Showing 27001 words to 30000 words out of 50413 words

Chapter 10 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1775

laifi ne, ba sai UWA ta maka baki ba, ba sai UWA ta maka mummunan addu'a ba. Yadda ka ɓata ma ta rai, ka ƙi ka ji tausayinta haka za ka ga lamurranka su na taɓarɓarewa, kayita addu'a amma kaji shiru, idan aka samu rashin sa'a kuwa kafin ka nemi gafaran iyayen ka Allah ya riga ya karɓi baƙuncin su.


Allah ya sa mu gyara amin...




***




Kwanaki biyu bayan tafiyar Raudha ƙasar waje Innayi ta fara rashin lafiya. Kewar 'yar ta ne ya sa ta wannan jinya.
Ado ya kira wani Nurse da ke anguwar su aka ma ta allura aka ƙara ma ta ruwa, bayan kwana biyar ta warware sosai sai dai har lokacin tana kewar Raudha.


Saboda maganar Sa'a sai Ado ya maida yaransa maza biyu manya zuwa cikin gida. Ɗakin Buba na da nan su ke kwana.
To abu da yara maza, Innayi ba ta jin ɗuriyar su sai dare idan sun shigo za su kwanta. Abinci kam yanzu safe zuwa dare duk ana kawo ma ta daga gidan Ado sai dai da ka ga abinci da ake zubowa ka san na dole ne ba wai su na so ba.
Ko kaɗan hakan bai dami Innayi ba, ita babban damuwarta Raudha. Kullum addu'ar samun nasara da kuma albarka ta ke mata, tana yiwa sauran 'ya'yan na ta addu'a amma na Raudha special ne, sai ta yi minti goma tana nanata addu'a ɗaya a Radha. "Allah ka yiwa 'yata Raudha albarka, Allah ka kareta daga sharri, ka ba ta sa'a a dukkan lamurranta" haka za ta yi ta maimaitawa har sai ta gaji kafin ta cigaba da wasu addu'o'in. Akwai wani addu'a ɗaya da ko farkawa daga bacci ta yi sai ta yi shi, wani lokaci idan tana zaune tana jin rediyo ta ji kaɗaici sai ta tuno da Raudha nan take zata shiga yi ma ta addu'a.
"Allah ka bawa Raudha miji na gari, ka ji tausayinta kamar yadda ta ke jin tausayina"


Wallahi idan kana kyautatawa iyayenka ba za su taɓa gajiyawa wajen yi maka addu'a ba...


Wani sabon salo da aka fito da shi shine sai Innayi na zaman-zamanta sai ka ga Jamilah ta shigo ta zauna ta yi ta kawo gulmar Amaryarta Aisha tana zaginta a gaban Innayi, itama Aishar wani lokaci itama ta shigo wajen Innayi ta faɗi gaskiya da ƙarya akan Uwargidan na ta. Su ka maida wajen Innayi wajen kawo gulma.


Asiya matar Iro ma ta shiga sahun wannan gulmar sai dai ita tana aibanta su Jamilah ne saboda tana ganin kamar harda su a wajen son ayi ma ta kishiya, Iro yana neman wata yarinya 'yar uwar su Jamilan.


Duk abinda za su zo su faɗawa Innayi ba ta tanka mu su, iya kaci ta basu haƙuri. Ana haka watarana sai ga Asiya ta zo wajen Innayi kuma lokacin Jamilah na wajen ta. Ba a jima ba aka fara cacarbaki ana zage-zage.
Innayi ta fara ba su haƙuri saboda yadda su ke masifa kaman za su ci kan su.


"Yi mana shiru! Innayi ke ce baƙar munafukar ai, ashe har a wajenki ya fara tara kayan aure ban sani ba amma kullum na zo sai ki dinga kwantar min da hankali kina bani haƙuri kamar baki san komai ba"


Idon Innayi ya ciko da hawaye, duk wani zancen neman aure da Iro ke yi ita bai sameta ya ma ta zancen ba a bakin matan 'ya'yan na ta kawai ta ji.


"Asiya a ina kika ji wannan maganar?"
Ta faɗa tana danne wani ƙunci da ya ke taso ma ta a wuyarta.


