Showing 6001 words to 9000 words out of 50413 words
tana wata na tara ba abinda ya tanada. Da ta ma sa magana ya ce ai yana sane dan haka ta ja bakinta ta yi shiru.
Sai da cikinta ya cika wata goma kafin ta haifi 'yan biyu maza. Ladi da Inna Maimunah ne su ka karɓi haihuwar, sai dai na farkon kuka kawai yai a duniya ya koma. Na biyun ne aka yi sunan sa wanda ya ci su na Hussaini. Idan da ta Buba ne to sai dai Faɗima ta sha kunya dan da ƙyar aka matse shi ya sayi rago bayan nan bai ba da komai ba. `yan uwanta su suka yi rawar gani a hidimar suna musamman Baffa Habu, jikan ɗan uwansa na farko kenan. Su ma a chan Ajili sun yi murna da haihuwar musamman ma da ya ke 'yan biyu ta haifa duk da ɗayan ya koma...
Wankan Kwana arba'in Faɗima ta yi a ƙauye kafin ta dawo Misau inda ta cigaba da renon ɗan ta. Duk kunyar da ake yiwa ɗan fari ita kan ta kasa yi, sosai ta ke zagewa ta yi wa ɗan ta wasa.
Hussaini na da wata bakwai ya fara rashin lafiya, zazzaɓi da gudawa, daga baya kuma wasu ƙuraje su ka feso ma sa. Tun farko Faɗima sai da ta nemi a kai Hussaini asibiti amma Buba ya ƙi, aka dinga ɗirka ma sa maganin gargajiya. Ranan da jikin Hussaini yai tsanani haka ta ɗauki mayafi ta saɓa ɗan ta a baya ta wuce clinic ɗin makaranta. Su ka dubi yaron su ka dinga faɗa akan miyasa ba a kawoshi da wuri ba sai da ciyo ya ci shi. Ta yi shiru dan ba abinda za ta ce, ba za ta taɓa faɗin gaskiya ba domin kamar ta tona asirin mijin ta ne.
Su ka ƙarɓe shi su ka bashi magani tareda faɗin dole a kai shi babban Asibiti. Ta ce sai dai idan Buba ya dawo.
A clinic ɗin Buba ya sameta inda likita ya rufeshi da faɗa akan ta ya zai bari ciwo ya ci ɗan sa haka. Dama likitan Bayarabe ne ya haɗa da cewa dama ku Fulani kun fi ba wa saniyar ku daraja fiye da 'ya'yan cikin ku. Buba yai ta ba da haƙuri, daga baya aka basu wata takarda akan gobe da safe su kai Asibiti.
Buba ya tisa matarsa gaba su ka dawo gida. Su na zuwa ya titsiyeta a ɗaki ya fara dukan ta wai a dalilin me za ta fita ba tareda izinin sa ba. Bai damu cewa tana cikin damuwar ciwon ɗan ta ba, damuwar sa shine an fita ba a tambayeshi ba. Shi mai girma miji wanda addini ya sa mace a ƙarƙashin ikon sa.
Haka ya fice daga gidan ya barta tana kuka. Tun zamanin da chan miji ya bugi matar sa ba a ɗaukar sa a komai, a lokacin na su ma ba komai ba ne balle kuma a zamanin mu na yanzu da abin ya zamo tamkar wani ado ko bajinta.
Ta ya za ka daki matar ka kuma ka kwanta lafiya? Ta ya za ka maida mace tamkar Baiwa?
Ta ya za ka ɗauki raunin Mace a matsayin hanya ta muzgunawa rayuwar ta?
Ta ya za ka daki matar ka wai dan kawai Allah ya ba ka daraja, kana gaba da ita?.
Maganar zuwa asibiti haka ta bi iska. Faɗima ta cigaba da ba wa Hussaini maganin da aka ba su a clinic. Ko kaɗan dukan da Buba ya ma ta bai dameta ba damuwarta shine ɗan ta ya samu lafiya.
