Showing 9001 words to 12000 words out of 50413 words
kwana biyu. Sa'a kawai ta ɗauka ta wuce ƙauye saboda sauran yaran su na zuwa Makaranta.
Ko da ta je ƙauye Baffa Habu maganar gado ya ma ta domin tunda aka raba gadon ɗan uwan sa bai damƙawa Faɗima na ta ba saboda ƙarancin shekarunta, ya cigaba da kula ma ta da dukiyarta, gashi yanzu cikin shanayen da aka ba ta har sun hayayyafa sun yi yawa.
Gaban sauran 'yan uwan sa Baffa Habu ya sa aka fitar wa Faɗima gadonta, wanda ba ƙaramin mamakin dukiyar ta yi ba. Shanaye talatin da bakwai da kuma gona, ga kuma gida mai ɗakuna biyu wanda cikin gidan gadon su ne dama mahaifinta Muhammadu ya gyara ya zauna da matarsa Aminatu kafin rasuwar ta.
Innayi ta yi kuka sosai domin Baffa Habu ya riƙe amana, tunda rainonta ya koma hannun shi bai taɓa banbantata da 'ya'yan sa na cikin sa ba, ga matar sa Hebbini itama Akwai kirki domin ta riƙeta tsakani da Allah...
Bayan ta dawo ne ta sanar da Buba duk abinda aka yi. Buba ya sha mamakin dukiyar da Innayi ta samu dan ko shi da ya ke ganin ya gaji dukiya sanda mahaifinsa ya rasu bai kamo rabin abinda Innayi ta samu ba.
Wannan dukiya da ya ji labari ya tsolewa Buba ido, nan da nan ya fara shiryawa Innayi magana akan yana so ta bashi aron wasu Shanu ya siyar zai ƙarisa ginin gida da shi idan ya samu kuɗi zai maida ma ta. Poor Innayi ta damƙawa mijinta ragaman dukiyarta, a tarbiyan da aka ɗaurata miji yana da damar da zai yi amfani da dukiyar mace a duk lokacin da ya ke so. Rashin ilimin addini da na zamani yakansa dayawa mazaje su na cutar da matan su simply because matan ba su san hakkin su ba.
Buba bai yi batun gini ba ma sai da maganar auren sa ya kankama. Ƙauyen Saɗe ya je ya nemi yarinya budurwa 'yar shekara shabiyar wacce ta ƙarisa makarantar primary, da ke yanzu an fara barin 'ya'ya mata a ƙauye su na karatu musamman primary school ba kaman da ba.
Maganar auren ma bai gayawa Innayi ba a bakin Harira ta ji wanda tunda yai ma ta maganar ta tada jijiyar wuya akan ba ta yarda ba. Shi kuwa ya ce mata huɗun nan sai ya cika su rus.
The only place da namiji ke iya bugan ƙirji kenan "namiji mijin mace huɗu ne"
Bai san hakkin mace ɗaya ba a kan sa balle har mata huɗu, amma haka zai dinga ɗaga kafaɗa yana burga, shi namiji ne, ai zai iya auren mata huɗu.
Ya ciyar da su? Ya tufatar da su? ya yi adalci tsakanin su? Duk ba damuwar sa ba ne. Shi dai damuwar sa yana da ƙarfin da zai iya saduwa da mata huɗu dan haka zai auri mata huɗu...
Koda daga baya da yai wa Innayi maganan auren itakam addu'a kawai ta ma sa duk da kuwa chan ƙasan ranta ta san Buba da dukiyar ta zai ƙara aure.
Ba a ɗau lokaci ba Amarya Aishatu Indo ta tare a gidan.
Ƙosai da Innayi ke yi ya fara kasawa, gashi cinikin ba kaman chan quarters ba dan a anguwar ta su gida uku ake tuyan ƙosai. Wannan ya sa ta yiwa Buba magana akan ya siyar ma ta da shanu ta yi jari da shi ta fara sai da wasu abubuwa a gida. Yadda ka san dukiyar sa ne haka ya dinga hura hanci yana kame-kame kafin daga baya ya amince.
