uku a sake yi ma ta wani gwajin.
Ya jaddada mu su akan lallai Innayi ta cigaba da shan maganin ta na hawan jini sannan ta cire damuwa a ranta.


Tun a waya AbdulWahab ya sanar da Idris yadda su ka yi da Likita, Idris ya ma sa godiya.


Bayan sun dawo gida Innayi ta haɗa 'yan kayanta dan ta san ba makawa gobe za ta koma Misau idan ya so bayan wata uku da aka ce sai ta sake dawowa. Ta gode Allah da ya sa ma ba su riƙeta a asibitin ba dan ta san yadda Idris da matar sa su ka nuna ma ta tun zuwanta ba lallai su iya yi mata wani jigilar asibiti ba...




"Ni da Fa'iza mun tsara za ki zauna a wajen mu har wata uku sannan idan kin koma Asibiti aka sake dubaki sai ki koma Misau"


Miyasa da iyayen mu sun girma sai mu dinga yanke mu su shawaran abinda za su yi ba tareda mun shawarce su ba?




Innayi ta kalli Idris ta ce "wata uku yayi yawa, ba na son saku cikin ɗawainiyata. Idan Allah ya nufemu wata ukun ya cika, Misau da Bauchi ba nisa sai na dawo"


"Ba abinda fa ki ke yi a Misau ɗin. Ga wahala da kikeyi a chan, ba a irin haka ba ne kika samu jinyar. Gara ki zauna da mu a nan, ki ci ki sha ki kwanta"




"Ban saba da zaman birni ba Idrissa ka bar ni na koma inda na fi sabawa"




"A'a Innayi, yanzu haka kowa zagina zai yi su dinga cewa na koreki na kasa kula da ke, dama Adda Sa'a da Raudha sun min mummunan shaida"


Duk yadda Innayi ta yi haka Idris ya ke ja har sai da ta haƙura za ta zauna da su na wata uku...




***




Satin farko zaman ba laifi da sauƙi sai dai kewa da ya ke damun Innayi a duk lokacin da su ka fita aiki, ko da su na nan ba wai suna zama su yi hira ba ne amma jin ɗuriyar mutane a gidan yana sa hankalinta ya kyauta. A wannan lokacin ne kuma ta yiwa Idris magana akan ya siya ma ta radio saboda ya dinga ɗebe ma ta kewa.


"Innayi ga TV ba za ki fito kiyi kallo ba" Idris ya faɗa yana dariya.


Innayi ta ce ba ta saba da TV ba gara radio ɗin. A ranan kuwa ya siya ma ta radio. Duk bayan kwana uku ko huɗu Raudha na kiran wayar Idris ya ba wa Innayi su gaisa. Koyaushe tambayar Raudhan shine ko tana nan lafiya? Ko tana cin abinci sosai? Ko tanajin daɗin zaman Bauchi?


Duka amsarta shine "eh" to mi za ta ce tunda dai da Idris ɗin da Raudha duka 'ya'yanta ne...






Wata safiyar Lahdi Innayi na ɗaki tana sauraron wani shiri a gidan radion Globe FM ta jiyo hayaniyar Faiza da Idris.


"Idan ba za ka faɗa ma ta ba ni zan faɗa ma ta, haka kawai mutum da gidan sa a zo a takurashi. Tun ɗazu na ke son yin bacci amma an hanani, shegen jin radio kamar wata journalist"


Innayi ba ta ji mi Idris ke faɗa ba dan da turanci ya ke magana. Ƙarshe dai Innayi ta kashe radio ta turashi gefe tareda sauke ajiyar zuciya. Daga ranan ba ta sake kunna radio ba haka nan shi Idris bai bi bahasin yadda ta dena kunna radio ba...




Huwaila ke yiwa Faiza da Mufeedah wanki duk weekend. A sati na biyu ta je ta karɓo kayan Innayi wanda tunda ta zo ba su ga ruwa ba, ba wai Innayi ba ta son wankin ba ne sai dai yadda sirikar na ta ke yi tunda ta zo gidan ya sa ta ke tsoron yi ma ta maganar a bata sabulu.
Bayan ta gama yin wankin ne tana ɗauraya bokitai sai ga Faiza ta fito ɗauke da socks. "Huwaila ga socks ɗin Baby ban gani b..." ta tsaya da maganar lokacin da ta hango zannuwan Innayi akan igiyar shanya.


"Kayan waye wancan" ta tambaya da kakkausan murya




"Na Inna ce"


"Wace Innar?"


Sai da Huwaila ta yi kasaƙe tana kallon ta kafin ta ce "Innar gidan nan"




"Ka da ki kuskura ki sake haɗa min wanki da ita, infact kada ki sake yi ma ta wanki a bokitina"


Huwaila ta zaro ido tana mamakin kalaman Faiza. Innayi fa Uwar mijin ta ne.


"Kina ji na?"


Huwaila ta gyaɗa kai...