Kwana huɗu da faruwar wannan abu Hussaini ya rasu. Da asubahi ta tashi za ta duba shi ta ga ɗanta kwance jiki a sake, dama daren jiya haka ya wuni da kuka saboda ciwo. Ta ma yi mamaki da bai farka cikin dare ba kamar yadda ya saba, ashe yaro kam ya koma.
Buba da ke kwance ta fara bubbugawa tana faɗin "Malam ka tashi ka ga yaro ba ya motsi, dan Allah ka zo ka duba shi" tana maganar tana hawaye. Buba dai da ya ga ta dameshi ya miƙe ya zo ya dubi gawar ɗan na sa. Kallo ɗaya ya ma sa ya tabbatar yaro kam ya tafi sai dai Allah ya sa mai ceto ne.
Ya kalli Faɗima da ke zazzare ido tana jiran ya ce wani abu ya ce " sai dai mu yi haƙuri Hussaini ya riga mu gidan gaskiya"
Faɗima ta tsugunna ƙasa tana girgiza kai domin ta ka sa gaskata maganar Mijin na ta mai kama da almara, shikenan ta rasa Hassan ta rasa Hussaini ? Kuka mai tsanani ya kufce ma ta...
***
Faɗima ta shiga wani yanayi da ake kira da depression a turanci. Bayan rasuwan ɗan ta komai ya fita ma ta akai, ta zabge ta lalace. Haihuwar da ta ke ta kuka a kan sa shine bayan ta samu kuma Allah ya ƙarɓe kayan shi. Ba ta ji mutuwar Hassan kamar yadda ta ji mutuwar Hussaini ba, Hassan ko nonon ta bai taɓa ba amma Hussaini fa?
Uwa ita tafi damuwa da mutuwar ɗa, ita ta san zafin haihuwa. Wata goma ta raini cikin su kafin haihuwa, ta zo ta raini Hussaini na wata bakwai da sati uku.
Buba dai shima ya ji ba daɗi dan ko ba komai ya sa rai da ɗan na sa amma shi abin bai taɓa shi ba kamar yadda ya taɓa Faɗima, dan shi cikin sati biyu ya koma dai-dai kamar yadda ya ke da. Ita kuwa Faɗima idan Buba ya tafi wajen aiki haka za ta wuni tana kuka tana rungume kayan Hussaini, saboda haka ne ma Ladi ta ke tura su Ma'u lle su je da ƙanin su Kabiru ɗan shekara biyu da rabi. A hakan dai duk sammakal.
Ko sati uku ba a cika ba Buba ya nemi matar sa ta bashi hakkin sa. Dan ya gaji da shiru-shiru da ta ke tuntuni, ai mutuwar Hussaini ba zai sa rayuwa ta tsaya ba. Ba abinda ta iya haka ta gyara ma sa ya samu nitsuwar sa...
Damuwa kam a hankali Ladi na ma ta nasiha har ta sake ranta ta rungumi ƙaddara. Cikin ikon Allah kuwa wata uku da mutuwar Hussaini ta samu ciki. Duk farin ciki da ɗoki da ta yi a cikin su Hussaini ba ta yi a wannan ba, dan gani ta ke wannan ma haka zai zo ya koma ba tareda ya girma ba.
Ciki ya shiga wata tara ta haifi ɗan ta namiji wanda ya ci sunan Adamu (Ado) Kyautar ta bai tsaya haka ba shekaran Adamu ɗaya da rabi ta haifi Ibrahim (Iro). Daga nan haihuwa ta buɗe ma ta, ta sake samun Halimah da Muhammadu da su ke kira da Baffa...
Tun bayan haihuwan Halima ta fara sana'ar ƙosai kuma Alhamdulillah tana samun ciniki sosai, haihuwa da ta fara yawa ya sa Buba da kan sa ya ma ta maganar sana'a dan yanzu hidima ta fara ma sa yawa, ga shi har yanzu ba wai ya dena halin sa ba ne na cin abinci a waje. ya gane cewa idan Faɗima na samun wani abu zai tare ma sa wata ƙofar...
Ado, Iro da Halima duk sun fara makaranta sai Baffah ne kaɗai ke gida wanda bai gama cika shekara uku ba.
