Showing 15001 words to 18000 words out of 50413 words
da ke zuwa gaban mai tsire ko balangu ko mai shayi ko wani abun maƙulashe ya cinye ba tareda ya kaiwa iyalen sa ba Allah ya shiryeshi. Its bad its very bad, mummunan hali ne da kan iya sawa mutum ya samu zunubi a wajen Allah. Za ka ga wasu 24/7 matan su ɗumame su ke ci da safe amma shi 24/7 da safe yana gindin teburin mai shayi yana karyawa.
Bai gama tura ledan ba ma Raudha ta shigo ɗakin.
"Shegiya 'yar tselen 'wa ko sallama ba za ki yi ba za ki shigo min ɗaki"
Da ke ta saba da halin Uban na ta ta murguɗa ma sa baki tunda ba gani zai yi ba ta ce " Baba ashe kana nan, dama Malam Sama'ila ne ya ce a faɗa mu ku Baaba Usaina ta rasu"
Ta faɗi mutuwar karangatsau saboda ba ta san zafin mutuwa ba, dan a lokacin shekarunta goma a duniya.
Usaina matar Malam Sama'ila maƙocinsa ne.
Da kaman zai tsaya ya cinye naman sai kuma ya ce bari sai ya dawo daga jana'iza tukunna. Bayan fitar Raudha daga ɗakin ya sake tura ledar ƙasan gado sosai ya jawo wani wandon sa ya rufe da shi...
Buba bai tuna da tsiren nan ba sai washegari da yamma da ya dawo daga zaman makoki. Jiki na rawa ya jawo ledar tsiren yana jin haushin rashin tsayawa da bai yi ya ci tsiren ba jiya. Ya buɗe ya taɓa ya ji tsire ya lalace har ta fara yauƙi-yauƙi. Kaman zai yi hawaye saboda tsabar baƙin ciki, shi damuwar sa ta ya zai zubar da tsiren nan bayan yanka uku kawai ya ci aciki. Ya ɗau yanka ɗaya ya sa a bakin sa ya tauna, taste ɗin dai gashi ga kamar sa amma haka ya daure yai ta ci har ya cinye tas saboda bayason zubar wa.
Da tsakar dare ciwon cikin ya ritse Buba ga gudawa, ya lalumi sandarsa yana cakwkwalawa yana sauri tun kafin ya kai banɗakin ya fara zawo a wandon shi. Bai ƙarisa ba ya tsaya a tsakar gidan yana riƙe ciki yana "wayyo wayyo" daga baya kuma ya koma kiran Innayi "Innayi Innayi...Faɗima...wayyo Iro...Ado"
Innayi ce ta fara fitowa daga ɗaki tana haska torchlight tana salati ganin mijinta a ƙasa yana juyi yana ihu, Kafin ta ƙarisa wajen sa itama ta fara ƙwala kiran sunan manyan 'ya'yan ta...
Kafin gari ya waye ciwon ciki da gudawa yai ajalin Abubakar da aka fi sani da Buba. Buba Yusufu Pakkari mutumin Ajili, uba ga 'ya'ya goma, mijin Faɗima Innayi mai ƙosai. Duniya kenan! yadda ka zo ba komai haka za ka koma ba komai. Daga ƙarshe aikin ka shi zai determining abinda za ka tarar, shiyasa mu dinga tunawa da mutuwa a kowani lokaci domin ita mutuwa ba ta sallama, zuwa ta ke bagtatan, ko da ciwo ko ba ciwo, ko an shirya ko ba a shirya ba...
Washe gari da safe aka yi jana'izar sa aka kaishi gidan sa na gaskiya. Mutane na ta al'ajabin abin kamar ba da shi aka yi jana'izar matar maƙocinsa ba ashe shima yana hanya...
Innayi tafi kowa shiga damuwa da mutuwar Buba. Gaskiya ne ba ya ma ta komai da ya kamata miji yai wa matar sa amma kasancewar sa raye wani rufin asiri ne gareta sai dai ya za ta yi ita karan kan ta jiran mutuwar ta ke yi.