Maimakon Asiya ta amsa ma ta sai ta kalli Jamilah ta ce " ke kuma wallahi ki cewa 'yar uwarki ta fita a hanyar miji na, yarinyar da Taliya ta ke siyarwa a Tasha ta gama zuwa an lallatsata shine za ta mannewa miji na yanzu"


Jamilah ta yi shewa ta ce " daɗin abin kema ɗin Kunu kike sayarwa ya ganki ya auroki. Kuma wallahi sai Hafsatu ta shiga gidan Yaya Iro, idan ma mutuwa za ki yi ki mutu"


Haka dai su ka cigaba da zage-zage kamar ma za su bigi juna, daga baya su ka fita. Asiya ce ta fara fita kafin Jamilah ta bi bayan ta, babu wanda ya damu da Innayi balle halin da ta shiga.


Innayi zama ta yi a bakin gado tana dafe ƙirjinta saboda zafi da ya ke mata. Maganar Asiya ya shigeta sosai, rabon da wani ya zageta haka tun lokacin zaman su da Harira. Duk yadda ta danne sai da hawaye ya zubo ma ta, tana tsakiyar kukan ne ta ji sallama. Ta yi saurin goge hawaye da gefen zaninta ta fito tana ɗaurawa fiskarta murmushin da bai kai zuci ba...




"Lale maraba, Hajiya Harira ce a gidan na mu, sannu da zuwa"


Harira ta tsaya tana ƙarewa Innayi kallo. Ko ita da ta girmewa Innayi a shekaru ba ta yi irin tsufan da Innayi ta yi ba. Idan ka haɗasu za ka ce Innayi ta ba wa Harira shekara goma ko ma fiye.


"Faɗima haka kika zama?"


Innayi ta kuma faɗaɗa murmushinta na bogi ta ce " tunda muna raye sai hamdala ai"


Tausayin Innayi ya shiga Harira, a yadda ta kalleta ta san har yanzu ba ta samu jin wani jin daɗi ba. Duk da itama tana fama da na ta 'ya'yan amma Alhamdulillahi babban ɗanta da ya samu aiki a Kaduna yana kula da ita sosai yanzu ma saboda ciwon ta da ke yawan tashi ya sa ya ce ta tattaro ta dawo wajen sa da zama shine ta zo yiwa Innayi sallama, rabon da ta ga Innayi tun da ta zo ma ta barka lokacin da Raudha ta gama bautar ƙasa.


"Wai ina Autan ki ne?" Ta faɗa dan ta kawar da shirun da ya ratsa ɗakin.


Innayi ta yi murmushi ta ce " ai Auta tana chan ƙasar turawa. Miye ma sunan ƙasar? Ehmmm Amelika, a Amelika ta ke karatu, a wata babban makaranta wai Hawad"


Harira ta ce Allah ya dawo da ita lafiya ya sa albarka a karatun ta. Innayi ta amsa da Amin.
Bayan sun ɗan taɓa hira ne ta sanar da ita za ta bar Misau za ta koma gidan ɗan ta a Kaduna. Innayi ta tayata murna sosai...




Bayan Harira ta tafi ta yi ta jimamin rayuwar Innayi, ko lokacin da su ke auren Buba haka ta rayu cikin ƙunci har Buban ya rasu gashi yanzu ma ba wani cigaban kirki da ta samu.
Kafin ta tafi cikin kayayyakin ta da ta ke son kyauta da su ta zaɓi wasu ta aikawa Innayi ta sani ko siyarwa Innayi ta yi za ta samu wani abu.


Babban katifa ce da ƙaramin fridge da wasu bokatai da robobi manya- manya wanda ta ke amfani da su da wajen sana'arta ta masa. Ta kira mai mota ya kai gidan Innayi.
Innayi da ta ga saƙo sai da ta yi hawaye, a daren ta sa hijabi ta tafi gidan Harira tana ma ta godiya. Harira ta ce ma ta ba komai ai an riga an zama ɗaya...