Dai-dai kuɗin da zai bawa Harira da Indo haka zai ba ta duk ranan girkin ta gashi kuma ita ke da 'ya'ya dayawa dan bayan Sa'a ta sake haihuwan Idrissa. Shiyasa ta ga dole ta ƙara da wani abun dan sana'ar ƙosai ya ja baya...
*RIBAR UWA*
*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*
Chapter 05
(Free book ne)
*Unwanted child*
A hankali rayuwar ta cigaba da tafiya, da daɗi ba daɗi haka iyalen wannan gida ke rayuwa.
Innayi kam ta zama mai sana'a goma da ashirin. Ita ce ƙosai, ita ce sai da icce, daddawa, ga kayan miya. Kuma Alhamdulillah akwai Albarka a ciki. Harira ma da ta ga halin Buba ba zai kai ta ba sai ta fara sana'ar ta ta sai da Masa.
Indo kuma sana'ar kitso ta ke yi. Zuwa yanzu dukkan su halin Buba ya bayyana mu su, Buba kan sa kawai ya sani, albashin sa bai taka kara ya karya ba amma a hakan ba ya mu su adalci, tun su Harira da Indo na faɗa akan ƙarancin kuɗin cefane da ya ke ba su har su ka haƙura su ka bi sahun Innayi su ka rungumi haƙuri. A gidan yanzu kowa tashi ta fishshe shi su ke.
Harira ta haifi ɗa ɗaya mai suna Yusufu, da ke sunan mahaifin Buba ne sai su na kiran shi da Babangida. Ita kuwa Indo yaranta biyu, Rabi da Maryam. Innayi kuma 'ya'ya shida.
Ado ya gama secondary school ya samu admission a Teachers College wacce yanzu aka upgrading na ta zuwa AD Rufa'i College for Legal and Islamic studies Misau ( ADR CLIS). Ranan ya zo ya sanar da Buba tareda maganar kuɗin registration da sauran abubuwa. Buba ya hau shi da faɗa akan shi lokacin da ya na shekarun sa ya fara aiki yana ciyar da kan sa amma shi a shekaru shatakwas ba abinda ya sani sai dai a bashi ya kashe. Ya haɗa da cewa Bokon banza Bokon Wofi.
Ado ya bar wajen sa cike da ɓacin rai. Kai tsaye wajen Innayi ya nufa ya na ƙorafi, duk abinda bai iya faɗa wa Uban sa ba shi ya ke gayawa Uwar sa tunda dama Uwa Uwa ce.
Innayi ta fara bashi haƙuri tareda alƙawarin za ta san yadda za ta yi a samu kuɗin makaranta. Har ranta tana so 'ya'yanta su yi karatu saboda yadda rayuwar ta ke chanjawa. Sai dai duk da haka Ado bai da niyyar taimakon kan sa dan ba sana'ar da ya nema ko kuma ya ke yi. Da farko ma Uban sa ya kaishi shagon ɗinki ya dinga zuwa idan ya dawo daga makaranta amma ya fara zuwa ya ji wahala ya gudu. Ƙanin sa Iro kuwa shi da kan sa ya kai kansa shagon wani bakanikin Mota ya na koya, gashi yanzu sosai ya iya gyaran Mota.
Kafin sati Innayi ta harhaɗo kuɗi ta ba wa Ado ya karɓa ya je ya fara registration.
Halima ta zama 'yan mata kuma alamu sun nuna aure ta ke so ba Makaranta ba dama Buba ya ce ba yarinyar sa Mace da za ta yi gaba da Sakandare, to Halima kuwa tun tana JSS 2 ta fara tsayawa da Samari. Innayi ta yi ma ta magana akai ta ƙi ji dan haka ta haƙura ta zuba ma ta ido. Ta so ace Halima ta ƙarisa Sakandare ɗin kamar yadda Buba ya ce amma a yadda ta ke yanzu duk ta watsar da karatun ta ma dena zuwa.
Farin fata da kyau shi ya ke ruɗar da Halima yadda Samari ke yayinta hakan ya ƙara ma ta falli. Cikin ma su zuwa wajen ta tafi ba wa Alhaji Nuhu mahimmanci saboda duk ya fi sauran arziƙi yana da gida da mota sannan ya je shi Makkah, Ɗan kasuwa ne da ya ke tashe a lokacin.