Dukkan 'ya'yan sa sun zo har da 'ya'yan Indo da ke Darazo wacce ɗaya ta yi aure ɗayar kuma tana aji shida a Sakandare. Babangida ɗan Harira ma ya zo anyi zaman makoki da shi. Bayan anyi uku aka fara maganar gado. Buba kam ba shi da komai da ya wuce gidan sa sai kuma kayan sawan sa. A hakan dai sai da aka raba gado da kowa banda Yusuf, wanda uwar sa Hajiya Harira ta ce yafi ƙarfin gadon Buba...
Wacce ba ta damu ko kaɗan da mutuwar Buba ba ita ce Raudha wanda dama ko da Buba na raye ita Innayi ce gatan ta, Innayi ce Uwa da Ubanta, Innayi ce komai na ta...
*RIBAR UWA*
*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*
Chapter 07
(Free book ne)
*A good son and a good daughter*
Shekara ɗaya kenan da Raudha ta sa Innayi ta fara zuwa Islamiyya. Da safe take zuwa duk ranan Asabat da Lahdi kuma sosai Innayi ta ke ƙaruwa da wannan Islamiyya. Shekara da shekaru ta na tafka kura-kurai a cikin sallolinta saboda sallan da aka koya ma ta kenan amma yanzu yanayin sallolinta ya gyaru sosai. Ƙaifin ƙwaƙwalwar ba kaman da ba amma a hakan Innayi ta fi mata dayawa a ajin na su ɗaukan karatu.
Yau ma daga Islamiyyar ta dawo ƙarfe shabiyu ta ɗan gota. Da sallama ta shiga ɗaki tana ƙoƙarin cire hijabin ta, Raudha na zaune gefen gado tana duba littafi, a hasale ta amsa sallamar ta cigaba da bubbuɗe littafi ran ta ɓace.
"Auta lafiya?" Innayi ta faɗa tana matsowa kusa da ita.
"Na kasa gane komai, ni dama chemistry wahala ya ke bani. Ba abinda na gane a nan" ta faɗa tana tura littafin gefe
Innayi ta ce "darasin ne ba ki gane ba?"
"Iyi, kuma gobe mu ke da jarrabawar" Raudha ta faɗa tana ƙara yatsina fiska.
Innayi ta ce "da yardar Allah za ki gane, ki bari anjima ki sake dubawa"
Raudha ta girgiza kai tana faɗin "gashi Yaya Baffa baya nan balle ya koya min"
Innayi ta ce "kar ki damu za ki fahimta Insha Allahu" ...
Matsananci shaƙuwa ce ke tsakanin Innayi da autar ta Raudha. Musamman yanzu da ya kasance kusan ita kaɗai ce a gaban ta.
Sa'adatu tun kafin ta gama karatu ta haɗu da mijinta Dr Mansoor amma ba ai bikin ba sai da ta ƙare karatu, Dr Mansoor mutumin Bulkachuwa ne amma yana zaune a Azare, yana aiki a asibitin FMC (Federal Medical Centre Azare). Ya auri Sa'a ne a matsayin matar sa ta biyu dan har lokacin da ya auri Sa'an shekaran su bakwai da aure da uwargidan sa amma ba ta taɓa haihuwa ba. Allah da ikon sa a shekaran da aka yi auren su a shekaran Sa'a ta haifi ɗa namiji. Suna zaman lafiya da ita da uwargidan ta hakanan Dr Mansoor ya sama wa Sa'a aiki itama a FMC ɗin.
Ado ya yi aure har da 'ya'ya biyu a lokacin. Iro ma shekarar sa ɗaya da aure ya yi gini amma ba a gama ba ya tare da matar sa akan zai ƙarisa ginin a hankali.
Baffah kuma ya gama ATBU yana service a jahar Kogi, ya ma kusa gamawa. Shi kuwa Idris yana ajin ƙarshe a BUK.
Tunda Innayi ta bawa Raudha labarin mahaifinta Muhammadu wanda yai burin ganin Innayi ta yi karatu mai zurfi har ta zama likita, Raudha ta sa a ranta za ta cika burin Innayi ta kowani hali, tunda 'yar Muhammadu Jo'o ba ta zama likita ba ai jikar sa sai ta zama. Hakan ya sa tana shiga SS 1 ta zaɓi shiga ɓangaren science, duk da kuwa ba wai tana jin daɗin darussan sciences ɗin ba ne...
