Showing 12001 words to 15000 words out of 50413 words
daga ward ɗin Innayi ta dubi jaririyarta, ta kira sunan da aka sa ma ta a hankali RAUDHA...
*RIBAR UWA*
*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*
Chapter 06
(Free book ne)
*A Mother alone*
Al'ada da ake yi da jimawa wanda ya fi ƙauri tsakanin Hausawa da Fulani inda za ka ga idan mace na jinya za ta koma gidan su har sai ta warke, Al'ada ce da kwata-kwata bai kama hankali ba. Idan ina da lafiya mu na tare amma idan jinya mai tsanani ya kamani to sai dai na koma gida wannan kwata-kwata bai dace ba. Amma Alhamdulillah tunda yanzu neman ilimi da ake ya sa an samu massive chanji sosai.
Duk jinyar Innayi da ta yi a asibiti 'yan uwanta ne su ka biya kuɗi su ka kuma yi ma ta hidima. Buba kam dama fama ya ke da kan sa balle ma ace zai iya taɓuka wani abu.
Daga wajen Alhaji Nuhu mijin Halimah ake tunanin samun kuɗi sai dai ko gaisuwa bai zo ya yi ba balle ya kawo wani abu.
Haka Innayi ta yi kwana ashirin da bakwai a asibiti kafin aka sallameta. Zuwa lokacin ta warke sosai kuma ta yi kyan gani, 'yar ta Raudha ma na nan cikin ƙoshin lafiya madaran da ta ke sha sosai ya karɓeta...
Bayan Innayi ta dawo aka shiga wani sabon rayuwa. Sosai aka ja ma ta kunne a asibiti akan ta rage ayyukan da ta ke yi idan har ta na son ta samu lafiya. Hakan ya sa ta ajiye sana'ar ƙosai da daddawa a lokacin, sai dai fa abubuwa ba su zo ma ta da sauƙi ba. Domin sai da ta ƙwammaci gara ta koma sana'ar ta saboda asirinta ya rufu da babu da ta ke fama da shi.
Mijinta Buba kam tun da ya ji ya fara samun sauƙi ya watsar da maganar komawa asibiti. Dama kuma rashin lafiyar Innayi ya ɗauke hankalin iyalin sa daga batun ciwon idon sa.
Raudha Auta, Raudha 'yar gata, Raudha Alkhairi, Raudha haske, kaɗan daga kirarin da Innayi ke wa 'yar tata kenan. Duk da kuwa a zahiri Raudha ba cikin gata ta taso ba, asalima duk cikin yaran Innayi ita kaɗai ce ba a yanka ma ta ragon suna ba balle har ayi wani hidiman suna. Hatta kayan sawa duk kunce ake sa ma ta sai da ta kwana biyu a duniya kafin aka samu kaɗan daga cikin ma su zuwa gaishe da Innayi su ka zo da kyautan kaya wa jinjira.
Wata uku da haihuwar Raudha Buba ya makance. Ya fara da ganin biji-biji ne, bayan kwana uku idon ya dena gani gaba ɗaya. Tashin hankali ya shiga wannan gida domin Buba tamkar mahaukaci haka ya dawo lokacin da idon sa ya makance, faɗa ya ke da kowa tareda baiwa iyalensa laifi bisa makantar sa. Anyi ƙoƙari an tara kuɗi an maida shi Kano amma abin duk maganar kuɗi ne, sannan bayan kuɗi an nuna mu su ko da anyi ma sa aikin ba su da cikakken yaƙinin idon sa zai koma gani kamar da.
Kuɗi su ka yi wahalar haɗuwa har ta kai 'ya'yan sa su ka yi shawaran sai da ɗaya ɓangaren gidan sa wanda bai ƙarisa ba. Buba yai fir akan shi ba za a saida ma sa gida ba. Daga ƙarshe aka nemo bashi da ƙyar akan za a koma da shi a ma sa aiki. Buba ya ce ya fasa, wai an ma sa kwatancen mai magani a ƙauyen Takadunga chan zai je. Akayi-Akayi da shi ya ƙi zuwa asibiti dan haka aka barshi.