Ƙarfe huɗu tana yi za ta tashi ta hau wanke wake tana gamawa za ta fitar da komai da za ta yi amfani da shi tareda ɗaura ruwan wankan yara. Tana idar da sallar asuba za ta ɗaura ɗumamen tuwo yayinda Ado zai ɗau markaɗen wake ya kai gidan Yarabawa, gidan wani Malami kusa da su wanda matar sa ke da injin markaɗe. Yana dawo da markaɗe za ta hau tuya ƙosai, dama ta riga ta yiwa Iro da Halima wanka shima Ado sai ya je ya ɗebi ruwan wanka yai na sa wankan. Kafin ka ce me za ka ji ana sallama ana tambayar ƙosan Sule ɗaya, Sule biyu har ma su ƙosan naira ɗaya. Kan ka ce kobo ƙosai ya ƙare.
Tana tattare kayan da ta yi amfani da su wajen tuya ƙosai 'yar ta Halima ta kirata
"Innayi ...Innayi"
Ba tareda ta juyo ba ta ce "Halime dama ba ki tafi makarantar ba?"
"Innayi na tsaya na yi fitsari ne, wai ki ga Baffah zai bini makaranta"
Sai alokacin Innayi ta juyo ta kalli Halima da ƙaramin ɗan ta Baffah tana murmushi. Kamar ba yau ne ta ke ganin rayuwar ta baya da ma'ana ba saboda ɗan ta Hussaini da ya rasu gashi yanzu yara ɗai-ɗai har huɗu kuma ba wai ta cire rai da sake haihuwan ba ne.
Allah ke nan, mai jinƙan Bayin sa...
*RIBAR UWA*
*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*
Chapter 04
(Free book ne)
*A man needs many wives*
Sana'a sa'a domin kuwa Innayi ta yi sa'a. A gaba ɗaya quarters ɗin makarantan na Teacher's college Misau idan ka na neman ƙosai mai daɗi, mai garɗi to ƙosan Innayi ne. Kuɗin da Innayi ke samu a wata ta hanyar sana'arta ya ninka albashin Buba sau huɗu, ganin matar sa na samu sosai ya sa Buba ya sake ma ta gaba ɗaya ragamar gidan. Ba dama ta tambayi abu sai ya ce ai tanada kuɗi ta yi amfani da shi, haka nan duk wani hidima da ya ke yi da ya rage da kusan kaso saba'in. Idan ya je ya ciwo bashin kuɗi to Innayi ne za ta biya, ba ya kunyar tambayarta kuɗi kamar wanda shi ya ke ma ta wahalar. Duk kuɗin da ya ƙarɓa da sunan aro kuwa babu ranan biyan sa, Kunya da girmamawa ga miji ya sa Innayi ba ta iya tambayarsa kuɗin. Tun tana jira akan zai biya har ta yarda cewa duk kuɗin da Buba ya karɓa to ya zama sadaka.
Mutane da dama da su ke ganin cinikin da Innayi ke yi su na mamakin yadda ko kaɗan babu chanji a tattare da ita. Ba ta saka kayan yayi ko kuma ta sayi abun yayi, koyaushe kuɗin ta ya ƙare akan hidimar gidan ta da 'ya'yan ta. A lokacin sallah haka za ta ƙoƙarta ta siyawa yaranta kayan yayi amma idan ka dubata sai ka ga ita ba ta saka irin kaya haka. Kullum aiki ta ke yi babu hutu, mutanen da su ka santa sosai su kan tausaya ma ta domin Innayi mace ce ta ƙwarai sai dai ba ta yi sa'an miji ba. Ɗabi'un Buba ko mutumin da bai taɓa shiga aji ba ba zai yi ba amma shi da ya ke da certificate ɗin primary school idan ka auna ɗabi'unsa abin sai ya baka mamaki. He's selfish and greedy...
Innayi na da tsohon ciki mahaifin Buba ya rasu, kafin sati biyu aka raba gado. Buba ne ɗa na biyu kuma su biyu ne maza sannan ɗaya ƙanin sa ya jima da rasuwa, sai mata guda huɗu. Da aka raba gado Buba ya samu gona da shanaye. Wannan gado ya sa Buba ya fara gini a cikin gari, domin wannan ƙaramin boys quarters da su ke ciki ya mu su kaɗan. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarisa ginin saboda dama gini ne da aka fara ba a ƙarisa ba, sai ya siya ya ƙarisa.
