Showing 45001 words to 48000 words out of 50413 words
ta so haihuwan mata dan har yanzu ba ta samu 'ya mace ba, yaranta yanzu sun zama biyar duka maza. Abu ya haɗu ya zamowa Sa'a biyu ga bikin suna ga bikin Raudha da za ayi.
Ba laifi an fara yiwa Raudha gyaran jiki wanda Sa'a ce ta haɗata da wata mata da ke yi. Kwana goma da ɗaura aure aka kawo kayan lefe, nan fa aka fara jinjinawa Prof dan ya yi abin kwatance. Akwatuna takwas aka kawo banda jaka manya guda biyu da su ma ke shaƙe da kaya. Tuni Sa'a ta sa aka kai ma ta ɗinki, dan abin ma yai sauri wasu Misau aka ba da wasu Azare wasu a Bauchi. Saboda rashin cika alƙawarin teloli, gashi idan ta tafi chan ba da wuri za ta dawo ba. Duk da haka wasu ba a kai su ɗinki ba.
Raudha ba ta da ƙawaye, iya ka ci class mates ɗin ta ne na Sakandare wanda kusan 90% ɗin su sunyi aure sai na ABU. Ta aika wa wanda za ta iya aikawa kuma yawanci sun ba ta haƙuri akan ba za su samu zuwa ba. Wanda ke Misau kam sun nuna za su zo ko dan ayi gulmarta tunda sun ji mijin na ta a chan America ya ke, wasu har sun fara yaɗa gulmar bature za ta aura.
Kullum sai sun yi waya da Prof yana ƙara jaddada ma ta soyayyar sa gareta tareda nuna ma ta tsananin kewarta da yai. Ita idan yana magana ma kunyar sa ta ke ji tana tunanin yanzu fa sun zama ɗaya tunda an shafa fatiha. Wani lokaci yakan ba wa Umma da yaran su gaisa...
Ranan Jummu'ah aka yi waliman aure, anci an sha kuma anyi sadaka. Tent aka kafa a ƙofar gida aka jera kujerun Roba inda maza da su ka zo su ka ci abinci bayan an sauko daga sallar Jummu'ah abin kamar wani ƙaramin reception. Mata kuma sun cika cikin gida ana ta bidiri. Da yamma aka kira wani Malami yai wa'azi, malamin su Raudhan ne lokacin tana islamiyya.
Ranan ta ci kuka kamar ba gobe saboda kewar Innayi, sai dai ƙaddara ta riga fata...
Washegari aka kai Amarya Zaria, gida ne Babba da ya ke da komai da komai a ciki. Dan haka kayan ɗakin Raudha ma wani ɗaki aka zuba su aka kulle. Washe gari kowa ya watse bayan anyiwa Raudha nasiha. Da yamma Sani ƙanin Prof da matar sa da wata yarinyar su budurwa su ka kai ta Abuja gidan Dr Ahmad, da ke Sani ya riga Prof aure ɗan sa na fari ma yana shekara shatara yanzu.
Jirgin su Raudha bai tashi ba sai ƙarfe goma na daren ranan Litinin. Wayaga Amarya za ta kai kan ta gidan Ango...
***
Shi ɗaya ya zo ɗaukanta, ba ta ankara ba sai gashi da yin abinda ya sa ta ji kunya sosai a airport ɗin. Prof yana zuwa ya rungumeta jikinsa yana ma ta sannu da zuwa, duk nuƙu-nuƙunta haka ta barshi sai da ya gaji ya saketa bayan kusan 3minutes yana rungume da ita.
"Welcome home my beautiful wife"
Ta sunkuyar da kai tana murmushi tareda mugun jin kunyar sa...
Da Bismillah ta shiga gidan Prof a karo na biyu, da ta zo a matsayin baƙuwa yanzu kuma ta zo a matsayin Uwargida.
Tana ganin Umma ta shiga ɓoye fiska saboda kunyar surikar na ta. Umma kam ba ruwanta domin cike ta ke da farin ciki dan ɗan zaman da su ka yi da Raudha ta karanci tana da hankali za ta iya riƙe amanar 'ya'yan marigayiya.