Raudha na tsintar shinkafar da za su dafa da rana sai ga Jamilah matar Ado ta shigo da sallama. Ƙasa-ƙasa Raudhan ta amsa sallamar tana kau da kai gefe. Jamilah ta wuce ɗakin Innayi ba tareda ta yiwa Raudha magana ba, dama yanzu tsakanin su ko gaisuwa babu. Tun tana Amarya su ke faɗa da Raudha, haka Ado zai kama Raudha ya ma ta shegen duka amma gobe ba zai hana ta yi faɗa da Jamilah ba. Musabbabin faɗan ta akan Innayi ne, a rayuwar Raudha idan kana so ka ga faɗan ta cikin sauƙi to ka taɓa Innayi. Tun Jamilar na Amarya ta ke nuna halin ko in kula ga Innayi, ganin uwarmijin na ta ba mai hayaniya ba ne ya sa ta ke ƙoƙarin rena ta sai dai Raudha ba za ta bari ba, dan rana na farko da ta fara yiwa Innayi maganar banza Raudha zuwa ta yi har falonta ta zazzageta duk da kuwa Jamilar ta girmeta da kusan shekara shida.
Jamilah na shiga ɗaki ta ajiye ɗan ƙaramin kwanon da ta ke zubawa Innayi abinci ta ce "Innayi zan fita unguwa, ga key nan idan Yaya ya dawo a bashi"
Innayi ta amshi key ɗin tareda addu'ar Allah ya dawo da ita lafiya.
Bayan Jamilar ta fita Raudha ta shigo ɗakin ta buɗe kwanon da Jamilah ta shigo da shi, ja dogon tsaki bayan ta ga ɗan abincin da aka zuba aciki duk da kuwa ba wai kwanon na da girma ba ne amma abincin ciki ko rabin kwanon bai kai ba. Tun tana Amarya da su ka yi faɗa Raudha ta dena cin abincin ta, ko da Innayi ta yi magana sai cewa ta yi ta yi haƙuri amma ko za ta mutu da yunwa ba za ta ci abincin Jamilah ba.
"A dinga zubo abinci kamar wanda za a ba mabarata" ta faɗa tana rufe kwanon.
Idan da ta ita ne to so ta ke Innayi ma ta dena cin abincin. Abincin da za a kawo ba nama ba komai idan kuwa aka saka nama to kitse ne ko ƙashi. Kuma na ranan da Yaya Ado baya haɗo cefane da nama ko kifi amma saboda Innayi ce ba ta san daɗi ba shiyasa matar sa ke ƙyashin saka ma ta nama a abinci.
"Allah ya dawo da Yaya Baffah lafiya. Ai duk gidan nan ba kamar shi, shiyasan darajan Uwa"
Innayi ta amsa da Amin cikin ran ta tana tuno kyawawan halayen Baffan.
Shi ne indai yana nan ba sa rasa cin nama ko kifi a abincin su. Watarana haka zai siyo mu su tsire ko balangu da dare ana cin tuwo ana haɗawa da shi. Kayan shayi kuwa indai yana nan ba sa rabuwa da shi dan lokacin har sabo da shayi Raudha ta yi, ko da ɗumame za ta ci da safe to sai ta kora da ruwan shayi...
Bayan sun ci abincin rana wanda shinkafa ce da wake da mai da yaji Raudha ta tattaro wankin ta da na Innayi ta je tsakar gida ta ja ruwa a rijiya ta fara wanki.
Bayan Innayi ta yi sallar Azahar kamar kullum ta hau addu'o'in da ta saba, tana so ta yiwa Raudha addu'ar gane darasi amma ta manta sunan darasin. Ta ɗan leƙo kan ta ta wajen window ta tambayi Raudha sunan darasin.
"Chemistry"
"Kamisiri"
"Innayi Chemistry fa" Raudha ta faɗa da ɗan ƙarfi.
"To na ji" ta amsa tana komawa kan sallayar da ta ke zaune. Ta ɗaga hannu tana yiwa 'yar ta addu'a
"Ya Allah ka sa 'yata Raudha ta riƙa fahimtar darasin Kamisiri, Ya Allah ka sa ta dinga fahimtar dukkan darussan da aka koya ma ta. Wannan darasin na Kamisiri da ke ba ta wahala ka sauƙaƙa ma ta shi Ya Allah..." ta jima tana wannan addu'an kafin ta cigaba da sauran kaman yadda ta saba. Ba wai ba ta yiwa 'ya'yan ta addu'a ba ne a da amma tunda a makarantar Islamiyya aka ce addu'ar Uwa ga 'ya'yanta yana saurin karɓuwa ya sa Innayi ta kuma dagewa akan yiwa 'ya'yanta addu'a. Kasancewa zuciya ta fi son wanda ke kyautata ma ta a duk lokacin da Innayi ke addu'a to addu'ar Raudha da Baffa sun fi na kowa.