Kaman jira ake yi a kawo kayan dan kuwa ko abu ɗaya Innayi ba ta tsira da shi ba. Halimah ce ta ɗauke fridge da wasu robobi, ita kuwa Jamilah ta wawure katifar wai 'ya'yan ta za su dinga kwana a kai. Ta san da cewa katifar da ke kan gadon Innayi ya lalace amma ba ta damu ba haka ta ɗauke ta tafi dashi, ai ba ruwan tsohuwa da jin daɗi ta cigaba da fama da yarjalelliyar katifa kawai. Ya Allah!😭




Innayi ba ta mu su magana ba ta bisu da ido kawai. Fatan ta a koyaushe Allah ya shiryesu...




***


Raudha da ta je Havard kafin ta gane yanayin makarantar sai da ta ɗau lokaci. Bayan komai ya fara dai-dai ta ne ta shiga neman aiki a cikin makaranta saboda ta samu abin aikawa gida dan hankalinta bai kwanta da tsarin Yayun na ta ba...




Safiyar wata laraba Innayi tana wajen dabbobi tana shara wani rago ya tunkuyeta ba ta ankara ba ta faɗi ƙasa, ashe faɗuwar da ta yi ta bugu sosai nan ta ke ta suma.
Tana kwance a wajen sai da Almajirin da ke zuwa duba dabbobin ya shigo ya sameta a wajen nan ya fara ihu ya shiga gidan Ado ya sanar da su abinda ya gani.


Sule Almajiri da ke ba wani biyan sa ake ba abinci kawai ake bashi kuma ya fara girma yana ɗan ji da kan sa shiyasa baya wani kula da dabbobin yadda ya kamata. Wani lokaci sai ya wuni bai leƙo su ba balle har ya mu su wata hidima. Su kuma yaran Ado da ke kwana a wajen Innayi ba damuwa su ka yi da dabbobin ba, kowa tsiyar sa ta isheshi.
Idan Sule bai zo ba shine Innayi ke kula da dabbobin wanda har yau ɗin ya zo da tsautsayi...




Kwana bakwai Innayi ta yi a asibiti aka sallameta dan bayan buguwa da ta yi jininta ya hau sosai. Zuwan da Sa'a ta yi ne ta dinga faɗa tana tuhumar Ado da rashin kula da Innayi da ya ke yi.


Idris bai zo ba da aka faɗa ma sa Innayi ba lafiya amma da Sa'a ta kirashi a waya ta titsiyeshi ta dinga kwarwa dole yammacin ranan Jumu'a ya zo dubiya.


Bayan an sallami Innayi ne aka sake zaman meeting, wannan karan kowa ya halarta banda Raudha da ba ta ƙasar.
Likita ya ba su shawaran su kai Innayi babban asibiti ta ga ƙwararren Likita saboda a tabbatar da babu matsala a kanta duba da irin buguwar da ta yi. Duk da Innayi na nan lafiya amma Likitan ya ce dole ayi wasu gwaje-gwaje saboda kar gaba a samu matsala.


Sa'a ta nuna za su kai Innayi Teaching Hospital da ke Bauchi.
Yadda Idris ke wani haɗe rai ka san bayason inda zancen ke dosa.


"Ni a shawarata Innayi za ta zauna gidan Idrissa, idan ya so bayan ta samu lafiya sosai sai ta dawo, ko ya kuka gani?"


Kafin sauran su sa baki Idris ya ce " ba zai yiwu ba, kun san gidan haya na ke ga kuma aikina baya bani lokaci, ina zan iya da wani jelan asibiti"


Wannan karan harta Iro sai da ya ji zafin maganar Idris ɗin. Ya ce " Idris na kwana nawa ne ma za ta gama ganin likita ta dawo, ga matar ka ba za ta rinƙa rakata asibitin ba"


"Matata ma'aikaciya ce ba ta da lokaci" ya faɗa kai tsaye.


"Ubanka Idrissa, na ce ka ci uban ka da kai da aikin matar na ka. Ɗan Iska wani hidima ka taɓa yiwa Innayi? Ba Innayi kaɗai ba a wa ka taɓa yiwa hidima tunda ka samu aiki? Za ka nuna mana kai da matar ka kuna aiki, to wallahi ba aiki ba Allah ya sa bauta ku ke yi Innayi za ta zauna a wajen ku na iya lokacin da za ta ga Likita"


Kamar dama jira su ke nan aka shiga yiwa Idris faɗa musamman yadda bai damu da koɗaya daga cikin 'yan uwan sa ba, tunda ya koma Bauchi da zama sai yai wata uku huɗu bai leƙo Misau ba. Kuma ko ya zo ba abinda ya ke tsinanawa, matar sa kam tunda ya aureta sau ɗaya ya kawota Misau ta gaisa da 'yan uwan sa. Gara Idris yana ɗan kiran 'yan uwansa a waya randa ya bushi iska amma ita matarsa ta watsar da kashin 'yan uwan mijinta ko a waya ba ta neman su.


