Showing 3001 words to 6000 words out of 50413 words

Chapter 2 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1777

yai wa Muhammadu rasuwa. Maciji ne ya sareshi a gona daga haka kuma ya fara jinya har ya rasu.
Riƙon Faɗimatu ya dawo hannun ƙanin mahaifinta Baffa Habu. Tunda mahaifinta ya rasu maganar makaranta ya watse tunda Goggo ba ta so duk da kuwa a lokacin an samu ƙarin mata uku da aka sa a makaranta...




***


Yau ma garin maganin da Goggo ta ƙarɓo aka jiƙa ma ta ta sha, maganin ba ƙaramin ɗaci ne da shi ba amma haka Faɗima ta shanye shi tas. Shekaru biyu kenan Goggo na nema ma ta magani. Idan watan azumin da za a shiga ya kai ƙarshe aka yi sallah da kwana huɗu to shekara goma shahuɗu za ta cika a duniya kuma har yanzu ba ta fara jini ba. Wannan ne ya hana a mata auren shabiyu sha uku da ake yiwa matan ƙauyen na su. Akwai Sama'ila da ya ke zuwa zance wajenta amma kuma mahaifiyar sa ta ƙi Faɗima saboda wannan lalura na ta. Inna Maimunah da ke aure a cikin Misau ta sha faɗawa Goggo akan ba lalura ba ce Faɗiman ke da shi, halitta ce kawai, wasu matan ba su fara jini da wuri.
Kunyar da fulani ke wa 'ya'yan su na fari ya sa duk lokacin da Maimunan ke mata bayani ta ke tashi ta bar wajen cikin fushi tareda yin biris da maganganun 'yar na ta.
Ta chanja ma su maganin gargajiya sun yi goma amma shiru ba labarin jini...


Cikin azumi jini ya zo ma ta. Ana gab da shan ruwa a ranan azumi na shabiyar. Bayan ta gama toya ƙosai ta tashi kenan Hebbini matar Baffa Habu ta hango jini a bayan zaninta. Da sauri ta zo wajenta ta kamata su ka shiga ɗaki inda ta tabbatar da jinin al'ada ne, cike da murna ta haɗa ma ta ƙunzugu ta ce ta je bayan gida ta saka. Faɗimatu na fita Hebbini ta wuce ɗakin Goggo ta sanar da ita. Goggo ta doka salati tana faɗin dole gobe ta yi sadaka saboda samun lafiyar Faɗimatu...






Bayan sallah aka tsaida magana tsakanin Malam Habu Jo'o da kuma Malam Yusufu Pakkari.
Ba a wani ɗau lokaci ba aka ɗaura auren Faɗimatu Muhammadu Jo'o da kuma Buba Yusufu Pakkari.


Buba ya yi primary daga nan bai cigaba ba. Ya samu aikin Masinja a makarantar Teachers College da ke cikin garin Misau. A lokacin da aka haɗa shi aure da Faɗimatu shekaransa ashirin a duniya ita kuma shahuɗu.


Faɗimatu ba ta taɓa ganin Buba ba, shi ɗan asalin ƙauyen Ajili ne, a nan ya taso, yai rayuwar sa kafin ya koma Misau da zama tunda ya samu aiki shekaru uku da su ka wuce.
Anyi shagalin biki dai-dai gwargwado kafin aka ɗauki amarya Faɗimatu zuwa gidan mijinta a cikin garin Misau.


Cikin quaters na TC ɗin za su zauna. Boys quarter aka ba wa Buba ya zauna da iyalin sa kasancewa shi ɗin ƙaramin ma'aikaci ne.


A shekarun ta shahuɗu ba wani ilimi da ta sani gameda aure da ya wuce ta yiwa Buba biyayya sannan ta zama uwar 'ya'yan sa. Hebbini ce ta kowa ma ta wankan tsarki irin na mutanen da ko na ce wanda ke cike da bidi'o'i. Kuma ta ce shi za ta yi a duk lokacin da ta tare da maigidan ta. A ɓangaren ilimi na ƙur'ani kuwa Faɗimah na ɗaya daga cikin 'yan matan da ake kwatance da su a ƙauyen domin duk ajin su ta fi kowa zarra tunda ta haddace suratul Nasi zuwa Suratul Dhuha kuma a rubutu ta kai suratul Yasin. Ko da shekaru uku da ta yi tana zuwa primary school a Ajili sai da ta yi suna saboda ƙwazon ta na ɗaukan darasi da wuri da kuma rashin mantuwa. Sai dai kash! Aure ya katse ma ta duk wani buri nata na cigaba da karatu balle har babban burin mahaifinta ya tabbata...






