Showing 33001 words to 36000 words out of 50413 words

Chapter 12 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1784

muka sa ma ta rashin lafiyar ne? ko ta gaya ma na ba ta da lafiya"


"Rashin lafiya kuma? Sanda na leƙata da safe fa lafiyarta ƙalau"


"Munafurci mana, munafurci irin na tsofi"


Yai ajiyar zuciya sannan ya zauna yana ƙoƙarin kiran numbar Sa'an. Ko kaɗan ba ta saurareshi ba sai ma cigaba da zaginsa da ta dinga yi. Da ya tambayi wani asibiti su ke sai ta kashe wayar.


Ranan dai Innayi ba ta kwana gidan su ba, Faiza kan ko ajikinta amma shi Idris ya ji ba daɗi dan kalaman Sa'a sun ɗan tsorata shi...




Washegari da safe kusan ƙarfe goma shaɗaya Halima ta iso Bauchi, yadda Sa'a ke maganar halin da ta samu Innayi itama jikinta yai sanyi. Ita kam rabon da ta yi waya da Innayi abin ya fi wata ɗaya tun an kusa fara Azumi. Shirye-shiryen bikin 'yarta da za ayi duk ya mantar da ita komai.


Bayan ta zo ne Sa'a ta wuce gida dan ta je ta ɗauko kayan Innayi da ke gidan ta yi magana da Likita za su koma asibitin Azare saboda Innayi ta samu kulawa sosai tunda Sa'a na aiki a chan.


Kasancewa Asabat ne ya sa dukkan su suna gida.
Faiza na kwance kan Idris tana zuba ma sa shagwaɓa su ka ji sallamar Sa'a.
Faiza ta ja dogon tsaki tana faɗin " ba za dai a bar mutum ya huta ba"


Idris ne ya tashi ya je ya buɗe ma ta ƙofa. Yana gaisheta ta daka ma sa tsawa " riƙe gaisuwar ka! Dan wallahi zan wankeka da mari "


Ya shiru ya bi bayanta da kallo. Ɗakin Innayi ta je ta tattaro kayan ta, ba wasu kayan kirki ba ne iya wanda ta tafi da su ne tun da.


Da ta fito ta kalli Idris ta ce "kai kuma za mu yi magana idan Innayi ta samu lafiya" tana faɗin haka ta fice daga gidan. Yana tambayarta wani Asibiti su ke ohoho ko kulashi ba ta yi ba...








***


Sati biyu Innayi ta yi a gidan Sa'a kuma Alhamdulillah jikinta da sauƙi sosai. Innayi dai tunda su ka bar Bauchi ta ƙuduri aniyar za ta koma ƙauye, za ta zauna har Raudha ta dawo.


A sati na uku ta yiwa Sa'a maganar tafiya. Ba wai dan ba ta samun kulawa a gidan ba sai dan tana jin kunyan zama a gidan Uwar mijin Sa'a na gidan kuma su biyu ne. Hakanan kuma tana son gwada zama a ƙauyen su. Rabon ta da ƙauye bayan rasuwan Baffah ta je sau biyu daga nan ba ta sake zuwa ba.


"Innayi ba kya so na samu lada ne? Har yanzu fa ba ki gama warwarewa ba"


"Ba abinda zan ce sai dai Allah ya saka miki da alkhairi. Sa'a da kunya na cigaba da zama da ku, ga surukar ki ga kishiyar ki"


"A'a Innayi, wallahi Hajiya ba ruwanta da zuwanki, tana ma jin daɗin zaman ki da mu"




Innayi ta kama hannun Sa'adatu ta ce "ko da na lokaci kaɗan ne ina son zuwa ƙauye. Ki barni na tafi idan da rabo zan sake dawowa" ta ja dogon numfashi kafin ta ce "Dan Allah ki min alkawarin ba za ki sanar da Auta abinda ya faru ba. Hankalinta zai tashi a inda ta ke kuma bazan ji daɗin haka ba"


Sa'a ta zaro ido tana girgiza kai tana faɗin"A'a Innayi, A'a"


"Ina so ta kasance cikin farin ciki,ta yi karatu hankali kwance"