Ganin dai an ma sa taron dangi haka ya haƙura ya amince bayan an nuna ma sa ba shi kaɗai zai kawo kuɗin jigilar asibiti ba.Ranan haka Idris ya bar gidan ran sa a ɓace.


Bayan kwana ɗaya aka shirya tafiyan Innayi wanda ya kama ranan Monday. Sa'a da Innayi su ka tafi Bauchi, direct Asibiti su ka je dan ganin likita, bayan an gama mu su komai aka ba su takardar gwaji akan washegari su je a yi ma ta.
Sa'a ta kai Innayi gidan Idris kafin ta wuce Azare bayan ta yiwa Idris da matar sa bayanin da likita ya masu tareda basu takardun gwajin da za a yiwa Innayi....




Tunda Idris yai wa Faiza maganar zuwan Innayi gidan su hankalinta ya tashi. Take ta nuna ma sa ba ta son zuwan Innayi, nan ya shiga lallaminta yana faɗa ma ta ai zaman Innayi na lokaci kaɗan ne.


Tunda Sa'a ta tafi aka bar Innayi a falo ita kaɗai, sanyin fanka ya ma ta yawa amma haka ta daure tana jiran fitowar su. Ba su fito ba sai da ana kiran maghrib.


"Ki shiga ɗakin chan anan za ki kwana" Faiza ta faɗa a yatsine


Innayi ta tashi ta shige ɗakin wanda ɗaki ne da su ka mayar ɗakin baƙi.
Chan baifi minti biyu ba Innayi ta fito ta samu Faiza na kallo ta ce "dan Allah Maman Mufeedah ina ne banɗaki?"


Faiza ta yi kamar ba ta jita ba, Innayi ta sake maimaita tambayarta.


Da ƙarfi ta ce " Na ji mana! Ai ni ba kurmiya ba ce. Ki je ƙofar da ke gefen ƙofar da ki ka shiga nan ne banɗaki"


Innayi ta juya jiki a sanyaye. Faiza ta harari bayan Innayi tana faɗin " Village Witch"...




Innayi ta shiga banɗaki ta yi alwala ta fito, tana son kama ruwa amma ta rasa gane kan banɗakin, ta dai ɗau buta ta yi alwala kawai ta fito.
Bayan sallar Isha Faiza ta shigo ɗaki ta kawo ma ta plate ɗin abinci da satchet water ɗaya.
Sai da Innayi ta gama addu'o'inta sannan ta buɗe abinci dan ta ci. Fried rice aka yi da coselaw a gefe. Saboda rashin imani abincin rana ne da bai ƙare ba Faiza ta zubowa Innayi. Abincin yayi sanyi salalau ga coselaw ɗin har ya fara ɓacewa.
Innayi ta yi Bismisllah ta fara ci, ba ta san coselaw ba dan haka ta turashi gefe ta ci fried rice ɗin kaɗai duk da shima bai mata daɗi a baki ba. Ita tafi gane shinkafa da miya ko da yaji ko jollof ba kasafai ta ke so ba, Raudha ce ma ke yi lokacin da ta ke nan...


Ko awa biyu da kwanciya ba ta yi ba cikinta ya hautsine, ta rasa yadda za ta yi. Tun tana jin abin kaɗan-kaɗan har abun ya zama idan fa ta cigaba da matseshi sai dai ya zubo mata ba shiri. Ta yi ƙarfin hali ta je banɗakin da aka nuna ma ta ɗazu duk da ba ta san a ina za ta yi gudawan ba, ta yi ta maza ta zauna akan toilet ɗin ta fara yi.
Iya rayuwarta banɗakin gargajiya ta ke amfani da shi shiyasa ganin toilet ɗin na zamani ya zamo ma ta sabon abu. Da ta gama ta yi tsarki ta fito.
Daren ranan sai da ta zaga sau uku, gaba ɗaya kunya da tsoro ya kamata dan ganin yadda toilet ɗin ya ɓaci da gudawa gashi ba ta san yadda za ta yi ba.
Baccin kirki ba ta yi ba saboda fargaban abinda ta yi (Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Wai UWA ce ta ke fargaba da tsoro a gidan ɗan ta)


