Showing 1 words to 3000 words out of 50413 words

Chapter 1 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1778

*RIBAR UWA*
Na Azizat


Chapter 01








*Shimfiɗa*




Friday 8:12pm in Boston, Massachusetts, USA.


Haka kawai jikinta yai sanyi, lokaci guda ta ji komai ya fita a ranta. Hatta littafin da ke hannunta sai da ya faɗi ƙasa saboda yadda hankalinta ya kauce daga karatun. Wani sanyi ne ya shigeta lokaci guda, zuciyarta ya ma ta wani nauyi. Ta dafe ƙirjinta tana maimaita kalmar Hasbunallahu wa ni'imal Wakeel. A hankali ta fara jin sauƙi bayan ta shafe kusan minti biyu tana maimaitawa, duk da haka ba ta dena maimata waɗannan kalmomi ma su ɗimbin lada ba.


"Excuse me, are you ok?" muryan wanda ke gefenta ya ankarar da ita daga halin da ta ke ciki. Ta juyar da kanta a hankali zuwa gefen sa tana mai gyaɗa ma sa kai domin ta tabbatar ma sa da lafiyarta ƙalau. Ya miƙa ma ta littafin ta da ya faɗi yana mai nuna littafin yana da daɗi shima ya taɓa karantawa. Ta ƙarɓi littafin tareda furta ma sa kalmar Thanks. Matashin Baturen da ke zaune a gefenta wanda ba zai wuce shekaru talatin da biyar zuwa da takwas ba yai ma ta murmushi sannan ya cigaba da kallon window.


Ta maida littafin cikin jakarta domin ba ta ganin za ta iya cigaba da karanta shi a wannan baƙon yanayi da ta tsinci kanta a ciki lokaci guda. Littafin mai suna The catcher in the rye da ta ke karantawa tun kwana huɗu da su ka wuce ba ƙaramin jin daɗin karatun sa ta ke ba, ta yi nisa da karatun dan lokacin da ta shiga motar bus da zai kai ta anguwar ta su ta Mission Hill daga Roxbury ta kusa ƙarisa karanta shi bai fi shafuka shida zuwa biyar ya rage ba amma lokaci guda komai ya chanja ma ta. Baƙon yanayin da ta tsinci kanta a ciki ya sa ta yi kewar gida musamman mahaifiyarta wanda ta ke matuƙar so a rayuwarta. Har aka isa anguwar na su ba ta dena addu'a cikin zuciyarta ba. Ta sauko daga bus ɗin ta dinga takawa a hankali har ta kai gida.
Alwala ta yi ta yi sallah sannan ta hau kan gado ta kwanta saboda yadda takejin yanayin jikinta ba daɗi. A hankali bacci mai daɗi yai gaba da ita bayan ta shafa addu'ar bacci...


Daddaɗan mafarkin da ta yi a daren na jiya ya sa har kusan makara ta yi da asuba. Lokacin da ta yi sallah ta jima tana yiwa iyayenta addu'a tareda sauran al'ummar musulmi. Ta shirya a gurguje cikin doguwar rigan atamfa wanda ke da kalar blue da fari, ta ɗauki babban mayafi fari ta yane jikinta da shi. Chocolate cornflakes kawai ta haɗa da madara na ruwa ta zauna ta sha kafin ta ɗau jakarta ta wuce makaranta.
Ba ƙaramin jin daɗin jikinta ta yi yau ba tana tafiya tana murmushi, duk wani damuwa da ta ke ji jiya da dare ya warware. Haka nan takeji ajikinta yau ranan za ta zo ma ta da alkhairi. Idan ta gama ɗaukan darasin yau tabbas dole ta kira gida ta ji lafiyar mahaifiyarta sannan ta sanar da ita labarin mafarkin da ta yi mai daɗi. Ta kan yi mafarki da mahaifiyar ta lokaci zuwa lokaci amma mafarkin jiya daban ne dana koyaushe mafarkin Aljannah ta yi...


Su Ishirin da ɗaya ne a ajin na su kuma su biyu ne kaɗai musulmai, daga ita sai wani ɗan ƙasar Pakistan mai suna Azhar Ali Durrani. A gaba ɗaya ajin kuma su huɗu ne ba 'yan ƙasar na America ba. Ita da ta zo daga Nigeria sai Azhar sannan Audrey mutuniyar Philliphine sai Lee Jung Bo ɗan ƙasar Korea ta Kudu.


