Showing 48001 words to 50413 words out of 50413 words

Chapter 17 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1792

kai kanta daidai ƙirjin Jamilah amma ba alaman bugun zuciya. Ta sa hannun ta a wajen tsintsiyar hannunta ba ta ji motsin jijiya ba. Nan ta saki Innalillahi...






Ado sai ƙarfe goma da minti arba'in na dare ya baro bakin hostel bayan Sady ta taimaka ma sa ya yi release. Ya nufo gida zuciyar sa saƙayau yana jin shi lafiyayyen namiji. Sai da ya kusa gida ma ya tuna ashe ɗazu matan sa sun kira shi yai tsaki dan ya san ba zai wuce haihuwa Jamilah za ta yi ba, idan kuwa haka me ai akwai keke Napep da za su iya kira ya kai su Asibiti miye za su wani dameshi da kira.
Yana nufo ƙofar gida ya hango Iro da Idrissa da maƙotansa guda biyu. Nan jikin sa yai sanyi. Yai parking mota ya fito a hankali.
Iro ne ya tareshi da faɗa akan ina yaje ana ta kiran sa ya ƙi ɗauka.
"Mi ya faru ne?" Ya faɗa yana ɗarɗar yayinda zuciyarsa ke gaya ma sa ƙila Jamilah ce ta haihu ɗan ya koma.


Malam Shu'aibu da duk ciki ya girme su ne ya zaunar da Ado a kan dakali ya fara ma sa nasiha akan mutuwa sannan ya sanar da shi mummunan labari. Jamilah ta haihu kuma ta rasu, ba nan abin ya tsaya ba duka 'yan biyun sun koma, ɗayar ko minti biyar da rasuwan Jamilah ba ta yi ba ta rasu ɗayar kuma har an yiwa Jamilah da 'yar uwarta wanka itama ta cika a bayan yayar Jamilah da ta goyeta tun zuwan su saboda kuka da ta ke yi.


Gumi ya fara ketowa Ado. Ba abinda ya ke tunawa irin yana chan yana saɓon Allah Malakul Maut ya ziyarci gidan sa ya ɗau rayuka uku. Ashe haka ake mutuwa ba sallama. Jamilah Uwargidan sa wanda akan ta ya fara sanin 'ya mace, sai gashi yau tana fama da naƙuda shi ya tura ƙafa ya tafi wajen wata karuwa yana jin daɗi, jin daɗi na lokaci kaɗan na 'yan wasu mintuna da ba su wuce ishirin zuwa talatin ba.


Jiki a sanyaye ya shiga gidan tareda Iro da Idris. Yana zuwa ɗakin Jamilah ya ga gawar mutum uku kwance nan ya yanki jiki ya faɗi. Da ya farfaɗo kuka ya ya fara wiwi kamar ƙaramin yaro yana faɗin "kaicona kaicona da son zuciya"...


Ba wanda bai ji rasuwan Jamilah ba. Asiya matar Iro kam kusan ƙaramar hauka ta yi dan tuni ta ji tsoron mutuwa ta fara fallasa abin da ta aikata na zuwa wajen boka da ta yi dan ta mallake Iro, shiyasa tun shekaru da su ka wuce da ya taɓa zancen aure ta sa aka rufe bakin sa ya rufe zancen ƙara aure har yau bai ma sha'awar auren.
Da ke da sauran imani a zuciyarta ya sa mutuwar ya girgiza ta har ta fallasa kan ta tana neman tuba a wajen Allah da wajen Iro...






***


Idan mutuwar Innayi bai ishi Ado ishara ba ga mutuwar Jamilah da 'yan biyunta wanda ya sa yai karatun ta nitsu wa kan sa da duniya wacce ta ke ba matabbata ba. Ba za ace ya dena saɓo ba saboda mu 'yan Adam ne muna da rauni. To amma tun rasuwan Jamilah ya watsar da neman mata da ya ke yi ya rungumi Matar sa Aisha abu da jiki da jini da kuma sabo da mata biyu. Shekaran Jamilah biyu da rasuwa ya auri wata bazawara da mijinta ya rasu, ba wata babba ba ce dan shekarunta ashirin da takwas kuma ɗan ta ɗaya.




