Showing 21001 words to 24000 words out of 50413 words

Chapter 8 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1779

hankali kuma ta dena dariyar yadda ta ji jikin Innayin ya sake bushewa ba kamar yadda ta san ta ba.
Ta janye jikinta tana kallon Innayin da kyau, ta rame ta yi baƙi.


"Innayi rashin lafiya ki ka yi ne?"




Innayi ta girgiza kai tana murmushi.


"Allah kin rame"


"Ba wani dama haka na ke. Ke ce kika rame sosai, kina cin abinci sosai kuwa?"


Raudha ta sake rungumeta tana faɗin " I miss you Innayi na"...




Rabon da Jamilah ko Aisha su shigo wajen Innayi sun yi wata amma jin Raudha ta dawo shine su ka jajuɓu jiki wai sun zo barka. A hakan Innayi ta ƙulla mu su dabino da gurasa da Raudha ta kawo tsaraba ta aika mu su.


"To duk ki basu ya ƙare, ni a ke kaɗai na kawo ba a kowa ba ehe"


"Auta duk wannan sai na ci ni ɗaya? ai sai Allah ya kama ni. Ko ba dan su ba ai dan jikokina zan ba su"


"Ni dai ke ki ka sani" ta faɗa tana ƙoƙarin gyara ɗakin Innayin wanda rabonda a gyara shi tun kafin ta tafi makaranta.


Lokacin da su na cin tuwon dare ne
Raudha ta tambayi batun dabbobi dayawa da ta gani a gidan.


"Ba dai duk naki ba ne?"


"A'a akwai na Ado da Iro a ciki"


"Kutumar chan! Ke ki ke mu su kiwo? lallai rashin kunya. Shi yanzu Yaya Iro ya bar gidan sa ya kawo miki dabbobi saboda kin zama 'yar aikin su"


"Kwantar da hankalinki, ni ce na fara kiwo shine su ka ajiye na su a wajen"


"Duk ɗaya ne Innayi, ai ganin kina nan ne ya sa su ka kawo miki nan ɗin saboda sun san za ki kula da su tareda na ki"


"Ƙyalesu lada na ke samu, kiwon dabbobi akwai lada"


Raudha ta girgiza kai ta cigaba da cin abinci ranta a ɓace.
Innayi ganin ta yi fushi ya sa ta tashi ta kawo ma ta surprise ɗin da ta tanada ma ta.


Raudha ta amshi kwalin wayar tana murna.


"Kai Innayi na gode. You're the best"


Ƙaramar waya ce Nokia wanda ake wa laƙabi da rakani kashi. Washe gari kuwa Raudha ta je ta sayi layi ta saka...




Hutun Raudha a gida ya samar wa Innayi sauƙi dan duk abunda ta ɗauko za ta yi sai ka ga Raudha ta karɓe tana faɗin ki huta tunda ina nan.
A hutun ne kuwa Raudha ta lura da ɗingishin da Innayin ke yi, ashe ciwon ƙafa take ji tuntuni ta ke dannewa.


Raudha ta sa dole sai da su ka je asibiti inda aka bata magani tareda basu shawaran akan Innayi ta dena aikin wahala.


Bayan sun dawo ne su ka tarar da Halimah ta zo, a zaure su ka haɗu dan har za ta tafi da ba ta same su ba.


Bayan sun zauna an gaisa ne ta faɗi buƙatan ta na son karɓan aron kuɗi a wajen Innayi.


Innayi ta ce " kamar nawa?"


"Dubu biyar" Halima ta faɗa


Sai alokacin Raudha ta sa baki ta ce " amma Adda kina ji dai na ce miki daga asibiti mu ke amma ki ke maganar a baki aron kuɗi. Idan da tausayi ai ba Innayi za ki tambaya kuɗi ba akwai ƙanin ki ma'aikacin banki sai ki tambayeshi, ko kuma ki nemi yayan ki Malami"


"Auta!" Innayi ta faɗa da ɗan ƙarfi.


"Bar ta Innayi, ai ta fara jami'a dole ta gwada mana rashin kunya" Halimah ta faɗa ranta ɓace


" gaskiya dai da ɗaci ta ke" ta faɗa kafin ta fice daga ɗakin.