Kuskuren da mu ke yawan yi kenan, ba za mu waiwayi iyayen mu ba sai mu na cikin matsala.
Mama dan Allah a tayani da addu'a ina neman kaza. Bayan kuma rabon da ka kyautata ma ta har ka manta, amma saboda kana cikin matsala sai ka tuna cewa addu'ar Uwa yana saurin karɓuwa, wani ba sa tare da mahaifiyar sa amma sai yai sati yai wata bai kira ta ba, sai yana neman abu ka ga jikin sa na rawa zai kira ya fara dan Allah Mama a taya mu da addu'a. Shame on us....
Da dare da Raudha ta sake waiwayan littafinta sai gashi ta iya gane wasu daga cikin abubuwan da aka koya mu su a darasin Chemistry ɗin. Ta je ta ɗakin Baffah ta binciki kayansa ta samo notes ɗin Chemistry ɗin sa lokacin yana Sakandare ta haɗa da nata ta yi karatun da shi sai taga ta gane sosai...
***
Sati biyu da gama jarrabawan Raudha Baffah ya dawo, ya gama bautar ƙasa.
Abu ne na farin ciki saboda Baffa shine ɗan Innayi na farko da ya kammala degree yai bautar ƙasa, shi Ado diploma kaɗai gareshi ya tsaya.
Kamar ya san ba zai yi nisa a duniyar ba ya kira mai hoto gida aka yi hotuna, ya ɗaurawa Innayi facing cap ɗin uniform ɗin sa ita da shi suka riƙe certificate ɗin sa aka ɗaukesu hoto su na murmushi.
Ranan Ado da ya ga ƙanin na sa ya kammala degree sai ya ji kishi ya ɗarsu a ransa, dan yana tunanin ya riga shi fara boko amma gashi yanzu ya ma sa nisa. Ranan kam ta zamo wa Innayi rana ta farinciki a rayuwar ta. Kaji biyu Baffah ya yanka aka yi miya da shi, Raudha acicin nama daren ranan baki har kunne saboda yadda ta ga nama dumu-dumu a miyar ta...
Kullu yaumin addu'ar Innayi Allah ya ba wa Baffah aiki mai albarka.
Yana da buri sosai akan Innayi, shi ne ya fara sa Innayi acikin plan ɗin sa kafin na shi plans ɗin.
"Innayi idan Allah ya hore min zan sa a rusa sashen nan kema a miki ginin zamani, Innayi Insha Allah zan kai ki makka" kaɗan daga cikin abubuwan da ya riƙa nanatawa kenan tun ma bai gama karatu ba.
Lokacin auren Sa'a yafi kowa zuba kuɗi da ake haɗa kuɗin da za a ma ta kayan ɗaki, duk da kuwa shine bai da aiki a lokacin.
A koda yaushe burinshi shine ya samu mace da za ta so Innayi kamar yadda za ta so na ta uwar ko ma fiye. Shiyasa bai sa harkan mata a gaban sa ba tukunna har sai ya kai wani mataki a rayuwar sa. Sai dai ka na naka tsarin ne amma Allah ya riga ya tsara komai da zai faru da kai tun kafin ka zo duniya.
Watanni biyu da dawowar shi ya applying wani aiki a Jos inda su ka kirashi interview. Ranan Lahdi ya shirya tafiya akan zai kwana a chan saboda interview ɗin da safe ne sai kuma ya chanja ra'ayi akan zai tafi da sassafiyar Litinin ɗin.
Da yamma ya kai ziyara gidan yayar sa Halima da Yayan sa Iro duk da kuwa sun haɗu da Iron da safiyar ranan...
Raudha na koyawa Innayi karatun ƙur'ani Baffah ya shigo ɗakin da sallama.
"Yaya akawo ma ka tuwon ne?"