Daga ƙauyen Takadunga sai da ya ziyarci ƙauyuka biyar amma still ba maganar sauƙi. Kuɗin da aka ci bashi dan a ma sa aiki a asibiti kaf ya kashe su wajen ma su maganin gargajiya. But still ba abinda ya chanja Buba ya zama makaho.
Da ya ga ba shi da sisi sai ya haƙura ya koma zaman gida. Saboda zuwa aiki ba zai yiwu ba ya sa ya yi voluntary retirement ya cigaba da jiran kuɗin pension.
A wannan lokaci ne Buba da ya ke ji da ƙarfi da kuma kyau da kwarjinin Fulani ya koma abun tausayi. A lokacin ne ya san cewa gani rahama ne na Ubangiji. Gashi dama lokacin da yana da ido bai jawo kowa ajikin sa ba hakan ya sa yanzu da ya rasa ido ya koma bashida kowa, bashida aboki da zai kira na shi sannan bashi da ikon gane fari ko baƙi.
Indo ce ta fara sarewa da shi. Ganin ga Makanta da baƙin hali ya sa ta ce ba za ta iya zaman ba ta nemi ya sawwaƙa ma ta. Sai da aka kai ruwa rana kafin ya amince ya sawwaƙa ma ta. Da za ta tafi ta ɗau yaranta biyu ta yi gaba da su. Ta sani ko ta barsu ma wahala za su sha, Harga Allah ta san Innayi za ta iya riƙe amanar su amma kuma itama fama ta ke da na ta 'ya'yan kuma ba wani samu ta ke ba shiyasa ta zaɓi tafiya da yaran.
Harira kam ba ta tafi ba amma kuma darajar Buba kaf ya zube a idonta. Dama tuntuni ta dena ganin sa da kima amma kasancewar sa makaho ya sa ko kaɗan ba shi da wani matsayi a wajen ta. Tun ana rabon kwana tana girki da shi har ta zo ta ce ba za ta iya ciyar da shi ba, idan dai bai ba ta kuɗi ba to ba za ta taɓa zuba ma sa abinci ba. Tun Buba na faɗa har ya gaji da kan sa ya bari, sai dai ya wuni yana zaginta a gidan, wani lokaci ta biyeshi su yi ta yi wani lokaci kuma ta shareshi.
Zaman ya koma Harira ke ciyar da kanta da 'ya'yanta ita kuma Innayi na ciyar da Buba da na ta 'ya'yan. Girkin da ba ya son ci lokacin da ya ke da lafiyar sa yanzu kam ba shi da zaɓi dole shi ya ke ci. Batun a je rumfar mai shayi ko rumfar mai tsire duk bai taso ba tunda ba kuɗi sannan ba ido.
Innayi ta nemi rancen kuɗi a wajen wani Baffan ta, shi kuma tausayinta ya sa ya ba ta kyautar shanu biyu. Ta siyar da Saniya ɗaya ta sa aka siya ma ta Injin markaɗe, sauran ta zuba a jarin ƙosai, maimakon ƙosai zalla da ta ke yi a da sai ya zamana ta fara yin ƙosai da Koko. A haka rayuwar ta cigaba da tafiya, Da aka fara biyan kuɗin pension Buba ba abinda Buba ya chanja na ha'inci, ya fara ba su kuɗi amma kuɗin da ya ke ba su ba adalci aciki. Kuɗi ne kaɗan zai bayar ya ce ayi cefanen sati da shi, bayan ko cefanen kwana biyu ba zai kai ba.
A irin wannan yanayin ne watarana su na masifa kamar yadda su ka saba yiwa junan su Buba ya ɗau sandar sa ya bugawa Harira a wuya. Harira ta sa ihu da kururuwa tana cigaba da zagin Buba tareda faɗin ba dan albarkacin Yusuf da ke tsakanin su ba da ba abinda zai hana ta rama dukan nan. Buba ya harzuƙa ya cigaba da zagi ƙarshe dai sai da ya sa Harira ta tofa ma sa yawu ta fita daga ɗakin tana zage-zage. Tana shiga ɗaki ta fara harhaɗa kayanta shi kuma Buba na ɗaki yana faɗin "Harira ki bar min gida na, tunda ba ki san arziƙi ba ki je chan ki yi iskancin ki a wani gidan ba nan ba. Na rufa miki asiri na aureki shine yanzu za ki min tijara, ki je na sakeki saki uku, Allah ya isa tsakanina da ke"
Duk zage-zagen su ba wanda Innayi ta tanka wa acikin su. Markaɗen Gero da ta ke yi nan ta maida hankalinta, lokaci zuwa lokaci kuma tana waiwayan Raudha da ke wasa a ƙofar ɗaki.