"Innayi duk wata sai na tura wa Idrissa dubu biyu da ɗari biyar, wata uku da suka wuce na mai da shi dubu uku, ban san ko sauran na tura ma sa kuɗi ba amma na san Raudha na tura ma sa kuɗi itama dan mun taɓa zancen da ita. Wai duk dan kar nauyi ya ma sa yawa shiyasa na ke tura ma sa kuɗi amma ɗan batalikin nan da shi da matarsa su ka maida ke kamar wata Akuya. Ai ko Akuya ka ajiye a gida za ka rinƙa kula da ita balle mutum, balle Uwar da ta haifeka. Dole Raudha ta ji komai dan ita ya fi cin amana. Yarinya na fama da karatu amma a hakan ta ke aiki duk dan ta samu kuɗin da za ta kula da ke"




"Sa'a na yafe ma sa. Fatana Allah ya shirya min shi, Dan Allah ki bari Auta ta yi karatunta cikin kwanciyar hankali"




Sa'a dai ba haka ta so ba amma ya za ta yi dole ta haƙura ta amince da maganar Innayi. Bayan kwana uku da maganar au aka shirya tafiyan Innayi.
Ko da su ka yi magana da Raudha itama ba ta goyi bayan tafiyan Innayi ƙauye ta so gane akwai abinda ya faru amma da Sa'an da Innayi duk su ka nuna ma ta komai lafiya. Sai da ta sa Innayi ta ma ta alkawarin ba za ta jima a ƙauye ba za ta dawo Azare sannan hankalinta ya kwanta...


Siyayya na musamman Sa'a ta yiwa Innayi tun daga kayan abinci zuwa situru. Kaya masu kyau kala shida ta ɗinka ma ta da sabbin hijabi da takalmi. Wata biyu ta ce za ta yi a chan za ta dawo, zai yi dai-dai lokacin bikin 'yar Halimah da za ayi nan da wata biyun.


Mijin Sa'a ne ya kawo su Misau a motar shi bayan sun ɗau Halimah sai su ka wuce Ajili. Sai da Innayi ta biya gidan su Buba ta gaishe da 'yan uwan sa da su ka rage kafin su ka wuce ƙauyen Tunfure a mashin tunda babu hanyar mota. Sa'a Halima da Innayi ne su ka tafi aka bar Dr Mansoor yana jiran su a Ajili...






***




Rayuwar ƙauye akwai daɗi, yanayi na damuna da ake ciki ya ƙara sawa ƙauyen na su ni'ima. Ba hayaniya ba damuwa, duk da shekaru sun ja da ƙuruciyarta a ƙauyen bai hanata tuno abubuwa da dama na ƙauyen ba. Har wayau babu wani chanji na azo a gani a ƙauyen, akwai ƙaramin primary school da aka gina mu su wanda yanzu yara mata da maza su ke zuwa. Su na da dispensary da su ke zuwa a dubasu idan ba lafiya, sai idan babbar jinya ce sai su wuce Babban Asibitin Misau, sai dai har yanzu ba su da wutar NEPA.




Gidan su na da ɗin ne dai su ke sai dai an kuma buɗa shi saboda 'ya'ya da jikoki da su ka yi yawa. Cikin ƙannen mahaifin Innayi akwai guda ɗaya da ya rage mu su da su ke kira da Baffa Tsoho. Tun da Ado ya aiko akan Innayi za ta zo ya sa aka gyara ma ta ɗakin Baffanta. Wasu jikokin sa ne ke kwana a ɗakin da amma ya ce su bar ɗakin mai ɗaki za ta zo.
Da su Sa'a su ka zo su ka ga ƙyamusashshiyar katifa ce acikin ɗakin shine da za su tafi su ka siyi Katifa a Misau su ka aika ma ta da shi...


Alhamdulillah ba ta da wani matsala yanzu, babu cima mai daɗi kamar na gidan Sa'a amma kuma za ta ci ta ƙoshi a wadace, ranan da ta zo ma an karramata sosai dan Kaji biyu Baffa Tsoho ya sa aka yanka.


Bayan ta ɗan kwana biyu ne ta ce a bata wasu yara su dinga kwana tare. Kulu da Zahra'u aka ba ta wanda su ke da shekara takwas da kuma shekara goma. Yanzu kam ta rage kaɗaici domin rayuwar ƙauye akwai daɗi, yayinda aka je aka dawo zakaga an zauna ana hira musamman da dare.


