Showing 39001 words to 42000 words out of 50413 words
ni chan bayan ya aikawa iyaye na. A ranan da aka kai ni a ranan aka min surgery saboda rashin yin surgery ɗin da wuri na iya sawa na mutu. Typhoid ne ke damuna har ta min katutu a jiki ta fara cin hanjina, rashin abinci mai kyau da kuma jiƙe-jiƙen maganin da aka yi ta bani ya kuma lalata min ciki. Wani Balarabe da ake kira da Dr Fu'ad Hamdan Al Sayyid shine shugaban pediatric a lokacin kuma shi ya jagoranci aikin da aka min. Shi kan sa bai da 100% yaƙinin zan yi rai saboda yadda na galabaita. Ya yi faɗa sosai wa iyayena kan yadda su ka bari har jinya ta ci ni haka. Na yi wata biyu da sati ɗaya kafin na samu sauƙi har ake shirin sallama na a lokacin Dr Fu'ad ya ce indai Almajiranci za a kaini to gara a barni a wajen sa ya sa ni a makaranta. Ba a wani ja lokaci ba Baba ya amince, aka bar ni a Maiduguri wajen Dr Fu'ad.
Ina shekara goma na fara aji ɗaya a primary, da ke ina da ƙwazo a aji biyar na zana jarrabawar gama primary na shiga Sakandare, ko da wasa ban taɓa zuwa gida ba saboda yadda na ke jin haushin Mahaifina da Uwar riƙona. Sau ɗaya Baba ya zo ya dubani amma bai sake zuwa ba. Shima ya san zaman wajen Dr Fu'ad ya fi mini a kan gidan sa. Ina aji uku a sakandare mahaifina ya rasu wanda hakan ya sa Dr Fu'ad ya ɗaukeni mu ka je gida ta'aziya. Har lokacin Umma ba ta nuna mini so ba sai ma cewa da ta ke na ƙi asalina ina bin Balarabe har da min addu'ar Allah ya sa na zama ɗan fashi ko ɓarawo, ranan na yi kuka sosai saboda mummunan kalamai da Uwar riƙona kuma yayar mahaifiyata ta yi ta jifana da shi. Bayan mun koma na watsar da kashin su na rungumi Dr Fu'ad wanda ya zame min Uba. Allah bai bawa Dr Fu'ad da matar sa haihuwa ba shiyasa ya ke son yara, kafin ni ya taimakawa yara dayawa ta hanyar inganta rayuwar su. Dr Fu'ad ne ya turani ƙasar America dan na yi karatun Likitanci. Ina nan ina karatu har na kai matakin da na fara yin residency ɗina. A lokacin ne na je Nigeria saboda Dr Fu'ad ba shi da lafiya yana ma shirin komawa ƙasar sa ta Asali wato Egypt. Shi ne ya nuna min akan na je gida na ga 'yan uwa na saboda duk min rashin adalcin su sune Asali na. Bayan na je ne na tarar da Umma a walaƙance, ta lalace sosai, ga jinyar da ya ke cinta ba mai kula da ita. Sai da ta ganni ta fashe da kuka tana neman na yafe ma ta. Ita ta yiwa Baba na asiri ya zamto duk maganar da ta ma sa ba ya iya mu su shiyasa duk abin da ta ke min ba ya iya cewa komai. Ko lokacin da ta ce ya kai ni Almajiranci bai iya musa ma ta ba. Ga uwa uba gadona da su ka cinye ita da 'ya'yanta. Da farko na ƙi na yafe daga baya na ce na yafe ma ta. Ni na kai ta Asibiti na ba da kuɗi aka yi jinyarta yayinda na koma aiki na. Watanni uku bayan dawowa na Dr Fu'ad ya rasu a ƙasar Egypt, sai da na samu lokaci na je na yiwa Matarsa da 'yan uwan sa ta'aziya saboda Dr Fu'ad ya min komai a duniya"
Prof Bamalli ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Raudha da ta yi shiru tana sauraron sa dan yanzu ta dena kukan.