Ba ta iya ɗaga ido ta kalli Buba ba daren ranan da aka kawota saboda kunya ta Fulani, ga kuma tsoro da fargaba da ya cika ta saboda rabuwa da gida da ta yi. Wannan ne karo na farko da ta yi nisa da ƙauyen su, iya kacinta Tunfure da Ajili. Ko irin zuwa hidimar biki ƙauyukan da ke gefen su ba ta yi saboda asalinta ba mai son hayaniya ba ce.


Buba bai ja dogon lokaci ba ya tare da ita kuma dayake shima ɗin ba wani ilimin addinin gareshi ba ko sallar nafila ta godiya ba a yi ba balle batun addu'ar saduwa da iyali. Ya dai kawo ma ta tsire da bredi da shayi, wanda ta tsakuri kaɗan ta ci shi kuma ya ƙarisa sauran.


Washegari a wahalce ta tashi sai dai ita ɗin dama tun asalinta mai juriya ce. Ta haɗa ice ta ɗaura ruwan zafi ta yi wanka ta gwada gasa jikinta kamar yadda Hebbini ta gaya ma ta. Shi kam Buba tun asubahi ya fita bayan ya tashi Faɗima daga baccin wahala da ta yi. Bai dawo ba sai ƙarfe takwas na safe inda ya taho da kunu mai zafi da ƙosai. Tun a wajen ya sha nashi ya ƙoshi dan haka Faɗima ce kawai ta sha wanda ya kawo.
Da rana ta fara girki saboda Buba ya ce zai zo ya ci abinci shi da abokanan sa....




Wata ɗaya kenan da auren Faɗima kuma har lokacin ba ta wani saba ba. Ba abinda ke shiga tsakanin ta da Buba sai dai ta girka ma sa abinci ya ci sannan idan dare ya yi ta bashi hakkin sa, kayan sa yai datti ta wanke. Su na zaune ne matsayin mata da miji amma babu shaƙuwa tsakanin su. Idan magana ta haɗa su to Buba ke buƙatar wani abu, asali dama Faɗima ba mai yawan surutu ba ne ya zo ya haɗu da cewa Buba kuma bai damu da ita ba balle duk lokacin da ya ke gidan ya dinga ma ta hira.


Yaran maƙotan su Ma'ulle da Uwani su ke ɗebe wa Faɗima kewa. Yaran sosai su ka shiga ranta, indai sun dawo daga makaranta to gidan ta za su garzayo su dinga ba ta labarin abin da su ka kalla a talabijin ɗin gidan su Zainab, kasancewa mahaifin Zainab ɗin Malami ne ya sa ya zamo ɗaya daga cikin tsirarun mutanen da ke da talabijin a quarters ɗin...


Kafin auren Buba da Faɗima, Buba na neman wata bazawara mai suna Harira, tana sai da Masa, shekaru uku da aure ta fito. Bakarkariya ce iyayenta 'yan asalin garin Jalam. Buba ya nace a kanta sosai, sai dai Harira ta rena ma samun sa duk da kuwa ba ƙaramin kuɗi ya ke kashe ma ta ba idan ya zo zance, sannan tana ma sa kallon saurayi kuma yaro, dan shekara ɗaya kawai ya bata a lokacin. Inna Furera mahaifiyar Buba sam ta ƙi zancen sa na auren bazawara kuma Bakarkariya. Shi dai ya nace akan yana son Harira. Sai da ya gama kashewa Harira kuɗi kusan shekara ɗaya da rabi kawai watarana ya je ƙauye ya yi kwana biyu, dawowar da zai yi ya ji labarin Harira ta yi aure har ta tare a gidan mijinta, abin ya ma sa ɗaci sosai. Rashin Harira ya sa ya amince da zaɓin mahaifiyar sa wato Faɗima...