Ganin yadda ake yawan sallama da Halima ya sa Buba ya ce ta tsaida ɗaya aciki ta turo shi saboda ba ya son a ɗau lokaci tunda ta dena zuwa makaranta.
Halima ta bi shawarar zuciyar ta da kuma shawarar ƙawayen ta ta amince da Alhaji Nuhu. Innayi da ta ji zaɓinta hankalinta ya tashi domin ta san mutum irin Alhaji Nuhu ba tsakani da Allah ya ke son Halima ba, soyayya ce kawai ta sha'awa ya ke yi ma ta saboda ƙuruciya da kyaun Haliman.
"Amma Halimah ni ina guje mi ki auren da babu farin ciki. Idan har za ki bi shawarata ki amince da Malamin makarantar ku"
"Allah ya kiyaye Innayi. Mi za ayi da Malam Faruƙ baƙin talaka, malamin primary ne fa. Ni ba zan yi aure na ƙare kamar ki ba kullum ba kwanciyar hankali"
Innayi ta yi murmushi ta ce " idan farin ciki ki ke nema, ina da yaƙinin Malam Faruƙ zai faranta mi ki rai har ƙarshen rayuwar ki. Yana da ilimin addini ga na boko ma Alhamdulillah yana da shi, zai riƙe ki da daraja kuma gaba za..."
"Dan Allah ki bari haka. Na riga na zaɓi Alhaji Nuhu shikenan, ki min addu'a kawai, idan kuma ba kya son na shiga gidan arziƙi ne sai na ji dalili"
Innayi ta girgiza kai kawai tanajin ɗaci a ranta domin ta hango kwaɗayi irin na Buba a tattare da 'yar tata, dalilin kenan da ya sa Halima ta rufe ido a kan sai Alhaji Nuhu.
Tun lokacin da Alhaji Nuhu ya fara zuwa Halima ta juyawa Malam Faruƙ baya saboda shi ba ya kashe ma ta kuɗi kamar yadda Alhaji Nuhu ke ma ta. Tun alokacin ta ke yiwa 'yarta nasiha amma sam ta ƙi ji, ga shi Buba ma ɗan kuɗi da Alhaji Nuhun ke sake ma sa idan ya zo ya sa ya fi nuna ra'ayin sa akan Alhaji Nuhun. Ba a ɗau lokaci ba Alhaji Nuhu ya turo mutanen sa aka sa lokacin aure zuwa wata uku.
***
Rabon da Buba ya waiwayi shimfiɗar Innayi ya fi wata takwas. Shi ya sa yau ɗin da ya buƙaci hakkin sa ta sha mamaki sosai. Duk ranan girkin ta ba ya kulata, iya ka ci ya ba ta kuɗin cefane, randa tsiyar sa ya tashi kuwa ya ce ba shi da kuɗi. A wajen sa Innayi ta tsufa, ba ta buƙatar namiji, to dama ai buƙatar sa kawai ya ke biya ya tashi ya tafi dan indai batun gamsuwar kwanciyar aure ne to kuwa tun ranar farko har zuwa yau Innayi ba ta taɓa samun wannan gamsuwa ba.
A jahilcin ta, ita ta ɗauka dama maganar shimfiɗa to aikin mace shi ne mijinta ya gamsu da ita, ita kuma ta ɗau ciki ta haihu. Ba ta san cewa yadda za ta gamsar da namiji haka shima namiji yana da haƙƙin gamsar da ita.
Dayawa maza na wannan kuskuren, da mace ta fara girma sai su dinga ja baya da ita su na ganin kamar ba ta buƙatar kwanciyar aure. Wa su za ka ji su na cewa ai yanzu an girma sai dai a barwa yara wannan. Ko kuma idan mace ta nuna buƙatar ta sai su ce wai ke ba kya girma ne? Ko so ki ke 'ya'yan ki na haihuwa kema ki na yi?.
Wasu mazan kuwa ba sa damuwa da gamsar da matan su, su na biyan buƙatar su za su tashi su yi gaba shikenan. Duk da yanzu abun ya fara raguwa amma har wayau wa su mazan ba sa damuwa da shin mace ta gamsu ko ba ta gamsu ba? Indai su sun samu gamsuwa to shikenan an wuce wajen...