Da ke a ɗakin Idris akwai banɗaki a nan shi da matarsa su ka yi buƙatun su. Washe gari da sassafe da Faiza ta fito ne ta ji wari hakan ya sa ta buɗe banɗakin da ke gefen ɗakin Innayi.


"Darling! Darling !" Ta fara kiran Idris da kakkausan murya.
Da gudu ya fito daga ɗakin na su kafin ya zo Innayi ta fito saboda dama tana dakon fitowar su dan ta ja Idris gefe ta ma sa bayanin abinda ya faru.


Ganin yadda Faiza ke toshe hanci ya sa jikinta yai sanyi, cikin i'iina ta ce " ki yi haƙuri gudawa ne ya kamani jiya kuma ban san..."


"Will you shout up!" Ta dakawa Innayi tsawa dai dai fitowar Idris.


Tana tsaye bakin ƙofar banɗakin ta nuna ma sa cikin banɗakin da yatsa tana faɗin " go look at what your crazy mother did"


Namiji kenan! Bai fa damu da abinda ta kira uwar sa ba haka ya shiga banɗakin ya je ya gani. Da ya fito ya ce "Innayi ai sai ki kora da ruwa, wannan ai ƙazanta ne"


Muryar ta da ke cike da kuka ta ce "ban san ya ake korawa ba ne"
Ya jata su ka shiga ya nuna ma ta yadda za ta flushing toilet ɗin.


Faiza na waje tana faɗin "Darling wallahi sai dai ta wanke banɗakin dan warin yayi yawa"


"Baby kinga ba ta da lafiya, ki bari idan Huwaila ta zo sai ta wanke" Idris ya faɗa cikin rarrashi.


Ita dai Faiza sai tsaki ta ke ja tana tottoshe hanci ƙarshe ta je ta ɗauko room freshner ta feshe gidan da shi.


Sai da Huwaila mai ma ta aiki ta zo kafin ta rage ƙorafi. Innayi na ɗaki tanajin matar ɗan na ta nata faɗa tana zage-zage ta yi da turanci ta yi da Hausa...




Huwaila wata bazawara ce amma ba wata Babba ba ce dan shekarun ta shatara. A chan ƙasan layin su Faizan gidan su ya ke, da sassafe za ta zo ta mata wanke wanke da shara ta yiwa 'yarta Mufeedah wanka ta shiryata. Bayan sun karya sannan ta tafi. Hakanan da yamma ma za ta zo ta yi gyaran gida ta kuma taya Faiza girki, da ke ƙarfe biyu Faiza ke dawowa daga Office.


Bayan Huwaila ta gama ayyukan ta ne Faiza ta ba ta biredi da ragowan tea ɗin da su ka sha ita da Mufeedah akan ta kaiwa Innayi.
Innayi ta karya a tsorace, ba abinda ke mata daɗi a baki amma haka ta daure ta ci.
Tuni Idris ya fita office, da Faiza ta gama shirinta ta ƙwanƙwasa ɗakin Innayi ta ce "idan kin gama ki fito Huwaila ta raka ki asibitin ni na tafi office"


Innayi ta amsa da toh.


Ita dai Huwaila tana ganin ikon Allah, ko ba a faɗa ma ta ba ta san Innayi ita ce mahaifiyar Idris saboda tsananin kamannin su. Amma yadda Faizar ta yi ka ce Innayi wata boyi- boyi ce a gidan.


Huwaila ta nunawa Innayi yadda za ta yi wanka a banɗakin bayan ta sa ma ta ruwan zafi. Da Innayi ta gama shiri sannan su ka fita, da ke an saba bar wa Huwaila Key kawai kulle gida ta yi su ka tafi Asibiti. Su na cikin keke Napep Innayi na sauke ajiyar zuciya. Ba abinda ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login