Wani lokaci haka za su zauna da Baffa Tsoho su yi ta hira ko matar sa Yawuro. Baffa Tsoho ya ɗan kwana biyu dan zai kai shekaru saba'in da takwas zuwa tamanin haka amma yana nan da ƙarfin sa dan har gona yana zuwa. Cikin wata ɗaya da sati biyu Innayi ta murmure, jikinta ya fara kyau, ta sake jiki cikin 'yan uwanta suna rayuwar ƙauye mai daɗi.


Ance idan mutuwa tana tunkaranka kana iya jin alamunta, wani lokaci har ka yi wasu abubuwa wanda zai nuna kana bankwana ne da duniyar ƙila sai ka mutu mutane su ankara akan dama abin nan da ka ke yi sallama ce ka ke yi da duniya.


Cikin 'yan kwanakin nan Innayi tana yawan yin mafarkin mahaifinta da kuma ɗan ta Baffah akwai ranan da ta yi mahaifiyarta wanda ba ta taɓa ganin kamanninta ba sai a mafarki.


Tana kwance akan tabarma a ƙofar ɗaki ta fara kallon yanayin gidan. Abu da Sumaye suna surfen gero su na yi suna waƙa. Chan gefe ga Zaliha na dakan borkono tana yi tana tari. Ta juya gefenta taga Yawuru matar Baffa Tsoho tana tauna goro tanayi tana koran wata Akuya da ke ƙoƙarin cin wani bushashshen tuwo da yara su ka bari a cikin tukunya, ita kan har yau ba ta iya cin goro ba lokacin cikin Idrissa ne ma ya sa ta cin goro. Tunowa da ta yi da Idrissa ya sa hawaye ya ciko a idanun ta, ta yi saurin kawar da tunanin ta hanyar faɗin Allah ya shirya mini ku gaba ɗaya...


Zahra'u ta fito daga ɗakin Innayi ɗauke da littafinta na makaranta ta zauna kusa da ita ta buɗe littafin tana rubutu. Chan yarinyar ta fara karatu cikin gurɓatacciyar turanci ta ke maimaita abinda aka koya mu su.


"Wat is yor name? My name is Zahara'u. How ol are you? Am am 8 yrs ol"


Wannan karatu ya sa Innayi ta tuno da karatun ta na firamare da ta yi kafin aure, ƙila da Baffanta ya yi tsawon rai da ta yi karatu mai zurfi sai dai Allah ne ya tsara komai kuma Alhamdulillahi dan ta sani da yardar sa 'yar ta kuma jikar Muhammadu za ta zama likita.


Lokacin da Zahra'u ta sake maimaita "wat is yor name?" Sai Innayi ta furta a fili "My name is Faɗima Muhammadu Jo'o"


Zahra'u ta saka dariya tana faɗin " Lah! Innayi ashe kina jin turanci"


Innayi ta yi murmushi ta ce "Ina ji kaɗan-kaɗan"




Yawuro ta ce " ai lokacin Innayi ce mace ta farko da ta fara yin makarantar Boko a ƙauyen nan, Allah ya jiƙan rai, Baffa shi zai ɗauke ki ya kai ki ayi ta zagin shi amma ko kaɗan bai damu ba"


Innayi tayi murmushin jin daɗi tana kuma tuno abun kamar yau ya faru. Yadda Goggo za ta yi ta faɗa idan Baffanta zai kai ta Makaranta...


Kiran sallar La'asar da aka yi ya sa Innayi ta miƙe ta je ta zaga kafin ta zo ta yi alwala.
Yawuro na cewa " Jumma'a babban rana kenan, yaushe yaushe har la'asar ta yi"


"Innayi ta ce ai duniyar gudu ta ke yi, ga mai nisan kwana zai ga ta ma sa nisa amma mai ƙarar kwana nan da nan za ta cimma sa"


Yawuro ta ce "Astangafurullahi, bari mu tashi mu yi sallah"


Innayi ta tuno itama a da irin abinda ta ke faɗa kenan kafin Raudha ta gyara ma ta.


"Innayi ba fa Astangafurullahi ake cewa ba Astagfurullahi ne" ta jiyo muryan Raudha a gefen ta, ta yi saurin juyawa amma wayam babu kowa ta yi murmushin farin ciki, ta juyo dan ta gyarawa Yawuro amma Yawuro ta yi nisa dan wasu raguna da su ka shigo gidan suna shirin sa baki a hatsin da aka surfa ta ke kora.