Buba ya saba da cin daɗi tun kafin aure shiyasa ko bayan aure kwaɗayin sugar da maiƙo bai barshi ba. Da safe zai je ya sayi shayi da buredi ya karya da rana idan yana wajen aiki zai sayi shinkafa da miya da nama da dare ma sai ya sha shayi kafin ya wuce gida. Yana zuwa kuwa zai tsatstsakuri tuwon da Fatima ta kawo ma sa ya ce ya ƙoshi. Idan ka ga Buba ya ci abincin safe rana da na dare a gida to bashida kuɗi ne kuma ya nemi bashi ya rasa.
Faɗima ba ta taɓa damuwa ba ko kuma ta tambayeshi akan ƙin cin abinci da ya ke yi, domin yana daga cikin ladabin da aka ɗaurata ba a yiwa miji ƙwaƙwƙwafi ko shishshigi. Idan ya kawo cefane haka za ta dinga lallaɓawa domin duk lokacin da ya ƙare ta buɗi baki ta ce "Malam ba bu cefane" to ranan haka zai ta masifa ya dinga zaginta akan ba ta tattali. Da ta gane haka sai ta yi shiru har sai ya lura ba komai kafin ya siyo ya kawo. Mahaifin su Ma'ulle gadi ya ke yi a bakin gate amma da ke shi ba kamar Buba ba ne wanda kan sa kawai ya sani ba ya barin iyalinsa cikin ƙunci. Komai a wadace ya ke kawowa duk da kuwa shi ɗin yana da 'ya'ya har uku. Amma su da su ke su biyu sai abu ya gagaresu.


A hankali ranaku su ka fara ja, kwanaki su ka zama sati zuwa watanni. Babu wani hali na Buba da bai bayyana ma ta ba, sai dai kamar kowacce Mace da akewa huɗuba da aure sai haƙuri haka itama ta riƙe wannan huɗuba. Domin kuwa tun bayan satin farko na aure to har wa yau zaman haƙuri ta ke da Buba. Abu ɗaya da ya tsaya ma ta a rai shine rashin samun ciki. Lokacin da ƙanwar Buba ta kawo mu su ziyara ta ke tambayarta ya aka yi shiru har yanzu.
"Wata takwas fa Faɗima" ta faɗa tana kallon Faɗiman.
Ta girmi Rabi ƙanwar Buba da kusan shekara amma da ke ta rigata aure kuma har ta haihu shiyasa Rabin ta ke ma ta kallon kamar ta girmeta.


Mi za ta ce ma ta?
Ba ita ke ba da haihuwa ba. Abinda ya kamata ta faɗa kenan amma ta yi shiru tana cigaba da sauraron maganganun Rabin...







*RIBAR UWA*




*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*






Chapter 03
(Free book ne)






*Motherhood*




A duk lokacin da aka samu ma'aurata su ka kwana biyu da yin aure, to kowa tsammanin sa shine ya ga an samu albarkar aure. Idan aka ji shiru Mace za a dinga nunawa ana tunanin gazawar da ga gareta ne. A kan manta cewa haihuwa na Allah ne, kuma shi Ubangiji ya kan ba da kyautar haihuwane a lokacin da ya so. Ya gaya ma na cewa wasu zai ba su Maza zalla wasu kuma Mata zalla, wasu ya haɗa musu Maza da Mata wasu kuma haka za su rayu su mutu ba tareda sun samu kyautar haihuwa ba...


Tun lokacin da Rabi ta tafi damuwar Faɗima ta ƙaru, babu sallah da za ta yi da ba za ta yi addu'ar Allah ya bata haihuwa ba. A lokacin da ma yanzu gani ake haihuwa shine Ribar aure, idan ka yi aure ba ka haihu ba gani ake ba abinda ka rabauta da shi.
A shekarunta shabiyar ta san rashin haihuwa babbar matsalace ga 'ya mace. Ta na fata kada ta zama Gaji da ake labari a ƙauyen su, wanda aka ce kusan shekaru Arba'in da aure amma ba ta taɓa haihuwa ba har ta rasu, kishiyoyinta uku kuwa duka sun hayayyyafa har ma da jikoki. Duk lokacin da mace ba ta haihu ba a ƙauyen su, da labarin Gaji ake tsoratar da ita. A dinga cewa "idan ba ki haihu ba haka za kiyi rayuwar kaɗaici kamar Gaji ki mutu ba tareda kin bar mai mi ki sadaka da addu'a ba".


