Showing 18001 words to 21000 words out of 50413 words

Chapter 7 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

1781

tuyar. Tana gama addu'o'inta ta kwanta daga nan kuma bacci mai nauyi ya ɗauketa.


Hayaniya da kururuwa ne ya fargar da ita daga baccin da ta ke yi wanda ba dan koke-koken da ta ke ji ba da sai ta ce baccin da ta yi ya ma ta daɗi sosai.
Ƙarfe shaɗaya da wani abu ne na safe lokacin da ta farka. Da sauri ta fito daga ɗakin jin kamar muryan Auta ke kuka.


Jamilah ne da Raudha a tsakar gidan yayinda Raudhan ke ta kuka tana birgima ita kuma Jamilar na ƙoƙarin riƙeta.
Ɗazu aka kira Ado a waya ake sanar da shi gameda hatsarin shine ya fita dan ya je ya sanar da Iro su je su karɓo gawan Baffah.


Fitar shi ke da wuya sai Jamilah ta fito ta samu Raudha a tsakar gida tana wanke-wanke shine ta sanar ma ta, da ta san haka Raudhan za ta birkice da ba ta yi saurin sanar ma ta da wannan mummunan labari ba.


"Lafiyah? Miyake faruwa?" Innayi ta faɗa cikin yanayin tsoro.


Raudha ta ɗago jajayen idanun ta ta kalli Innayi ta ce "Baf..Baffah, Innayi Baffah"


"Mi ya sameshi?" Ta faɗa zuciyarta na bugawa da ƙarfi ƙarfi kamar zai bulluƙo. Tun kafin ace komai idonta ya fara fitar da hawaye domin duk abunda zai sa Raudha irin wannan rikicewan to mummunan abu ne.


Da Raudhan da Jamilar duk ka sa furta komai su ka yi yayinda jikin Innayi ya mutu murus, cikin ƙaramar murya ta ce "ba zai dawo ba ko?"
Raudha ta faɗa jikinta ta cigaba da kuka...




Kafin Yamma an kawo gawan Baffah wanda ya sa gidan ya kuma birkicewa da koke-koke, abin mamaki ba wani ciwo ya ji ba dan buguwa ce yai a kai sai kuma kafaɗarsa da ya ji ciwo. Mutuwa ba ruwanta da ciwo ko rashin ciwo, lokacin mutum na cikawa ta ke ɗaukan sa.
Zuwa ƙarfe biyar da rabi aka kai Baffah makwancinsa, har lokacin kuwa ba abinda Innayi ke yi sai hawaye tana faɗin "Baffah na, Muhammadu na, na yafeka duniya da lahira, yadda ka faranta mini rai Allah ya sa Aljannah ce makomarka"
Mutane da dama sun ga jarumtar Innayi dan ko kaɗan ba ta yi wani kururuwa ko tashin hankali ba.
Idan ana yi ma ta ta'aziya kuwa sai ta fara cewa "shi kan ya huta ai, dama duniya ba ta dameshi ba gashi ya barta lafiya"


Raudha ce tafi kowa birkicewa dan lokacin da ta ga gawar Baffah sai da ta suma... Baffah kam ya riga ya tafi sai dai labari.




***


Rayuwa ya cigaba da tafiya, yayinda mutuwar ta jijjiga Innayi da Raudha sosai, sauran 'yan uwa da abokan arziƙi sun ma fara mantawa da mutuwar domin kowa ya cigaba da daily activities ɗin sa yadda ya saba...




Innayi ta leƙo ɗaki a karo na uku dan ta tashi Raudha wanda take kwance tuntuni ta ƙi fitowa.
"Auta dan Allah ki fito ki shirya ki tafi makaranta, sati biyu kenan fa da komawar ku"




Daga inda ta ke kwance ta ce "ba zan je ba"


Innayi ta sauke ajiyar zuciya ta shigo ɗakin. Ta sani har yanzu mutuwar Baffah bai gama sake jikin Raudha ba dan kusan kullum sai ta yi kuka musamman idan ta tuna irin alkhairin Baffan wanda har yanzu cikin sauran yayunta babu wanda ya kwatanta ko rabin abinda Baffan ke mu su ita da Innayin.


"Haba Auta, a haka za ki zama likitan?"