A hakan sai da Innayi ta lalubo dubu uku ta ba ta kafin ta tafi.


Da Raudha ta shigo ɗakin ta yi ta mita tana faɗin ita ba za ta kawo ba amma ta iya zuwa ta karɓa.
Kusan kullum hakane dan ko da ba kuɗi ba indai Halimah ta zo gidan sai ta nemi abun tafiya da shi...




***




Yau da gobe sai Allah. Haka Innayi ta cigaba da sana'arta tana rufawa kan ta asiri. Ciwon ƙafa da ciwon ido ta ke fama da shi wanda duk aikin wahala ne ya zamo sababin su. Sai dai duk da haka ba ta ji gazawa ba tunda dai duk cikin sauran 'ya'yan ta ba wanda ya iya ɗaukan nauyin karatun Raudhan dole ta ɗau na Auta kamar yadda ta ɗau na sauran.


A shekaran Raudha na uku a Jami'a ne Idris yai aure. Zo ka ga ƙarya a wajen ɗan Innayi.
Dama duk wani maƙo da Idris ke yi tanadi ya ke yi wa auren sa da matar sa. Shekara ɗaya kafin auren ya samu aiki a Firstbank da ke Bauchi. A nan ya haɗu da Fa'iza wacce 'ya ce ga marigayi Justice Bala Gumau, wanda bai jima da rasuwa ba. Kasancewa Fa'iza 'yar babban gida ne ya sa ya ke ta rawan ƙafa a kanta kar a raina shi. Ba ƙaramin kuɗi ya kashe ba wajen haɗa ma ta kayan lefe a hakan 'yan uwanta sai da su ka raina kayan. Ba su so auren Fa'iza da Idris ba dan dai kawai Fa'izar ta nace akanshi ne. Amma sun so da Kabir ɗan gidan minister ta aura.




Anyi bidi'a kala-kala a auren. A lokacin bikin ne Idris ya iya fidda kuɗi ya siyawa Innayi Atamfa guda biyu dan ta yi shigar biki.
Sa'a, Halima, matan Ado da matar Iro mai suna Asiya su suka je Bauchi akayi bikin da su, Raudha na makaranta ba inda ta je, ko da kuwa tana gida yadda ba sa shiri da Idris da wuya ta je Bauchi saboda bikin sa...






Duk yadda samari ke kawo ma Raudha wargi babu wanda ta bawa dama a cikin su dan karatu ne a gabanta. Dr Ambi shi ne project supervisor na ta kuma jajircewan ta da kamun kan ta ya sa su ka samu shaƙuwa tsakanin su. Lokacin tana hidiman project ɗin ne ya tambayeta mi za ta yi bayan ta gama bautar ƙasa, amsar da ta bashi ne ya sa shi gano ita ɗin mai burin zama likita ce kuma har a lokacin tana son zama ɗin ba ta cire rai ba. Shawara ya bata akan ta nemi scholarshinp a ƙasar waje saboda hakan zai fi ma ta sauƙi, ba lallai ta nemi Direct entry MBSS ta samu ba saboda competition da ke course ɗin.
Raudha ta yi dariya ta ce ai idan da halin fita waje itama tana son fita ɗin sai dai babu hali. Ya ce mata wani ɗan yayansa ma da scholarship ya tafi ƙasar canada yai karatu.
Ita kan ta bar labarin a ranta ne dan ta san ba mai yiwuwa ba ne. Dan samun scholarship ma a ƙasar ta Nigeria sai a hankali...


Raudha Abubakar Pakkari ta fito da first class a ajin su lokacin da ta gama makaranta. Ranan da ta karɓi result haka ta haɗa result ɗinta da na marigayi Baffah tana kallo tana kuma addu'ar Allah ya sa ta yi nisan kwana saboda ta ci amfanin Bokon da ta yi har ta inganta rayuwar mahaifiyarta Innayi...




Ranan da ta dawo gida Innayi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda farin ciki, finally Auta ta gama makaranta. Dama wuyar karatu fara shi.