Ya cigaba da cewa " A lokacin da na samu rufin asiri na kai matsayin da zan iya tallafawa iyayena sai ya zama na ba sa tareda ni. Duk abin da na zama, duk abin da na tara ba zan taɓa iya taimakawa iyayena ba domin ba sa raye. Abu uku zan iya yi mu su yanzu musamman ma mahaifiyata wanda ko kamanninta ban sani ba, abu ukun nan su ne za su zamo ma ta RIBAN kasancewar ta UWA kafin ta rasu. Na farko addu'a da zan dinga yi ma ta. Na biyu Sadaka da ayyukan alkhairi da zan yi da sunan ta. Na uku kasancewata mutum na gari zai zamo ma ta abun alfahari duniya da lahira"
Sai da yai shiru na ɗan daƙiƙu kafin ya kira sunan ta "Raudha"
Ta amsa a hankali "Na'am "
"Ki riƙe abu ukun nan daga yau, domin su ne abun da mahaifiyar ki ke buƙata daga gareki. Ki godewa Allah kin rayu da mahaifiyar ki har tsawon lokaci haka, kin ga fiskar ta, kin ji maganar ta, kin ga murmushin ta, haka nan kin ga fushin ta, ga uwa uba ta yi ta miki addu'a kafin rasuwar ta. Akwai wanda mahaifiyar su ke rasuwa wajen haihuwar su, wasu irin mu kuma su na ƙananun yara su ke rasa ta su, wa su kuma sai sun ɗan girma kafin ta rasu. Almuhim shi ne ko da UWA ba ta raye akwai haƙƙin da ya rataya a kan ka wanda idan ka sauke shi a koda yaushe za a dinga isar mu su da ladan"
Wannan karon maganar cikin lallashi ya yi shi "ki yi haƙuri ki dinga yi ma ta addu'a domin abunda ta fi buƙata a wajen ki kenan"...
***
Bayan sun bar Asibitin gidan ta ya kaita dan ta ɗauko kayan ta a cewar sa bai kamata ta zauna a gida ita ɗaya ba a wannan lokaci. Ko da ta shiga ɗaki ta ga hoton su da Innayi da ta ajiye a desk ɗin ta kawai sai ta fashe da kuka, kuka ta ke sosai tana ƙanƙame hoton a jikin ta. Prof Bamalli ganin ta fi minti talatin ba ta fito ba ya sa ya shiga cikin gidan dan ya ga ko lafiya. A nan ya samu Raudha riƙe da hoto tana kuka, ta bashi tausayi haka kuma ta sake shiga ran sa. Sai da ya ƙara ma ta nasiha kafin ta haƙura ta shiga ɗaukan kayan da za ta tafi da su...
Bayan sun iso gidan sa a hankali ta dinga bin sa a baya har su ka shiga cikin gidan. Wata farar mata tsohuwa guntuwa ce ta tare su da fara'arta. Prof Bamalli ya ce "Hajiya Umma ga Raudha nan"
Raudha ta ɗaga ido ta kalli Prof Bamalli wanda yai ma ta alama da ya nuna cewa wannan matar dai ita ce Uwar riƙon sa da ya ba ta labari ɗazu. Hajiya Umma ta kamo hannun ta ta kaita wajen kujera ta zaunar da ita tana tambayarta mi za ta ci, Raudha ta ce a ƙoshe ta ke. Hajiya Umma ma nasiha ta yi ma ta kafin ta nuna ma ta ɗakin da aka shigar ma ta da kayanta ta ce ta je ta yi sallah dan lokacin sallar magariba ya yi.
Bayan ta yi sallah ta zauna ta ɗaga hannu tana yiwa Innayi addu'a, tana yi tana hawaye.
Ba a jima ba Umma ta zo ta kirata akan ta fito su ci abinci, Rhauda ta ce ta ƙoshi Umma ta ce ba ta yarda ba, dole dai ta fita zuwa dinning ɗin, a nan ta haɗu da yaran Prof Bamalli guda biyu babban Aisha Yusrah za ta kai shekara shabiyu sai ƙaramin mai suna Fou'ad ɗan shekara takwas. Ba wani abincin kirki ta ci ba dan abincin ma ɗaci ya ke ma ta a baki dan ta loosing appetite. Da ta gama tana son tafiya ɗaki Umma ta riƙeta da hira, ta sani duk dan ta kawar ma ta da raɗaɗin mutuwar da ta ke ji ne. Su na zaune a falo Prof Bamalli ya dawo inda ya sanar da ita yayar ta Sa'adatu ta kira kuma sun yi magana da ita.