Tun daga shekarar farko zuwa yanzu da ya saura ƙiris su ƙarisa shekara ta biyu suna tare a ajin tamkar 'yan uwan juna, kowa da ka gani a wajen karatu ne a gaban sa sannan karatun bai hana suna taimakawa junan su ba idan akwai wanda ya ke da rauni wajen fahimtar wani darasi. Daga sun kammala wannan sashi to saura mu su shekara biyu suna zuwa asibiti dan koyon aiki kafin su tafi residency na su...


Yau ma tana cikin wanda su ka zo ajin da wurwuri, kaman kullum a gaba ta zauna bayan ta gaisa da sauran mutane bakwai da ta samu a ajin. Ta buɗe littafi tana ɗan dududdubawa kafin malamin ya shigo, yau su na da darasin Professor Umar Audu Bamalli wanda ta san halin shi na yawan tambaya idan yana darasi. Tana jin daɗin darasin sa saboda gaskiya Allah ya bashi baiwar koyarwa gashi kuma ba ƙaramin jin daɗi ta ke yi ba idan ta ga baƙin fata na nuna zarra a ƙasar da ba tashi ba. Prof Bamalli ya yi ƙaurin suna a makarantar na su kuma kasancewar sa baƙin fata kuma ɗan Nigeria ya sa ya ke burgeta sosai kuma ta ƙe ƙara jinjina ma sa.
Makarantar su na Harvard Medical school ba ƙaramin ƙaurin suna yai ba a ɓangaren ilimi a duniya baki ɗaya. Idan za ka irga Jami'o'i da su ka yi fice da suna kuma su ka yi zarra a duniya idan ba ka saka Harvard ba kamar lissafin ka bai cika bane. A duk lokacin da aka yi ƙididdiga aka ware Jami'o'i fitattu goma ko fitattu biyar da su ka fi kowanne a duniya sai ka ga sunan Harvard yana zaune ƙyam acikin su. Taimakon Allah da addu'ar Uwa shi ya kawota wannan babbar makaranta da ba kowa ke samun daman shigan sa ba...


Ajin na su yai tsit saboda shigowar Prof Bamalli. Kamar yadda ya saba sai da ya gaisa da 'yan ajin kafin ya fara gudanar da darasin. Kusan rabin awa da fara darasin na su ya jefo wata tambaya wanda Jack Stafford yai saurin ɗaga hannu ya amsa ta sai dai kuma amsar ta shi ba dai-dai bane. A maimakon ya gwaleshi ko ya nuna ba dai-dai ba ne sai ya ce "great, but we need something better"


Wata baturiya mai suna Emilia ta ɗaga hannu ta sake amsa wannan tambaya sai dai ita ma ɗin ba dai-dai ba ne. Prof yai murmushi ya ce "nice try Miss Stevenson"


Ya kalli budurwar da ke gefen Emilia wacce ya sani 'yar ƙasar sa ce kuma ya san ta da ƙoƙari sosai. Hankalinta na kan wayar ta shiyasa ya ɗan kira sunan ta da ɗan ƙarfi. "Pakkari"
Budurwar ta yi saurin ɗago idon ta tana ƙoƙarin ba da nitsuwarta ga malamin na su.


Ya sake maimaita ma ta tambayar sa ko za ta iya amsawa sai kuwa ta bashi mamaki domin amsar da ta bayar ɗin shi ne dai dai. "Good" ya faɗa sannan ya cigaba da bayanin darasin da ya ke yi.


Wata baƙuwar number ne ke kiranta daga Nigeria shi ya ɗauke ma ta hankali ma daga ajin na su. Yadda numban ke kira akan kira ya sa ta yi tunanin ko akwai matsala ne. Ta dai daure ta ba da nitsuwarta a ajin da zimmar ana gamawa za ta kira numbar domin ta ji wanene ke kiran, cikin zuciyarta tana ayyana wa ranta ƙila mahaifiyarta ne ke son gaisawa da ita.
Prof Bamalli ya gama darasin sa inda ya ke tsaye domin amsa tambayoyin ɗaliban na sa kamar yadda ya saba a kowani lokaci.
Tana son tambayar Prof Bamalli amma kuma ƙaran shigowar text zuwa wayarta ya sa ta maida hankalin ta ga wayan domin ta ga wani irin saƙo ne...