Kwanci tashi bikin Halima na matsowa ana ta kan shirye-shirye wanda duk da dukiyar Innayi ake yi dan idan ka cire gida to Buba ba shi da komai. Shanun sa gaba ɗaya sun ƙare, hakama gona ya siyar.
Ba laifi an yiwa Halima kayan fidda kunya duk da kuwa Alhaji Nuhun ya nuna ba sai anyi ma ta komai ba. Aka yi biki lafiya aka kai Halima ɗakinta tana shekara shashida a duniya. Ba ita ɗaya ce ba dan Alhaji Nuhu na da mata biyu kuma dukkan su sun haihu...
Tun ana hidimar biki Innayi ta gane tana da shigar ciki wanda ya sa ta yi mamaki ƙwarai dan autan ta Idrissa ya cika shekara bakwai kenan, har ma gani ta ke ta wuce haihuwa yanzu. Maimakon cikin ya sa ta farin ciki sai ya zama kunyar cikin ta ke yi.
Mutanen gidan ba su farga da cikin jikinta ba sai da ya kai wata shida. Harira ce ma ta taɓa tambayarta ko ciki gareta lokacin cikin na wata uku, amma rashin samun amsa daga wajen Innayin ya sa ta watsar da zancen.
"Yanzu ke Innayi a wannan talauci ki ke samun ciki. Yo ko Indo ai ta haƙura da haihuwa a gidan nan"
Innayi ta sunkuyar da kai cike da kunya ta cigaba da cura daddawa da ta ke yi. Harira kam ba ta yi shiru ba ta cigaba da mita, kafin dare kowa ya san Innayi na da ciki. Wai abin takaici shine Buba da kan sa ya ke zagin Innayi akan ta ɗau ciki bayan ta san ba kuɗi gareshi ba. Hmmm Namiji kenan!
A yadda Buba ya ke yanzu yana samun kuɗi kaɗan aure zai ƙara amma shi ne dan za su samu ƙaruwa da uwargidan sa ya ke jin haushi.
Haka Innayi ta shanye duk wasu maganganu da ake ta faɗa ta cigaba da renon cikin ta cikin wahala, tunda cikin sana'o'inta ba wanda ta fasa.
Ana haka Buba ya fara ciwon ido, tun abun ɗaukan sa wasa yana shan maganin gargajiya har abu ya munana dan yanzu ido ɗaya ba ya gani ɗayan ma ba wai sosai ya ke gani ba. Da ya ga ba Sarki sai Allah sai ya amince ya je asibitin General Hospital Misau wanda su kuma su ka tura shi asibitin Aminu Kano saboda ya ga ƙwararren likitan ido.
Jin bayanin kuɗi Buba ya ce a barshi ba inda zai je. Daga baya da aka takurashi sai ya amince amma dai ba shi da kuɗin tafiya sai dai idan za a biya ma sa. Innayi ta ma sa magana akan cikin shanun ta a siyar da wasu ayi kuɗin magani, sai ya hauta da faɗa.
"Kina ta maganar shanu, wai shanun nawa ne kam? To bari kiji ba bu ko shanu ɗaya da ya saura. Bikin Halimatu duk da mi aka yi?"
Innayi ta danne ɓacin ranta ta fara bashi haƙuri. Saboda gani ta ke babban zunubi za ta samu idan mijinta yai fushi da ita.
Sai da ya fice daga ɗakin ta sauke ajiyar zuciya wanda ya sa hawayen da ke maƙale a idonta su ka sauko. Ita kan ta ba lafiyar gareta ba daurewa kawai ta ke yi amma tun lokacin da Buba ya fara ciwon ido ta ke cikin damuwa.
Gona guda da ya saura ma ta cikin gadon Uban ta wanda ɗan uwanta Aliyu ya ke noma aciki ta nemi siyarwa shi kuma Aliyun ya siya. Da kuɗin da kuma wasu kuɗaɗen ta na kasuwancin ta ta haɗa ta damƙawa ɗan ta Iro ya wuce da Buba Kano. Iro ya ƙare Sakandare kuma alamu sun nuna ba shi da niyyar cigaba da Boko dan yana tunanin buɗe nashi shagon kanikanci nan ba da jimawa ba.