Duk kauɗin Prof dai ya ɗagawa matar ta sa ƙafa saboda shi ba yaro ba ne yasan akwai gajiya a tattare da ita. A yammacin ranan Jumu'ah ne aka gudanar da ƙaramar liyafa a gidan Prof inda abokanan aikinsa lokacin yana asibiti da kuma abokanan sa Malamai da Muslim Community na Boston duk aka hallara aka ci aka sha sannan aka bawa Amarya da Ango gifts. Raudha ma ta gayyaci 'yan ajin su kuma kusan duka sun zo...
Ranan Asabat Umma da Yaran su ka tafi ziyaran kwana uku gidan Uncle ɗin Zainab wato marigayiya matar Prof da ke Connecticut. Ta zo karatu ta zauna a wajen ƙanin Babanta har kuma su ka haɗu da Prof lokacin tana ajinta na ƙarshe Allah ya ƙaddara aure tsakanin su. Umma ce ta shirya tafiyar saboda Amarya da Ango su samu su sake.
A wannan lokaci ne Prof ya samu damar kula da amaryarsa yadda ya kamata, yai ta lallaɓata a hankali har ya samu kan ta kuma Alhamdulillah ta riƙe tarbiyan da Innayi ta ma ta. Asabat da Lahdi duka Prof na tare da Amaryar sa, ko fita baya yi, yana nan yana lallaɓata, yana nuna ma ta tsantsar soyayyar sa gareta wacce ta ke tsakani da Allah babu Algus. Ranan litinin da yamma su Umma su ka dawo saboda makarantar su Yusrah.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya, tun Raudha na jin kunyar Prof tana ɗari-ɗari da shi har ta zo ta sake jiki dan yanzu kam an riga an zama ɗaya ana batun wata uku da 'yan kai.
Da ke yanzu clinical round su ke zuwa ba aji ba, Asibiti mafi kusa da su ta zaɓa ta ke zuwa kuma Alhamdulillah tana fahimtar abubuwan da ake nuna mu su.
*RIBAR UWA*
*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*
Chapter 15
(Free book ne)
*Epilogue*
Rasuwan Innayi ya zo da sauyi da dama, da masu daɗi da marasa daɗi. Kuma dukkan su babu wanda bai ga darasin rayuwa ba.
Raudha tun tana irga watanni da aure har ta fara irga shekara. Kaman Innayi itama ba ta samu haihuwa da wuri ba. Ba ta sa damuwa a ranta ba dan addu'ar ta shine Allah ya bata 'ya'ya ma su albarka 'yan'yan da za su jiƙanta su ji tausayinta, 'ya'yan da za su zamowa musulunci abun alfahari.
A ƙarshen shekarar su ta uku da aure ne ita da Prof su ka tafi aikin Hajji. Aikin Hajjin da sai wanda Allah ya kira ya ke zuwa. Duk yadda ita da Baffah su ka ci burin kai mahaifiyar su Hajji Allah bai ƙaddara hakan ba.
Bayan dawowar su ne su ka shirya zuwa Nigeria sai dai laulayin ciki da ya sata a gaba ya sa su ka janye tafiyar zuwa wani lokaci.
Tundaga laulayi Raudha ta fara jin tsoron haihuwa, ta ke kuma jinjinawa Innayi da ma duk wata Uwa. Ashe ciki da haihuwa ba sauƙi, a hakan ka gama haifan yaro ko yarinya su zo su muzguna ma ka ko kuma su ɗaukeka ba a bakin komai ba.
Laulayi tun watan farko har sai da ta shiga wata na biyar kafin ta fara jinta garau. Tana samun kulawa sosai a wajen Mijinta da Umma. Duk wani aure ana samun saɓani itama natan akwai sai dai soyayya, haƙuri da addu'a su suka zaunar da su lafiya ta inda ba a taɓa jin kan su ba. A yayi yawa shine ka ga anyi fushin kwana biyu amma yawanci a yini ake faɗa a kuma shirya.