Sai da ta shekara ɗaya da wata uku da aure kafin ta je ƙauye ziyara. Ta na kewar gida amma ba yadda za ta yi, idan mace ta yi aure sai da dalili ta ke zuwa gidan su abinda ta taso da shi kenan. Goggo ce ba lafiya kuma jikin ta yayi tsanani sosai shiyasa Buba ya ce ta je ta yi kwana biyu. Gidan su Buba ta fara zuwa dan ta gaishe su daga nan kuma ta wuce na su ƙauyen. Rashin sakin fiska da ma habaici da ta ci karo da shi a gidan ya sa ta sha jinin jikinta, har ta bar gidan hankalinta a tashe ya ke.
A chan ƙauyen su Tunfure kuwa ta samu tarba mai kyau. Goggo ta yi marmarin ganin jikarta sosai wanda rabonta da ita tun da aka kai ta ɗakin miji.


Ta na son faɗawa Goggo akan ta nema ma ta maganin haihuwa amma yanayin da ta samu Goggon ya sa ta yi shiru.


Tsab Goggo ta karanci damuwar da ke fiskar jikar ta. Yadda itama a baya ta damu lokacin da Aminatu ta wuce shekara ba ta haihu ba, ta san dole ne 'yan uwan Buba su damu.
Zurfin cikin Aminatu Faɗiman ta ɗauko, ba za ta taɓa gaya ma ta damuwar ta ba.


"Ki yi haƙuri Faɗimatun Baffa. Ina ga jinin Aminatu ki ka ɗauka shiya sa ki ka ji shiru har yanzu. Allah ya sa ina da rabon ganin 'ya'yan ki Faɗima"


Faɗima ta amsa da Amin.


Dawowar Faɗima Misau da kwana biyar Goggo ta rasu, ta so ta je ta'aziya amma Buba ya hana wai ai ba ta jima da dawowa ba, haka ta haƙura akan sai wani lokaci idan ta je ƙauye sai ta yi mu su ta'aziyar. Mutuwar Goggo ya shigeta sosai saboda shaƙuwar da su ka yi musamman bayan rasuwar Baffan ta, duk soyayyar Goggo ga Muhammadu to ta juyeshi zuwa kan 'yar sa Faɗima...


Wasa-wasa shekaru biyu su ka shuɗe babu labarin ciki. Buba dai bai damuba hidimar gaban sa kawai ya ke yi, tunda zai ci ya sha sannan ya tara da iyalin sa ai ba wata matsala. Damuwar rashin haihuwa da kaɗaici ya sa Faɗima ta fige ta lalace, dama ba ƙiba gareta ba sai ta ƙara bushewa. A irin wannan zaman ne Ladi maƙociyar ta ta bata shawaran akan ta dinga sana'a saboda ta rage kaɗaici. Da farko ta yi watsi da shawarar daga baya kuma ta amince, ko dan yadda Buba ke yawan zaginta da rashin tattali.
Namiji ke ciyar da mace ya tufatar da ita ya kuma ɗauke duk wata ɗawainiya na ta, sai dai miji kaman Buba wannan haƙƙoƙi da ya rataya a wuyan sa kaman wani nauyi ne da ke hanashi sakewa. Kuɗin da zai fitar dan iyalinsa ta ci ta sha ba ƙaramin takura ya ke yi ba.