Saƙon da ta karanta ne ya sanya numfashinta ya ɗauke na 'yan daƙiƙu. Ta miƙe zumɓur tana faɗin "Ƙarya ne, ƙarya ne" hannunta na rawa ta shiga dialing numbar da ta turo saƙon. Mancewa ta yi da inda ta ke burinta kawai shine ta ji gaskiyan abinda aka turo. Wani bagidajen ne zai tura ma ta saƙon baƙin ciki irin haka, mahaukacin ne ya ke tura saƙon mutuwa haka.
Innayi ta rasu shi ne abinda aka turo. Ta ɗara wayan a kunne tana girgiza kai hawaye na zubo ma ta.
Wanda ta amsa wayar ne ta sanar da ita abinda ya faru a tsanake. Hakan yai sanadiyar suɓutuwar wayar da ga hannunta ya faɗi ƙasa gamida yin ƙara wanda ya sa hankalin duka 'yan ajin ya tashi domin tunda Raudha Abubakar Pakkari ta miƙe tsaye tana kuka su ka san ba lafiya ba. Tambayarta su ka farayi randomly akan mi ya ke faruwa amma kwata-kwata ba ta jin su balle ta iya ba su amsa.
A hankali ta fara takawa tana tafiya hannunta ɗaya a miƙe kaman zata taɓa wani abu. Hawayen da ke ziranya a idon ta ne ya ƙara ingiza yadda ƙwaƙwalwarta ke tuno ma ta lokuta na farin ciki da su ke tare da Innayi...


A mafi yawancin lokuta idan ka ji saƙon mutuwar wani na kusa da kai to abu na farko da ka ke tunowa shine kyawawan halayen sa. Za ka dinga tuno su a ranka kamar yau ne abin ya faru, abin zai shiga jikin ka sosai har ka ji duniyar nan fa ba madogara ba ce kuma kaima ɗin lokaci ka ke jira. Amma daga zaran wannan jimami ya huce sai mutum ya shagala da duniya ya manta cewa wannan nakusa da shi da ya mutu yana chan yana cin sakamakon abin da ya yi a duniya haka nan kuma shima ɗin ko ba daɗe ko ba jimawa zai je chan ɗin.


Ku biyoni domin jin labarin wata uwa da 'ya'yanta, labari ne mai shiga rai da taɓa zuciya. Labarin da ban rubutashi dan komai ba sai dan ya zama kaman wani hanya na tunasarwa garemu ba ki ɗaya. Burina shine a ƙarshen labarin nan a samu mutum ɗaya ko biyu da su ka gyara zamantakewar su da kuma yadda su ke da iyayen su musamman iyaye mata.
Saboda darasin da na ke so na isar ta sigar labari ya sa na ke so dan Allah idan ka karanta ka yaɗa shi saboda wani ma ya samu ko zai ƙaru ko kuma ka baiwa wani labarin a taƙaice ko za a samu wani da zai faɗakantu da wannan labari.
Labarin daga farkonsa har ƙarshen sa kyauta ne ga duk wata Uwa da ke doron ƙasa. Its all about motherhood.
Allah ka jiƙan iyayen mu ka gafarta mu su amin
Wanda na su ke raye a daure a kyautata mu su wanda na su suka rasu a cigaba da mu su addu'a


Ta ku Azizat


#read
#vote
#comment
#plz share








𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*








*RIBAR UWA*




*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*






Chapter 02
(Free book ne)




*The bride*


Muhammadu Jo'o shi ne ɗa na huɗu a gidan su ya na da yayye mata uku da ƙanne maza uku da autar su Faɗimatu. Da ke auren wuri ake yiwa yara mata a ƙauyen na su shiyasa bai wani shaƙu da su ba, lokacin da ya taso an aurar da 'yar farin su Maimunatu mai bi mata ma ba a jima ba aka aurar da ita. A taƙaice dai ya taso da tsananin son 'yar ƙaramar ƙanwar na su Faɗimatu wanda kuwa duk gidan sun fi kama da juna. Sai dai shekarar Faɗimatu shida a duniya ta rasu sakamakon zazzaɓin cizon sauro.