Musabbabin son zuwanta Nigeria ma saboda Idrissa ne. Har ga Allah ba ta ma sa fatan da zai samu iftila'in da ya faɗa ma sa ba sai dai dama hakan yana daga cikin ƙaddarar sa. Prof ya riga ya ɗage tafiyar sai bayan ta haihu amma ta so ta je Nigeria ta ga yadda rayuwa ta juya da ɗan uwan na ta...
Tun bayan auren Raudha Idris bai sake zuwa Misau ba. Kunyar 'yan uwan sa ya ke yi yana kuma ƙoƙarin haɗa kuɗin da ya ci. Ita kam Faiza ko ajikinta dan nunawa ta yi ba ta damu ba gida ne dai za su tare tunda an gama. Ba yadda ya iya haka su ka koma gidan watanni goma shaɗaya da rasuwan Innayi kenan.
Komawar su ba da jimawaba aka yiwa Idris transfer zuwa Maiduguri, haka ya tafi ya bar Faiza a Bauchi duk ƙarshen wata yana zuwa hutu.
A wani hari da 'yan Boko Haram su ka kai wa bankin da Idris ya ke aiki ne iftila'i ta faɗawa Idris. Bomb aka jefa mu su lokacin da ta tashi ta yi awun gaba da rayuwan wasu yayinda wasu kuma su ka rasa wani sassa na jikin su ciki har da Idris wanda ya rasa hannunsa na hagu.
Da farko ma da aka ji labarin an ɗauka ya rasu sai daga baya aka gane da ransa. Daga Maiduguri aka fara jinyarsa kafin su Ado su ka dawo da shi Bauchi ƙarshe dai Ado da Iro ne su ka sai da gidan sa aka yi duk wani hidimar asibiti da shi. Sai gashi Idris ɗan gaye ya koma mai hannu ɗaya, ɗaya hannun dumgulmi ne kawai a wajen kafaɗar sa. Tashin hankali Idris ya shiga ba kaɗan ba, ta ina zai fara rayuwa a haka.
Bayan an sallameshi Misau aka wuce da shi, ɗakin zaure aka bashi dan ɗakunan ciki an gyara an sa haya a ciki. Tun yana asibiti ya fara ganin izina domin matar sa Faiza 'yar ƙwalisa da ya ke ji da ita kamar zinare ko diamond ita ne dai ta fara nuna ma sa ƙyashi saboda yanzu ya koma mai hannu ɗaya. Ya kirata ta zo Misau amma ta ce ba za ta iya zama a Misau ba ga kuma aikinta. Tunda ya bar Bauchi watanni huɗu da yai a Misau ko mai kamar Faiza bai gani ba. A wata na biyar ne sai ga ɗan saƙo wani ƙanin ta wai ya zo karɓan takardar sakin Faiza. Ya ɗau waya ya kira Faizan dan ya ji dalilin wannan saƙo.
"Kai ma Idris tundaga asibiti ya kamata ka sani auren mu ya ƙare kai ne dai ba ka sa shi ya zama offficial ba. Na ɗauka rashin zuwana Misau zai sa ka gane amma ka ƙi, yanzu kam haƙurina ya ƙare ka turo min takardata"
Tsabar takaici kasa magana yai sai hawaye.
"Ina I love you? I'll never leave you, I promised to be with you till the end of my life ɗin su ka shiga"
Dama soyayyar gaskiya ce ke tsayawa through trying times through thick and thin. Kwata kwata ba su gina soyayyar su tsakani da Allah ba.
Ita Faiza ta ga ɗan farin bafulatani zubin larabawa shi kuma Idris ya ga wayayyiyar mace 'yar ma su kuɗi.
Idris bai ba ta takardar ba sai ma shirya zuwa Bauchin da yai dan ya ga ko dai za ta iya kallon sa ido cikin ido ta ce za ta rabu da shi. Washegari ya wuce Bauchi yanzu har ya fara sabawa da hannu ɗayan. Tarban walaƙanci ya samu a gidan su Faiza domin ko falo ba a shiga da shi ba, a tsaye acikin compound ɗin su Faiza ta fito ta sameshi ta tabbatar ma sa da maganarta na son rabuwa da shi da ta ke yi. Ya ce ma sa ko za su rabu sai dai ta bar ma sa Mufeedah tunda dai ita ɗaya ce rabon da ke tsakanin su.