"Innayi na yafe zuwa makarantar, ina ce nan nan Baffah ya gama haɗa degree, shekaru biyar cur yai a ATBU ya zo yai bautar ƙasa shekara ɗaya amma ko amfani da bokon bai yi ba ya bar duniyan"


Innayi ta yi murmushi mai ciwo wanda ya sa hawaye su ka zubo ma ta. Ta ce "Auta ko bai amfana da boko ba ni na amfanu da shi, kuma duk dan ya faranta min rai ya ke karatun saboda ya cika min burina na samun 'ya'ya ma su ilimin zamani. Har na bar duniya ba zan taɓa manta cewa ɗana mai ilimi ba ne"


Kuka ya ci ƙarfinta domin an kwana biyu ba ta yi kuka saboda tunowa da ɗan na ta ba.
Raudha ta tashi zaune ta fara sharewa Innayi hawaye ta ce " ki dena kuka dan Allah, zan je makaranta, Insha Allahu zan yi ilimi ni ma kuma za ki yi alfahari da ni"...


Sai da ta gama shiryawa kusan ƙarfe goma na safe ta buɗe akwatin kayanta ta ɗauko wani file wanda ajikin file ɗin harda bushashshen jini ajiki. Ta shafa file ɗin tana faɗin "Allah ya haskaka kabarinka Yaya"
Takardun bokon Baffa ne a file ɗin tundaga shedar gama primary har zuwa certificate na NYSC. Ta ƙurawa certificate ɗin ido inda sunan Bafffah ke rubuce a jiki ɓaro-ɓaro MUHAMMADU BUBA PAKKARI sai dai shi ma'abocin sunan ba ya duniya wanda ya maida takardar marar amfani, second class ɗin da ya fita dashi a makaranta iya duniya ta tsaya bai kai lahira ba.


"Insha Allah zan yi karatu sosai Yaya kuma zan kula da Innayi. Zan gyara ma ta ɗaki kuma zan kai ta Hajji kamar yadda ka ke so" ta kissing takardar ta maidashi cikin file sannan ta sa a akwati ta rufe ta fice daga ɗakin domin ta wuce makaranta...




Tundaga wannan rana Raudha ta dage da karatu kuma Alhamdulillah tana ɗauka sosai. Chemistry ɗin da ba ta ganewa yanzu ya zame ma ta favourite subject ɗinta saboda yadda ta ke fahimtar sa sosai...




Cikin ikon Allah sai gashi har Raudha ta shiga aji shida har ta fara zana jarrabawar Waec a lokacin ne kuma ake ta kan shirye-shiryen bikin Ado wanda ke shirin ƙara aure. Shi ɗaya ya ke shawara da kan sa shiyasa ko da yai zancen ƙarin auren ba wanda ya tanka ma sa illa addu'ar Allah ya sanya alkhairi da 'yan uwan sa su ka ma sa...




Amarya Aisha da ta zo farko-farko ta fara karanbanin yiwa Innayi ladabi da biyayya a shirinta na neman guri a wajen mijin su, sai dai ganin shi Ado baya yabawa da abubuwan da ta ke yiwa Innayin ne ya sa ta fara janye jiki har itama daga baya ta koma kamar uwargidan ta Jamilah.
Yanzu kam ma sai sun bushi iska su ke kawo ma ta abinci, ba kamar kullum da rana ba kamar yadda Jamila ke yi da.
Hakan ko kaɗan bai dami Innayi ko Raudha ba, dama ita Raudha tun da ta ga take-taken Aishan ma irin na Jamilah ne ta haɗasu duka ta watsar, iya kacin su gaisuwa. Su na tare gida ɗaya amma Raudha sai ta yi wata biyu uku ba ta shiga ɓangaren su ba, idan ma ta shiga to abu ne ya kaita ba wai ta je dan karan kanta ba ne. Duk yadda ta ke da maitar kallo haka ta ke haƙura ta zauna su yi hira da Innayi ko ta ɗau littafin soyayya na Hausa ta yi ta karantawa, hakan ya fi mata akan ta ce za ta shiga gidan Ado yin kallo...