Bayan 'yan gaisuwa sun tafi kawai Innayi ta fashe da kuka, ba abinda ta tuno irin ɗan ta marigayi. Ta sani da Baffah na raye da ita da Raudhan ba su wahala haka ba. Amma tana addu'ar Allah ya bawa Raudha tsawon rai ya kuma sa ma ta albarka a karatun da ta yi. Raudha ma maimakon ta ba da haƙuri sai ta shiga rera kukan aka rasa mai rarrashin wani...


Ga dai 'ya'yan Innayi Shida da su ke raye wanda dukkan su Allah ya wadatasu da ƙoshin lafiya da buɗi.
Rayuwar ta zai chanja kuwa?
Shin za ta ci riban 'ya'yanta kuwa?
Shin waɗannan 'ya'ya za su kula da Innayi a lokacin da tsufa ya kamata ganin yadda kowannen su ya kama gaban sa ya manta da wahalhalun da ta ma sa?




Mu kan manta da iyayen mu a lokacin da su ka fi buƙatar kulawan mu. A lokacin da ya kamata su huta sai kaga mun ka sa basu hutun nan, su yi hidima da mu tun muna ciki har kuma iya ƙarshen rayuwar su.


Wata simple katin waya ba ta iya tura wa iyayenta, tana jira sai ta zama Hajiya, may be lokacin da ta zama Hajiyar iyayen ta ba sa raye ko kuma suna rayen ma amma ta shagala da duniya ta kasa yi mu su komai.
Wani kafin ya kira mahaifiyar sa sai an ja lokaci. Wani matarsa da 'ya'yan sa kawai ya sani ya manta da iyayen sa wanda su ka yi ɗawainiya da shi a lokacin da babu mata kuma babu 'ya'yan.


Rashin daraja iyayen mu da kyautata mu su ya kan sa mu samu koma baya a harkokin mu na rayuwa. Ko iyayen ka na da buɗi su na da arziƙi akwai hanyoyi dayawa da za ka nuna musu kulawa garesu.


Allah ya sa mu dace amma idan ba mu ba su hutu ba a lokacin da ya dace su huta tabbas muma idan mun tsufan namu 'ya'yan ba za su bari mu huta ba...








*RIBAR UWA*




*Na...Azizat*
*Wattpad@Azi_zat*






Chapter 09
(Free book ne)


*Raudha*








(Ina ba da haƙurin jina da kuka yi shiru kwana biyu)


Aikin koyarwa na hucin gadi Raudha ke yi a wasu private school guda biyu kafin ta tafi bautar ƙasa. Duk da albashin bai wani taka kara ya karya ba amma a hakan da shi ta ke samu ta ke kula da kan ta da kuma mahaifiyar ta.
Abu na farko da ta farayi bayan dawowan ta gida shine hana Innayi yin aikin wahala.
Ta sani suna samun riba sosai a sana'ar ƙosai sai dai lafiyar Innayi ta fi ma ta komai. Bayan ta dawo ne ta lura da ciwon ƙafar da Innayin ke yi hakan ya ƙara ba ta ƙarfin gwiwa wajen hana Innayi ayyukan da ta ke yi na wahala.
Dan ta sani ciwon ƙafan ya samo asali ne saboda ayyukan wahala da Innayi ta yi a baya kuma ta ke kan yi har yanzu.




Cikin wata biyu Innayi ta samu kwanciyar hankali, duk wani yawan ciwon kai da ciwon jiki da ta ke ji duk ta ji sauƙin su. Wannan nitsuwa ya sa ta maida hankali wajen karatu da ta ke yi, bayan na kwana biyu da ta ke zuwa a ranakun weekend ta shiga Islamiyyar dare wanda ake yi a ta kusa da gidan su. Sau huɗu a sati. Ta dena tunanin komai sai addu'ar Allah ya ba wa Raudha aiki ya kuma ba ta miji na gari domin ta ga tausayi a idon Raudha hakan ya sa ta ke da yaƙinin Raudha za ta kula da ita har iya ƙarshen rayuwar ta...


Yammacin ranan wata Lahdi Raudha na zaune tana marking assignment na yara wayarta ya shiga ƙara, Innayi da ke kusa da wajen ta miƙa ma ta wayar.