"Astagfirullahi" ta furta a fili...




Bayan ta yi sallar la'asar ta jima tana yiwa 'ya'yanta addu'a, addu'ar Allah ya shirya su ya kuma haɗe kan su sannan addu'ar Allah ya bawa Auta miji na gari da 'ya'ya ma su tausayinta. Ta kwanta tana jan carbi tana tuno rayuwar ta, idan ta riƙe lissafin Goggo daidai to yau shekarunta sittin da kwana arba'in da huɗu a duniya. Mi za ta ce ban da Alhamdulillah, a lokacin da ake kukan ba ta fara jini ba Allah ya sa ta fara, a lokacin da ta yi aure ake ganin ba ta haihu ba Allah ya ba ta haihuwa, a lokacin da 'yan biyunta duka su ka rasu Allah ya ba ta wasu 'ya'yan.
Akwai ranakun ƙunci da baƙin ciki, Akwai ranakun da ta kwana kuka, Akwai ranakun da ta yi tunanin ya rayuwarta za ta kasance idan Allah bai ba ta haihuwa ba kamar Gaji da ta mutu ba haihuwa.


Ta yi murmushi lokacin da ta tuno ɗan ta Baffah.


*"Innayi Insha Allahu zan kai ki Makkah, duk wahalhalun da ki ka mana za ki samu hutu idan na fara aiki"*


"Allah ya haskaka ƙabarin ka Muhammadu na" ta faɗa hawaye na fita ta gefen idon ta.


Ta tuno Raudha da ke fesa ma ta turare ranan sallah bayan ta sa lace ɗin da ta ɗinka ma ta.


*"Wato ke fa Innayi da Allah yayiki a gidan masu kuɗi da ba ƙaramin Hajia mai kyau za ayi ba, gashi kin tsufa amma har yanzu ke ɗin Beauty ce"*


Innayi ta shafa fiskarta da ya riga ya fara yanƙwanewa ta ɗago hannunta ta kalli yadda su ka koma, anyi zamanin da ta yi ƙosai, daddawa, markaɗe, ɗaukan itace idan anzo siya, ga matsar man gyaɗa da ta yi na lokaci kaɗan kafin daga baya Baffah ya hanata. Ta kai duka hannunta biyu kan cikinta ta shafa har zuwa maranta, haihuwa akwai daɗi akwai kuma wahala.


Yau idan babu ita a duniya akwai 'ya'yanta, wannan kaɗai ya isa zama *RIBAR UWA*.
Akwai ɗan ta Adamu akwai ɗan ta Ibrahim akwai ɗan ta Idrissa akwai Halimatu akwai Sa'adatu sannan akwai Auta Rhaudatu.
"Allah Sarki Rhaudatu na, gashi ke ce ko ragon suna ba a miki ba. Allah ya albarkace ki da ke da zuri'ar ki Amin" Ta yi saurin goge hawayen da ke fiskanta ta sauke ajiyar zuciya tareda rufe idon ta ko za ta samu ta yi bacci aikuwa bacci mai daɗi ne ya tafi da ita bacci na har abada...




Lokacin da Kulu ta kawo mu su tuwon dare har lokacin Innayi na bacci an idar da sallar magariba kenan.


"Innayi ki tashi mu ci tuwo kar yai sanyi" ta faɗa tana taɓa Innayin ganin ba ta kula ta ba ne ya sa ta fita dan ta ɗebo mu su ruwan sha sai dai a ƙofar ɗakin ta haɗu da Zahra'u da kofi a hannu. Sai dukkansu su ka koma ɗakin.


Kulu ta sake taɓa Innayi amma shiru.


"Innayi mu kan za mu fara ci" ta faɗa tana komawa wajen 'yar uwarta da tuni ta fara kai loman tuwo.


"Zahra'u Innayi ta yi sallar Magariba kuwa? Na ga tun da ta shiga ciki da la'asar ba ta fito ba" muryan mahaifiyar su Sumaye ya katse mu su cin tuwon.