Idris na gama bautar ƙasa ya samu aiki a AfriBank da ke Misau. Yadda Baffah ya sha buri a albashinsa na watannin farko lokacin yana raye, shi Idris ba wanda ya gane ma sa. Albashinsa na farko ɗakin su na zaure da ya ke kwana ya gyara aka saka sabbin labulaye aka sake floor ɗin ƙasan ɗakin sannan ya zuba kayan kallo a ciki. Da ƙyar ya iya bawa Innayi ɗari biyar ranan da Innayi ta yi ma sa maganar batun Jamb ɗin da Raudha ke son cikawa. Innayi ta amshi kuɗin ta ma sa addu'a.
Dama tun jimawa baya cin abincin gidan shiyasa bai damu da su na da cefane ko basu da cefane ba. Tunda yanzu yana samun kuɗi zai ci mai kyau ya sha mai kyau a duk lokacin da ya ke so.
Ko dan Innayin ba ta tambayar su kuɗi ne ya sa su ke kasa bata kuɗi a lokacin da su ke da shi.
To wai shin sai mahaifiyar ka ta tambayeka kuɗi kafin ka bata? Wai shin sai ta nuna tana cikin matsala kafin ka yi yunƙurin yi ma ta Alkhairi?




***




Dawowar Raudha daga cafe ta zauna a tsakar ɗaki tana kuka a haka Innayi ta shigo ta sameta.
Cike da tsoro ta fara tambayarta abinda ya faru.


Raudha ta ce ai Jamb ɗinta bai yi kyau ba, ba za ta samu zuwa jami'a ba balle har ta karanci ɓangaren likitanci.


"Inba ke ba Auta shine ki ke kuka haka kamar wanda aka yi mutuwa. Ai wata shekaran sai ki zana wani jarrabawan"


"Innayi karatun likitanci fa yawa gareshi. Shekaru bakwai za ka yi kafin a kiraka likita, sai na tsofe a gida kenan kafin na yi karatun" ta faɗa tana sake wani sabon kukan wanda ya fi kama da na sakalci.


Innayi ta fara rarrashinta wanda da ƙyar ta haƙura ta yi shiru...


Ko da ta gayawa Ado cewa yai ta nemi school of nursing ita kuma ta ce ba ta so. Bayan kwana biyu ne Addarta Sa'a ta kawo mu su ziyara inda ta tarar da abinda ke faruwa. Itama shawaran Adon ta bata amma Raudha ta ce ba ta son nursing daga baya kuma Sa'a ta ce mi zai hana ta chanja wani course ɗin wanda ke layin likitancin idan ya so idan ta gama sai ta sake applying DE MBBS. Shima dai shawaran ba ta amince da shi ba har sai da Sa'a ta haɗata da mijinta a waya wanda ya bata labarin wani abokinsa da ya fara karanta Microbiology kafin daga baya ya koma MBBS ganin dai shawaran daga bakin Likita ne ya sa ta amince tunda dai points ɗin na ta ya kai ta samu wani course ɗin.


Sa'a ce ta bata kuɗi ta je ta sayi green card ta chanja course daga MBBS zuwa Biochemistry, ta xaɓi Biochemistry ɗin ne saboda gwanancewa da ta yi a chemistry duk dan saboda addu'ar Innayi, wanda har yau duk sallah ba ta fasa addu'ar Allah ya sa Raudha ta fahimci dukkan darussan ta musamman darasin Kamisiri.






*RIBAR UWA*




*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*






Chapter 08
(Free book ne)


*A mother to successful children*






ABU Zaria Raudha ta cika kuma tun day one da ta sanar da Innayi cewa ga makarantar da ta cika a ranan Innayi ta duƙufa da yiwa Raudha addu'a akan Allah ya sa ta samu.
A ka sake first batch babu sunan Raudha hakan ya sa gwiwar Raudha yai sanyi amma ko kaɗan Innayi ba ta gaza ba tunda Raudhan ta ce ma ta sau uku ake sake list ɗin.
Innayi ta cigaba da addu'a ba dare ba rana, a second list da aka sake sai ga sunan Raudha Abubakar Pakkari ba ma Raudhan ba ne ta je ta duba saboda ta karaya. Usman yaron maƙotansu da su ka cika tare ne ya duba ma ta sai gashi ita ta samu shi bai samu ba.
Farin ciki a wajen Innayi da Raudha ba a magana.
Bayan an gama murnan samun admission ne aka shiga lissafin kuɗin da za a kashe a makaranta da abubuwan buƙata idan ta samu hostel. Dama tuntuni Innayi ta fara jefa kuɗi a asusu saboda irin wannan rana. Da su ka fasa asusun su ka irga kuɗin bai kai kuɗin makaranta ba amma ya kusa kaiwa hakan ya sa lokacin da Ado ya shigo washegarin ranan da safe Raudha ta mishi maganar registration.
Da Raudha da Innayi haka su ka buɗe ido da baki su na kallon yadda Ado ke banbami saboda kawai an ma sa maganar kuɗi.