Muhammadu kowa ya shaideshi wajen kyawawan halayen sa da jajircewan sa wajen harkan noma. Yayinda tsaransa ke kora shanu su na tafiya da su Kudu, ma su Noma kuma na saida gonakin su suna shiga birni , shi ya jajirce ne wajen noma sosai yana ƙoƙarin inganta rayuwar sa da ta ƙannen sa. Domin a shekarunsa shashida Allah yai wa mahaifin su rasuwa da ake kira da Baffa Jo'o. Daga wajen mahaifiyar sa ya samu umurni a kan yai aure saboda ya zama yana da iyalin sa, dan ya fi jin daɗin kula da ƙannen sa sosai.


***
Aminatu 'ya ce ga Malam Isiyaku Chadi. Malam Isiyaku da iyalen sa su ka zo ƙauyen Tunfure kusan shekaru ashirin da su ka wuce. Ilimin addini da Malam Isiyakun ke da shi ya sa ya samu gindin zama a ƙauyen Tunfure ba tareda mutanen ƙauyen sun damu da rashin sanin asalin sa ba. Malam Isiyaku ya kan ce daga chan gabashin Chadi ya shigo Nigeria inda yai ta yawuce-yawuce kafin har Allah ya sa ya samu gindin zama a Tunfure.


Kafin Aminatu, Malam Isiyaku sai da ya busine 'ya'ya takwas sannan Allah ya sa Aminatu ta tsaya, kuma har ya rasu ita kaɗaice 'yar sa...


Muhammadu ya yi karatun Allo a gaban Malam Isiyaku ne, inda tun Aminatu na ƙarama ta ke burgeshi.

Yana saurayi ɗan shekara shatakwas Aminatu na shaɗaya aka yi auren su bayan an sha fama kafin Goggo Talatu mahaifiyar sa ta amince, dan a da ta nuna ra'ayin ya auri 'yar ƙanwar ta amma ya ƙi saboda soyayyar Aminatu da ya rufe ma sa ido. Shigowar Aminatu gidan kyawawan halayenta da sanyinta ya sa Goggo ta sake jiki da ita har ta fara son ta. Duk da ƙarancin shekarunta tana bin Goggo sau da ƙafa tamkar Goggo ce ta haifeta.


Shiru-shiru shekara ɗaya ta shuɗe ba maganar haihuwa ta biyu ma ta shige shiru, hankalin Goggo ya tashi ta fara ƙorafi saboda shekaru biyu ba wasa ba ne a wajenta. Ƙwatsam sai ga ciki ya ɓullo, murna a wajen Muhammadu ba a magana, Goggo ma ta yi farin ciki tunda ya tabbata ɗanta na da lafiya. Tun cikin na ɗan ƙarami ya ke ba wa Aminatu wahala har ta kai da cikin yai nisa. Muhammadu ya nemi a kai Aminatu Asibiti a dubata amma Goggo ta ƙi ta ce lalaci da ragonta ke sa Aminatu wannan tsirfe-tsirfen ciwon, a cewarta komai zai wuce idan cikin ya girma. Cikin na girma Aminatu na ƙara bushewa, ta yi wani fayau da ita kamar ba ta da jini. Ana haka aka wayi gari da rasuwan Malam Isiyaku wanda ya kwana lafiya amma ya mutu cikin baccin sa. Aminatu ta yi baƙin ciki da wannan rashin yayinda ta ke kuma fama da nata ciwon.


Sosai Muhammadu ya ke ƙoƙarin kula da ita daidai gwargwado kuma ya damu da rashin lafiyarta. Wani lokacin idan ya shiga garin Misau ya kan siyo wa Aminatu tsire ko balangu ya kawo ma ta a ɓoye ta ci, dan ya kan ji ana cewa idan mace na da ciki ana so ta riƙa cin abu mai daɗi. Har buredi ya ke siyo ma ta idan ya shiga cikin garin na Misau.