Ya girgiza kai ya ce " ba na jin cin tuwo yau ƙila gobe na ci ɗumame"
"Yaya gobe Litinin fa ko ba za ka ɗauki Azumi ba ne?"
Ya ce " af na manta zan ɗauka Insha Allah. Bari mu ga ko zan iya cin tuwon anjima"
Raudha ta yi saurin jawo ledar da ya ajiye tana faɗin "Yaya ka san na fi son balangu fa amma ka siyo tsire"
"Yi haƙuri Auta balangun ne ya ƙare shiyasa na siyo tsiren"
Tana yiwa Innayi karatu tana cin tsiren har su ka gama kafin Innayi ta ci sauran naman wanda kusan Raudha ta cinye fiye da rabi.
Innayi ta lura da yadda Baffah yai shiru ba ya magana saɓanin yadda ya saba yi mu su hira idan yana ɗakin.
"Baffa na lafiya?"
Yai murmushi ya ce " lafiya, kawai ina tunanin aikin nan ne"
Raudha ta ce " Yaya ai ka samu aiki angama da yardar Allah. Waya Reza za ka siyamin da albashinka na farko Yaya"
Yai dariya ya ce "ki dai dage da karatu ba abinda ba zan siya mi ki ba"
Raudha ta ce "yawwa Baffan Innayi"
Gaba ɗaya su ka sa dariya.
Saboda kar ya ɗaga hankalin Innayi ya sa ya saki ran sa su ka cigaba da hira kamar kullum yayinda Innayi ke ƙara jaddada ma sa zai samu aikin idan ma bai samu ba zai samu wanda ya fi wannan. Ya jima a ɗakin na su dan har sai da Raudha ta yi bacci ta bar su suna hira da Innayi. Kusan ƙarfe shaɗaya na dare ya bar ɗakin bai ci tuwon ba haka ya kwanta.
Washe gari da sassafe ya shirya, ƙarfe shida ba ta gama cikawa ba ya fito daga ɗakin sa da ke zaure ya nufi cikin gida. Raudha ta gama wanke wake kenan tana zubawa a roba za ta kai markaɗe ya shigo.
Bayan sun gaisa ta ce " Yaya ka yi kyau"
Na gode ya amsa sannan ya shiga wajen Innayi. Tana zaune a sallaya tana lazimi ya shigo. Bayan sun gaisa ya miƙa ma ta ɗari biyu kuɗin cefane.
"Insha Allahu zan dawo da wuri" ya faɗa a hankali
Innayi ta ma sa addu'a tareda fatan Allah ya tsare ma sa hanya.
Ya tashi jiki a mace ya fita daga ɗakin, Kiciɓis su ka yi da Raudha za ta shigo har su na bugan juna.
"Sorry Yaya" ta faɗa tana kallon sa, gani ta yi ya ma ta kyau sosai, ta fara kallon sa kamar wanda su ka yi shekara basu haɗu ba.
"Raudha wannan kallo haka?" Ya faɗa yana murmushi.
"Yaya kar fa 'yan matan Jos su sace ka irin wannan gayu haka"
Ya ja kunnen ta tareda cewa " na tafi, ki kula da Innayi"
Ta gyaɗa ma sa kai ta shige ɗaki shikuma ya fita.
Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya leƙo ɗakin ya ce "Auta ki faɗawa Yaya Ado na tafi, bai fito sallar Asuba ba da na ma sa sallama"
"Zan gaya ma sa"
"Sai na dawo ko" ya faɗa yana murmushi Raudha da Innayi su ka haɗa baki wajen faɗin "Allah ya kiyaye hanya"...
Ashe ganin ƙarshe da za su ma sa kenan. Tafiyar Baffah kenan ta har abada, kowa da lokacin da aka ɗiba ma sa a duniyar nan. Wa'adin ka na cika za ka mutu ba tareda ka ƙara ko da daƙiƙa ɗaya ba.
Tun kafin su isa Jos motar su ta yi hatsari. An kai su asibitin da ke Toro amma shi Baffah tun kafin a isa asibitin ya cika, cikin motar ta su da shi da wata mata ne su ka rasu sauran sun ji raunuka amma ana tsammanta za su rayu.
Tun tafiyar Baffah Innayi ta kasa gane yanayin jikinta hakan ya sa ko fitowa tuya ƙosai ba ta yi ba, Raudha ce ta yi