Showing 42001 words to 45000 words out of 50413 words
yi sallah, idan na dawo zan kira ki sai ki yiwa Yayan na ki magana mu ƙariso"
Ta gyaɗa ma sa kai tana ƙunshe kukan ta.
"Please ban da kuka" nan ma gyaɗa ma sa kai ta yi.
Da Bismillah ta buɗe ƙofa ta fito tana ƙoƙarin gyara gyalenta tareda maimaita Hasbunallahu wa ni'imal wakil a zuciyarta.
"Ehohoho! Wallahi Anty Raudha ce" wani matashi cikin samarin ya faɗa yana tahowa da gudu. Idon matasan chui a kan ƙofar motar lokacin da su ka ga alamun ana buɗewa. Jin Salihu ya ambaci Raudha ya sa su ma su ka sa ihu wasu su ka bi bayan sa.
Salihu kaman wani ƙaramin yaro haka ya rungumi Raudha yana murna. Salihu ɗan Yayan ta Ado ne kuma zai kai irin 14-15yrs haka.
"Antyn mu sannu da zuwa, sannu mutan America" haka su ke ta faɗa, su ka tisa ta a gaba kamar za su ɗauketa sama, haka su ka rakota har ƙofar gidan na su. Da da ne sashen su za ta fara shiga ta ga Innayinta sai dai yanzu ko ta shiga ba ta san mi za ta tarar ba, ƙila gidan ma ya gama nurƙushewa.
Ta daure ta bi Salihu su ka shiga ƙofar Yaya Ado.
Tun kafin ta ƙariso Salihu ya ɗaga murya yana shelar isowarta sai ga Matan gidan su na rige-rigen fitowa.
Yadda ka san sun shekara goma ba su ganta ba haka su ka rungumeta su na washe baki.
Daurewa kawai ta ke yi kar ta yi kuka kamar yadda Prof ya ce.
Sai da ta zauna a falo ne Jamilah ke cewa Salihu ya je masallaci ko majalisin su Abban sa ya kira shi.
Da ke ta riga ta sanar da zuwanta sun shirya ma ta abin tarba na karramawa. Kan kace me an cika gabanta da maltina, 5alive, ruwa mai sanyi da soyayyar naman kaza.
"Zan yi sallah tukunna" ta furta a hankali...
Ɗakin Jamilah ta shiga ta gabatar da sallar Azahar da La'asar. Tana cikin addu'a Jamilah ta shigo ta ce " Yaya ya shigo, idan kin gama sai ki fito"
Ta gyaɗa ma ta kai...
Lokacin da ta fito yana zaune yana amsa waya, kallon sa ta ke yi tana ganin fiskar Innayi a fiskar sa. Da shi da Idris da ita, su ukun nan ne su ka ɗauko kamannin Innayi, duk da su maza ne amma kana ganin su ka kalli Innayi ka san ko shakka babu ita ce uwar su, dan kamannin yai yawa.
Yadda ta san shi tun da haka nan ya ke, sai ma gani da ta yi ya ɗan ma ta duhu.
"Auta" ya kira a hankali. Ji ta yi kamar Innayi ce ta kirata, maimakon ta bashi amsa sai ta fashe da kuka. Da sauri ya taso ya riƙeta yana ba ta haƙuri " Dan Allah ki dai na kuka, yanzu daga zuwa sai kuka. Innayi fa ta yi rabo saura na mu, wallahi Innayi ta tsira"
Yana magana ne a raunane dan shima gani yai mutuwar ta dawo ma sa sabuwa...
Bayan ya samu ta yi shiru ne ya ce ina baƙon da su ka zo tare. Ta ce ma sa ya je masallaci.
"Yayan ki Iro ma na hanya, Idrissa ma ya ce gobe zai zo"
Ta jinjina kai. Ba a fi minti biyu ba sai ga kiran Prof, ta amsa ta ce ma sa za ta turo da yaro ya ƙariso da shi.
Ta ƙwallawa Salihu kira ashe ya fita, ana kiran Ridwan ne sai ga Prof ya kuma kira inda ya ce ma ta gasu nan zuwa wani yaro a majalisa ya na rako su. Ta ce shikenan...