Iro ya saki Asiya inda ya ƙara aure ya auri budurwa 'yar ƙauyen Baban sa wato Ajili , shekaranta shabakwai, to abu da yarinya da kuma yara har bakwai da Asiya ta bari dole dai ya dawo da Asiya bayan shekaran su ɗaya da rabi da rabuwa. Ta nitsu dan ta rungumi ƙaddararta, tana kaffa da kaffa da mijinta tana kuma ƙoƙarin danne kishinta ga amaryarta Na'ima wacce ke ji da ƙuruciya. Anci sa'a Na'iman ba ta da wani karambani da falli tana mutunta Asiya sosai sai Asiyar itama ta ci girma tana ƙoƙarin tare duk wani kafa da zai jawo matsala tsakanin su.




Idris bai yi aure da wuri ba dan sai da yai shekara biyar da rabuwan su da Faiza sannan yai aure. Wata student ɗin sa ya aura wacce ta nace ma sa akan tana son sa, kasancewar sa mai hannu ɗaya bai dameta ba ita dai tsakani da Allah ta ke son sa, tana gama NECO aka yi bikin su gashi yanzu Allah ya azurtasu da ɗiya mace wacce ta ci sunan Innayi suna kiran ta Ummi. Wani madaidaicin gida Idris ya siya a ɗan gefen layin su bayan ya ɗau shekaru yana tara kuɗi. Gidan dai zai kai shekaru goma da gina shi mai gidan ma matsi ce ta sa shi sayar da gidan amma gidan na da kyau, ɗakuna uku manya ne agidan. Su na nan zaune lafiya da matarsa Khadija da baby Ummi.
Bayan ya samu iyali ne kuma ya samu gida, ya je Abuja ya karɓo Mufeedah. Ashe Mufeedan ba jin daɗin gidan ta ke yi ba, yaran gidan ba sa son ta kasancewarta Agola sai su dinga hantarar ta. Fa'iza ba ta iya magana dan ba ta da wani daraja a gidan. Alhaji Khalill ba mazauni ba ne kuma ya hanata aiki ga shi tunda ya gane dan kuɗin sa ta aureshi ya ke ma ta walaƙanci, ga uwa uba Uwargidan ta wanda ta ke ji da bala'i. Sau biyu Alhaji Khalil ɗin na ƙara aure tana koran su da masifarta. Wannan Fa'izar ma tayi-tayi ta tafi ta kasa amma ba za ta gushe ba dan sai ta raba auren duk da ma ba ta da damuwa tunda ta san abinda ta yi Fa'iza ba za ta taɓa haihuwa da Khalil ba. Ita ɗin ce dai magajiyar gida mai 'ya'ya biyar, biyu maza uku mata...








Shekarar Innayi goma da rasuwa mijin Halimah Alhaji Nuhu ya rasu. Ga shi ba wani abu ya bari ba amma a hakan sai faɗa ake yi akan gadon sa da 'ya'yan da ya bari da 'yan uwa. Su gani su ke Alhaji Nuhu ya ɓoye kadarorinsa a wani waje amma Halima ta san Alhaji Nuhu ba shi da komai, cikin zaman auren su ta gane kuɗin Alhaji Nuhu da yazo lokaci guda yai tashe har ya zo ya gushe ba komai ya ja haka ba sai bin malamai da Alhaji Nuhun yai a ƙuruciyar sa, aka bashi layar da za ta bashi sa'a a kasuwancin sa. Abin ya ma sa amfani amma na lokaci kaɗan dan kwata-kwata arziƙin sa bai wuce na shekaru bakwai ba komai ya rushe ma sa.


Abun mamaki ko wata biyu ba ta yi da fita takaba ba ta samu manema. Ciki ta zaɓi Malam Muhammad wanda ya kasance headmaster a Primary school. Rashin haihuwa ya sa duka matan sa ke rabuwa da shi. Ya nemeta ne tunda shi baya haihuwa ita kuma tunda ta riga ta hayyafa rashin haihuwa ba zai dameta ba.