A ranan kaf kayan Harira sai da ta zo ta kwashe. Abunka da dama ba tsakani da Allah ake zaman ba, Da sana'ar Masa da Harira ke yi ta riga ta sayi fili ta fara gini kuma duk ba tareda Buba ya sani ba. Shiyasa ta ke gani rabuwa da Buba alkhairine ma a gareta dan za ta samu daman ƙarisa gininta ta koma gida ba tareda damuwa da wani Buba ba. Yanzu kam ko da za ta kuma wani auren to a gidan ta za ta zauna sai dai Mijin da ta aura ya dinga zuwa...
Babu Indo babu Harira, gidan ya koma na Innayi ita ɗaya kamar farkon auren su, sai dai wannan karan akwai 'ya'ya har bakwai tsakanin su.
Wasa wasa rana ɗai ɗai ya haɗu ya zama sati ya zama wata sannan ya zama shekara, daga nan shekaru su ka dinga ja. Abubuwa sun chanja a wannan gida haka nan kuma wasu abubuwan su na nan yadda su ke.
Indo ta sake wani aure a garin Darazo, duk lokacin da ta samu zuwa garin Misau ta kan zo su gaisa da Innayi, haka nan za ka ga ta zo ma ta da abun alkhairi wani lokaci sabulu, Omo ko kuma kuɗi. Su biyu ne a wajen Mijinta, kuma ta ga chanji sosai a gidan na ta saɓanin gidan Buba. Mijinta Malam Muhammad sana'ar sai da Kifi ya ke yi kuma yana da tausayi ba kamar Buba ba, yana ƙoƙarin kula da iyalinsa gwargwadon ikon sa, kuma ba laifi masanin addini ne mai son Ibadah.
A ɓangaren Harira kuwa ba ta sake wani auren ba. Tana nan a gidan ta da ta gina. Sana'ar ta ta ma sa ta kuma haɓaka, domin yanzu burinta shi ne zuwa Makkah. Ta samu tayin aure a wajen mutane da dama amma ta riga ta ce aure ba ya gabanta yanzu, ko da za ta yi wani auren to sai dai idan ta cika burinta ne na zama Hajiya...
Innayi kam tana nan ba wani cigaba a tattare da ita a babin karan kan ta. Tana samun kuɗin amma a wajen 'ya'yanta ya ke tafiya. Ko da Buba zai yi adalci, kuɗin Pension da ya ke samu ba wani abun kirki ba ne, ga shi da ya ke ƙaramin ma'aikaci Masinja, balle kuma shi ɗin ba adali ba ne.
Halimah da ta ke tunanin samun arziƙi a gidan Alhaji Nuhu ba abinda ta samu sai tsiya, Alhaji Nuhu irin mazan nan na da za su iya kashewa Mace ko nawane a waje amma da zaran ta shigo to shikenan ita da tsumman goge ƙafa ba maraba. Watannin farkon auren su ta ga gata a wajen sa kamar ba gobe amma tunda ta samu ciki ya fara chanja ma ta. Lokacin haihuwan Raudha da Innayi ta yi kusan wata a Asibiti sau ɗaya ya bari ta je ta ga Mahaifiyarta hakanan ba abunda ya ba ta na alkhairi, haka ta je ta dawo hannu lami. Sai daga baya ne ma ta ɗauki zannuwanta biyu ta siyar a ɓoye ta aikawa Innayi kuɗin.