Babban tabarma aka fita da shi aka shimfiɗa, Ado ya fita ya tare su. Bayan sun gaisa ne Prof da Driver su ka ma sa ta'aziya. Ba a jima ba Iro ya iso da tsohuwar machine ɗin sa, shima ya zauna aka gaggaisa. Daga nan aka fito mu su da abinci dukkan su huɗu su ka ci, ana ci ana hira...
Kusan awa ɗaya da zuwan Raudha kafin Halima ta iso, itama dai da ta zo sai da aka koka. Ƙarfe shida Prof ya kira Raudha akan ta fito za su tafi.
Wajen da su ka parker mota ta je dan ya ce a mota ya ke jiranta. Tana shiga ta hau yi ma sa godiya dan ɗazu su na tare da Halimah yara su ka shigo da kaya niƙi-niƙi wai baƙon Raudha ya kawo.
Yadda idon ta ya ƙanƙance yai ja ya jaddada ma sa ba ƙaramin kuka ta yi ba.
"Baby kin saɓa alƙawari, jibi yadda idon ki yai saboda kuka"
"Da gaske hawaye kawai nayi ba kuka ba" ta tareshi tun kafin ya fara ma ta faɗa.
Sai da ya murmusa kafin ya ce " Raudha zan wuce Zaria, idan Allah ya kaimu ranan talata zan zo saboda Laraba zan wuce Abuja and from there zan koma kin san ku ne da hutu, mu malamai koyaushe muna bakin aiki"
"Allah ya kai ku lafiya, ya tsare mu ku hanya"
Prof ya amsa da Amin. Shiru ya biyo baya na wasu seconds kafin ya ce "Raudha idan kin amince min zan turo magabatana ranan Lahdi saboda a tsaida magana kafin na tafi kin san ba samun lokaci na ke ina shigowa ƙasar akai-akai ba. Idan son samu ne a ɗaura auren kawai"
Ta ƙwalalo ido waje su na haɗa ido sai ya kashe ma ta ido. Ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin rufe fiskarta.
"Dan Allah a taimakawa ɗan tsoho, ko zai samu kuzarin komawa gida lafiya"
Shiru ba ta ce komai ba.
"Raudha kin amince?"
Ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofa amma a rufe ta ke.
"Yau de ko 'yar Fulani za ta nitse sai ta ba ni amsata, idan ba haka ba ta kwana a cikin mota"
Ganin da gaske ya ke ya sa ta ce " zan yiwa Yaya magana idan ya amince zan gaya ma ka"
"Na gode Raudha, Insha Allahu ba za ki yi dana sanin amincewa da ni ba"
Ta kuma buɗe ƙofan still a rufe.
"Saurin mi ki ke yi ne Gimbiya ta. Ko ɗan I love you fa ba ki ce min ba za ki gudu"
"Abban Yusrah ba fa mu kaɗai ba ne"
Dariya yai kafin ya ce "zan kira ki idan mun isa"
Tare su ka fito ya raka ta har ƙofar gida kafin ya juya su ka kama hanya da Driver...
Bayan sallar Isha Halimah ta tafi tareda alƙawarin za ta zo gobe tunda gobe za ayi meeting...
Kusan ƙarfe shabiyu na dare ta gota kaɗan Prof ya kirata ya sanar da ita sun isa Zaria, dama shi ta ke jira dan haka bayan sun gama wayar ta yi bacci.
***
Washegari ƙarfe shaɗaya aka sa meeting ɗin da yaran Innayi za su yi.
A cikin gidan sun dai aka shirya yin meeting ɗin. Cikin gidan da ya ajiye tarihi. Ɗakin zaure akwai samari biyu a ciki sauran ɗakunan ciki kuma ba kowa sai dabbobi da aka ajiye.
Ƙarfe goma da kwata Sa'adatu ta dira a gidan, tsohon ciki gareta haihuwa ko yau ko gobe. Lokacin mutuwar Innayi cikin da ke jikinta ya sa ta dinga daurewa kar ta sa damuwa a ranta ya taɓa lafiyar cikinta wanda an tabbatar 'yan biyu ne.
"Auta haka ki ka zama kamar wata baturiya!"
Raudha ta yi dariyan yaƙe dan tun jiya Sa'adatu ta ce idan har ta san za ta ma ta kuka to ba za ta zo ba. Maganar Sa'an yai kama da irin maganar Innayi, tabbas da Innayi na nan itama ɗin sai ta faɗi hakan ko makamancin haka.