"A ƙauye ta rasu ko?" Ta yi tambayar tana kallon cikin idon Prof Bamalli.
"Ki yi haƙuri Raudha"
Kawai sai ta fashe da kuka. Nan da nan Umma ta shiga rarrashinta tana ba ta haƙuri. Bayan ta tsagaita kukan ne ta ce za ta je ta kwanta Umma da Prof Bamalli su ka ma ta sai da safe. Tana shiga ɗakin wani sabon kukan ta buɗe tana yi a ciki ciki saboda kar su Umma su jiyota, tana kukan har baccin wahala ya ɗauketa...
Washegari ba ta tashi da wuri ba, kuma kasancewar Lahdi ne duk suna gida, bayan sun karya ne Prof Bamalli ya ba wa Raudha wayarta ya ce ta kira Sa'a. Bugu ɗaya aka ɗauka maimakon ta yi magana sai ta fashewa Sa'a da kuka, ita ɗin ma a wajen zaman makokin daurewa kawai ta yi ta shiga ba wa Raudha haƙuri tana danne na ta kukan, bayan ta yi shiru ne su ka yiwa juna ta'aziya kafin ta ba wa Halima wayar dan su gaisa, itama tana magana tana hawaye, Inna Mairo 'yar uwar Innayi ta karɓi wayan itama su ka gaisa, sai aka miƙawa Yawuro wayan dan tun jiya ta ke cewa tana son magana da Raudha.
Yawuro ta fara exaggerating mutuwar
"Allahu Akabar, Auta Allah bai yi za ki gana da mahaifiyar ki ba. Wallahi Innayi ta yi rabo, tana sallah fa ta rasu. Ta yi sujjada aka ɗau ran ta, ai kinga ta yi rabo. Kai Innayi Allah ya jiƙan ki, Allah ya miki albarka Raudha kafin ta rasu kullum sai ta yi zancen ki, ta ce Allah ya..."
Raudha ta fashe da kuka wanda ya sa dole Prof Bamalli ya ƙarɓi wayan ya kashe...
***
Duk yadda ta so Prof Bamalli ya bar ta ta zo gida ya ƙi cewa yai komawar ta Nigeria ba zai dawo da Innayi ba, ta bari idan aka yi hutu sai ta je.
A haka kwanaki su ka dinga tafiya, tun tana kuka kullum har ta sawa kan ta salama ta daina saboda gaskiyar Prof Bamalli ne kuka ba abinda zai ƙarawa Innayi. Ta kan yi hawaye kam amma banda zama ta yi kuka har na tsawon lokaci kamar yadda ta ke yi farko farkon rasuwan. Ko a aji sai da su ka ga chanji tattare da ita kuma sun tausaya ma ta bayan ta gaya mu su mahaifiyar ta ce ta rasu. Tun sati biyu da faruwan abun ta shirya komawa gidan ta amma Prof ya ƙi ya ce ta je ta kwaso sauran kayan ta daga yanzu ta dena zama ita ɗaya. Ba yadda ta iya dole ta haƙura ta cigaba da zama a gidan sa. A hankali ta lura iya zamanta ba ta taɓa ganin matar Prof ba, ranan ta yi ƙaurin baki ta tambayi Umma wanda ta sanar da ita shekaran matar sa biyar da rasuwa shiyasa ma ya ajiye aikin asibiti ya koma koyarwa dan ya samu lokacin kula da 'ya'yan sa. Sai a lokacin ta ji jikin ta ya yi sanyi, ashe fa yadda ta rasa UWA haka Yusrah da Fou'ad su ka rasa ta su. Gaskiyar Prof ne da ya ce ta godewa Allah, tunda gashi waɗannan yara sun rasa mahaifiyar su da ƙananun shekaru. Ta shiga ba wa yaran kulawa tana jawo su jiki, yanzu kan har ta kai sun saba da ita, za ka ga sun zauna su na taɗi har da dariya.