Haihuwa ɗaya biyu duk ta lalace ba wani jin daɗi, musamman gashi ya ƙara aure yana yayin Amarya a lokacin. Shekaran Amarya na uku ne karayar arziƙi ta sameshi, ta kai bai tsira da komai ba sai gidan sa. Taurin ran sa ya kuma ƙaruwa. Gashi ya ƙi sakin ko ɗaya daga cikin matan sa, su kan su matan sun ka sa neman saki a wajen sa duk tsiyar da ya ke mu su, abun dai kamar magani.
Sai gashi cikin shekaru goma na aure da ta ke hangowa kan ta zama wata babbar Hajiya sai ga shi ta koma da ita da uwar ta Innayi banbancin kaɗan ne. Har wani lokacin tana tunanin gara Innayi tunda ita tana sana'a tana samu, ita sana'ar ma ta kasa yi saboda tsoron Alhaji Nuhu.
Ta yi dana sani a lokacin da ya zame ma ta ƙeya. Ina ma ta ji maganar Innayi, ina ma da Innayi ta yi shawara ba da ƙawaye ba, Inama ta bi maganar Uwarta ba ta bi son zuciyar ta ba. Ba abinda ke ƙara ma ta ɗaci a rayuwar ta irin yadda ta ga lokaci guda Malam Faruƙ da ta rena a baya kasancewar sa Malamin Makarantar Firamare ne, sai ga shi Allah ya ɗaukaka shi. Zuwa yai ya ƙaro karatu da ya dawo aka bashi koyarwa a CLIS. Yanzu ya zama Lecturer yana chan da matar sa hankali kwance.
Dama duniya kenan, Allah kaɗai ke ba da arziƙi. Shi ya ke ɗaukaka wanda ya so ya kuma ƙasƙantar da wanda ya so, samu da rashi duk daga gareshi ne...
Saɓanin Halima ita Sa'adatu ta so karatu, domin bayan ta ƙare Sakandare ta nuna kwaɗayin cigaba da karatu. Da ke Jamb ɗinta bai yi kyau ba yayanta Ado ya ba da shawaran ta nemi makarantar Health Technology da ke Ningi. Hakan kuwa aka yi ta cika form ɗin ta je ta yi jarabawa ta samu. Da aka zo maganar tafiya ne Buba ya fara faɗa wai taya zai bar 'yar sa mace ta je har wani gari karatu shi lallai bai yarda 'yar sa ta je Ningi ba. A lokacin har Innayi ta nuna rauninta duk da kuwa tafi kowa kwaɗayin 'yarta mace ta yi karatu amma ganin mijinta ba ya so ya sa ta fara ba wa Sa'a haƙuri akan ta haƙura da tafiyar. Magana dai ta kawo cece- kuce har ta kai sai da Baffan Buba ƙanin mahaifinsa wanda ya ke kamar Kakan su Sa'a ya shigo zancen. Daga baya Buba ya ce ya yarda, abin ma har da abin dariya. Babu ko sisin Buba da zai yi ciwo idan Sa'a ta tafi makaranta amma haka nan ya ke ta ɗaga jijiyar wuya akan shi 'yar sa ba za ta cigaba da karatu ba...
A wannan gaɓar Innayi tana ɗan samun sauƙin wasu abubuwan saboda Iro ya buɗe shagon gyaran mota yana ɗan samu kuma ba laifi yana kawo wani abu gida. Sai kuma Baffah wanda ya ke aji biyu a ATBU kuma duk lokacin da ya ke gida yana 'yan buga-buga yana samun kuɗi. Duk cikin yaran shine zai iya kashe ko nawa ne saboda Innayi. Yana aji huɗu a sakandare lokacin wani sallan Azumi ya je yai buga-bugan sa ya siyawa Innayi Atamfa ya kawo ma ta tareda hijabi. Ranan Innayi sai da ta yi hawaye, domin ranan ne na farko da ɗaya daga cikin 'ya'yan da ta haifa ya siya ma ta kaya.
Ado da ya ke Babba ya ƙare Diploma kuma ya samu koyarwa a wata Sakandare school, duk kuɗin sa tarawa ya ke akan zai yi gini yai aure. Gefen da Mahaifinsa Buba ya ka sa ƙarisawa ne ya siya ya rusa aka fara ma sa ginin zamani na block a wajen. Da an taɓashi maganar kuɗi zai fara cewa "wai bakwa ganin gini na ke yi ne?"