Murmushi ta yi bayan ta ga sunan da ke jikin screen ɗin sannan ta amsa wayar da Sallama. Idan akwai mutumin da za ta kira da Uba to Dr Ambi ne, akan samu malamai dayawa ma su neman ɗaliban su a makaranta amma Dr Ambi baya ciki, kowa ya shaideshi da kyawawan halayensa. Tunda ta bar makarantar lokaci zuwa lokaci yakan kirata su gaisa ko ita ta kirashi. Ya ƙarfafa ma ta gwiwa sosai wajen ganin ta cigaba da karatu.


Bayan sun gaisa ne ya ma ta maganar wani scholarship da ake cikawa na wa ta makaranta a Malaysia. Ta ma sa godiya tareda alƙawarin a ranan za ta je cafe ta cika...


Ganin yadda ta ke murmushi bayan sun gama wayar ne ya sa Innayi tambayar ko dai sirikinta ne?


"Kai kai Innayi rufa min asiri, ni da aure ai sai na zama likita"


Innayi ta yi dariya ta ce "Allah ya nuna ma na. Amma auren ma idan ya zo za ayi shi ko?"


"Innayi kenan. Wa ki ke ga zai aureni kuma ya bar ni na cigaba da karatu?"


Kafin Innayi ta ba ta amsa sai ga Ado ya shigo gidan yana ƙwalawa Raudha kira da ƙarfi




"Yaya lafiya?"


"Lafiyan uwar ki. Na ce lafiyan uwar ki. Wato Raudha har wuyan ki ya yi ƙwari da har zan yi magana ki tsallake"




"Mi na yi kuma?" ta faɗa a kausashe




"Dan uwar ki ba na ce ki bar dabbobina a cikin gida ba, miye nufinki da za ki kora min su waje ki ƙi bari su shigo gida jiya?"


Miƙewa tsaye ta yi tana kallon Yayan na ta ido cikin ido ta ce " Yaya tun ba yau ba na ce ka nemi mai kula ma ka da dabbobi amma ka ƙi. Yaya Iro da ya ke da zuciya ai ya kwashe na sa, wallahi matuƙar ina gidan nan ba za ka kwaso dabbobi ka ajiye mana da niyyar ni da Innayi ne za mu dinga kula ma ka da su ba"


"Haka za ki ce? To wallahi dabbobin nan su na nan gidan ki ka ƙara kora min su waje sai na saɓa miki"




"Yaya Ado!" Ta faɗa da ƙarfi har sai da ya ɗan tsorata




"Wallahil Azim indai ka ga na bar dabbobin nan a nan to kai ko matarka ko 'ya'yanka za ku dinga shigowa kuna kula da su ne amma idan ba haka ba ba za su zauna a nan ba. Fisabilillahi Yaya wannan adalci ne, ni da Innayi za mu dinga ciyar maka da dabbobi mu na kula ma ka da su, mu ba su ruwa mu share kashin su, ko sisi ba ka taɓa ajiyewa ba. Wallahi..."


Saukar mari ya hanata cigaba da maganar.




"Raudha ki fita a hancina, dan kina ƙarɓan albashin dubu biyar ɗin ki ba shine zai sa ki ga ina daidai da ke ba"


"Innayi ki ja wa 'yar ki kunne dan wallahi zan faffasa ma ta jiki"




Raudha ta fusata ta ce "duk abinda za ka yi sai dai ka yi amma dabbobin ka ba za su zauna a cikin gidan nan ba"


Mari Ado ya kuma kai ma ta, bai tsaya a nan ba ya shiga dukan ta ta ko'ina.


"Ado ka ƙyaleta, Ado, Adamu ka ƙyaleta dan Allah" Innayi ta faɗa da ƙarfi, sai dai kamar a ice ta ke yiwa magana dan ko kula ta bai yi ba ya cigaba da dukan Raudha.


Innayi ta shige ɗaki ranta a ɓace, hannunta har rawa ya ke yi. Ta rintse ido tana cigaba da sauraron kukan Raudha...




A ranan ya dawo da dabbobin cikin gidan amma kuma yadda Raudha ta rantse haka ta watsar da dabbobin na sa wanda ya haɗa da raguna biyu, tinkiyoyi biyar sai taure ɗaya da akuya ɗaya da ƙananan 'ya'ya biyu.