"Mufeedah ba za ta zauna a cikin talauci ba, zan dinga turota hutu ko da na sati ɗaya ne"
Idris ya rasa bakin magana domin ba shi da ta cewa, shi ya ba ta soyayya ya ba ta kulawa ya darajata fiye da kowa na sa shiyasa yanzu da ta gujeshi ba shi da ta cewa.
A wajen ya furta ma ta saki ɗaya sannan ya bar gidan cike da takaici...
Duniya ta koya ma sa darasi, gashi Innayi ta yi ma sa nisa balle ya nemi gafaranta duk da kuwa Sa'a ta nuna ma sa Innayi ta yafe ma sa kafin ta rasu amma har wayau ya kasa samun nitsuwa.
Ganin Lafiya ta samu ne ya shiga neman aiki tunda dai tun jinyar sa su Ado ne ke ciyar da shi da kuma buƙatun sa na yau da kullum.
Shekaran sa biyu da rasa hannunsa ɗaya ya samu aikin koyarwa ya fara yi, albashin dai bai kai na sa na da ba amma Alhamdulillah he will manage.
Wata tara Cif da sakin Faiza ya ji labarin ta yi aure. Ba ma Bauchi mijin ya ke ba a Abuja ya ke dan haka ta tarkata ta tafi ma sa da 'ya chan Abuja. Tun rabuwar su ma sau ɗaya ta sa aka kawo Mufeedah wanda sati ɗaya na cika ta turo aka ɗauketa.
Duniya kenan!
***
'Yan biyu Raudha ta haifa mace da namiji, duk da ta samu kulawa sosai daga wajen ƙwararrun likitoci hakan bai hanata jin zafin haihuwan ba.
Umma ta shiga kula da ita da yara. Ranan suna Prof ya raɗawa yara sunan Aliyu da Faɗima. Raudha ta ji daɗi sosai dan bai gaya ma ta sunan da yai niyyan sawa ba sai ranan suna.
Haidar da Noor ne inkiyar yaran.
Yaran su na wata uku su ka je Nigeria dukkan su. A Zaria su ka sauka inda su ka yi sati kafin Raudha ta je Misau.
Tana hawaye Idris na yi haka ya riƙe hannunta yana ba ta haƙuri yana neman yafiyarta. Ta nuna ma sa ta yafe wancan maganar da ta yi ma ranan ta yi ne cikin fushi.
Sati ɗaya ta yi a Misau kafin ta je Azare ta yi wa sa'a kwana biyu sannan ta koma Zaria, watan su ɗaya su ka koma.
Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya...
A ɓangaren Ado kuwa a shekarar da Innayi ta rasu a shekarar ya samu lecturing a Legal yana haɗa masters na shi ya samu appointment.
Adamu Buba Pakkari yana ji da kan sa a yanzu da ya ke jinsa cikakken mutum da ya bawa arba'in baya.
Yadda sabbin lecturers ke kauɗi idan 'yan mata na tururuwan su haka shima Ado bai tsira ba daga wannan hali. Wani jan aji yake yi yana tafiya da tinƙaho da jiji da kai.
A shekaru biyar da ya fara lecturing ya shiga neman Sadiya. Shekarun sa arba'in da takwas amma jinsa ya ke kamar ɗan shekara talatin. Sadiya Mustafah ta yi ƙaurin suna cikin ɗalibai, yarinya ce da ta ke ji da kanta a matsayinta na wacce ta yi rayuwa a Abuja. A zahiri a Mararraba su ke zaune amma kullum taɗin ta Abuja su ke a nan aka haifeta a nan ta taso, sau uku da ta taɓa shiga garin Abuja ya sa ta ke taɗi tamkar ta jima a ciki, abu da waya tuni ta browsing sunan anguwanni da manyan wajaje na cikin garin tana yiwa mutane taɗi tana sako su, su kuma na ganin ai ita ɗin a Abujan ma a anguwannin ƙusosin gwamnati su ke. Mahaifinta ɗan Harɗawa ne amma ya jima da komawa Mararraba inda ya ke sai da kifi.