Wannan hali na sa ya sa ko da wasa Innayi ba ta taɓa tambayar sa kuɗi ba tunda ta ji yanai wa ƙannen sa irin waɗannan maganganu...
Idrissa Buba Pakkari wanda daga shiga aji uku a sakandare ya maida sunan sa zuwa Idris Abubakar Pakkari, hot guy kenan, aka IDAP aka sexyfulani, aka Baban love, aka Babban yaro.
Tsayin sa, farin sa, dogon hanci da kuma lallausan baƙin gashin da ke kwance a kan sa, su suka zama abin tinƙahonsa a zamanin da mata ke tururuwa a wajen namiji mai kyau. Ɗan farin Bafulatani mai kyau da kwarjini kenan, ga ilimi ga murya mai zaƙi. Tun yana yaro halayyarsa ta burga ta fara bayyana balle kuma da ya fara girma ya ga yadda mata ke zancensa.
Ko kaɗan hidimar gidan su ba ta gaban sa, shi dai ya ci ya sha ya kuma dinga turawa mata wasiƙun soyayya yana haɗa ƙawaye faɗa. Lokacin da ya zama Headboy a makarantar Government Comprehensive Day Secondary School Misau zo ka ga girman kai da ɗagawa. Yadda ya ke yi a waje ka ɗauka ɗan gidan mai martaba Sarkin Misau ne, alhali kuma shi ɗin ɗa ne a wajen Buba Makaho da Innayi mai ƙosai ko Innayi mai Daddawa. Ba ya aikin komai sai dai a bashi ya kashe, duk kuɗin da ya ke tarawa kuwa wajen turare, ƙananun kaya da takalmi ya ke ƙarewa.
Cikin ikon Allah bayan ya ƙare secondary school ya samu admission a BUK, wanda lokacin sai da Innayi ta haɗa da sayarda Injin ɗin ta na markaɗe kafin kuɗin makarantar sa su ka haɗu.
Da ya je Jami'a idon sa ya kuma buɗewa sai son duniya da girman kai ya ƙaru. Shine kullum cikin yiwa mata hidima, assignment, notes da kuma goya su idan za a yi test ko exam. Indai mace na da kyau ko kuɗi to haka za ka ga Idris yana kaffa-kaffa da ita yana maƙale ma ta kaman chewing gum. Su ma matan dai duk sammakal domin Idris na da kyau ga shi da ilimi shiyasa da mata 'yan ajin su da wanda ba 'yan ajin su ba haka za ka ga ana ta wani shishshige ma sa...
***
Buba yana zaune a ɗakin sa yana cin tsire ya ji muryan Raudha na ƙwalawa Innayi kira.
"Baba Baba ina Innayi?" Ya jiyo muryan 'yar ta sa tana nufo ɗakin sa. Ya sani za ta iya shigowa ɗakin shiyasa yai saurin tura ledan tsiren ƙarƙashin gado. Yanzu ya fara ci dan yanka uku ya ci gashi yadda ya ji nauyin ledan ya san dayawa aciki dan yana ji Alhaji Yamai ya ce a sawa Buba tsire na ɗari biyu. Ya fita ne wajen Isa mai tsire ya na doddogarawa da sandar sa ya jiyo kamar muryan Alhaji Yamai a wajen sai ya shiga yiwa Alhajin daɗin baki har Alhajin ya ce a sawa Buba tsire, da a wajen zai ci sai ya ji wani a wajen na cewa yawwa Buba ka gyara zama mu sa ma ka albarka, hakan ya sa yai wuf ya ƙarɓi ledan ya ɓoye a rigar sa ya yiwo gida.
Normally idan ya je wajen Isa mai tsire haka zai yi ta daɗin baki har Isan ya gaji ya bashi alakoron tsire kaman yanka uku haka. Randa Buban ke da kuɗi kuwa haka zai zauna ya siya ya cinye a wajen kamar yadda ya saba tun ƙuruciyar sa tun kuma yana da lafiyar ido.
Duk namijin