Kulu ta ce " bacci ta ke yi"


"Amma shine za ku fara ci ba za ku jirata ba"


Da ƙatoton lomar tuwo a bakinta ta ce " ta ƙi tashi ne"


Sumaye ta shigo ɗakin dan ta tashi Innayi ta sani tunda ta zo ba ta fashin sallah akan lokaci. Ba dan ita ta nemi a dinga haɗa mata abinci da su Kulu ba ma da ba abinda zai sa ta haɗa mu su.


"Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'oun, wayyo Allah! Innayi Innayi Innayi" ta shiga bubbuga gawar Innayi.


Jin kukanta ne ya sa matan da ke kusa su ka yo ɗakin da gudu. Kafin ka ce me gaba ɗaya gidan ya kaure da koke-koke. Aka je aka sanar da Baffa Tsoho a masallaci. Sai da yai ƙwalla da ya ji wannan labari ashe Innayi ta zo su gana ne na ƙarshe shiyasa ta dawo ƙauye da zama.
A daren aka ma ta sutura sannan aka aika Misau akan aje a sanar da 'ya'yanta dan da safe za a kaita.


Kusan ƙarfe tara na dare aka kawo saƙon mutuwar Innayi wajen Ado. Yana kallon Ball a falo aka yi sallama shine ya fita.
Ganin Harisu da Habu wanda 'ya'yan Baffa Tsoho ne ya sa ya yi mamakin ganin su da dare haka.


Sai da su ka gaisa sannan Habu wanda shine Babba ya ce " Hamma Ado Allah yayiwa Innayi rasuwa"


Turus ya tsaya lokacin da ya ji abinda Habu ya faɗa. Ya girmi Habu dan da Baffah na da rai to sa'anni su ke da shi. Ya sani Habu ba zai ma sa wasa ba.


Cikin i'iina ya ce "mi ka ce?"


"Hamma Sai haƙuri amma Innayi rai yayi halinsa. Baffa Tsoho ya ce gobe ƙarfe takwas za ayi jana'izar ta"


Ado ya dafe gini hawaye na zubo ma sa ganin sa na ƙarshe da Innayi lokacin da ta ke Azare ne wajen Sa'a, har ga Allah wannan Lahdin ya sa niyyar zai je Tunfure ya dubota ashe ba za ta kai Lahdi ba...


Sai da su ka yi ta bashi baki kafin su ka bar wajen bayan sun tabbatar ya dawo hayyacin sa.
Haka ya shiga gida ransa a jagule, sai da ya zauna ma tukunna hawaye su ka fara zubowa da dalili ya kusan 30mins kafin ya samu ƙarfin saka kaya ya fita dan ya je ya sanar da Iro dan ba maganar waya ba ce...




Washe gari aka je aka taho da gawar Innayi bayan anyi Jana'izar ta a ƙofar gidan Mahaifinta, a tushenta, dama aka ce gida-gida ne. In the end ita ɗin 'ya ce a wajen Muhammadu Jo'o, da wannan aka fara sanin ta, ba da matar Buba ko kuma uwar su Ado ba.
Daga Tunfure aka wuce da ita maƙabartar Misau inda aka sa ta a gidan ta na gaskiya. Yadda Idrissa ke kuka a wajen ka ce ya fi kowa son Innayi...






***




Fiskar Innayi ta ke gani, tana ma ta murmushi, irin murmushin da ta ke yi a duk lokacin da ta ke cikin farin ciki, irin murmushin da ta ke yi idan Raudha na ba ta labarin makarantar su, irin murmushin da ta keyi idan suna zaune su uku a ɗaki su na cin tsire ko balangun da Baffah ya kawo mu su. Ta kai hannu za ta shafa fiskar lokaci guda kuma fiskar Innayin ya ɓace ma ta da gani, dama she's just hallucinating.


*"Innayi ki tsaya dan Allah, Innayi na kar ki tafi please, Innayi Innayi"* ta yi luu za ta faɗi ƙasa yai saurin tarota ta faɗa jikin sa amma tuni ta sume...










Mutuwar Innayi ya taɓani ni da na ke rubutawa, infact with tears in my eyes na ke rubutun. character ɗin Innayi kacokam ɗin ta na ɗauko ne daga combination na different mothers da na witnessing irin ƙuncin da su ka shiga sakamakon 'ya'yan su.


Da ido na naga 'yar da ke dakawa Uwar ta tsawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login