"Ni ma fa makarantar zan koma na yo degree, albashina bai taka kara ya karya ba ga kuɗin makarantar yara ga hidiman gida. Shi Idrissa da bashida kowa ba za ku tuntuɓeshi ba sai ku tuntuɓeni bayan kun san iyalai biyu na ajiye a gida..." haka yai ta kwarwa babu wanda ya tanka ma sa daga ƙarshe da kan sa yai shiru ya ce zai san ya za a yi idan wata ya ƙare.
Bayan ya fita Innayi ta yi murmushi mai ɗaci. Kamar ba yau ne ya zo gabanta kaman zai yi kuka ba saboda ya samu admission Buba ya ce ba shi da kuɗi. Yadda ta shiga ta fita a kan sa haka za ta yi komai saboda karatun Auta.


"Innayi ba za ki ma sa magana ba? ya san da zai ƙaro karatun ya ke auran Mata biyu har zai nuna mana shi mai iyalai ne"


Innayi ta ce "Auta mi zan ce? Gaskiya ya faɗa ai. Yana da iyali dole mu yi ma sa uzuri, ki tambayi yayanki Idi mu ji mi zai ce"


Raudha ta tafa hannu ta ce " Allah ya sawwaƙa. Nan nan zan je zana jarrabawar post UTME na ce ya bani kuɗin mota ya ce wai bai da kuɗi ya bani naira ɗari biyu. Wallahi ko zan mutu ba zan tambayeshi kuɗi ba"


Innayi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah shi kyauta"...


Lokacin tafiyar Raudha na matsowa Innayi ta saida kajin gida da ta ke kiwo ta haɗa da kuɗin da ke ƙasa. Aka ci sa'a da Iro ya zo gidan ya tarar da zancen tafiyar sai ya ba da wani abu. A haka dai aka haɗa komai Raudha ta je ta yi registration ta dawo.
A komawar ta na gaba ɗaya ne Sa'a ta ba ta dubu biyu ta kuma yi ma ta shopping na kayan abinci, yayinda Halimah ta aiko ma ta da dakekken yaji cikin ƙaramin roban custard da naira ɗari biyu. Shi kuma Ado ana gobe za ta wuce ya kawowa Innayi dubu ɗaya wai a ba ta. Bai damu da sanin ya aka yi aka haɗa kuɗin makaranta ba shi dai ya dai ji ana maganar za ta tafin ne wanda he assumes ta riga ta yi registration kenan.


Duk yadda Innayi ta yi akan Raudha ta ƙarɓi kuɗin da Ado ya bayar ƙi ta yi, ƙarshe da Innayi ta takura ta ce ta riƙe kawai ta yi amfani da shi dan ko ta karɓa ma sai dai ta yi sadaka da shi. Ya je ya riƙe iyalen sa tunda shi ya fi kowa iyali a duniya.
Ta riga ta san halin 'yartata shiyasa ta haƙura ta ajiye kuɗin...


Safiyar ranan da za ta tafi ansha kuka kam dan wannan ne karo na farko da Raudha da Innayi za su rabu har na tsawon watanni. Bayan tafiyar Raudha Innayi ta shiga kaɗaici. Ita ɗaya a sashen na ta wanda ya sa ta ƙara ganin faɗin gidan. Ba kasafai jikokin ta ke shigowa ba saboda kallon talabijin da ke ɗauke mu su hankali a duk lokacin da su ke gida, matan 'ya'yanta kuwa sai sun bushi iska su ke shigo ma ta.