Za ta yi sana'a ne ba dan ta samu kuɗi ko ta nuna gazawar Buba ba sai dan ta taimaka ma sa. Goggo ta yi sana'ar daddawa kuma ba abinda Faɗiman ba ta sani ba gameda harkan. Hebbini kuma ta yi sana'ar ƙosai wanda shekaru uku kafin aurenta ita ke tuyawa Hebbini ƙosan.
Cikin Daddawa da ƙosai da ta iya ta zaɓi ƙosai domin shi zai fi ma ta sauƙi kuma Ladi ta ce za ta fi samun kasuwa.
Da ta gama yanke shawara sannan ta tuntuɓi Buba akan ya ba ta izini ta fara sana'ar ƙosai. Ranan kuwa sai da ta ƙwammaci ba ta yi zance mai kaman wannan ba, ta inda Buba ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Ya haɗa da cewa ta san yadda za ta yi ta haihu tun kafin maganganun da ake faɗa akan ta ya tabbata.
Kenan shi ma ya damu da rashin haihuwar na ta?
Ya za ta yi da ranta ne?, duk magungunan da ake kawo ma ta daga ƙauye babu wanda ba ta sha amma shiru. Ta yi yunƙurin zuwa asibiti Buba ne bai bata dama ba ya ce ba shi da kuɗi...


Daga wannan rana ba ta kuma ɗaga zancen sana'a ba, ta fawwalawa Allah lamarinta, idan da rabon za ta haihu to, idan kuma itama haka za ta ƙare rayuwar ta kamar Gaji shikenan, haka Allah ya tsara ma ta.


Shekaru uku su ka shige rus ba tareda ta yi ɓatan wata ba. Daga ɓangaren Buba bai ƙara ma ta maganar ba tun ranan da ta ma sa zancen sana'a. Sai dai duk lokacin da dalili ya kawo 'yan uwan sa gidan daga ƙauye to haka za su yi ta hantarar ta. Shekarun ta shabakwai amma gani su ke irin ta kai talatin ɗin nan ba tareda haihuwa ba.


Allah ma ji roƙon bawan sa kenan. Acikin shekara na huɗu da auren su sai ga ciki ya ɓullo. Ita kan ta Faɗima ba ta ankara da cewa cikin ba ne lokacin da ta haura sati ba ta ga jinin ta na wata ba. Haka ta tattara ta tafi ƙauye karo na biyu tun aurenta.


Auren 'yar Baffa Habu za ayi mai su na Mairo. Cike da tsoro ta tambayi Buba gameda zuwa bikin abin mamaki sai ya amince ma ta. Ta ji daɗi sosai dan rashin zuwa ƙauye ya dameta, tun tana sa ran za ta je ta yi mu su ta'aziyar Goggo har ta haƙura da zancen, gashi Goggo ta kai shekaru biyu da rasuwa.


A wajen hidimar bikin ne ta dinga kela amai lokacin da ake kan aikin biki. Umma Asabe ta ja ta gefe tana ma ta tambayoyi.


"Anya ba ciki gareki ba Faɗima?"


Faɗima ta sunne kanta cikin cinyoyinta tana fata Allah ya sa maganar Umma Asaben gaskiya ce...
Haka dai aka yi hidimar biki aka gama wanda Faɗima ta yi ne cikin laulayi. Hatta Hebbini sai da ta tabbatar ma ta da cewa tana da juna biyu amma kunnen ta sun ƙi gaskata zancen duk da kuwa zuciyar ta na son amincewa da maganar ta.
Ta koma Misau ta cigaba da hidiman ta, duk da kuwa laulayi ya sa ta a gaba. Sai da Ladi ta tabbatar ma ta da ciki gareta sannan ta amince zuwa lokacin alamu dayawa sun bayyana dan cikin ya shiga wata na uku.
Saboda kunya ba ta iya gayawa Buba ba, sai da cikin ya kai wata na biyar kafin ya gane. Shi kam ina ma ya ke tsayawa ya kalleta balle ya dinga lura da chanjawar da ta ke yi. Da dare kuma ana kashe fitila zai ɗaga zani ya raya dare babu maganar wasa balle ya lura da cikinta da ya taso...


A hankali cikin Faɗima ya shiga wata tara haihuwa ko yau ko gobe. Cikin gashi tulele da shi, ko sau ɗaya ba ta je asibiti ba duk da alamu sun nuna tana buƙatar hakan amma Buba ba ruwan sa. Matan ƙauye sai su haihu sau goma shabiyu a gida ba tareda sun je Asibiti ba kuma lafiya-lafiya su ke haihuwar su. Abun da ya sa a ran sa kenan.


Buba bai wani shiryawa sunan ba dan har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login