Rayuwan su da Malam gwanin sha'awa, shi mutum ne mai riƙo da addini shiyasa tun zuwanta ya duƙufa da koya ma ta karatu saboda ta yaƙi jahilci. Ita kam tunda ta yi aure ba ta sake waiwayar ƙur'ani ba iya kacinta karatun sallah. A lokacin rasuwan Jamilah ma da aka rarraba ƙur'ani dan a karanta ba abin kirki ta yi ba tunda ba iyawa ta yi ba. Sai yanzu ta ke kaicon rashin bin maganar Innayi, ta ƙi karatun Arabi ta ƙi na boko ta buge da guguwar 'yan matanci wanda ya kaita ga ƙarewa da Alhaji Nuhu wanda ko kaɗan bai san darajar ta ba har ya rasu.




***






Shirye-shirye su ke na dawowa Nigeria gaba ɗaya. Cikin shekaru goma shabiyu da aure sun samu cigaba da ɗaukaka. Umma ta rasu lokacin 'yan biyun Raudha na shekaru biyu a duniya. Bayan 'yan biyu ta haifi Abdullah sai Muhammad wanda a haihuwar sa ne ta samu complications har aka ba ta shawaran idan da hali ta tsaida haihuwa saboda lafiyarta. Prof bai ɓata lokaci ba ya amince dan lafiyar matarsa ya fi ma sa komai. Itama ɗin yara huɗu kam sai dai godiyar Allah tareda addu'ar Allah ya raya ma ta su da imani. Ko a haka ita UWA ce tunda Allah ya azurtata da haihuwan, wasu nema su ke ruwa a jallo amma Allah bai ba su ba, wasu kuma ɗaya Allah ya mallaka mu su...


Last year aka yi bikin Yusrah wanda ɗan ƙanin Baban ta Sani ta aura mai suna Habib. Prof ne ya ɗauko shi karatu shine ya ke zaune da su. Shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin sa da Yusrah ƙarshe ta koma Soyayya.
Yusrah ta fara residency ɗin ta dan itama layin Prof da Mom Raudha ta bi ɓangaren Raudhan ma ta ɗauka wato gyneacology. Shima Habib ya samu aiki a inda yai internship na shi dan haka suna zaune da matar sa lafiya.


Yana latsa wayar sa yana ganin yadda Raudha ke faman tattara kaya tana yi tana mitar hayaniyar yaran da ta ke ji a ƙasa.


"Baby take it easy, tafiyar da saura fa"


"Kai ka ke ganin da sauran lokaci 5days fa ya rage gashi ko rabin shiri ba a yi ba"


Murmushi yai ya ajiye wayar ya zago bayanta ya rungumeta yana faɗin " ba na so kina ɗaga hankalin ki. All that matters shine Allah ya kaimu gida lafiya. Kin ji Baby Love"


Ya ƙarisa maganar yana kissing wuyanta, ganin bai barta ba ne ya sa ta ce
"My Ɗan Tsoho akwai aiki a gaba na fa"


Prof ya ƙanƙance murya ya ce " to a fara sallama na tukun"


Dariya ta yi kafin ta shiga biye ma sa dan ko ta ƙi ma ba bari zai yi ta yi aikin ba.


Sai da ya shimfiɗa ta kan gado ya je ya kulle ƙofa dan yaran na su sai a hankali ba dai rigima ba. Ai kuwa suna tsaka da raya sunna Noor ta fara buga ƙofa tana kukan sakalci tana kiran Mom Mom... Jin ba a amsa ma ta ba ya sa ta koma tana cewa Haidar Mom na banɗaki idan ta fito za ta gaya ma ta abinda ya ma ta, kuma sai Mom ta rama ma ta. Shi kuma Haidar na ma ta gwalo yana faɗin sai ta faɗa ɗin shima zai ce ta sha ice cream ɗin da Mom ta ajiye a fridge.


Prof da Raudha su ka yi murmushi su ka cigaba da aikin lada...