Da sanyin safiya ta fara aikin wake wanda yanzu sana'ar ƙosai kawai ta ke yi ta dena daddawa ta dena Koko. Rabon da ta wanke wake ta manta saboda Raudha ke wankewa ta yi komai iya kacinta tuyawa wani lokaci idan ba makaranta kuwa Raudhan ta tuya.
Da ta gama komai ta saka hijabi ta fita dan ta kai markaɗe daɗin abin ma gidan da ake markaɗen ba nisa da su. Tana wuce zaure kiɗa na tashi a zauren alamun Idris na ciki kenan ta yi ma sa addu'an shiriya dan shikan ba dare ba rana indai a wajen kiɗa ne. Yana gidan amma sai ya ga dama ya ke leƙo ta. Ba ta sanin shigan sa ko fitan sa.


Da ta karɓo markaɗe ta shiga fara shirin suya dan har yau a gida ta ke abunta, kuma duk da akwai ma su yi a waje dayawa hakan bai hanata ciniki ba. Musamman saboda kasancewa da wurwuri ta ke farawa kuma ƙosanta akwai daɗi. 'Yan makaranta da masu fita office da sassafe su su ke zuwa su siye, dan kafin bakwai da rabi ya ƙare, randa kasuwa ya ja baya ne za ka ga har ta kai takwas ɗin bai ƙare ba...




Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi, ba abinda ke damun Innayi face kewar 'yar autar ta. Wata ɗaya amma gani ta ke kamar shekara. Har lokacin kuwa ba ta bar sana'arta ba dan ba ta so a samu matsala a karatun Auta, yadda ta tallafawa Ado, Sa'a, Baffah da Idris haka za ta yi komai saboda Auta.
Da farko ta hango sauƙi a karatun Auta saboda yadda ta ga yayunta su na da rufin asiri za su taimaka amma yadda lamarin ya juye ya sa ta duƙufa da neman kuɗi.


Ɗan kwana biyu da ta samu riba ta sayi Akuya ta ɗaure, dama ta kwana biyu ba ta yi kiwon ba. Na baya da ta siyar duk saboda kuɗin makarantar Idris ne.


Ranan tana wanki Ado ya shigo yana ƙwala kiran ta.


Ta tsame hannu a ruwa ta fara goge hannun a jikin zaninta.


"Gashi Raudha ke son magana da ke" ya faɗa yana miƙa ma ta wayar. Jiki na rawa ta amshi wayar ta ƙara a kunne tana murmushi, tana jin muryar Raudha ta fashe da dariya wanda sai da haƙoranta da su ka ɓace da cin goro su ka bayyana.


Wayar ƙawarta ta amsa ta kira wayar Ado da shi dan a lokacin ba ta da waya.
Da ƙarfi Innayi ke magana dan ita a tunaninta hakan zai sa Raudhan ta ji maganarta sosai.
Sun jima su na magana kafin Raudha ta ce Innayi kuɗin zai ƙare sai anjima,
Innayi ta ce Allah ya miki albarka.


Ta miƙawa Ado waya tana murmushi irin murmushin da rabon da ta yi tun kafin rasuwan Baffah.


A wasa Ado ya ce " to Innayi tunda kina son waya da Autar ta ki ki siya ma ta waya mana" ya ƙarisa maganar yana ƙaramar dariya.


Innayi ta kalleshi ta ce "Allah ya kawo buɗi"


Tunda ta ji muryar Raudha ta ji wani ƙarfi ya shigeta, ƙarfin ta cigaba da fafatawa har Allah ya sa Raudha ta gama karatu lafiya.


Sana'ar Daddawa da ta ajiye kusan shekaru huɗu da su ka wuce ta dawo da shi, haka nan ta saro Kuka da Lalle da Borkono tana saidawa. Burinta yanzu shine ta siyawa Raudha waya saboda ta dinga sawa Ado ya kirata duk lokacin da ta yi kewarta...


A hankali wata huɗu su ka cika Raudha ta yi exams ɗin ta na farko ta dawo gida.
Innayi na bawa raguna abinci ta jiyo sallamar Raudha da ƙarfi daga zaure.
Tana juyowa taga Raudha ta saki jaka ta nufota, tana zuwa ta rungumeta tana dariya. A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login