Ƙarfe shaɗaya da minti arba'in tukunna Idrissa ya iso daga nan aka shiga cikin gida dan a gabatar da meeting ɗin. Tabarma aka shimfiɗa guda biyu, ɗaya mazan su ka zauna ɗayan kuma matan su ka zauna.
Raudha na shigowa gidan jikinta ya fara rawa, Sa'a ta riƙeta ta ce "Kul Raudha, ki kwantar da hankalinki. Idan akwai abinda Marigayiya ba ta so to bai wuce tashin hankalin ki ba. Ki daure ki yi haƙuri ki composing kan ki"
Ta gyaɗa kai tana goge hawayen da sun riga sun zubo...
Bayan an zauna ne Ado ya buɗe taro da addu'a. Sa'a tana ganin Idrissa ta fara aika ma sa harara.
Ado ya fara yiwa ƙannen sa Ya haƙurin rashin UWA da su ka yi sannan yai jawabin abinda ya sa ya kira wannan taro.
"Da farko barin fara da batun Raudha. Ke ce ƙarama cikin mu, kuma kusan shekaru biyu kenan ba kya tare da mu. Bayan tafiyar ki tun ma kafin rasuwar Innayi anyi ta samuna akan maganar na bar ƙanwata marar aure ta tafi karatu har wata nisan duniya, har ga Allah ba dan Innayi ba da ban amince kin tafi har America karatu ba, duk da kuwa scholarship ki ka samu. Yanzu ma dai a matsayina na Babba zan sanar da ke hukuncin da na yanke wanda ba dan son zuciya na yanke shi ba sai dan kare martabar ki. Ki daure ki fito da miji kafin azumin bana, aure shine rufin asirin mace. Idan ki ka yi aure kin ga za ki dinga zuwa akai-akai ko kuma shi mijin ya dinga zuwa miki har ki Ƙare karatun"
"Yaya ba sai ka ja wani dogon turanci ba, Raudha ta samu miji. Infact ya ce idan an bashi dama zai turo magabatansa ranan Lahdi"
Raudha ta sunkuyar da kai tana jin kunyan yayun na ta. Tun da Prof ya ma ta magana ta sanar da Sa'a, itace ma ta bata shawaran ta yi istikhara akai. To jiya bayan sun rabu da Prof ta kirata ta gaya ma ta abinda ya ce Sa'a ta ce za ta yiwa Ado magana sai ga shi shima ya Ɗauko zancen auren Raudhan.
"Waye shi?" Iro ya tambaya yana kallon Sa'a
"Wanda ya kawota jiya. Malamin su"
Nan su ka fara washe baki dan tun jiya Prof ya burgesu. Ga shi da kamala da kwarjini, zai girmi Ado da shekara ɗaya ko biyu amma a ido za ka ɗauka Ado ya girmeshi saboda yadda hutu ya ratsa shi ga whether ɗin Massachusetts da ya Ƙarɓeshi.
Ado ya ce "Masha Allah. Yanzu sai magana ta gaba, maganar gadon Innayi"
Yai shiru yana nazarin fiskokin su.
"Tun bayan rasuwanta an tattara abinda ta bari an ware waje guda, duka abinda ta bari gasu nan a rubuce a wajena, za a kaiwa Malami ya raba"
Takaici ya cika Raudha. Miye Innayi ta bari a duniya. Ko wata uku ba ta cika ba amma maganar gadonta ake yi.
"Kafin aje ga maganar rabon gado, ni ba na son komai na yafe amma ban yafe cin amanar Idrissa ba, ƙwandala ba zan yafe ma sa ba sai ya biya idan ya so a tattara kuɗin ayi wa Innayi sadaka da shi amma sai kuɗin nan sun fito daga wajen shi" tana magana kaman ta je ta bangaje Idrissan.
"Sa'adatu kin san ni ne dai Babba ko, ki bari abi maganan a hankali"
Idrissa ya fara zuru-zuru da ido. Tun da ya samu labarin rasuwan Innayi har yau bashida kwanciyar hankali. Yayi dana sanin biyema Faiza da yai su ka ci kuɗin Innayi.