Watan su biyu da settling a Nigeria aka buɗe asibitin Prof wanda dama tun kafin auren su da Raudha ya fara ginin, a hankali a hankali har komai ya kammala aka zuba kayan aiki da duk abubuwan buƙata. Sunan matar sa Zainab ya ke son sawa amma auren Raudha da yai ya sa shi chanja ra'ayin sa. Ita kan ta Raudha ba ta san sunan da zai sa ba kenan sai da ta je bikin buɗe asibitin ta ga sunan da aka rubuta.
Duk 'yan uwanta sun halarci Bikin kuma su ma sun yaba da karamcin Prof da wannan suna da ya sawa asibitin sa. Dr Ambi ma ya zo da iyalen sa dan tun bayan aurenta da Prof su ka ƙulla zumunci da shi, matsayin sa na wanda ya taimakawa Raudha ya sa Prof ke darajashi sosai. Ya yi retire ya koma mahaifansa a Kano.




*FAƊIMA INNAYI MEMORIAL HOSPITAL*




"Ɗan tsoho na" ta kira a hankali hawaye na zubowa a idonta. Prof ya so ta, ya ƙaunaceta, ya darajata, tun da ta aureshi duk Jummu'ah sai ta yiwa Innayi da Baban ta sadaka, tun kafin ta ma sa maganar yin sadaka ma shi ya fara ma ta saboda shima abinda ya ke yiwa na sa iyayen kenan duk Jummu'ar Allah. "Raudha matuƙar Ina raye zan mu su abinda za a tura mu su lada a kabarin su, saboda nima watarana zan je inda su ka je kuma zan ji daɗi ace nawa 'ya'yan su na min sadaƙatul jariya"
Ba abinda za ta ce sai dai Allah ya saka ma sa da alkhairi ya sa su tashi a Aljannah a matsayin mata da miji.


"Bana son kuka Baby na, idan ba haka ba a gaban mutane zan goyeki na yi ta lallashi" ya faɗa yana share ma ta hawaye da babbar yatsar sa.


Ba ta san lokacin da ta saka dariya ba musamman da ta tuno shekarun baya kafin auren su da ya taɓa magana makamancin haka. Shima ya sa dariyan yana hamdala a ransa. Raudha ta zamo ma sa abin tinƙaho, ko da wasa bai taɓa dana sanin aurenta ba sai ma hamdala da ya ke yi da Allah ya bashi ita a matsayin mata... Rayuwa kenan!




Addu'ar Innayi ta karɓu a kan 'ya'yan ta, sun fuskanci ƙalubalen rayuwa bayan rasuwan ta amma daga ƙarshe Allah ya shirya ma ta su kaman yadda ta yi ta mu su addu'a a koda yaushe Lokacin da ta ke raye.


*ke ma UWA ka da ki gajiya da yiwa 'ya'yan ki addu'an shiriya, ko ba daɗe ko ba jima Allah zai amsa addu'ar ki. May be kina raye, may be kuma sai ba kya nan. Allah ya albarkaci yaran ku amin, muma Allah ya bamu mijin ya kuma azurtamu da 'ya'ya ma su albarka Amin*






*Alhamdulillah!*


*a nan na kawo ƙarshen labarin RIBAR UWA. Darasin da ke ciki Allah ya bamu ikon waiwayar su mu gyara a cikin tamu rayuwar. Kurakuren da na yi Allah ya yafe min. Duk wanda su ka min addu'a saboda yadda labarin ya shigesu Ina godiya kuma nima ina addu'ar Allah ya biya muku buƙatunku ya kuma gafartawa iyayen ku Amin*




*akwai paid story da zan yi nan ba da jimawa ba, ina fata za ku yi supporting ɗina kamar yadda ku ka yi a Sakatariya ta da kuma Tsohuwar Soyayya*




*jinjina da godiya ga duk wanda ya karanta labarin nan, haƙiƙa na ji daɗin yadda ku ka yi ta bina da addu'o'in ku. I'm happy*






*Ta ku Azizat*






********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels


WhatsApp Number: 08138873799




Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login