Ƙarancin shekaru, rashin jini da cutar malaria da typoid da su ka haɗu su ka yiwa Aminatu katutu a jiki ya sa wata rana da safe Aminatu na daka ta faɗi ta suma. Bayan ta farfaɗo naƙuda ta fara gadan-gadan da cikin ta da ke wata takwas. Muhammadu ya tafi ya nemo Amalenke da za a kai Aminatu asibiti dan hankalinsa ya tashi da halin da Aminatun ta shiga. Lokacin da ya shigo gidan ya samu Goggo na rusa kuka yayinda Delu ungozoma ta ke riƙe da jaririyar da Aminatu ta haifa. Bai bi ta kan jaririyar ba ya shiga ɗaki ya tarar da gawar Aminatu kwance cikin jini ya buɗe zanin da Delu ta rufe ma ta yana ganin yadda matar sa kuma masoyiyarsa ke kwance kamar mai bacci amma kuma ba rai. Ya shiga kiran sunan ta da ƙarfi yana faɗin ta tashi ta ma sa magana. Da ƙyar ƙanin sa Habu da abokin sa Iro su ka zo su ka janyeshi a wajen gawar...


Inna Hauwa mahaifiyar Aminatu ne ta ke renon jaririyar da ta ci suna Faɗimatu. Baban ta kaɗai ke kiranta da Faɗimatuz zahra yana ma ta kirari da Tauraruwa ta.


Koyaushe Muhammadu na maƙale da 'yar sa Faɗima. Maganar ƙara aure da Goggo ke ma sa duk iska ya ke bi domin ya ka sa manta Aminatun sa haka kawai sai ya je maƙabarta ya je wajen Kabarin Aminatu ya zauna ya wuni a chan. A hankali suna ganin abin da wasa har shekaru huɗu amma Muhammadu bai ƙara aure ba, ta kai har Goggo na nema ma sa magani dan gani ta ke ya samu matsalar ƙwaƙwalwa ne musamman idan ta ga irin kulawar da ya ke bawa 'yar sa Faɗimatu. Yana da dogon buri a kan Faɗimatu yana da burin ta yi karatu, tun ranan da ya je asibiti gaida Baffan abokin sa da ba lafiya ya ga wata likita mace musulma amma mutuniyar Minna Banufiya, hankalinsa ya kwaɗaitu da son 'yar sa Faɗimatu ta samu ilimi, har ta kai matakin da Dr Hassana ta kai. Duk da kuwa ya sani abu ne mai wuya musamman yadda a lokacin karatun 'ya'ya maza ma ba kowa ke yi ba balle 'ya'ya mata.


A shekaran Faɗimatu na biyar Inna Hauwa ta rasu bayan ta yiwa Muhammadu bayanin asalin su, saboda kar gaba ayiwa Faɗimatu gori. Kamar yadda Malam Isiyaku ya faɗa, su mutanen ƙasar Chad ne daga wani gari da ake cewa Moundou. Mahaifin Malam Isiyaku Allah ya albarkaceshi da arziƙi, yana da mata huɗu kuma dukkan su sun haihu sai dai ciki ya fi son Ruƙayyatu wacce Allah yai wa baiwar kyau da Ilimi na addini kuma haka yaranta su ka taso da kyakykyawar tarbiya da ilimin addini. A hankali a hankali kissa da munafurci tareda mugunta yasa yaranta biyu su ka halaka ya saura Isiyaku kawai, hakan ya sa ta tura Isiyaku Ndjamena wajen yayan mamanta akan ya koyi karatu. A nan Isiyaku yai karatu har ya auri 'yar uwarsa ta ɓangaren uwa. Mutuwar ElHajj Abdoullahe ya sa 'ya'yan sa da matan sa dama 'yan uwan sa su ka fara farautan junan su saboda dukiya, ƙarshe su ka yiwa Ruƙayya asiri har ta kai ta rasu cikin jinya. Hakan ya sa Malam Isma'il ya ba wa Isiyaku shawara akan yai nisa da Chad saboda kar 'yan uwan sa su halaka shi. Wannan ya sa ya ɗau iyalin sa su ka shiga tafiya neman mafaka har Allah ya zaunar da su a ƙauyen Tunfure bayan sun zauna a wajaje da dama...


Faɗimatu 'yar gatan Baban ta, duk ƙauyen ba macen da aka sa ta a makarantar boko sai Faɗimatu, inda ta ke tafiya primary school da ke ƙauyen Ajili. Muhammadu shi zai kai ta ya kuma dawo ya ɗauketa ya maidata gida. Tun Goggo na faɗan har ta haƙura ta dangana. Shekarun Faɗima tara Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login