***




Kwance ta ke kan wani tsohon gyalenta da ta mayar sallaya tana sallah da shi. Ta jima da yin sallar Azahar ta gama addu'o'inta tana kwance ne tana tuno ƙuruciyarta. Wani waƙa da su ke yi a dandali ta tuno nan ta ke ta fara rerawa, tana waƙar tana ɗan daddanne cikinta da ke kukan yunwa.
Tunda ta zo gidan za ta iya irga ranakun da ta ke cin abincin rana. Ranakun Asabat da Lahdi kenan, tana ci ne saboda dukkan su ba sa fita office amma kwana biyar na ranakun aiki daga safe ne sai dare. Wani lokaci saboda tasan za ta ji yunwa da rana sai ta rage biredin ta na safe ta ci sauran da rana. Wani lokaci kuma Huwaila na kawo ma ta abincin rana daga gidan su kafin Faiza ta dawo, dan yanzu Faizar kulle kitchen ta ke idan za ta fita.
Tsabar mugunta ko Faiza ta dawo da wuri to ba za ta yi girkin rana ba, idan ka ga tayi to indomie ce za ta bawa Mufeedah ko kuma ta haɗa ma ta cornflakes. A wasu ranakun kuma take away ɗin abinci ta ke siyowa ita da 'yarta su ci, ko leƙa ɗakin Innayi ba za ta yi ba balle har ta kawo ma ta abinci.
Abincin safe da na dare ma da ta ke miƙo ma ta ba ƙaramin zafin sa takeji ba.
Ita fa kunyar ma azo a ga Innayi a gidanta ta ke ji, wai local Innayi ce Uwar mijinta. Mijin ta handsome ɗan ƙwalisa. Ba dan abinda su ke ci dalilin Innayin ba da ba abinda zai sa ta bar Innayi a gidan ta. Har yau ba wanda ya san da zaman Innayi a gidan su dan ko 'yan uwanta ba ta gayawa ba dan kar su ma ta dariya.


Idris kam ya kan ɗan leƙo Innayi su gaisa amma mafiya yawanci lokuta gaisuwan ma daga bakin ƙofa ya ke tsayawa ya yi ta, idan ka ga ya shigo ɗakin to Raudha ce ta kira zai ba wa Innayi su gaisa, da ke ba shi da gaskiya haka zai zauna ya yi ta zazzare idanu yana sauraron maganganun su saboda sabon saran da ya kawo shine ya sa wayar a handsfree saboda ya dinga jin mi Raudhan ke faɗi...




Lissafin kwanaki Innayi ta ke yi zuwa lokacin da wata uku zai cika har ta koma Asibiti dan ta samu ta tafi gida. Tun ranan ƙarshe da ta je Asibiti ba ta sake fita ko da ƙofar gida ba.


Ranan da ta cika wata uku dai-dai da Idris ya leƙota ta tunasar da shi maganar zuwa Asibiti, shi kam gaba ɗaya ya manta. Ya ce zai ware lokaci su je.


Bayan kwana uku ya ɗauketa su ka je asibitin, an sake gwajin kuma an tabbatar ba ta da matsala sai dai jininta ya hau sosai. Amma da Sa'a da Raudha su ka kira shi sai ya ce mu su Likita ya ce ta dinga zuwa check up na wata-wata saboda su monitoring sugar level ɗin ta. Ko yaushe Innayi ta samu sugar oho.


Innayi na jiran ta ji an ma ta zancen tafiya sai ta ji shiru, ranan da ta yiwa Idris magana sai ya ce wai ba yanzu ba sai bayan wani wata ukun...




Magana ma Rahama ne, rashin magana da kowa ya sawa Innayi wani ƙuncin gashi yanzu sai ayi sati biyu ko uku kafin ta yi waya da Raudha. Ta na yiwa Raudhan uzuri saboda ta san karatu ta ke ba ta taɓa nuna ma ta tana cikin damuwa ba saboda kar ta ɗaga hankalinta...




***


"Hello Adda Sa'a"


"Mutanen Havard ya kike? ya sanyi na san yanzu lokacin sanyi ne a chan?"


"Ina lafiya Adda. Dan Allah yaushe rabon ki yi waya da Innayi?"




"Gaskiya an kwana biyu, zai kai kwana tara haka"


"Ni fa koyaushe na kira wayan Idris ba ta shiga kuma wallahi kwana biyu ina yawan mafarkin Innayi"




"Ayya Autan Innayi! dole kiyi kewa kusan shekara ɗaya da watanni fa. Nima ina son zuwa dubota tun last month to dayake kishiyata ta je Umara shiyasa ban je ba na ce zan je bayan sallah amma ban samu lokaci ba"


"Dan Allah ki ƙoƙarta ki je, hankalina Allah a tashe ya ke koyaushe"


"Shikenan zan je Insha Allah"


***


Watanni biyu su ka shuɗe bayan komawar su Asibiti, a wannan lokacin ne aka yi Azumi har aka yi sallah wanda babu maraba da sauran lokutan a wajen Innayi. Cikin Azumi Innayi ta sha fama da ulcer da gudawa. Sai ta gama Azumi sai a kawo ma ta abincin ƙwalame-ƙwalame na zamani wanda cikinta bai saba da shi ba ta ci ta zo ta yita gudawa. A haka dai ta daddafa ta ƙarisa Azumin.