Yarinya mace Innayi ta haifa wanda ta ci sunan Sa'adatu. Da ke akwai ɗan kuɗi a wajen Buba wannan karan sai ya yi abun kirki, ya sayi kaya sosai lokacin suna. Rabon da ya siyawa Innayi kayan suna haka tun lokacin haihuwar Ado, Atamfofi ma su kyau guda huɗu ya siya ma ta ta yi shigar suna. Ya so ma ace ayi sunan yarinyar a sabon gida amma haka bai yiwu ba dan bai ƙarisa ba.
Innayi ta yi farin ciki sosai ganin irin hidimar da yai ma ta har ta ke tunanin Buba ya chanja ne...
Kafin rasuwar mahaifin Buba Harira ta fito daga gidan mijin ta, ta fara zawarci a karo na biyu. Akwai matan da kwata-kwata ba su ganin chanja aure a bakin komai, inda za ka ga sai mace ta yi aure ta fito ya fi sau uku. A lokacin da ta ke zawarci Harira ta ji labarin dukiyar da Buba ya samu lokacin da Uban sa ya rasu. Duk da yanzu ba da ba ne hakan bai hana ta ƙoƙarin neman Buba ba. Domin cikin manemanta duk tsofaffi ne 'yan shekaru hamsin zuwa sittin.
Wani lokaci maza su kan yi wani abu dan su nuna isa da mulki akan mace. Hakan ce ta faru a wajen Buba domin yana jin labarin auren Harira ya mutu ya danno kai cikin manemanta. So ya ke ya nuna ma ta iyakarta kasancewa ta ƙi shi a baya. Ba a wani ɗau lokaci ba Harira ta amince da Buba inda shi kuma ya kawo kuɗi ma su yawa a matsayin sadaki aka ɗaura mu su aure. Batun tarewa ya ce sai nan da sati uku, zuwa lokacin ya kammala komai na gidan sa.
Hakan kuwa aka yi, domin a cikin sati ukun ya kammala komai, yayinda Buba ya kai Harira ta je ta ga gida ta kuma zaɓi ɗakin da ta ke so.
Dayawa maza su kan tafka wannan kuskure ko na ce cin fiska. Namiji ne za ka ga yana tareda mace shekara da shekaru, alokacin da ba shi da shi ta zauna da shi ta taimaka ma sa. Amma daga zaran ya samu abun hannunsa sai ya fara maganar ƙara aure, ba anan ne matsalar ba, matsalar shine amarya na zuwa za ka ga ya juyawa Uwargida baya, ya dinga fifita amarya akan uwargida, ya dinga ganin ai Uwargida is outdated.
Innayi na zaune tana ba wa Sa'a nono Buba ya shigo da sallama muryarsa ɗauke da annashuwa. Innayi ta ma sa sannu da zuwa cike da ladabi tana tambayarsa ko ta kawo ma sa ruwa ya ce ta barshi. Ledar da ya shigo da shi ya miƙa ma ta ya ce "gashi nan sai ki ɗinka dan ranan Jumma'a za mu tare a sabon gida"
Innayi ta amshi ledar tana godiya tareda addu'ar Allah ya sa su tare a sabon gida lafiya.
Bayan ta gama shayar da 'yar ta ta fara ƙoƙarin shimfiɗata dan yarinyar ta riga ta yi bacci. Abunka da jariri wanda bai san komai ba sai abinci da bacci. Kaman daga sama ta ji Buba ya ce "Faɗima na yi aure fa" da fillanci ya faɗa duk da kuwa Buba bai cika yin yaren na su na Fulatanci ba, kaso tamanin cikin maganganun sa Hausa ne dan ko a yaran su ma Hausa ya ke mu su. Innayi ce ta dage da yi mu su Fulatanci har ta kai su na ji.