Wasa-wasa har wata biyu ta cika, Raudha su ka fara jarrabawa, duk da dai yanzu ta rage karatun sosai amma duk da haka jarrabawar ta zo ma ta da sauƙi.
Yau su ka ƙare jarrabawar su kuma yau ɗin ne ta sanar da Prof a kan za ta je Nigeria. Yana zaune a Library ɗin sa yana karatu ta sameshi da maganar.
"Na riga na yi booking, flight ɗin mu Jibi zai tashi"
Ta ɗan ɗago ido ta kalleshi da mamaki.
"Ni ma zan je ta'aziyar ko ke kaɗai ki ke son ladan?"
Raudha ta girgiza kai
Har ta tashi za ta tafi ya ce ta zauna.
Ya ce " barin ba ki wani labari. Last year na je wani cafe zan haɗu da wani, sai na ɗaga hannu na kira waiter dan ta kawo min coffee. Na kirata ne saboda ƙaramin gyale da ta yane kan ta da shi ya burgeni, ban ɗauka musulma ba ce sai da ta juyo na ga tabon sallah a goshin ta. Da turancin ta na gane cewa ita ɗin 'yar ƙasa ta ce Nigeria kuma a Nigerian ma Arewa. Na karanta tag ɗin da ke jikin apron ɗin da ta sa na ga an rubuta RAP na yi mamakin wannan suna. Bayan ta kawo min coffee ɗin ne na tambayi sunan ta ta gaya min. Ban sake komawa cafe ɗin ba saboda ayyuka da su ka min yawa. Bayan kamar wata uku watarana ni da yarana mun je sallar Jumma'a a masallacin da ke Roxbury na hango yarinyar ranan. Shigar Atamfa da ta yi ne ya banbantata da jerin matan da su ke tare a bakin masallacin. Tun daga lokacin na ke lura da zuwanta masallacin duk Jumma'ah, wani lokaci na ci karo da ita wani lokaci kuma ba na ganin ta. Na je cafe ɗin da ta ke aiki aka ce ta bar aiki a wajen. Ikon Allah sai ga shi farkon shekaran nan da na shiga wani aji zan koyar sa ga yarinyar nan mai yawan murmushi"
Tunda ya fara magana Raudha ta sunkuyar da kai tana murmushi.
"Tunda na fara koyar mu su ta kuma burgeni saboda ƙwazon ta, lokuta da dama ina son yi ma ta magana amma ina jin tsoron ka da ta fassarani da wata manufa shiyasa na yi shiru na ke son sai na gama karantar ta kafin na gabatar da kai na gareta, kuma Alhamdulillahi na karance ta tsaf" ya ɗanyi shiru yana kallon yadda Raudha ke wasa da yatsunta ya ce "Ban san ko yarinyar nan mai yawan murmushi za ta ba wa tsoho mai 'ya'ya biyu damar gabatar da soyayyarshi gareta ba. Idan son samu ne ya tura magabatan sa wajen 'yan uwan ta"
Ai kuwa Raudha ta tashi da sauri ta bar ɗakin tana murmushi.
Sai da ta shiga ɗaki ta kwanta a kan gado sannan ta fara jujjuya maganar Prof a ranta. Ta san dai ta taɓa ganin shi a Cafe ɗin da ta fara aiki amma ba ta sake ganin sa ba sai da ya fara koyar da su. Ta sani Professor Umar Audu Bamalli na burgeta, kuma kyautata ma ta da yai a watanni biyun nan sun ƙara ma sa kima a idon ta amma gaskiya ba za ta kira hakan da soyayya ba. Ko kuma dai dan ba ta san SO ba ne?
Saƙon sa ya shigo wayar ta a kan ta daure ta bashi amsa.
Ta jima tana shawara da zuciyarta kafin ta tura ma sa reply kamar haka "ka bani lokaci zan yi tunani"...