Ranan sallah kuwa duk shige da ficen da ake yi a gidan tana kwance tana fama da zazzaɓi...




Yauma wuni ta yi da ciwon ƙirji da ciwon ciki. Tana kwance tana jiyo hiran Faiza da ƙawarta suna hira su na shewa da alama bikin wata ƙawar su za ayi wanda za ta auri wani tsoho. Tana ji ƙawar na cewa Faiza ta yi sa'an miji, miji kamar Idris yana da wuyar samu ga shi da kyau Masha Allahu.


Innayi ta cigaba da kallon ceiling kamar yadda ta saba a mafiya yawan lokutan, yau ta yi karatun ta yi waƙan har ta gaji.




Sallamar Sa'a ne ya katsewa su Faiza hiran su.
Ganin Sa'a ya sa jikinta yai sanyi.
Gaisawa su ka yi sannan Faiza ta tashi dan ta ɗauko ma ta ruwa.


Sa'a ta kalli Mufeedah da ke assignment a falon ta ce " Mufeedah where's your GrandMa?"


Ba tareda ta ɗago ba ta ce "she's inside her room"


Sa'a ta ce " go and call her"


"She wont come out, she's always inside the room"


"Wai haka?" Sa'a ta tambayi Faiza da ta fito ɗauke da tray.


"Ina ga bacci ta ke yi" Faiza ta amsa kai tsaye.


Sa'a ta tambayi ina ne ɗakin Faiza ta nuna ma ta...




Tana buɗe ɗakin ta hango Innayi a kwance tana nishin wahala.


"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" Sa'a ta faɗa ta yi wajen Innayi da sauri.


Daga inda ta ke kwance a ƙasa ta tallafota. Ta sake firgita da yanayin da ta ga fiskar Innayi, ta ƙyamushe ta bushe, idanunta sun firfito yayinda ƙasan idonta yai wani rami. Yadda ka san wata skeleton haka ta dawo.


"Innalillahi! na shiga uku ni Sa'adatu. Innayi ke ce haka?" Sa'adatu ta faɗa tana fashewa da kuka.


Innayi ta kalli Sa'adatu da kyau wanda sai da ta ɗau kusan 15seconds kafin ƙwaƙwalwarta ya iya processing ko wacece ke tare da ita.


"Sa'adatu" ta furta a hankali tana murmushi...








*RIBAR UWA*




*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*






Chapter 12
(Free book ne)




*A mother's sad demise*






Har lokacin da aka gama sakawa Innayi ruwa Sa'adatu ba ta bar kuka ba. Ba abinda ta ke yi a zuciyar ta sai tsinewa Faiza da Idris. Jinyar jikin Innayi ba na kwana ɗaya ba ne ba na kwana biyu ba, jinya ne da ya ke cin ta tun da jimawa.


Lallai a gaishe da Innayi da ƙarfin hali ko sau nawa idan su ka gaisa a waya ba ta nuna ma ta tana da damuwa. Kullum idan ta tambayeta ya jiki cewa ta ke da sauƙi.


Bayan nurse ɗin ya tafi ne Innayi ta kalli Sa'a ta ce "miye na kuka kuma? Ba fa mutuwa na yi ba Sa'adatu sa'ar mata"


"Yanzu Innnayi haka kike zaune tsawon watanni kina cikin ƙunci ba ki taɓa faɗa ba, Innayi haka za ki yi ta shiru har sai sun kashe ki?"


"To mi zan ce?"




"Kai Allah ya isa Idrissa, wallahi kai da matarka ba za ku ga alkhairi a rayuwar ku ba"


"Kul Sa'a, ka da ki sake mu su mummunan addu'a. Addu'ar shiriya kawai za ki mu su, ita na ke yi mu su tuntuni.


Sai da Innayi ta yi bacci kafin Sa'a ta fita ta je wajen Likita dan ta ji bayanin abinda ke damun Innayi.
Ba ƙaramin ruɗewa ta yi ba lokacin da aka ce mata Ulcer ce ke damun Innayi da ciwon zuciya.
Dama ma su haƙuri irin na Innayi ba sa rasa damuwan zuciya. Ko mi aka mu su suyi shiru su yi ta zurfin ciki, ƙarshe idan akayi rashin sa'a a haka za su mutu da baƙin ciki...




Koda Idris ya dawo ya tarar da matarsa tana ta kunfa akan cin mutuncin da Sa'a ta ma ta a gaban ƙawarta da 'yarta.


"Darling mari na fa ta yi. Wallahi dan tana yayarka ba shine zai hana in mata rashin mutunci ba. Ka warning ɗinta dan wallahi ba za mu wanye lafiya ba. Haka kawai mutum bai neme su ba su dinga zuwa gidan mutane shishshigi"


"Calm down dan Allah, mi ya ke faruwa ne? Nima ta kirani ɗazu tana ta zagi na"


Faiza ta tura baki ta ce "wai Innayi ce ba lafiya. To Darling mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login