"Akwai wanda ya yafe gado bayan Sa'adatu?"
Idrissa ya ce " na yafe"
"Munafuki, ai ko ka ci sai ya tokare ma ka wuya. Mugu Azzalumi"
"Sa'a dan Allah ki yi haƙuri" Halima ta faɗa tana kama hannun Sa'an.
Raudha dai ba ta fahimci maganar Sa'an ba amma ta ce " nima na yafe amma ina son zoben azurfan Innayi idan kun amince a bar min"
Zobe ne na zallar azurfa wanda tun da su ka tashi da shi su ka ganta. Ta taɓa gayawa Raudha cewa zoben na Baffanta ne saboda yawa da ya ma ta ma a babbar yatsa ta ke sa shi.
"Ba sai kin roƙa ba zobe na ki ne"
Sa'a ta fito da zobe a cikin jakarta ta ce " gashi nan halak malak ɗin ki, ranan da mu ka kai Innayi ƙauye ta cire ta bani ta ce na ajiye miki"
Raudha ta karɓi zoben tana jujjuyashi tana tuno abubuwa da dama...
Bayan Ado ya sake jawo hankalin kowa ne tukunna ya fara magana da Idrissa inda ya nemi bahasin kuɗi da ake tura ma sa wanda Sa'a ta je ta ga shaida ƙarara ba a kula da Innayi balle ya ce yayi amfani da kuɗin wajen kula da ita.
Ado dai duk wata yana tura dubu biyun amma Iro na wata uku ya tura, itama Halima sau ɗaya ta tura ma sa dubu ɗaya ba ta kuma turawa ba.
Kan Raudha ya ɗaure jin maganar da ake yi.
"Adda ban gane ba" ta faɗa tana kallon Sa'a. Sa'a ta fara ma ta bayanin komai dalla-dalla har zuwa yadda ta samu Innayi da yadda Innayin ta yi jinya a wajen ta.
Wani dariyar renin hankali Raudha ta yi. Tana chan tana haɗa karatu da aiki, tana chan tana hana kanta bacci, wani lokaci baccin awa huɗu ko uku kawai ta ke yi da dare duk dan ta samu a ƙarshen wata ta tura wa Innayi wani abu ashe Innayi ba ta ci gumin ta ba. Duk wahalar da ta yi a banza ta yi shi, a Idris da matarsa ta yiwa.
Kyawawan maruka guda biyu da Raudhan ta saukewa Idris ne ya fargar da su, dan su na kan alhinin abinda su ka ji Sa'a ta faɗa, sai yanzu jikin su ya kuma sanyi gameda mutuwar mahaifiyar ta su.
Ado ya dakawa Raudha tsawa akan ta maida hankalinta ko mi Idrissa yai shi Yayan ta ne, Yayan da ya ba ta kusan shekara takwas.
Jikin Raudha ya fara rawa, tana son magana amma ta kasa sai hawaye. A rayuwa mi Innayi ta yiwa Idris da zai ma ta haka. Laifin ta ne ita ɗin bagidajiya ce wacce ba ta yi karatun zamani ba, laifinta ne da ta kasance 'yar ƙauye, ƙauyen ma ƙauye futuk. Laifinta ne da ya kasance ɗa gareta bayan shi ɗin ɗan zamani ne, ɗan ƙasaita mai ji da kan sa.
Tun yana yaro ya ke da son nuna shi ɗin wani ne ya ke rena gidan su da kuma iyayen sa. Lokacin da mahaifinsu Buba ya makance ƙyashi ya ke ji a ran sa ace Baban sa makaho ne.
Saboda son gayu da Jiji da kai Idrissa Buba Pakkari da aka sa ma sa a makaranta lokacin yana ƙarami ya gyara saboda ya waye, yana son sunan gayu, sunan swagga, daga Idrissa ya koma Idris Abubakar Pakkari. Ya gyara sunan ne ba dan dama haka sunan ya kamata ya zama ba sai dan yana ƙyashin a kira surname ɗin sa da Buba maimakon asalin sunan Abubakar, sannan Idrissa ya yi local dayawa Idrees shi ne sunan zamani.
Ta dafe ƙirjinta tana kuka, kuka sosai. Halimah ce ta ƙariso gabanta ta fara lallashinta dan Sa'a kam mita kawai ta ke yi tana nuna dole Idris ya fito da kuɗin nan.