Duk wani dusa ko ƙanzo da ta ke zuba mu su a da ta dena shi. Ta ƙwammaci ta zuba a shara da ta zubawa dabbobin su ci, Innayi kam ba haka ta so ba amma ta yi shiru saboda ta ga har lokacin Raudha fushi ta ke da Yayan ta. Shara kuwa za ta share ko ina amma banda wajen su, gaba ɗaya wajen ya cakuɗe ya zama ba kyan gani ga uban wari.
Innayi ce ma ke basu ruwa idan Raudha ba ta nan, bayan kwana huɗu da Ado ya shigo gidan ya ga dabbobin yadda su ka lalace ya sa dole ya nemi Almajiri wanda zai dinga kula ma sa da su safe da yamma...


Wata huɗu Raudha ta yi a gida aka tura ta bautar ƙasa a Yobe state har lokacin kuma ba ta samu scholarship ɗin da ta cika ba.
Innayi daurewa kawai ta ke yi amma idan da son ran ta ne Raudha kar ta yi nisa da ita. Ba ƙaramin kewarta za ta yi ba idan ta tafi.
Raudhan ma ta ji tafiyar a jikin ta sosai musamman idan ta tuna yadda ta dawo ta samu Innayi farkon dawowar ta.




"Innayi ban da aikin wahala dan Allah, na yi magana da Salisu zai dinga kawo miki kuɗi duk wata sai ki dinga buƙatun ki da shi. Dan Allah duk lokacin da ki ke da buƙata ki gayawa Salisu shi kuma zai kira ya gayamin sai na turo kuɗi"


"Na gode, Allah ya saka miki da alkhairi"


Raudha ta amsa da Amin tana danne kukan da ke cin ta.




Ranan kusan kwanan zaune ta yi da ita da Innayin na ta su na hira. Washegari Raudha ta wuce Camp a chan Yobe state inda aka losting na ta.


Gidan yai wa Innayi faɗi, kaɗaici ya isheta. Ba ta aikin komai daga Islamiyya sai gida, jikokinta ba wani sabawa su ka yi da ita ba, ga gida ga gida amma sai su kwana biyu ba su leƙo ƙakar ta su ba. Musabbabin haka kuwa shine yadda tun farko iyayen su ba su nuna mu su muhimmancin Kakar ta su ba ga uwa uba kuma zamani da ya kawo talabijin wanda ke ɗauke hankulan yara. Ko acikin gida ma yaran sai anyi da gaske su ke zuwa aika indai akwai wuta, idan su ka ƙurawa TV ido za su iya kwana a haka ba su gaji ba.
Abinci da matan Ado ke kawowa kuwa tunda Raudha ta hanasu su ka basar, dama abin kamar ba dan Allah su ke ba shiyasa ko bayan ta tafi ba su cigaba da kawowa ba.


Salisu ɗan maƙocin su Innayi ne, kusan sa'anni su ke da Raudha, tare su ka ƙare Sakandare amma shi bai cigaba ba, gyaran generator ya ke yi.


Raudha na fitowa daga camp aka turata wani secondary school na gwamnati a cikin garin Yobe. Cikin albashin da ake ba su duk wata Raudha ke ware dubu bakwai ta ke turawa account ɗin Salisu dan ya dinga yiwa Innayi cefane sauran kuma ya bata a hannu.
Ado ganin Raudha ba ta nan ya sa duk sati ya ke ba wa Innayi dubu ɗaya wato dubu huɗu a wata kenan. A watan Raudha na uku ne watarana ya zo wajen Innayin su ke gaisawa sai ga Salisu ya shigo gidan da sallama. Da ke ɗan gida ne kai tsaye ya shigo ɗakin ya gaida Innayi tareda miƙa ma ta kuɗi saboda bai jima da ciro su ba ma.


"Innayi za mu je bikin wani abokinmu a Kaduna shiyasa ban miki cefanen ba amma na gayawa Usman anjima ya zo ya karɓa kuɗi sai ya siyo miki abubuwan da ki ke buƙata"


Innayi ta ma sa godiya. Bayan ya tafi ne Ado da ya ƙyalla ido ya ga kuɗin da Salisu ya ba ta ya ce "Innayi ashe kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login