Da su ka je aka duba Buba aka bashi wasu magunguna tareda cewa su dawo nan da sati biyu, saboda za'a gani ko aiki za su ma sa ko kuma za a cigaba da ɗaura shi akan magani...
Bayan su Buba sun dawo daga Kano da kwana uku Innayi ta fara naƙuda cikin dare, duka haihuwanta a gida ta ke yin su. Lokacin haihuwan Idrissa kam ita ɗaya ta haihu sai kawai ganin ta aka yi da jariri. Wannan karan ma so ta ke ta gwada haihuwan da kan ta musamman saboda dare ne ba ta son tayarda kowa, balle cikin da kowa baya so, ba ta so ta hanasu bacci saboda shi.
Tana jin jiki amma haka ta daure ta cize tana ƙoƙarin ganin ta haihu ita ɗaya. Ta kai awa ɗaya tana jin jiki kafin kyakykyawar jaririyarta ta fito. Ta yi hamdala a ranta tare da ƙoƙarin ɗauko reza dan ta yanke cibiyar yaro amma kawai sai ta sake jiki ta faɗi...
Kukan da jaririyar ke tsalawa ya fargar da Harira da ke bacci, da farko ta share kukan daga baya ta tuna ai ba su da jinjiri a gidan sai dai idan Innayi ce ta haihu. Da kukan yai yawa sai ta tashi ta fito tana ƙunƙuni.
Tana zuwa ɗakin Innayin yanayin da ta sameta ya tsorata ta, ta rinƙa salati tana kiran sunan Buba da ke ɗakin Indo da kuma Ado da Iro da su ke ɗakin zaure...
Kwanaki biyar Innayi ta yi ba ta san inda kan ta ya ke ba, dan ba ta buɗe ido ba ma sai a kwana na huɗu. CS aka yi aka cire ɗaya jinjirin da ke cikin ta wanda ya riga ya mutu a ciki saboda wahala. Likitoci sun yi faɗa sosai dan yadda su ka ga Innayin. Ba dan an kawota asibiti da wuri ba mutuwa za ta yi. Babu jini ajikinta ga kuma haihuwar da ta yi ƙoƙarin yi da kan ta duk ya wahalar da ita.
Su kan su 'ya'yanta da kishiyoyinta ba su ɗauka za ta rayu ba sai ga shi Alhamdulillah da ita da 'yarta sun rayu. Ɗaya yaron kuwa ana ciro shi aka je aka ma sa sutura aka bisine shi...
Sai da Innayi ta sha jini leda uku kafin ta ɗan fara samun kuzari. A hankali da ta yi kwana goma a asibitin kafin ta iya tunowa da komai har ta tuna cewa fa haihuwa ta yi. Da ke Innayi ba ta da ruwan nono tuni aka ɗaura jinjira akan madara. Har lokacin kuwa ba a raɗawa jinjirar suna ba, balle maganar yanka rago.
Ranan da Dr Imtiaz ya ke round ya iso wajen Innayi ya samu tana bawa 'yarta Madara ya tambayi sunan yarinya, Mairo 'yar Baffa Habu da ke jinyar Innayi ta ce ai har yanzu ba a sa ma ta suna ba, Dr Imtiaz wanda balaraben ƙasar Egypt ne ya tambayi dalili. Mairo ta ce ai ba abunda za a yi sunan da shi ne. Dr Imtiaz ya girgiza kai saboda jin wannan tsagoron jahilcin.
"Idan na ba ta suna za ku kirata da shi?"
Mairo ta kalli Innayi, Innayi ta gyaɗa ma sa kai. Dr Imtiaz ya ƙarɓi yarinya ya ma ta huɗuba da suna RAUDHA
"Sunan ƙanwata ce amma Allah ya ma ta rasuwa" Innayi da Mairo su ka ce Allah ya jiƙanta.
Ya saba ganin Fulani ma su sakaci da lafiyar su hakanan ya kan nuna ɓacin ran sa garesu amma haka kawai Allah ya haɗa jinin sa da Innayi. Tausayinta ne ya shigeshi tun daren ranan da aka kawota asibitin rai a hannun Allah.
Bayan fitar Dr Imtiaz