Da ƙyar Raudha ta dena kuka ta ce " abu ɗaya na ke so na sani Idrissa" ta cire Yayan da ta ke kiran sa da.
Ya ɗago jajen idanuwan sa da su ka ciko da hawaye yana kallon ta.
"Mi ka tsinana da kuɗi na?"
Kunya, danasani da kuma nadama ya shigeshi lokaci guda. Faiza ce ta bashi gurguwan shawara shi kuma ya hau kai. A niyyar sa idan komai yayi settling zai maida wa Innayi kuɗin.
Muryar sa a dashe ya ce " dama na fara gini amma na tsaya saboda ba kuɗi so shine na cigaba da ginin saboda Faiza ta matsa na gama mu koma sabon gida ta gaji da gidan haya"
Raudha ta yi murmushin baƙin ciki ta ce " yadda Innayi ba ta ci gumina ba haka kai ma Insha Allahu gumina zai zame ma ka haram, ga ka ga gida a ƙare gini lafiya"
Daga haka ta fice a gidan, su Ado na kiran ta haka ta mu su biris ta ƙi dawowa. Sa'a ta ce a barta...
Raudha na shiga ɗakin Jamilah ta fashe da kuka, ba abin da ta ke hangowa irin Innayi kwance tana murƙususun yunwa a gidan ɗan da ta haifa. Yanzu ba kukan rasuwan Innayi ta ke yi ba sai kukan wahalan da Innayi ta yi kafin ta mutu. Allah kenan mai yi yadda ya so, wa su kam jin daɗin su sai a Aljannah...
***
Gabaɗaya kwana ukun da ta yi garin ya fita ma ta a ka, haushin kowa ta ke ji tareda ita kan ta, tana ganin da ba ta yi nisa da Innayi ba da Innayi ba ta mutu cikin wahala ba.
Kamar yadda Prof ya gaya ma ta hakan aka yi, ranan Lahdi magabatansa su ka zo. Ƙanin sa Sani da su ke uba ɗaya ne da Ƙannen Baban sa guda biyu su ka zo tambayan auren Raudha. Bayan an basu su ka ajiye sadaki dubu hamsin tareda neman alfarmar a ɗaura auren ranan Talata tunda Prof zai bar ƙasan ranan Alhamis. Idan ya so ayi sauran bikin ba tareda shi ba. Su Ado ba su yi watawata ba su ka amince sannan su ka tura saƙo Ajili da Tunfure akan za a ɗaura auren Raudha ranan Talata...
Tunda Raudha ta ji batun sai wani kewan mahaifiyarta ya taso ma ta, ashe duk burin da ta sha na yadda Innayi za ta shiga ta fita a bikinta ashe hakan ba zai yiwu ba.
Ranan Talata da misalin ƙarfe biyu da rabi aka ɗaura auren *Professor Umar Audu Bamalli* da amaryarsa *Raudha Abubakar Pakkari*
Aaaf 🤔ashe Prof ma ya kamata ya maida sunan sa na swagga kamar Idris.
Doctor kuma Professor *Omarr Abdullah Bamally* 😂
Gaskiya anyiwa Raudha kara domin kuwa mutane dayawa su ka halarci ɗaurin auren. 'yan uwan su na Ajili da Tunfure sun zo dayawa. Yayanta Yusuf ma ɗan Hajiya Harira ya zo hakanan Yayunta mata ma na wajen Baba Indo sun zo, duk da ma sai ƙarshen wata za ayi waliman aure, wanda ya kama saura kwana ashirin da huɗu kenan.
Ya so ganin Amaryar sa kafin su tafi amma ba hali, a ranan za su koma Zaria kuma ƙofar gidan a cike ya ke balle ya kirata ta fito, dole haka ya haƙura ya bi 'yan uwan sa su ka juya.
Da ke ance Prof na da gida a Zaria shiyasa aka shirya kai ma ta kayan ɗakinta chan Zarian. An haɗa kuɗi an ma ta kaya kuma ba laifi sun yi abin kirki. Baffa Tsoho Sa guda ya bayar a yi hidimar biki da shi.
Bayan kwana biyar da ɗaura aure Sa'a ta haifi 'yan biyu maza,