Wasan ɓuya ta fara yiwa Prof saboda kunyar sa da ta ke ji har ranan da su ka shirya tafiya Nigeria.
A cikin jirgi kujeran su kusa da na juna hakan ya sa duk ta takura da shi.
"Na ga alama ɗan tsoho dai sai dai yai haƙuri"
Raudha ta ji kaman ta nitse saboda kunya. Ta yi Istikhara akan maganar tun shekaranjiyan da yai maganar amma har yanzu ba ta cimma wani matsaya ba.
"Na yi haƙuri ko?" Ya tambaya yana tsareta da ido ta yi saurin girgiza kai
Ya ce "Kin amince kenan?" ta sunkuyar da kai tana murmushi.
Ya ce "Allah ya shige mana gaba"
Ta amsa da Amin...
*RIBAR UWA*
*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*
Chapter 14
(Free book ne)
*A bride*
Jirgin su ya sauka a Abuja wajajen sallar maghrib, a tunanin Raudha a wannan lokacin za su nemi motan Bauchi ko ma na Jos su ka samu su tafi sai ta ga sun nufi cikin gari.
"Hotel a cikin gari akwai tsada" ta faɗa a hankali.
Maimakon Prof ya ba ta amsa sai kawai yai murmushi.
Maimakon Hotel wani Babban gida su ka nufa a Wuse II.
"Gidan abokina ne, tare mu ka yi karatu" ya faɗa dan ya cire ma ta damuwa.
Matar Dr Ahmad ta tarɓeta da kyau. Umaimah da Dr Ahmad auren haɗin gida aka mu su kuma dukkan su 'yan boko ne, dan Umaimah chartered accountant ce, mahaifin Dr Ahmad tsohon Minister ne wanda ya rasu shekaru kusan biyar da su ka wuce.
Bayan ta ci abinci ta yi sallah su ka ɗan taɓa hira da Umaimah kafin ta kwanta, kusan ƙarfe goma ta gota bacci mai daɗi ya tafi da ita.
Washe gari Dr Ahmad ya ba su Driver wanda zai kai su har Misau. Ƙarfe tara na safe su ka kama hanya, sai a lokacin kuma Raudha ta shiga fargaba, bugun zuciyar ta ya ƙaru. Ina ma za ta iya maida hannun agogo baya, ina ma ko da sau ɗaya ne za ta sake ganin Innayi, tana cikin wannan tunani sai hawaye.
"Ya Allah! Kin manta alƙawarin da ki ka min kenan?" Prof ya faɗa da sigar lallashi
Ta girgiza kai tana ƙoƙarin goge hawaye, tanayi wa su na zubowa.
Nasiha prof ya fara ma ta wanda ya sa dole ta haƙura da kukan. Daga baya ma ta sa earpiece a kunne ta kunna ƙur'ani tana sauraro.
Tun da su ka iso Jos ta fara bacci ba ta farka ba sai da su ka wuce Bauchi har sun kusa isowa Darazo.
"Abban Yusrah ashe na jima ina bacci kaman na ga mun wuce Bauchi ko?"
"Da ba ki tashi ba idan mu ka iso goya ki zanyi na shiga da ke ciki. Ta yi saurin rufe fiskarta da gyalenta tana murmushi
"Ko na gwada ne idan mun je?"
"Kayya ni kam" ta dunƙunƙune gefe tana cigaba da rufe fiskarta...
***
Tunda su ka shiga garin na Misau jikinta yai weak, ba ta yi kuka ba amma sai sauke ajiyar zuciya ta ke a kai-akai. Shekara biyu da sati biyar rabonta garin. Akwai 'yan chanje-chanje da ta spotting tun a hanya. Ta dinga yiwa Driver kwatance har su ka iso anguwar su. A dai-dai bakin layin su motar ta tsaya, da ke yamma ne kwalbatin da ke wajen matasa sun kafa majalisa ana ta gulma, ganin dalleliyar motar da ta tsaya gefen su ya sa gaba ɗaya su ka zurawa motar idanu, suna tunanin wa ke da irin motar a garin.
"Ni da Malam Isa za mu samu masallaci mu