Sadiya rayuwar ƙarya ta sawa kan ta shiyasa tun da ƙarancin shekarunta shabakwai ta fara tara samari daga baya ta buge da bin manyan mutane. Tunda dai ta fara shafa mayukan dubu ishirin dubu talatin.
Tana da hasken ta amma da ta fara shafa mai sai ta koma ita ba baturiya ba ita ba zabiya ba, fiskan yai wani yellow da shi. Ga wanda bai san kyau ba Sadiya za ta burgeshi amma wanda ya san kyau ya san Sadiyan da ta fi ta yanzu kyau nesa ba kusa ba.
Tunda ta shigo CLIS ta ke gwara samari da lecturers. Ado ma ya tsinci kan sa cikin ma su neman ta. Yana da maƙo shiyasa ba sa shiri da ita, abu ɗaya ya sa ta ke biye ma sa shine kyaun sa. Tana bala'in son namiji fari dogo mai dogon hanci sai gashi Ado ya haɗa. Ba dan kyaunsa ba da tuni ta rabu da shi dan baya iya ba ta dubu goma, iya kacin sa dubu biyu dubu biyar ita kuma tafi ƙarfin wannan dan ko kuɗin shower gel da ta ke amfani da shi bai kai ba balle uwa uba mayukan da ta ke shafawa...
Yau ma su na tare cikin motar sa yana lallaɓata a kan yaushe zai sake samunta tana gaya ma sa sai wani sati wayar sa ta shiga ringing. Ya duba wayan ya ga sunan Jamilah yai saurin mai da wayar aljihu.
"Ka ɗauka mana" Sadiya ta faɗa tana maƙe muryanta
"No zan kira idan mun rabu its not important"
Namiji kenan. Matar sa da ya bari da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe ya ke cewa not important saboda ya ga budurbazar.
Ganin an sake kira ya sa shi sa wayan a silent ya cigaba da lallaɓa Sady har ta haƙura akan za su haɗu jibi, bai tafi ba dan ta fara sarrafa shi yadda zai samu nitsuwa. Yana nishin jin daɗi a cikin mota matar sa na nishin wahala a gida...
Jamilah tun safe ta fara naƙuda ta je asibiti amma haihuwan shiru, su ka ce ta koma gida ta yi ɗan exercise zuwa yamma sai ta dawo. Cikin ya ma ta nauyi gashi jiki ya girma dan yanzu haihuwarta na tara kenan za ta yi a shekarunta arba'in da ɗaya.
Ta fito da wankinta da na yaran Aisha ta farayi sai da ta gama ta shiga gyaran ɗaki, still har bayan maghrib haihuwan bai zo ba. Ƙarfe tara na dare haihuwan ya tashi gadan-gadan. A lokacin da duk wani miji na ƙwarai indai ba kasuwanci ya ke ba ko aiki ya zama yana tareda iyalinsa shi Ado yana wajen Budurwa yana shan minti.
Aisha ce ta ɗau wayar Jamila ta fara kiran mijin na su ko zai zo da mota a kai ta asibiti sai dai ya ƙi ɗauka. Ganin bai ɗauka ba ta ɗauko na ta wayar ta shiga flashing dan ba kuɗi, daga baya ta ci bashin mtn ta shiga kira amma shiru. Da haihuwan ya zo daf ne har ta sa yara su kirayo mai Napep ta fasa saboda kan yaro ya fara fitowa ta ce yara su shiga maƙota su kira Anty Ladi wanda ta girme mu su sosai dan za ta yi shekara hamsin haka.
Anty Lahdi da Aisha su ka karɓi haihuwan jaririya, bayan kaman minti shida sai ga wani na shirin fitowa su kan su ba su san 'yan biyu ba ne. Wannan karan Jamilah ta wahala sosai yayinda ta challah ƙara lokacin da jinjirar ta gama fitowa. Suna kan kula da yaran ba su san Jamilah rai ya yi halinsa ba. Sai da Anty Lahdi ta fara magana tana faɗin "Jammy ashe 'yan biyu ne shiyasa cikin ki yai girma" ta tsaya lokacin da ta ga fiskar Jamilar.
Ta ɗaga hannun Jamilah ta ji shi yaraf, ta