Murmushi ta yi mai ciwo ta ce "Allah ya sanya alkhairi"
Duk wani abu da ke taso ma ta tana ƙoƙarin danneshi. Ba wai ta sa a ranta ita kaɗai za ta rayu da Buba ba ko kuma tana kishin auren da yai, ko ɗaya ba wannan ba ne. Ɗacin da ta ke ji a ranta shi ne yadda har yanzu Buba bai ɗauketa a bakin komai ba, idan da adalci ai tun kafin ayi auren ya kamata ya sanar da ita, amma kwatsam sai dai kawai ya ce ma ta ya yi aure.
Irin rashin adalci da mazaje dayawa ke tafkawa matan su Allah ne kawai zai saka mu su. Daga ƙarshe duk wani zagi da tsinuwa akan mace ake saukewa.
Buba bai tsaya a nan ba ya ƙara da cewa "ita Amarya gobe Laraba za ta tare a gidan"
Wannan karan ma murmushi Innayi ta yi ta ce Allah ya sa ta tare lafiya. Buba ya amsa da Amin yana murmushi.
Wani lokaci idan mace ta fiye sanyi dayawa namiji ya kan ɗau wannan sanyi na ta a matsayin wata ƙofa ce da ya samu domin ya muzguna ma ta. Yayinda mace ta ke da zafi sai ka ga namiji yana kaffa-kaffa da ita. Wannan ya kan sa dayawa mata su zama ba sa iya yin wannan sanyi-sanyi ɗin ko kuma idan ma sun fara sai ka ga daga baya sun dai na. Mutane kaman Innayi kam ba sa iya chanja halin su ko da kuwa za su ƙare rayuwar su da namijin da ba ya ɗaukan su da daraja...
Ranan Jumma'a kuwa Innayi da 'ya'yan ta su ka baro quarters su ka dawo cikin gari a gidan Buba da ya gina a Unguwar Kukadi. Innayi da ta zo ta yi tsammanin ta na zuwa za ta ga Amarya budurwa sai ta ga bazawara wacce ta ke gani idan Hariran ba ta fi Buba ba to za su zo dai-dai a shekaru. Sai dai miye na ta a ciki, Buba da ya gani yana so shi ya ɗaukota.
Gidan na su ba laifi wadatacce ne domin da ka shigo akwai zaure inda aka yi ɗaki ɗaya sai idan ka shiga cikin gidan kuma akwai ɗakuna biyu a jere sai wasu ɗakuna biyun su ma a jere su na kallon juna. Chan wani fili kuma an fara gina ɗakuna huɗu irin na farkon amma ba a ƙarisa ba. Akwai banɗaki guda biyu akwai kuma ɗakin dafa abinci. Akwai rijiya da kuma ƙatuwar bishiyar dabino.
Ɗakin da Buba ke son maidawa na sa saboda ya fi girma shi Harira ta zaɓa dan haka dole ya koma ɗaya ɗakin. Ko kaɗan girman ɗakin Harira bai tsolewa Innayi ido ba ita kan tunda akwai wadataccen wuri Alhamdulillahi.
Rayuwa kam ta juyawa Innayi domin a da tana nan ita ɗaya da 'ya'yanta yanzu kuma sun koma su biyu ga Agola guda uku da Harira ta zo da su.
Wani lokaci wasu mazan na da sakaci za ka ga 'ya'yan su ba wai yara ba ne sosai amma da zaran sun rabu da mace sai su bari ta tafi da su Agolanci wani gida, ba wai Agolanci ba kyau ba ne A'a amma wani lokaci duk munin gidan Uba ya fi ma akan ka je ka yi zaman Agola a wani gida...
Yadda Buba bai daraja Inna yi ba haka Harira ma ba ta daraja ta, ta kowani kafa da ta samu ƙoƙarin muzgunawa Innayi ta ke yi. Ganin Innayin ba ta tanka ma ta ya sa maimakon ta dinga ragewa sai abinma ya dinga gaba-gaba.
A haka sai ga labarin Baffa Habu ba lafiya aka aiko wa Innayi akan ta je ƙauye domin Baffa Habu na son ganinta.
Innayi ta faɗawa Buba inda ya amince ta je ta yi